Hanyoyin Rage Saurin Fushi

    Hanyoyin Rage Saurin Fushi

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu. Malam Hamisu Allah Ubangiji ya saka maka da alkhairi da gudunmawarka a wannan group Amin. Tambaya ta a nan shine Ni na kasance mai saurin fushi idan akayi min ba daidai ba, wacce addu’a zanyi ko wacce hanya zan bi don rage yawan fushi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa’alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu:

    Fushi fisga ne daga fisgar shaiɗan, sanadiyar fushi mutum yana faɗawa cikin munanan abubuwa, da masifu wanda ba wanda ya san iyakarsu sai Allah, saboda haka shari’a ta zo da bayani yalwatacce wajan ambaton wanan dabi’a abar zargi, an ruwaito a cikin Sunnar Manzon Allah sallallahu Alaihi wasallam magani na wannan cuta da kuma hanyoyin kubuta daka tasirantuwa da ita, daka ciki:

    1. Neman tsarin Allah daga shaiɗan, ( A UZU BILLAHI MINASH SHAIDAN).

    Hadisi ya inganta wanda bukhari da muslim suka ruwaito, wasu mutane suna jayayyah a wajan Annabi sallallahu Alaihi wasallam, ɗaya daka cikinsu fuskarsa tayi murtik tayi jah saboda fushi jijiyoyin wuyansa sun tattaso, sai Annabi sallallahu Alai wasallam Yace: ( Nasan kalmar da inya faɗeta abunda yake ji na fushin zai tafi daga gare shi, da zai ce " A UZU BILLAHI MINASH SHAIƊAN", da fushin ya tafi daga gare shi. Manzon Allah sallallahu Alaihi wasallam Yace: Idan dayan ku yayi fushi yace: ( Ina neman tsarin Allah daga shaiɗan ) fushin sa zai kwanta. sahihul jami’ul sageer ( 695).

    2. Yin shiru yayin da kai fushi, Manzon Allah sallallahu Alaihi wasallam Yace: ( Idan ɗayanku yayi fushi yayi shiru) Imamu Ahmad yaruwaici wannan hadisin acikin musnad nasa ( 1/ 329) da sahihul jami’i ( 693, 4027.

    Sabida galibi mai fushi ya kan fita daga hayyacinsa yayi furuci da kalmomin dawani lokacin ma kafirci ne, ko tsinuwa, koya furta kalmar saki wanda zai ruguza gidansa, ko zagi da cin mutunci, wanda zai janyo masa kiyayyar wasu mutane, a dunkule yin shiru shine maganin faɗawa cikin Waɗannan a babe.

    3. Zama, Manzon Allah sallallahu Alaihi wasallam Yace: idan ɗayanku yayi fushi yana tsaye to ya zauna, idan fushin ya tafi shikenan in bai tafi ba, toh mutum ya kwanta.

    Fai’dar wannan umarni na Annabi Sallallahu alaihi Wasallam shine lokacin da kake tsaye kana da cikakkiyar damar da zaka iya yiwa wani illah ko mugun aiki, idan ka zauna kuma wannan damar ba ka da ita sosai, yayin da ka kwanta damar ta kubce maka gaba ɗaya. yanda ba zaka aikata abunda za kai nadamarsa ba.

    4. Kiyaye wasiyyar Manzon Allah sallallahu Alaihi wasallam, daga Abu huraira Yardar Allah ta kara tabbata a gare shi Yace: wani yazo wajan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace: Ya Manzon Allah kaimun wasiyyah sai Yace: kada kai fushi har sau uku yana mai-maita masa, bukhari fat hul baari ( 10/456).

    A wata ruyawar sai mutumin yayi tunani lokacin da Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yafadi Abunda yafada, sai naga fushi ya tattare sharri baki ɗayansa, Musnadu Imamu Ahmad ( 5/ 373).

    5. Karkayi fushi sakamakonka Aljannah, hadisi ne ingantacce sahihul jami’i ( 7374).

    Tuno abunda Allah ya tanadarwa masu hakuri na ni’imoni da girman matsayi zai taimaka wajan nisantar abubuwan da suke kawo fushi ɗin da kuma danne zuciya yayin da ya zo.

    WALLAHU A’LAMU.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.