𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum warahmatullah Malam ina da tambaya Dan Allah macen da tayi zina kwana nawa me ISTIBRA’I ɗin ta?
Macen
Da Ta Yi Zina, Kwana Nawa Me Istibra’i Ɗin Ta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaikumus salam, To ‘yar’uwa Allah ya haramta
zina kuma ya sanyata daga cikin mayan zunubai wadanda şuke jawo narkon azaba.
Idan mazinaciya ta tuba, malamai sun yi saɓani game da iddarta.
1. Akwai waɗanda suka tafi
akan cewa za ta yı jini uku, saboda maniyyin ya shiga mahaifa, don haka ya
wajaba ayı abin da zai tabbatar da kubutarta, kamar yadda wacce aka sadu da ita
da kuskure za ta yi, da kuma wacce aka şaka.
2. Za ta yi jini ɗaya kawai, saboda faɗin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam "Ba’a saduwa da
mai ciki har sai ta haihu, wacce ba ta da ciki kuma sai ta yi haila ɗaya" Kamar yadda Abu-dawud da Ahmad suka rawaito.
Don neman Karin bayani duba Almausu’a Alfikhiyya
Alkuwaitiyya 30/341.
Zance na karshe ya fi inganci, saboda kusancinsa
da saukin sharia, Saboda babban manufar idda ita ce kubutar Mahaifa kuma tana
tabbata da jini ɗaya, sannan
iddar matar aure ta banbanta da ta mazinaciya, saboda iddarta ana tsawaitata ne
don fatan miji zai yı iya yın kome, hakan kuwa babu shi a iddar zina.
Allah shine mafi Sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.