Shin Allah Zai Karbi Tuban Wanda Ya Taba Aikata Luwadi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam Allah yaja kwana ya Ƙara maka ɗaukaka Ameen.

Dan Allah Malam tambayace dani kamar haka :

1. Mutum ne Allah ya shiryarshi yai tuba daga luwaɗi. ya taɓa aikatawa tun lokacin da ya fara balaga baifi shekara ɗaya zuwa da rabi ba. Kuma Abun da zai iya tunawa shine : Wani ɗan makarantarsu ne a boarding school Allah ya jarabceshi su kuma sai suke ta yayatawa, suna ɗora wa mai yin karar tsana (wato sun tsaneshi) har in yana kusa dasu wallahi bai isa ko magana yayi ba suna ta yayata shi acikin mutane, har dai shima Allah ya jarabceshi yaje ya aikata luwaɗin da wani.

Shin wannan ɗan makarantar nasu da suka yayatashi (suka kunyatashi) dole ne suje su nemi afwarsa koda sun tuba.

Shin Malam koda yayi cikakken tuba dolene Wanda ya nemi suka aikata abin sai ya nemi afwarsa ??

Shin Malam har iyayen wanda aka aikata laifin luwaɗin dasu, basu san an aikata ba, dole sai mutum yaje ya nemi afwarsu??

A yanzu dai babu wanda yasan hakan ta faru, sai Ubangiji da kuma masu aikata laifin kuma sun daina. Malam neman tuba yafewa daga garesu akwai tunanin zai iya haifar da bayyanar al’amarin tabbas tare da ruguza zumunci gaba dayansa.

2. Malam mutum ne ya je aiki gidan matar aure daya shiga matar Allah ya bata murya da kyakkywar sura mijin yananan sai ya Ɗan fita shaiɗan ya Kama rayawa mai aikin abubuwa aransa amma bai yi zina da ita ba. Sai dai yayin da yazo amsar kuɗi a hannun matar kawai hannunsa ya taɓa hannun matar sai yaji daɗi aransa badai yayi zina ba, kuma itama alamun kamar ta Lura da abinda ya faru.

Malam A yanzu Allah ya kawo shiriya mai wannan aikin ya shiryu. Kuma har tsawon wannan lokaci babu wanda ya sani har mijin nata. Dan Allah Malam yaya mutum zai yi ya tuba ??

Kuma menene hukuncin hakan a addinance?

3. Malam Mutane na cewa duk abunda mutum yayi sai anyi mar. Shin koda ya tuba tsakaninsa da Allah kuma ya roƙi Allah ya kareshi daga sharrin abinda ya taɓa aikatawa?

Dukka wadannan laifuka na wannan bawa yai tuba na hakika, Bazai karaba. ya kyamaci Mai yi, Laifin ma baison jin fadar irinsa kwata kwata. Ya daukarwa Allah alkawari bazai sake ba har tsawon rayuwarsa.

SHIN ALLAH ZAI KARƁI TUBAN WANDA YA TAƁA AIKATA LUWAƊI?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Allah Maɗaukakin Sarki wanda shi ya halicci Ɗan Adam, ya riga ya san muna da rauni wajen biyewa ruɗani da yaudara irin ta babban makiyinmu wato shaiɗan (La’anatul Lahi alaihi). Don haka sai ya buɗe mana kofar tuba kuma ya shimfida rahamarsa garemu, yana karɓar tubanmu mutukar mutum bai je gargara ba. Wato karshen lokacin fitar numfashi yayin rasuwa.

Allah ya gaya wa Annabinsa (Sallallahu alaihi Wasallam) cewa :

۞ قُلۡ یَـٰعِبَادِیَ ٱلَّذِینَ أَسۡرَفُوا۟ عَلَىٰۤ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُوا۟ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِیعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِیمُ

"KACE YAKU BAYINA WAƊANDA SUKA AIKATA WA KANSU ƁARNA! KADA KU FIDDA TSAMMANI DAGA (SAMUN) RAHAMAR ALLAH. HAKIKA ALLAH YANA YAFE DUKKAN ZUNUBAI BAKI ƊAYA, SHI SHINE MAI GAFARA MAI JINƘAI". (Surah Az-Zumar: 53)

Kuma Yace:

إِلَّا ٱلَّذِینَ تَابُوا۟ مِنۢ بَعۡدِ ذَ ٰلِكَ وَأَصۡلَحُوا۟ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورࣱ رَّحِیمࣱ

