Akwai wata Aya da Allah ya koyar da mu wani ladabi mai muhimmanci, musamman a irin wannan zamani. A cikin Ayar Allah ya ce:
{وَإِذَا جَاءَهُمْ أَمْرٌ مِنَ الْأَمْنِ أَوِ الْخَوْفِ أَذَاعُوا
بِهِ وَلَوْ رَدُّوهُ إِلَى الرَّسُولِ وَإِلَى أُولِي الْأَمْرِ مِنْهُمْ لَعَلِمَهُ
الَّذِينَ يَسْتَنْبِطُونَهُ مِنْهُمْ } [النساء: 83]
"Idan labarin lamarin aminci ko na tsoro ya
zo musu sai su yada shi, alhali da sun mayar da shi ga Manzon Allah da
majibinta lamari daga cikinsu (shugabanni), da wadanda suke bincike daga
cikinsu da fitar da ingancinsa sun san hakikaninsa (sun fitar da abin da shi ne
Maslaha ga al’umma)".
Al- Shaikh Ibnu Si’idiy ya ce:
وفي هذا دليل لقاعدة أدبية وهي أنه إذا حصل بحث في أمر من الأمور
ينبغي أن يولى من هو أهل لذلك ويجعل إلى أهله، ولا يتقدم بين أيديهم، فإنه أقرب إلى
الصواب وأحرى للسلامة من الخطأ. وفيه النهي عن العجلة والتسرع لنشر الأمور من حين سماعها،
والأمر بالتأمل قبل الكلام والنظر فيه، هل هو مصلحة، فيقدم عليه الإنسان؟ أم لافيحجم
عنه؟
تيسير الكريم الرحمن (ص: 190)
Ma’ana; wannar Ayar dalili ce a kan ka’idar nan ta
Ladabi a cikin al’umma.
Idan wani lamari ya faru to a bar shugabanni da ma’abota
abin su tinkare shi, kar wani ya wuce gaban makadi da rawa.
Kuma a cikin wannan akwai hani a kan gaggawan yada
labarai da zaran mutum ya ji su. Don akwai abin da babu maslaha cikin yada shi,
akwai kuma abin da bai kamata na kasa ya tsoma baki a cikinsa ba.
Shin haka muke?
✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.