Neman Zaɓin Allah A Kan Mijin Aure

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam da fatan kana lafiya. Allah ya saka da alkhairi. Mutum biyu daban daban sun nuna suna sona da aure, kuma dukkansu mutanen kirki ne. Kowannensu yana so in bashi damar turowa iyayensa suzo gidanmu wajen Mahaifina domin atsaida magana. Malam na rasa yadda zanyi domin hakika dukkansu ina sonsu. Don haka nakeso ka bani shawara. Na iya addu'ar istikhara (na haddaceta) amma ban san yadda akeyi ba. Kuma shin idan nayi istikharar me zan gani amafarki?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Ita dai ma'anar istikhara da manufarta duk abu guda ne. Shine neman zaɓin Allah acikin lamarin da mutum ya himmantu akansa. Kuma ita dai wannan isrikharar wacce Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya koyar, idan kin yita ba wani abinda zaki gani amafarki. Sai dai a zahiri zaki ga taimakon Allah da yassarewarsa cikin tabbatuwar abinda kika nufa, ko kuma samun nutsuwa azuciyarki koda baki samu abinda kika fi so ba.

    SHAWARATA GAREKI ITA CE:

    Wajen zaɓar miji kar ki kalli abun duniyan dake tare dasu ko matsayinsu. Kedai ki kalli kyawun hali da rikon addininsa. Kada zaqin bakin mutum ya ruɗeki, ko kyawun fuska ko iya ado, ki kalli abun ta fuskar yanayin zaman da zakiyi dashi, Sannan ki yiwa kanki wasu tambayoyi kamar haka:

    1. Shin wannan mutumin zai iya jagorancin rayuwata da addinina yadda zamu samu dacewa alahira ni dashi?

    2. Shin wannan mutumin yana da kyawun halin da zai iya ɗaukar nauyin iyali tare da basu tarbiyyar da ta dace?

    3. Shin wannan duk randa nayi masa laifi, zai bini ahankali ta fuakar nasiha ne, ko kuwa cin mutuncina zai yi?

    4. Shin idan na zaɓi wane amatsayin mijin da zan aura, anya Aranar Alkiyamah bazan yi nadama agaban Allah ba kuwa?.

    Daga karshe ina yi miki fatan alkhairi da fatan Allah shi zaɓa miki wanda zaifi zama alkhairi ga rayuwarko ta duniya da lahira. Ameen.

    DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.