Hukuncin Wanda Ya Kashe Kansa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mene ne hukuncin wanda ya kashe kansa da kansa, ko ya halatta a yi wa wanda ya kashe kansa sallah?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    Kisan kai dai babban hatsari ne, kuma zunubin aikata shi ba ƙarami ba ne. Allaah Taaala ya yi gargaɗi ga Bani-Isra’ila a farko, sannan kuma a gare mu cewa:

    أَنَّهُ مَنْ قَتَلَ نَفْسًا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي الْأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَمِيعًا

    Lallai duk wanda ya kashe wani rai guda ɗaya ba domin wani rai da shi ya kashe ba, ko domin wata ɓarna a doron ƙasa ba, to shi kawai kamar ya kashe dukkan mutane ne! (Surah Al-Maaidah: 32).

    Sannan kuma sakamakon mai kashe musulmi ma babban bala’i ne. Allaah ya ce:

    وَمَنْ يَقْتُلْ مُؤْمِنًا مُتَعَمِّدًا فَجَزَاؤُهُ جَهَنَّمُ خَالِدًا فِيهَا وَغَضِبَ اللَّهُ عَلَيْهِ وَلَعَنَهُ وَأَعَدَّ لَهُ عَذَابًا عَظِيمًا

    Kuma wanda ya kashe mumini da gangar, to sakamakonsa Wutar Jahannama ce, yana mai dawwama a cikinta, kuma Allaah ya yi fushi da shi, kuma ya la’ance shi, kuma ya yi masa tattalin azaba mai girma. (Surah An-Nisaa’: 93).

    Kisan kai yana daga cikin manyan kaba’irai masu hallakar da ɗan’adam. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    Ku nisanci abubuwa bakwai masu hallakarwa. Suka ce: Manzon Allaah, waɗanne ne su? Ya ce:

    «الشِّرْكُ بِاللَّهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ النَّفْسِ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالحَقِّ، وَأَكْلُ الرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ اليَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ الزَّحْفِ، وَقَذْفُ المُحْصَنَاتِ المُؤْمِنَاتِ الغَافِلاَتِ»

    Tarayya da Allaah; Sihiri; Kashe ran da Allaah ya harammata sai da haƙƙi; cin riba; cin dukiyar maraya; juyawa a ranar karo da maƙiya; da yin ƙazafi wa mata muminai tsarkaka kuma tsararru daga laifin zina. (Sahih Al-Bukhaariy: 2766; Sahih Muslim: 89).

    Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    «لَنْ يَزَالَ المُؤْمِنُ فِي فُسْحَةٍ مِنْ دِينِهِ، مَا لَمْ يُصِبْ دَمًا حَرَامًا»

    Mumini ba ya gushewa a cikin yalwar samun gafara a cikin addininsa matuƙar bai zubar da jini na haram ba. (Sahih Al-Bukhaariy: 6862).

    Mutum ya kashe kansa shi da kansa ma laifi ne mai girma a cikin musulunci. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    « مَنْ تَرَدَّى مِنْ جَبَلٍ فَقَتَلَ نَفْسَهُ، فَهُوَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ يَتَرَدَّى فِيهِ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا، وَمَنْ تَحَسَّى سُمًّا فَقَتَلَ نَفْسَهُ، فَسُمُّهُ فِي يَدِهِ يَتَحَسَّاهُ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا، وَمَنْ قَتَلَ نَفْسَهُ بِحَدِيدَةٍ، فَحَدِيدَتُهُ فِي يَدِهِ يَجَأُ بِهَا فِي بَطْنِهِ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدًا مُخَلَّدًا فِيهَا أَبَدًا »

    Wanda ya gangaro daga kan dutse ya kashe kansa, to yana nan madawwami a cikin Wutar Jahannama yana ta gangarawa har abada. Wanda kuma ya sha guba ya kashe kansa, to gubarsa tana nan a hannunsa yana ta kwankwaɗar ta a cikin Wutar Jahannama, yana madawwami a cikinta har abada. Haka wanda ya kashe kansa da wani ƙarfe, to ƙarfensa na nan a hannunsa yana ta soka wa cikinsa a cikin Wutar Jahannama, yana madawwami a cikin ta hakan har abada. (Sahih Al-Bukhaariy: 5778; Sahih Muslim: 109).

    Wannan ya nuna: Duk wanda ya kashe kansa da wani abu, to da wannan abin za a yi masa azaba a cikin Wutar Jahannama.

