𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam saurayina ne yake matsa min akan in aikata
zina dashi (har mun aikata sau da yawa) to sai mukayi faɗa naji labarin zai auri wata bayan kuma munyi alkawarin
aure kafin na yarda mufara aikata saɓon Allah, to
malam sai naje gidansa ba tare da saninsa ba, na ɗauke takardun karatunsa na makaranta dana shaidar
filayensa na yayyagasu to malam inada laifi?
Duba da irin cin zarafina da shima ya yi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Abu na farko shine laifin zina, biye wa son rai da
kikayi, kika ruɗu da Ƙaryar da wannan saurayin
yayi miki alhali a hakikar gaskiya mafiya yawan samarin dake fakewa da haka su
aikata ma sha’a, daga karshe tserewa sukeyi. Sun san cewa ke sun gama lalata
rayuwarki don haka ba zasu yarda su aureki ba.
kiji tsoron Allah ki fara tuba daga wannan laifin
da kikayi, domin hakika baki san yaushe ne mutuwa zata riskeki ba. Kuma ki ɗauki niyyar har abada bazaki sake komawa cikin laifi irin
wannan ba. Kuma koda saurayi ya biya sadakinki, duk da haka baki zama matarsa
ba, har sai an ɗaura muku aure
tukunna.
Shi kuwa laifin yaudararki da yayi, yana nan
akansa. Domin hakika yaci amanarki, yaci amanar iyayenki tunda ya aikata fasadi
dake. Sannan ga laifin zina wanda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace
"BAYAN YIN SHIRKA DA ALLAH, BABU WANI LAIFIN DA YAFI GIRMA KAMAR MANIYYIN
DA MUTUM YA JEFA ACIKIN MAHAIFAR DA BATA HALATTA GARESHI BA".
Yayyaga takardunsa kuwa da kikayi, hakika kin
cutar da rayuwarsa ta hanyar da zai daɗe bai dawo
daidai ba. Wannan ramukon da kikayi ya zarce iyaka, ya zama zalunci kuma, Allah
Maɗaukakin Sadki Yace: "IDAN AKA CUTAR DAKU, TO KUYI
RAMUKO DA MISALIN ABINDA AKA CUTAR DAKU.."
Kiji tsoron Allah ki nisanci irin waɗannan laifukan, ki yawaita istighfari da ayyukan
alkhairi, da sannu zasu wanke miki laifin da kika aikata a baya. Shi kuma
saurayin naki idan ba zai zama matsala ba, kije ki nemi yafewarsa bisa zaluncin
da kikayi masa. Idan kuma babu damar haka, ki cigaba da yi masa addu’ar neman
shiriya da yafewar zunubansa.
WALLAHU A’ALAM.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.