𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Dafatan kana lafia. Malam matana ta kasance tana bleeding Amma bleeding ɗin Bana period bane. Baya karni normal flow yakeyi. Zata ajiye sallah ne ko zatayi?. Nagode.
HUKUNCIN JININ ISTIHADHA:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Rashin yin Ƙarninsa kaɗai bazai zama dalili ko
hujjar da zata tabbatar da cewa ba jinin haila bane.
Ana hukunta jini amatsayin jinin Istihadha ne idan
ya kasance yana zuwa ma mace tun daga lokacin hailarta har ya wuce kwanaki sha
biyar bai tsaya ba, daga nan sai ta daukeshi amatsayin jinin jinya ne, bazai
hanata yin sallah ko azumi ba, kuma zata iya zuwa shimfidar mijinta.
Amma idan ya zamanto jinin yazo ne alokacin da
take tsammanin zuwan jininta na haila, koda yazo da bambancin kala ko wari,
zatayi masa hukunci ne amatsayin haila. Zata ajiye sallah da azumi har sai
bayan daukewarsa.
Daga cikin rangwamen da addininmu ya yiwa matar
dake fama da jinin Istihadha, an halasta mata zata iya haɗe sallolin azahar da la’asar, hakanan magriba da isha’i.
Kuma ko yaushe kafin tayi alwala sai tayi tsarki ta wanke jikinta musamman
wuraren da jinin ke iya taɓawa, sannan ta
chanza kunzugunta tayi alwala tayi sallah.
WALLAHU A’ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.