"Malam Bawa Magajin Doka" Inji Dakta Mamman Shata Katsina

    An haifi Malam Abdullahi Attahiru da ake yi wa laƙabi da Malam Bawa a garin Shinkafi, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Mulkin Shinkafi ta Jihar Zamfara a shekarar 1942.

    Ya yi karatun Addinin Musulunci gwargwadon hali, haka zalika ya halarci Makarantar Elimentare ta garin Shinkafi wadda ake kira Magaji Dango a halin yanzu, a cikin shekarun 1950s, daga nan kuma ya shiga aikin Doka.

    An naÉ—asa Magajin Doka na Shinkafi a lokacin mulkin Marigayi Mai girma Dagacin Shinkafi, Alhaji Ibrahimu wanda ya yi mulki tsakanin shekarar 1950 zuwa rasuwarsa a shekarar 1990. Allah ya jaddada masa rahama, amin.

    Malam Bawa Magajin Doka ya shahara sosai a cikin wannan aiki nasa saboda ƙoƙari da ƙwazo da gaskiya da riƙon amanarsa. Mutum ne mai basira da hikimar aiki ainun.

    Bayan an mayar da aikin Doka zuwa aikin ÆŠan Sanda sai aka canza masa aiki ya zuwa hukumar kula da Yan Sanda. Aikin da ya ci gaba da gudanarwa har zuwa lokacin da ya yi ritaya. Ya yi ritaya a daidai lokacin da ya ke aiki a "Yar Marina Police Station" dake cikin Birnin Sakkwato wadda tana cikin muhimman wurare na aikin Yan Sanda dake Sakkwato da kewaye a wancan lokaci.

    Ya amsa kiran Mahaliccinsa, Allah SWT a watan Nuwambar shekarar 2012, a lokacin ya na da shekaru 70 daidai a duniya. Allah ya jiƙan sa da rahama shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.

    Ya bar matan aure, da 'ya'ya guda 8. Maza 2, Mata 6 kuma suna nan raye a wurare daban daban na Nijeriya suna ci gaba da rayuwa. 

    "Malam Bawa Magajin Doka" Inji Dakta Mamman Shata Katsina

    Ibrahim Muhammad ÆŠanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.
    08149388452,
    08027484815.
    birninbagaji4040@gmail.com
    Talata, 10/09/2024.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.