Kwadago Don Gina Masallaci

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. A ƙauyenmu mun yi tsarin fita yin ƙwadago domin tara kuɗin gina masallaci, da aikin da’awa da sauransu. Kuma mun sanya ƙaidar cewa, duk wanɗanda ba su fita tare da mu ba, to ba za mu je jana’izarsu ko ɗaurin aurensu ko walimansu, da sauran irin hakan ba. Ko a hakan mun saɓa ƙaidar Sharia?

    Ƙwadago Don Gina Masallaci:

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

    [1] Da farko dai Manzon Allaah (Sallal Llahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    «مَنْ بَنَى لِلَّهِ مَسْجِدًا بَنَى اللَّهُ لَهُ مِثْلَهُ فِي الجَنَّةِ».

    Duk wanda ya gina Masallaci domin Allaah, Allaah zai gina masa irinsa a cikin Aljannah. (At-Tirmiziy (318) ya riwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi).

    Haɗin kai a kan aiki don samun kuɗin yin aiki na-gari kamar gina masallaci aikin alheri ne, kuma daidai ne. Ubangiji Ta’aala ya ce:

    {وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَى وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ}

    Kuma ku taimaki junanku a kan alheri da taƙawa, kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ta’addanci. (Surah Al-Maa’idah: 2).

    [2] Jana’iza farilla ce ta Kifayah a wurin malamai, wato ba dole ne sai kowa ya je ba. Zuwa ɗaurin aure shi ma ba dole ba ne, matuƙar dai an samu shedun da ake buƙata a wurin ɗaurawar ko daga bayan ɗaurawar. Amma shi kuma zuwa walimar aure farilla ne ta Ain a kan duk wanda aka gayyace shi. Saboda maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:

    «وَمَنْ لَمْ يُجِبِ الدَّعْوَةَ، فَقَدْ عَصَى اللهَ وَرَسُولَهُ»

    Kuma duk wanda bai amsa gayyatar ba, to lallai ya saɓa wa Allaah da Manzonsa. (Sahih Muslim: 110).

    [3] Cutar da musulmi da baƙanta musu ko ɓata musu rai, domin kawai ba su yi wani abin da ya ke mustahabbi ba, wannan babban kuskure ne. Domin maganar Ubangiji Ta’aala da ya ce:

    {وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ بِغَيْرِ مَا اكْتَسَبُوا فَقَدِ احْتَمَلُوا بُهْتَانًا وَإِثْمًا مُبِينًا}

    Kuma waɗanda suke cutar da muminai maza da mata ba domin wani laifi da suka yi ba, to lallai sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi mabayyani. (Surah Al-Ahzaab: 58).

    [4] Mafita a kan irin wannan in sha’al Laah, ita ce: A janyo hankulansu da hikima da kyakkyawan wa’azi, kamar yadda Ubangiji Ta’aala ya faɗa:

    {ادْعُ إِلَى سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ وَجَادِلْهُمْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ}

    Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da kyakkyawan wa’azi, kuma ka yi jayayya da su da wacce ta ke ita ce mafi kyau. (Surah An-Nahl: 125).

    [5] Don haka, sai ku yi ƙoƙarin kafewa a kan aikin alherin da kuke yi, kuma ku cigaba da janyo hankalin wanda bai gane ba daga cikin mutanenku ta amfani da kalmomin hikima da kyakkawan waazi, kamar ta janyo ayoyin Alƙurani da Sunnah Sahihiya masu nuna fa’idoji da alherin wannan aikin. Sai kuma ku bar ƙofarku a buɗe domin karɓar duk wanda ya so shigowa a kodayaushe, muddin dai kun amince da shi da manufarsa. Domin ba lallai kowa ya gane ko ya yarda da matafiyarku a lokaci guda ba.

    Allaah ya taimake ku, ya ƙara muku ƙarfin gwiwa, kuma ya sanya muku albarka.

    Wal Laahu A’lam.

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    +2348021117734

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.