Marigayi Alhaji Alu Haidara Ƙaura Namoda

Marigayi Alhaji Alu Haidara Ƙaura Namoda

.. Bakin gidan Alu Haidara, kun ji masu kuɗɗi Ƙaura..

Haka☝️ Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan Anace Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato ya ce a faifansa na Ɗan Dambe Shagon Bakura. 

Wannan shi ne Marigayi Alhaji Alu Haidara Ƙaura Namoda da Makaɗa Ɗan Anace ke nufi.

Asalinsa Bafulatani ne daga jinsin Torankawa. Kakanninsa sun yi Hijira ne daga Sakkwato zuwa Kudu maso yammacin Cibiyar Daular Usmaniya tare da Malam Umaru Nagwamatce ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I /Abubakar Atiku /Mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi, inda suka taimaka masa wajen ƙirƙirar Masarautar Kwantagora a shekarar 1859.

 Fatauci ne ya kawo shi garin Ƙaura Namoda,  ya samu nasibi a cikin lamarin har ya shahara sosai. Attajirin gaske ne da ya yi suna wajen tallafawa al'umma har ma ana faɗin cewa "wutar dafa abinci ba ta mutuwa a gidansa  a kowane lokaci" domin tsayuwarsa akan ciyarwa.

Zuriyarsa ta shahara ainun wajen sha'anin kasuwanci da ilimi na addini da na zamani.

Alh. Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji.

Post a Comment

0 Comments