Saurayi Ya Yi Zina Da Budurwarsa Ta Samu Ciki, Shin Za A Iya Ɗaura Musu Aurae A Hakan?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Malam da fatan kana lafiya please tambaya garemu kamar haka: Yarinya ce 'yar shekara (14) Saurayinta yayi mata ciki wata (2), amma ya amsa cewa zai aureta a haka. Shin za'a jira har seta haihu ko za'a iya ɗaura musu auran a haka? Na gode.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Allah Maɗaukakin sarki Yace:

    الزَّانِي لَا يَنكِحُ إِلَّا زَانِيَةً أَوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لَا يَنكِحُهَا إِلَّا زَانٍ أَوْ مُشْرِكٌ وَحُرِّمَ ذَٰلِكَ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ

    Mazinãci bã ya aure fãce da mazinãciya kõ mushirika, kuma mazinãciya bãbu mai aurenta fãce mazinãci kõ mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan mũminai. (Suratun Nuur Aya ta 3)

    Ya halasta mazinaci ya auri mazinaciya amma bayan dukkansu sun tuba. Amma idan har ta samu ciki (juna-biyu) to babu damar ɗaura aure sai bayan ta haife abinda take ɗauke dashi tukunna. Wannan ita ce fatawar mafiya rinjayen Maluman Musulunci tun daga Sahabbai da Tabi'ai har zuwa Maluman fiqhu na Mazhabobin Ahlus Sunnah wal Jama'ah.

    Duk Matar da tayi Zina, ko budurwa ce ko bazawara bai halatta a ɗaura Mata aure ba har sai tayi istibra'i. Wato Jini uku, ko kuma a Qalla jini guda (a faɗar wasu Maluman).

    Kuma bai halatta azubar da wannan cikin ba, don gudun abun kunya, ko maganganun mutanen gari. Wata mata (ALGAMIDIYYAH) tazo wajen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam alhali yana ɗauke da cikin da ta samu asanadiyyar zina. Amma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam bai ce aje a zubar dashi ba. Ya umurci waliyyinta cewa yaje ya kula da ita har zuwa lokacin da zata haihu. Sai bayan da ta haihu kuma yaron yayi Qarfi sannan aka dawo da ita aka yi mata haddi.

    Malamai suka ce idan ta haife yaron, ba za'a jingina nasabarsa zuwa ga wannan wanda yayi zinar da ita ba. Sai dai ajinginashi zuwa ga mahaifiyarsa kaɗai. Kuma babu gado tsakaninsa da wannan mutumin, hakanan matayen dake dangantaka da wannan mutumin da muharramai ne awajen yaron ba.

    RA'AYI NA BIYU: Al Imam Ibnu Qudamah Almaqdisiy yace "Aliyu bn Aasim ya ruwaito daga Imam Abu Hanifah (rah) yace : "Idan wani mutum ya aikata zina da wata mata kuma ta samu ciki daga gareshi, banga laifin shi ya aureta ba, duk da cewar tana ɗauke da juna-biyu. Domin ɓoye laifinta (wato rufa asirinta). Kuma abinda ta haifa ɗin, nashi ne". Aduba Almughniy na Hafiz Ibnu Qudamah Almaqdisiy (juzu'i na 9 shafi na 122).

    Ibnul Muflihi (rahimahullahu) Almajirin Ibnu Taimiyyah yace "Shaikhinmu, (yana nufin Shaikhul islam Ibnu Taimiyyah) ya fifita ra'ayin Malaman da suka ce Mutum zai iya jingina kansa zuwa ga yaron da ya haifa ta hanyar zina da matar da bata da aure". (Alfuru'a juzu'i na 6 shafi na 625).

    Ibnu Qudamah ya Qara da cewa "Mafiya rinjayen Malamai sun tafi akan cewa yaron da aka haifa ta hanyar zina, ba za'a jinginashi zuwa ga Mazinacin ba, (wato wanda yayi zina da wacce ta haifi yaron).

    Amma Al Imam hasanul Basariy da Ibnu Sireena (daga manyan Maluman tabi'ai) sun ce za'a iya jingina nasabar yaron zuwa gareshi mutukar an riga an zartar masa da haddi, kuma yaron zai gajeshi.

    Al Imam Ibraheemun Nakha'iy yace : "Za'a iya jingina yaron zuwa gareshi mutukar anyi masa haddin bulalar nan, ko kuma idan daga baya yazo ya auri matar da ya aikata zinar da ita. Za'a jingina yaron zuwa gareshi. Kuma yace an ruwaito irin wannan fatawar daga magabata na kwarai (Salafus Salihi) irin su Urwatu bn Zubair, Sulaiman bn Yasar, da sauransu. Daga Fatawal Kubra (juzu'i na 3 shafi na 178).

    A takaice dai fatawar maluman farko ita tafi hujjah mai karfi acikinta. Wato Malaman da suka ce ba zai aureta ba, sai bayan ta haihu. Kuma babu dangantakar nasabah tsakaninsa da abinda ta haifa kuma babu gado tsakaninsu.

    A wasu lokutan idan abu yayi tsanani kuma an rasa mafita acikin fatawar Maluman mazhabinmu na malikiyyah, akan tsallaka zuwa wasu Mazhabobin, ko ra'ayin wasu daga magabata domin a toshe wata baraka. Domin shi addinin musulunci kullum so yakeyi a magance matsala idan ta taso.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.