𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin Mace zata rama sallar Maghriba da Isha’i idon
Jini ya ɗauke mata kafin hudowar alfijir?
Ko idon ya ɗauke mata kafin faɗuwar Rana zatayi sallar Azahar da La’asar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan mai haila tayi tsarki bayan shigar lokacin
sallar isha’i wajibine tayi sallar isha’i ɗin domin tariski lokacinta, haka zatayi sallar magariba
domin ana haɗasu yayinda aka samu
uzuri.
Hakanan idan tai tsarki bayan shigar lokacin la’asar
zatayi sallar la’asar da azahar, wannan shine abunda wasu daga cikin shabban
Annabi Sallallahu alaihi Wasallam sukai fatawa dashi, shine kuma abunda
jamhurdin malamai sukai fatawa dashi.
Amma idan tayi tsarki bayan sallar asuba, ko
sallar azahar, ko sallar magariba bazatayi wata sallah ba sai guda ɗaya kawai, itace sallar datayi tsarki acikin lokacinta, (
Asuba ko azahar ko magariba) domin waɗannan sallolin
ba’a haɗasu dawani abu dayake kafinsu.
Ibnu ƙudama rahimahullah acikin Almugni ( 1/238) yace: Idan mai haila tayi tsarki
kafin rana tafadi zatayi sallar azahar da la’asar,
idan tayi tsarki kafin hudowar alfijir zatayi
sallar magariba da isha’i, anruwaito wannan daka Abdurrahman bin Auuf, da
Abdullahi dan Abbas, da dawus, da Mujahid, da Annaka’i, da zuhuri, da rabi’ah,
da malik, da lais, da shafi’i, da ishaƙ, da Abissauri.
Imamu Ahmad yace: gaba dayan tabi’ai sunyi fatawa
da wannan maganar sai hasanul basari shi kaɗai yace: abunda ya wajaba agareta shine sallar datayi
tsarki acikin lokacinta kawai, itace fatawar sauri dalibansa, domin lokacin
sallar farko yafita lokacin tanada uzuri, saboda haka bata wajaba akantaba.
An ruwaito daka malik cewa idan tariski lokacin
sallah tabiyu gwar-gwadon yanda zata iyayin raka’a biyar lokaci baifitaba,
sallar farko tawajaba agareta, domin gwar-gwadon lokacin raka’a ɗaya shine lokacin sallar farko ahalin uzuri, tawajaba
akanta da riskarsa, kamar yanda zata risketa afarkon lokacinta.
Asram da ibnu munzir sun ruwaito daka Abdurrahman
bin Auuf da Abdullahi dan Abbas sunce: Idan mai haila tai tsarki kafin hudowar
alfijir da gwar-gwadon lokacinda zata iya raka’a ɗaya, zatayi magariba da isha’i, idan tai tsarki kafin faɗuwar rana zatayi azahar da la’asar gaba ɗaya, domin lokacin sallah tabiyu shine lokacin tafarko
ahalin uzuri, idan mai uzuri yariskeshi wajabcinta yakamashi, kamar yanda
wajabcin ta biyu yahaushi.
Abunda yafi shine aiki da fatawar jamhur ɗin malamai, zatai sallah biyu ahaɗe, bazata rama dukkan sallolin wuni ba, idan kuma tarama
iya wacce tariski lokacinta Ana fatan babu komai akanta.
WALLAHU A’ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.