Na Tuba Daga Zina, Shin Allah Zai Karbi Tubata Kuwa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam Allah yakara basira. Malam na kasance mai saɓon Allah akwanakin baya na biyewa san zuciya da biyan bukatan raina na ringa aikata saɓon Allah wato zina, to malam ayanzu na tuba na daina yi. Shin wadanne addu’o’i ya kamata na ringa yi? Kuma shin Allah zai karbi tubana kuwa? Ngd.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu

    Tunda kin tuba, ki cigaba da istigfari da nadama bisa abinda kika aikata a baya, sannan ki ɗauki niyyar cewa har abada ba zaki sake komawa cikin wannan laifin ba. Kuma ki guje wa duk wani sanadin da zai iya kaiki zuwa ga komawa cikin wannan kuskuren, kamar miyagun Ƙawaye ko mayaudaran samari, ko zuwa wuraren da basu kamata ba. Ki guje wa tunanin batsa, kallon batsa, ko shiga shafukan internet masu nuna tsaraici. Sannan ki guje wa yin chatting da mutanen banza. Idan kikayi haka to tubanki zai fi karfi, zai fi inganci in sha Allahu.

    Allah zai gafarta miki domin tabbas Shi mai gafara ne mai jin Ƙai bayinsa. Kuma gafara da rangwame da jin Ƙai, siffofinsa ne. Allah ya gaya wa Annabinsa (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa:

     ۞ قُلۡ یَـٰعِبَادِیَ ٱلَّذِینَ أَسۡرَفُوا۟ عَلَىٰۤ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُوا۟ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِیعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِیمُ

     "KACE YAKU BAYINA WAƊANDA SUKA AIKATA WA KANSU ƁARNA! KADA KU FIDDA TSAMMANI DAGA (SAMUN) RAHAMAR ALLAH. HAKIKA ALLAH YANA YAFE DUKKAN ZUNUBAI BAKI ƊAYA, SHI SHINE MAI GAFARA MAI JINƘAI". (Surah Az-Zumar: 53)

    Kuma Yace:

    إِلَّا ٱلَّذِینَ تَابُوا۟ مِنۢ بَعۡدِ ذَ ٰلِكَ وَأَصۡلَحُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ

    "SAI DAI WAƊANDA SUKA TUBA BAYAN NAN (WATO BAYAN SUN AIKATA LAIFIN) KUMA SUKA KYAUTATA AIKI, TO HAKIKA ALLAH MAI GAFARA NE MAI JIN ƘAI GARESU". (Surah An-Nuur: 5)

    Ki yawaita ayyukan alkhairi waɗanda zasu goge miki wancan laifukan na baya. Allah Yace "HAKIKA KYAWAWA (WATO AYYUKAN LADA) SUNA TAFIYAR DA MUNANA".

    Manzon Allah (sallal Lahu ‘alaihi wa aalihi wa sallam) Yace "Hakika Allah yana shimfida rahamarsa da daddare domin karɓar tuban waɗanda suka aikata zunubbai da rana. Kuma yana shimfida rahamarsa da rana domin waɗanda suka aikata zunubai cikin dare su tuba. (Bazai gushe yana yin haka ba) har zuwa sanda rana zata ɓullo daga mafadarta".

    Al Imamun Nawawiy (rahimahul Lahu) acikin shahararren littafinsa mai suna RIYADHUS SALIHEEN MIN KALAMI SAYYIDIL MURSALEEN (Sallallahu alaihi Wasallam} afarkon babin tuba, yayi wata magana inda yake cewa: "Malamai sun ce tuba wajibi ce daga dukkan zunubai. Idan laifin ya kasance tsakanin bawa ne da Allah Ta’ala babu hakkin wani Ɗan Adam aciki, to tana da sharuɗa guda uku kamar haka :

    1. Dena aikata Saɓon nan take.

    2. Yayi nadama bisa abinda ya aikata ɗin nan.

    3. Ya ɗauki niyyar cewa bazai sake komawa zuwa ga wannan aikin ba, har abada.

    Idan aka rasa ɗaya daga cikin waɗannan sharuɗan, to tubansa bata inganta ba.

    Don haka ki cigaba da gyara ayyukanki tare da kyautata alƙarki da Allah.

    WALLAHU A’ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.