Kyakkyawar Manufa Ba Ta Gyara Bidi’a Da Mummunan Aiki

    Akwai batattu da yawa masu kyakkyawar manufa, wadanda suka bata a dalilin mummunar fahimta ga Addini da Guluwwi a cikinsa, har suka kauce hanya, suka saba Shari'a, suka afka cikin barna, alhali ba tare da mummunan nufin saba ma Shari'ar ba.

    Khawarijawan farko, sun yi nufin su bi Alkur'ani ne, su yi aiki da Shari'arsa, har suka ce: Dole a kadaita Allah wajen hukunci "Hakimiyya", amma da yake suna da Guluwwi a Addini, da mummunar fahimta game da Addinin sai suka bata, suka saba ma Shari'a, suka dace da wa'eedin da Annabi (saw) ya yi a kansu, duk da cewa: suna zaton Allah suke bi, Addini suke yi, aikin Allah suke yi, gaskiya suke bi, kyakkyawan aiki suke yi. Shi ya sa Sayyidina Aliyu (ra) yake fadi a kansu, da aka tambaye shi kamar haka:

    ((عن أبي الطفيل عامر بن واثلة قال: سمعت عليا رضي الله عنه، قام فقال سلوني قبل أن تفقدوني، ولن تسألوا بعدي مثلي، فقام ابن الكواء فقال: من الذين بدلوا نعمة الله كفرا وأحلوا قومهم دار البوار؟ قال: منافقوا قريش قال: فمن الذين ضل سعيهم في الحياة الدنيا وهم يحسبون أنهم يحسنون صنعا؟ قال: منهم أهل حروراء)).

    المستدرك على الصحيحين للحاكم (2/ 383) جامع البيان ط هجر (15/ 426 - 427)

    ((Abu al-Dufail (ra) ya ce: Na ji Aliyu (ra) ya tashi yana cewa: "Ku tambaye ni kafin ku rasa ni (mutuwa), a bayana ba za ku samu wanda za ku tambaya kamata ba".

    Sai Ibnu Kawwa'u ya tashi ya ce: Su wanene wadanda suka canza ni'imar Allah da kafirci, suka janyo wa mutanensu shiga gidan halaka?

    Sai Aliyu (ra) ya ce: "Munafukan Quraishawa".

    Sai ya ce: Su waye wadanda aikinsu ya bace a rayuwar Duniya, alhali suna zaton suna kyautata aiki ne?

    Sai Aliyu (ra) ya ce: "A cikinsu akwai mutanen Haraura'u (Khawarijawa)")).

    Saboda haka a kullum, a kowane zamani, ana samun irin wadannan mutane, saboda mummunar fahimta ga Addini, da Guluwwi a cikinsa, sai su zo da barna a cikin Addini, su zo da ra'ayoyi da suke kai wa ga kafirta al'ummar Musulmi da zubar da jinanensu, amma duk da haka su suna zaton kyakkyawan aiki suka yi. Ma'ana; ba da mummunar manufa suka yi hakan ba. Wannan shi ne irin abin da al-Maududiy da Sayyid Qutub suka yi a wannan zamani. Kafirta al'umma da suka yi, bisa "Hakimiyya", bisa fassara Addini a ma'ana ta Siyasa, irin yadda Khawarijawan farko suka yi, shi ya shiga tunanin Kungiyoyin Gwagwarmayan zamani, har daga karshe suka zo suna kashe Musulmai, suna barin Kafirai da sunan Jihadi.

    Dr. Muh'd Imarah, yana magana a kan al-Maududiy sai ya ce:

    ((ولقد يدهش كثيرون – من أنصار المودودي وخصومه – إذا علموا أن الرجل قد ذهب إلى أن "تيار الجاهلية الجارف" قد وجد سبيله ثانية إلى النظام الإسلامي منذ عهد الخليفة الراشد عثمان بن عفان! وأن النظام الإسلامي – في الحكم والسلطة – "قد قام على قواعد الجاهلية بدلا من قواعد الإسلام" منذ الانقلاب الأموي على الخلافة الراشدة!...

    قد يدهش الكثيرون لهذا التقييم الذي بلبلت نصوصه جماعات إسلامية معاصرة، وقادت كتّابا إسلاميين إلى الحكم بكفر الأمة وجاهلية المجتمعات الإسلامية منذ قرون وقرون))

    قال في الحاشية: ((سيد قطب: معالم في الطريق (ص: 8، 39، 101، 103، 173) طبعة القاهرة سنة (1980))

    أبو الأعلى المودودي والصحوة الإسلامية (ص: 67)

    ((Hakika mutane da yawa – cikin mabiya Maududiy da abokan husumarsa – idan suka san da cewa; mutumin yana da ra'ayin cewa; "ambaliyar Jahiliyya da ta kwashe al'umma gaba dayanta" ta samo hanyar shigowa cikin al'umma ne a karo na biyu, zuwa ga tsarin Muslunci tun lokacin Khalifa Usman bn Affan (ra). Kuma tsarin Muslunci - a Mulki da shugabanci - "ya tsayu ne a kan ginshikan Jahiliyya a maimakon Ginshikan Muslunci", tun daga lokacin da Banu Umayya suka yi juyin Mulki wa Khalifanci na shiriya…

    Hakika mutane masu yawa za su rude game da wannan hukunci da Maududiy ya yi, wanda maganganunsa suka janyo bala'i da rudani a cikin Kungiyoyin Gwagwarmayan Muslunci na zamani, kuma suka ja marubuta Musulmai zuwa ga yin HUKUNCI DA KAFIRCI GA AL'UMMA, DA HUKUNCI DA JAHILIYYA GA AL'UMOMIN MUSULMAI TUN KARNONIN BAYA CAN)).

    A can kasa (hashiya) sai Dr. Imarah ya ambaci littafin Sayyid Qutub "معالم في الطريق" da shafuka na misalan irin maganganun kafirta al'umma da suke cikin littafin.

    A nan sai ya nuna irin fitinar da Fikirorin Maududiy suka haifar a cikin Kungiyoyin Gwagwarmaya, da kuma yadda suka yi tasiri a kan Marubuta, har ya yi ishara zuwa ga Littafin Sayyid Qutub "معالم في الطريق" (Milestones), a matsayin misali na irin wannan tasiri.

    Abin nufi shi ne irin su Maududiy da Sayyid Qutub, da kyakkyawar manufa, bisa mummunar fahimta suka haifar ma al'umma babban sharri mai girma, suka gadar mata ta'addanci da kashe Musulmai ba bisa hakki ba.

    Kuma a hakan ake samun wadanda suke ruduwa, kyakkyawar manufar wadannan mutane take rufe musu ido, ba sa iya kallon mummunan sharri da suka haifar ma al'ummar Musulmi, don a yi maganin matsalar.

    Saboda haka kyakyawar manufar mutum ba za ta taba gyara wani mummunan aikinsa ba. Ibnu Mas'ud (ra) ya ce:

    «وكم من مريد للخير لن يصيبه»

    سنن الدارمي (1/ 287)

    ((Mutum nawa ne masu nufin alheri amma ba su dace da alherin ba?)).

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.