Hakikanin Jayayya Tsakanin Madakhila Da 'Yan Sururiyya

    Wato duk hayaniyar nan da ake yi a kan mas'alar "Inkari wa shugabanni" ba fa masa'il din ne asalin matsalar ba, kawai fada ne tsakanin bangarori biyu, wadanda kowane daya daga cikinsu yake kan Manhaji karkatacce. Wato Manhajin Ikhwan/Sururiyya, da kuma Manhajin masu Guluwwi a Jarhi/Kungiyar Salafiyyun/Madakhila.

    In ba haka ba, mas'alar inkarin nan a fili take. Akwai inkari na Khawarijawa, wadanda da ma su ba su yarda da shugabannin ba. Kullum burinsu su samu laifukan shugabannin su yada don su tunzura talakawa, su fito su yi bore wa shugabannin don a kifar da Gomnatin.

    A nan Facebook muka ga wani ya ambaci wasu kasashen Larabawa, har da Saudiyya a cikinsu, ya ce shugabanninsu duka Dagutai ne. Ma'ana; har Saudiyya shi bai yarda ana Shari'ar Muslunci ba, don haka shugabannin Dagutai ne, shugabannin kafirci, wadanda ya halasta a yi musu bore da tawaye.

    Akwai kuma inkarin da bai ginu a kan haka ba, inkari ne na neman a gyara kurakurai, tare da ganin halascin Gomnatin da shar'ancinta, da kuma haramci yi wa shugabannin tawaye da bore.

    Misali a kan haka: Idan Dr. Salman Auda ya fito ya yi inkari wa Gomnatin Saudiyya a fili, babu abin da za a fahimta face nau'i na farko, saboda sanin Manhajinsa, da kuma yunkurin da suka yi na haifar da zanga-zanga a kasar.

    Amma idan Shaikh Abdulmuhsin Abbad ya yi inkari a fili, to a nau'i na biyu za a dauke shi, saboda sanin cewa Manhajinsa ba na kira ga tawaye wa Gomnati ba ne.

    To amma su wadannan bangarori biyu sun ki yarda da tafsili, don tafsilin ya kunshi rushe wa kowane bangare barnarsa.

    Su Madakhila ba za su yarda da wannan tafsili ba, don ba za su samu daman bidi'antar da Malaman Sunna a Nigeria ba, wadanda suke jifa da Sururiyyanci.

    Su kuma 'Yan Sururiyyar ba za su yarda da tafsilin ba don an rabe tsakanin karya da gaskiya, ba za su samu gaskiyar da za su boye karyarsu a bayanta ba, wajen yada mummunan Manhajinsu na "thaura" wanda suka dauko daga Sayyid Qutub.

    Wannan ya sa hatta Hadisai da "Aathar" da suke labewa a bayansu ba suna magana ne a kan inkarin Khawarijawa ba, a'a, misalai ne na inkarin wadanda suke ganin shugabancin shugaban halastacce ne. Ka koma "جامع العلوم والحكم" ka ga sharhin Hadisin Abu Sa'eed (ra), don ka fahimci Hadisin ba ya ba da kariya wa Manhajin masu khuruji da tawaye wa shugabanni.

    Don haka wajibi ne a cigaba da fayyace karya da gaskiya, kuma dole a yaki wadannan Manhajoji guda biyu, da hujja da ilimi da adalci, har mutane su fahimci Salafiyya tsabtatacciya, ta su Ibnu Baaz, Albaniy da Ibnu Uthaimeen.

    Allah ya shiryar da mu gaba daya.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.