Hin Ko Dawowar Maniyyi Daga Farjin Mace Bayan Saduwa Na Hana Haihuwa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Barka dai Dr. inna yaba maka da amsar tambayayoyinmu, matsala shekara biyar da aure ban samu ciki ba Kuma kowane lokaci bayan Na sadu da mijina maniyyin mijina sai ya yadinga dawowa  yana malala daga gabana tsawon awa ɗaya ko biyu bayan gama saduwa - ban tsammanin wannan ko wacce mace tanayi. Shin maniyyin nasa Yana kaiwa ga kwan mahaifata  ko kuwa duka ficewa yakeyi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    To Fitar maniyyi daga cikin farji abu ne na al’ada ba matsala bane, ga ko wacce mace indai mijinta yana da ruwan maniyiii wadatacce mai yawa Zata dinga ganin ruwa na dawo mata bayan saduwa wata ma zakiga wuni guda zatayi ruwan na bin jikinta.

    Yawancin mata suna gani cewa fitar maniyyin Kai tsaye daga gama saduwa Wai yana hana samun ciki ko dalilin hana haihuwa  sam ko ɗaya ba haka bane.

    Ruwan da yake fitowa daga farji bayan inzalin shi wani yanki ne na fitar maniyyi, Amma kasa da kashi 5% na ruwan da ke dawowa a zahiri maniyyi ne - sama da kashi 95% sun haɗu da wasu ruwaye ne, kamar ruwan farjin mace, maniyyin ita kanta mace ga kuma maziyyi da ni’imarta duk sun haɗe.

    Amma Fitar  maniyyi gaba ɗaya daga farji abu ne mai matukar wuya ya hana samun ciki  A zahiri ba matsala bane kwata-kwata dan  maniyyin Yana fita daga farjinku bayan saduwa.

    Idan  Lokacin da namiji ya tsatta Maniyyi cikin farji ya ratsa sosai cikin farji, to ku tabbata cewa komai yawan fitar maniyyin daga baya, To dole  wani maniyyi zai isa ga jijiyar mahaifa. Amma a  shawara ga mace ta iya tsayawa a Kwance bayan saduwa na tsawon mintuna 15 ko 20 , amma zuban maniyyi bayan saduwa ba shine dalilin rashin haihuwa ba.

    Allah ta’ala yasa mudace.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.