    Malamai sun ce: ‘Har abada’ yana nufin ga wanda ya halatta kisan kenan. Idan kuma bai halatta ba, sai ya zama zai zauna ne zama mai tsawo wanda ba wanda ya san iya tsawonsa sai Allaah shi kaɗai kawai. Allaah ya tsare mu.

    Dalilan da ke sa wani mutum ya kashe kansa a galibi su ne:

    Aikata wani abin kunya wanda yake ganin zai iya janyo masa ko danginsa zuban mutunci ko gori ko abin faɗa a cikin mutanensa da zuriyarsa, kamar sata ko zina da sauransu.

    Matsatsi ko tsanani ko ƙuncin rayuwa, kamar wanda ya kasa biyan wani bashi da ke a kansa, ko ya kasa ciyar da iyalinsa da ɗaukar nauyinsu da makamantan hakan.

    Duk waɗannan ba dalilai ba ne da za su halatta wa mutum aikata wancan mummunan ta’addancin. Domin wannan ba zai hana cigaba da gori da sukar da ya guda ba a mas’ala ta farko. Sannan kuma, a matsala ta-biyu: Rashi ba ya taɓa zama dalilin wannan ɓarnar da taaddancin. Domin a duk wani halin tsanani da wahala da mutum yake ciki, akwai wanda ya fi shi tsananin wahala. Sai dai in bai yi nazari ya duba da kyau ba. Don haka kashe kansa ba zai taɓa zama hanyar warware irin waɗannan matsalolin ba.

    Maganin wahalhalu da sauran matsalolin duniya tun tuni, kuma har zuwa yau kawai shi ne:

    Duk mu koma ga Allaah. Mu fahimci dokokinsa. Mu yi aiki da umurnisa, kuma mu nisanci haninsa gwargwadon iko da iyawarmu, tare da ƙanƙan da kai da neman kusanci gare shi.

    Duk mu san cewa: Rai ajiya ne ga kowannenmu, ba mallakakken abu ne a gare mu ba. Don haka ba mu da ikon yin yadda muka ga dama da shi, ba tare da izinin Allaah wanda ya ajiye shi a cikin jikkunanmu ba.

    Shiyasa Allaah Ta’aala zai yi tambaya ga kowannenmu a kansa gobe Ƙiyama. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    «لَا تَزُولُ قَدَمُ ابْنِ آدَمَ يَوْمَ القِيَامَةِ مِنْ عِنْدِ رَبِّهِ حَتَّى يُسْأَلَ عَنْ خَمْسٍ، عَنْ عُمُرِهِ فِيمَ أَفْنَاهُ، وَعَنْ شَبَابِهِ فِيمَ أَبْلَاهُ، وَمَالِهِ مِنْ أَيْنَ اكْتَسَبَهُ وَفِيمَ أَنْفَقَهُ، وَمَاذَا عَمِلَ فِيمَا عَلِمَ»

    Ƙafafun ɗan’adam ba su motsawa a ranar Ƙiyama a wurin Ubangijinsa har sai an tambaye shi a kan abubuwa guda biyar: A kan tsawon rayuwarsa: Ta yaya ya ƙarar da shi? A kan samartakarsa: Ta yaya ya tsofar da shi? A kan dukiyarsa: Ta yaya ya tara ta? Kuma a kan me ya kashe ta? Kuma me ya aikata da ilimin da ya sani? (Sunan At-Tirmiziy: 2416, kuma Al-Albaaniy ya hassana shi).

    Amma a kan sallar gawan musulmi mai zunubi ko saɓo akwai hadisai sahihai da suka zo a kan hakan, kamar riwayar Salamatu Bn Al-Ak-wa’i (Radiyal Laahu Anhu), cewa:

    Watarana suna zaune tare da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam): Sai aka zo da wata gawa. Suka ce: Manzon Allaah! Ka yi mata sallah. Sai ya ce: Ko ya bar wani abu? Suka ce: A’a. Ya ce: To ko ana bin shi bashi? Suka ce: E, dinare uku. Sai ya ce:

    «صَلُّوا عَلَى صَاحِبِكُمْ»

    Ku yi wa mutuminku sallah! (Sahih Al-Bukhaariy: 2289).

    Daga irin waɗannan hadisan ne malamai suka gano karhancin cewa: Manyan mutane masu daraja su halarci sallar gawan wanda ya mutu a halin yana aikata wani mummunan aiki, kamar sata ko fashi ko zina ko luwaɗi da makamantansu.

