Hukuncin Wanda Ya Yi Niyar Yin Aikin Sabo Ko Zalunci A Garin Makkah Ko Madinah Kuma Bai Aikata Laifin Ba

    TAMBAYA

    Assalamualaikum malam ina wuni da fatan kana cikin ƙoshin lafiya dan Allah Tambaya nake Shin akwai wani aya ko hadisi da yake nuni akan idan ka ayyana wani abu na sharri a cikin Makkah ko madina za a rubuta maka zunubi koda baka aikata ba.

    AMSAH

    Dukkan godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, salatin Allah da amince su ƙara tabbata ga jagoran shiriya annabin mu Muhammad ɗan Abdullah (S.A.W).

    Haka yake akwai aya ta Alƙur’ani da Allah mai rahama yayi nuni akan dukan wanda yayi niyar yin wani sharri ko zunubi acikin aramin Makkah zai samu zunubi mai girma ko muce azaba mai radadi in dai ya mutu bai tuba ba saboda faɗin Allah maɗaukakin sarki acikin Suratul hajji aya ta Ashirin da biyar 25

    إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا وَيَصُدُّونَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ وَالْمَسْجِدِ الْحَرَامِ

    الَّذِي جَعَلْنَاهُ لِلنَّاسِ سَوَاءً الْعَاكِفُ فِيهِ وَالْبَادِ ۚ وَمَنْ يُرِدْ فِيهِ بِإِلْحَادٍ بِظُلْمٍ نُذِقْهُ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ

    (الحجّ 25:22)

    LALLE WAƊANDA SUKA KAFIRTA SUKA KUMA TOSHE HANYAR ALLAH DA KUMA MASALLACIN HARAMI WANDA MUKA SANYA SHI BAI-DAYA GA MUTANE, MUZAUNA CIKIN SA DA KUMA MAI ZUWA {DAGA WAJE}. WANDA KUWA YA NUFE SHI DA WATA FANƊARA {WATO ƁANNA DA AIKATA AIKI NA SAƁO} DA ZALUNCI TO ZA MU ƊANƊANA MASA AZABA MAI RAƊAƊI.

    Sheikh Dr Muhammad Umar Sani Musa rijiyar lemo ya gaya acikin littafin tafsirin sa mai suna audahul bayani lima,ani wa hidaayaatul ƙur,an ƙarƙashin tafsirin wannan Aya, ya ce:-

    ........... Sai kuma Allah mai tsarki da ɗaukaka ya yi kashedi ga duk wani wanda zuciyarsa za ta riya masa yin wani aikin assha a cikinsa (wato garin Makkah)na zalunci ko na saɓon Allah, to lalle Allah zai ɗanɗana masa azaba mai radadi.

    Kuma ya ce daga cikin ayar zamu fahimci abubuwa kamar haka

    A numba ta biyu yace, zamu fahimci girman lamarin (wato girman)Makka; saboda ƙudirin niyyar aikata wani zalunci ko wani sabon Allah a cikin sa kawai ya isa ya jawo wa mutum azabar Allah ko da kuwa bai aikata ba, to ina kuma ga wanda har ya kai ga aikatawa.

    Haka kuma garin Madinah shi ma yana da wannan alfarmar, kamar yanda aka yiwa samaahatush Sheikh Bin Baz (r.m)kusan irin wannan tambaya sai ya fada acikin amsar da ya bayar ya ce: dukkan wanda ya yi niyyar yin saɓon Allah acikin haramin Makkah to ya chanchanci uƙuba, wannan abu ne da ya keɓanci haramin Makkah, domin haƙiƙa Allah ya na gaya acikin littafin sa mai albarka {sai malan ya karanta ayar da muka ambata a baya ta cikin suratul hajji aya ta 25 }ya ce wannan alƙawarin azaba ne mai RAƊAƊI akan wanda yayi himmar yin wani zunubi acikin aramin Makkah ko da bai aikata shi ba, ya chanchanci uƙuba, wajibi ne taka tsantsan ga wanda ya kasance a garin Makkah matuƙar taka tsantsan, hakama acikin garin Madinah wajibi ne ayi taka tsantsan, domin haƙiƙa manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya girmama Madinah ( sai ta zamanto mai alfarma kamar garin Makkah) kamar yanda Annabi Ibrahim (s .a.w) ya girmama Makkah, wajibi ne ayi taka tsantsan wajen aikata zunubi gaba daya, da kuma yin niyyar aikatawa,

    Allah shine mafi sani

    {AMSA WA ABU ABDULLAH}

    *Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.