A da Malaman Ahlus Sunna suna samun shahara ne saboda matsawa a kan kira ga Tauhidi da Sunna, da raddi ga masu shirka, masu zuwa kabarburan shehunai suna rokonsu biyan bukata, da raddin bidi’o’i, da sauran almaran Sufaye. Shi ya sa har yau Sufaye suna cike da jin haushin Malam Kabir Gombe, da ire - irensa wadanda suke bin wannan Manhaji, na rashin sassauci wajen inkarin Shirka da Bidi’o’in Sufaye. Kai, haka Malam Ja’afar ma, babban misali.
Abin takaici, a yau Malamai masu dangantuwa ga
Sunna, suna samun shahara ne da wa’azozin mata, da na ma’aurata, a ciki har da
fadin abubuwan da bai dace kamilin mutum yana fada a bainar jama’a ba, idan ba
da bukata ta musamman ba, kuma ba da wargi ba. Wasu kuma sun shahara da yawan
ba da labaru, har ya kai ga ana fara jin labari mai hatsari a bakin Malami mai
wa’azi, alhali idan aka yi bincike labarin bai tabbata ba. Wasu sun zama ‘yan
comedy, masu barkwanci da ba da dariya wa ‘yan mata da samari, a kan kujerar
wakiltar Manzon Allah (saw), suna fadin yasassun maganganu, wasu ma irin na ‘yan
tasha, don birge ‘yan mata da samarin, suna status da clip na bidiyonsu. Wasu
ka ji suna fatawa a kan abubuwan da ba su da ilimi a kansu. Wani lokaci har da
zagi, alhali a Masallaci dakin Allah suke.
Amma asalin Malamai da suke karantarwa, wanda babu
tarkace a cikin karatunsu, sai ka samu gama
-garin mutane ba su cika mai da hankali a kansu
ba, duk da muhimmancin abin da suke karantarwa, na Akida da Ibada da Tarbiyya,
da hanyar gyaran zuciya, don al’umma ta gyaru, har a samu saukin rayuwa da
iznin Allah.
Saboda haka muna kira ga manyan Malamanmu - duk da
cewa muna kyautata zaton suna iya kokarinsu na Nasiha ga irin wadancan Malamai
- su kara kaimi wajen jan hankali gare su, kar su gajiya, da fatan Allah zai sa
su gyara.
Kuma ni ma daga wannan minbari na Facebook, ina
gabatar da Nasiha ga dukkan Malamin da ya san yana bin solo irin wadancan salo
da suka saba salo mai kyau, ya ji tsoron Allah ya gyara. Saboda a zamanin yanzu
al’umma ta fi bukatar gyara Akida da Tarbiyya fiye da sauran babukan Addini,
balle kuma barkwanci da comedy da ba da dariya wa mutane.
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.