    Amma waɗansu malaman sun ƙara bayanin cewa, wannan karhancin yana nan ne idan hakan zai tsoratar da alumma, ya hana su aikata irin hakan. Amma a lokacin da galibin mutane ba su damu da waye zai tsaya a kan gawarsu ba, ko kuma ma ba su damu da ko a yi musu sallah ko kar a yi musu a bayan mutuwarsu ba, sai malaman suke ganin: Bai kamata musulmi su bar abin da Sunnah ta tabbatar na haƙƙoƙin musulmi marigayi a kansu saboda hakan ba. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    « حَقُّ المُسْلِمِ عَلَى المُسْلِمِ خَمْسٌ: رَدُّ السَّلاَمِ، وَعِيَادَةُ المَرِيضِ، وَاتِّبَاعُ الجَنَائِزِ، وَإِجَابَةُ الدَّعْوَةِ، وَتَشْمِيتُ العَاطِسِ»

    Haƙƙin musulmi a kan musulmi guda biyar ne: Mayar da sallama; da dubo mara lafiya; da raka gawa; da amsa gayyata; da gai da mai atishawa. (Sahih Al-Bukhaariy: 1240; Sahih Muslim: 2162).

    Raka gawa kuwa - kamar yadda aka sani - yana da matakai ne guda biyu, kamar yadda hadisai sahihai suka nuna:

    «مَنِ اتَّبَعَ جَنَازَةَ مُسْلِمٍ، إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا، وَكَانَ مَعَهُ حَتَّى يُصَلَّى عَلَيْهَا وَيَفْرُغَ مِنْ دَفْنِهَا، فَإِنَّهُ يَرْجِعُ مِنَ الأَجْرِ بِقِيرَاطَيْنِ، كُلُّ قِيرَاطٍ مِثْلُ أُحُدٍ، وَمَنْ صَلَّى عَلَيْهَا ثُمَّ رَجَعَ قَبْلَ أَنْ تُدْفَنَ، فَإِنَّهُ يَرْجِعُ بِقِيرَاطٍ»

    Wanda ya raka gawar musulmi yana mai imani da neman ladan Allaah, kuma ya zama tare da ita har aka yi mata sallah kuma aka gama rufe ta, to lallai zai dawo da qiraat biyu na lada, kowane qiraat ɗaya kamar dutsen Uhud. Amma wanda ya yi mata sallah sannan ya komo kafin a rufe ta, to shi kuma zai komo da qiraat guda. (Sahih Al-Bukhaariy: 47).

    A ƙarshe: A riƙa bincike. Ba duk wanda aka gan shi a rataye ko a sarƙafe ne yake kasance wa shi ya kashe kansa da kansa ba. Sarƙafe kai baƙuwar hanyar kashe kai ce a cikin alummarmu, domin galibi daga fina-finan turawa aka koyo su. Kamar haka, fina-finan suna nuna yadda ake kashe wani amma a nuna kamar shi ya kashe kansa, domin a kawar da hankali mahukunta da masu bincike a kan hakan.

    Abin da nake tunawa kullum a kan irin wannan matsalar, maganar wani inyamuri ne a ofis ɗin mu a shekarun baya, a lokacin da aka gaya masa cewa wani daga cikin tsofaffin ma’aikatan kamfani ya nemi kashe kansa! Ya ce: Ta yaya? Aka ce: An ji shi ne yana kici-kicin sarƙafe kansa a cikin ɗakinsa. Da ya ji haka sai tsohon ya ja dogon tsaki: Mts!! Sannan ya ce: “He never want to die!” Wai, da ma can ba son mutuwar yake yi ba! Aka ce saboda me za ka faɗi haka? Ya ce: ‘A unguwarsu ba a sayar da fiya-fiya maganin ɓera ne?! Ko kuwa babu wutar lantarki ne a ɗakinsa?!!

    Ma’ana dai: Don me mai son kashe kansa da gaske zai tsaya bin doguwar hanya, alhali ga hanya mai sauri kuma sassauƙa?

    A taƙaice dai, dole a yi taka-tsantsan wurin jingina wanda aka gani a rataye ko a sarƙafe cewa, ya kashe kansa! Ko da kuwa an samu rubutacciyar takarda da sa-hannunsa, ko dai wanɗansu shedu a kan hakan. Domin komai na iya faruwa a duniyar yau.

    Allaah ya ƙara tsare mu daga dukkan hanyoyin hallaka.

    Wal Laahu A’lam.

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.