"SAI DAI WAƊANDA SUKA TUBA BAYAN NAN (WATO BAYAN SUN AIKATA LAIFIN) KUMA SUKA KYAUTATA AIKI, TO HAKIKA ALLAH MAI GAFARA NE MAI JIN ƘAI GARESU". (Surah An-Nuur: 5)

Al Imamun Nawawiy (rahimahul Lahu) acikin shahararren littafinsa mai suna RIYADHUS SALIHEEN MIN KALAMI SAYYIDIL MURSALEEN (Sallallahu alaihi Wasallam} afarkon babin tuba, yayi wata magana inda yake cewa :

"Malamai sun ce tuba wajibi ce daga dukkan zunubai. Idan laifin ya kasance tsakanin bawa ne da Allah Ta’ala babu hakkin wani Ɗan Adam aciki, to tana da sharuɗa guda uku kamar haka :

1. Dena aikata Saɓon nan take.

2. Yayi nadama bisa abinda ya aikata ɗin nan.

3. Ya ɗauki niyyar cewa bazai sake komawa zuwa ga wannan aikin ba, har abada.

Idan aka rasa ɗaya daga cikin waɗannan sharuɗan, to tubansa bata inganta ba.

To idan kuma laifin yana ratayuwa ga hakkin wani Ɗan Adam, to sharuɗan tuban sun zama huɗu kenan. Bayan waɗannan sharuɗan guda uku, akwai kuma ya nemi kubuta daga hakkin ma’abocin alhakin, idan dukiya ce ko wani abu daban, to ya mayar dashi ga maishi. Idan kuma haddi ne na Ƙazafi (wato yarfe) ya bashi damar ɗaukar mataki akansa, ko kuma ya nemi afuwarsa. Idan ta kasance gulma ce, to ya nemi halastuwarsa daga gareta.

To idan mun dawo kan mas’alar da kake tambaya akai, tunda dai ka riga ka tuba, kuma zuwa neman yafewar waɗannan da ka aikata laifin dasu, ko yafewar iyayensu, zai iya zama dalilin yankewar zumunci da zubewar mutunci, abinda zai fi gareka shine kaci gaba da nemar musu gafara awajen Allah, sannan kai kanka kaci gaba da gyara ayyukanka tare da yawaita aikin alkhairi kamar su zikirin Allah, Ƙara dagewa wajen kula da hakkin iyaye, sadaƙoƙi, sadar da zumunci, taimakon marassa Ƙarfi, yawaita azumi, sallolin dare, da sauransu.

Itama waccen Matar, dakai da ita da mijin nata duk kun aikata kusakurai. Ita aɓangarenta bai halatta gareta ta bayyanar da muryarta har wani namiji ya saurara yaji daɗi ba. Shima mijinta bai halatta gareshi ya bar mai lebura ya shigo har inda matarsa take ba. Ballantana har ya bata kuɗi don ta mika wa leburan. Kai kuma anaka ɓangaren bai halatta gareka kallo ko jin daɗin muryar matar da ba taka ba, ballantana har ka shafi hannunta. Kuma shuru ɗin da tayi, yana nuna alamar rashin kishin kanta ne. Da tana da kishin kanta ko na addininta, da ta tsawatar dakai alokacin da hannunka ya shafi jikinta.

Hakika yazo acikin hadisin Imamut Tirmidhiy Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace "ALLAH YANA KARƁAR TUBAN BAWA MUTUKAR BAI KAI GARGARA BA.

acikin wani hadisin kuma daga Sayyiduna Abu Hurairah wanda Imamu Muslim ya ruwaito Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yace "DUK WANDA YA TUBA TUN KAFIN RANA TA FITO DAGA MAFADARTA, TO ALLAH ZAI KARƁI TUBANSA".

Don haka kaci gaba da gyara ayyukanka tare da kyautata alƙarka da Allah. Kada ka Ƙara yiwa wani dariyar Ƙeta ko shakiyanci saboda wata jarrabawar da yake ciki. Sai Allah ya yaye masa kai kuma ya jarrabeka kamar yadda yazo a wani hadisi.

"HAKIKA KYAWAWAN AYYUKA SUNA SHAFE MUNANA". (Inji Allah) Don haka tunda dai ka tuba, to in shaAllahu Ubangiji bazai bibiyeka da wani mummunan abinda ka aikata abaya ba. Domin Ubangijinmu mai rahama ne, mai karamci ne, mai yalwar baiwa ne. Yana sonka fiye da yadda mahaifiyarka take sonka, fiye ma da yadda kake son kanka.

WALLAHU A’ALAM.

DAGA ZAUREN FIƘHU 07064213990

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments