Shin Ya Tabbata Abdullahi Bn Zubair (Ra) Ya Yi Tawaye Wa Shugabanni?

    Abdullahi bn Zubair (ra) daya ne daga cikin Sahabbai wadanda suka shiga cikin fitina da ta afku a zamaninsa. Wannan ya sa masu da’awar rusa Ijma’in Ahlus Sunna a kan haramcin tawaye wa shugaba fasiki suke kafa hujja da shi, don halasta tawaye wa shugaba.

    To kamar yadda ya gabata game da Hussain (ra), haka shi ma Ibnu Zubair (ra) ya kamata mu tsaya mu nazarci wannar mas’ala da ake jingina ta gare shi, ta tawaye wa shugabanni, don mu san gaskiyar lamari game da ita.

    A baya mun gabatar da ma’anar tawaye, shi ne mutum ya dauki MAKAMI ya yaki shugaba mai iko, wanda MUTANE SUKA HADU A KARKASHINSA. Ko kuma wanda ya warware BAI’AR DA YA YI WA SHUGABAN.

    To za mu amsa wannar tambaya ce ta fiskoki kamar haka:

    1- A karon farko Abdullahi bn Zubair (ra) bai yi Bai’a wa Yazidu ba:

    Ya gabata cewa; Yazidu ya aika wa mutanen Madina wasika don su yi masa Bai’a, sai Sahabban da ya ambace su a cikin wasikar tasa suka yi masa bai’ar, amma Hussain (ra) da Abdullahi bn Zubair (ra) ba su yi masa bai’a ba. Ibnu Sa’ad ya ruwaito cewa:

    "لم يزل ابن الزبير مقيما بالمدينة في خلافة معاوية بن أبي سفيان، فتوفي معاوية، فبعث يزيد بن معاوية إلى الوليد بن عتبة ابن أبي سفيان - وهو يومئذ والي المدينة ينعي معاوية - ويأمره أن يبايع من قبله من الناس. فجاءه الرسول ليلا، فأرسل إلى ابن الزبير فدعاه إلى البيعة فقال: حتى تصبح، فتركه. فخرج ابن الزبير وهو يقول: هو يزيد الذي نعرف، والله ما أحدث خيرا ولا مروءة.

    وخرج من ليلته إلى مكة. فلم يزل مقيما بها حتى خرج حسين بن علي منها إلى العراق".

    الطبقات الكبرى (2/ 42 - 43)، تاريخ دمشق لابن عساكر (28/ 207)

    To wannan a farkon lamari kenan. To haka Yazidu ya cigaba da aiko wa Ibnu Zubair (ra) sakon neman ya yi masa Bai'a. Ibnu Qutaiba ya ce:

    "العتبي: بعث يزيد بن معاوية عبيد الله بن عضاه الأشعري إلى ابن الزبير فقال له: إن أول أمرك كان حسنا فلا تفسده بآخره. فقال ابن الزبير: إنه ليست في عنقي بيعة ليزيد".

    عيون الأخبار (1/ 293)

    A wannan karo sai Ibnu Zubair (ra) ya yi ikirarin cewa: Babu Bai'ar Yazidu a wuyansa.

    Saboda haka asali Abdullahi bn Zubair (ra) bai yi Bai’a wa Yazidu ba, balle a ce ya yi tawaye ya warware Bai’a.

    2- Mutane ba su hadu suka mika wuya ga Mulkin Yazidu a Hijaz ba:

    Daga cikin abin da ke nuni ga yin tawaye shi ne idan ya zama Mulki ya gama tabbatuwa a hanun shugaba, kowa cikin masu ruwa da tsaki ya yi masa Bai'a. To ya gabata a baya cewa; a Hijaz mulkin Yazidu bai yi karfi ba, ba dukkan mutane ne suka hadu a karkashinsa ba. Wannan ya sa Abdullahi bn Zubair (ra) ya samu karbuwa a wajen mutanen Makka da kewaye:

    "وتحلب الناس على ابن الزبير من نواحي الطائف يعاونونه ويدفعون عن الحرم".

    أنساب الأشراف للبلاذري (5/ 313)

    Galibin mutanen Hijaz suna goyon bayan Abdullahi bn Zubair (ra) ne. Wannan ya sa ya yi karfin da har zai iya hana Gomnan Yazidu a Makka, Harith bn Khalid jan mutane Sallah a Masallacin Harami, daga karshe ma ya kore shi daga Makkan, ya nada Mus’ab bn Abdirrahman bn Auf yana yi wa mutane Sallah a Masallacin Harami:

    "قال الزبير: ويحيى بن حكيم بن صفوان ولي مكة ليزيد بن معاوية، كان عبد الله بن الزبير مقيما معه بمكة، لم يعرض له يحيى بن حكيم، فكتب الحارث بن خالد بن العاص بن هشام بن المغيرة إلى يزيد يذكر له مداهنة يحيى بن حكيم عبد الله بن الزبير، فعزل يزيد يحيى بن حكيم، وولى الحارث بن خالد مكة، فلم يدعه ابن الزبير يصلي بالناس، وكان الحارث يصلي في جوف داره، والناس طاعنين عليه. وكان مصعب بن عبد الرحمن يصلي بالناس في المسجد الحرام بأمر عبد الله بن الزبير، فلم يزل كذلك حتى وجه يزيد بن معاوية إلى الزبير مسرف بن عقبة فبويع ابن الزبير في الخلافة، وصلى بالناس بمكة".

    تاريخ دمشق لابن عساكر (11/ 415 - 416)، (28/ 208)، (34/ 371)، الطبقات الكبرى - متمم الصحابة (2/ 48 - 49)، تاريخ الطبري (5/ 344)

    Yazidun da hatta Gomnansa a Makka ya kasa fitowa ya ja mutane Sallah a Masallaci, sai a cikin gidansa yake Sallar, ta yaya zai zama shugaba mai iko a Hijaz?!

    Kai, har ma sai da Ibnu Zubair (ra) ya kori Gomnan Yazidun daga Makkan:

    "وأخرج ابن الزبير الحارث بن خالد من مكة".

    تاريخ دمشق لابن عساكر (11/ 416)

    To ka ga wannan shi yake nuna maka cewa: Mulkin Yazidu a Hijaz bai kafu ba, bai samu karbuwa a wajen mutane ba. Don haka babu yadda za a yi a jingina wa Ibnu Zubair (ra) tawaye.

    3- Karfi da goyon bayan da Abdullahi bn Zubair (ra) ya samu:

    Sa’annan Gomnan Yazidu a Madina, Amru bn Sa’id ya tura wa Abudullahi bn Zubair (ra) runduna karkashin jagorancin dan’uwansa Amru bn Zubair, da Anis bn Amr, amma a karshe rundunar Abdullahi bn Zubair (ra) karkashin jagorancin Mus’ab bn Abdirrahman bn Auf da Abdullahi bn Safwan ce ta yi nasara, saboda karfin Ibnu Zubair (ra) a Makka da Hijaz baki daya:

    "وجه عمرو بن سعيد يعني ابن العاص والي المدينة إلى ابن الزبير عمرو بن الزبير وأنيس بن عمرو الأسلمي في سبع مائة، فوجه ابن الزبير عبد الله بن صفوان فلقي أنيسا فهزم أنيسا وأصحابه، وبعث ابن الزبير مصعب بن عبد الرحمن بن عوف فلقي عمرو بن الزبير، فأسر عمرو بن الزبير، وتفرق عنه أصحابه، قال خليفة: فحبسه ابن الزبير حتى مات".

    تاريخ دمشق لابن عساكر (46/ 9 - 10)، أنساب الأشراف للبلاذري (5/ 328 - 329)

    Wannan ya sa Yazidu ya tabbatar bai samu karbuwa a Hijaz ba, har ya zargi Gomnansa Amru bn Sa’id, har sai da Gomnan ya mayar masa da jawabi:

    "ثم إنه عاتبه في تقصيره في أشياء كان يأمره بها في ابن الزبير، فلا ينفذ منها إلا ما أراد.

    فقال: يا أمير المؤمنين، الشاهد يرى ما لا يرى الغائب، وإن جل أهل مكة وأهل المدينة قد كانوا مالوا إليه وهووه وأعطوه الرضا، ودعا بعضهم بعضا سرا وعلانية، ولم يكن معي جند أقوى بهم عليه لو ناهضته، وقد كان يحذرني ويتحرز مني، وكنت أرفق به وأداريه".

    تاريخ الطبري (5/ 478)

    Sai Gomnan ya tabbatar wa Yazidu cewa; Mafi yawan mutanen Makka da Madina suna tare da Abdullahi bn Zubair (ra). Gomnan ya bayyana cewa; rundunar Abdullahi bn Zubair (ra) ta fi tasa karfi.

    4- Abdullahi bn Zubair (ra) bai dauki makami ya yaki Yazidu ba, kai daga karshe ma ya yi Bai’a wa Yazidu:

    Yana daga cikin tawaye mutum ya dauki makami don yakar shugaba. To amma ba a samu Ibnu Zubair (ra) ya dauki makami don yakar Yazidu ba. Kai, an ma ruwaito cewa; a karshen lamari Abdullahi bn Zubair (ra) ya yi Bai’a wa Yazidu, ta hanun Gomnansa Yahya bn Hakam:

    "وقال الواقدي: عزل يزيد الوليد بن عتبة لأن مروان كتب يذكر ضعفه ووهنه وإدهانه، وولى المدينة عمرو بن سعيد الأشدق، وولى يحيي بن الحكم بن صفوان بن أمية بن خلف الجمحي مكة - وقال هشام ابن الكلبي: هو يحيى بن الحكم بن صفوان - ولاه عمرو بن سعيد مكة وصار إلى المدينة. قال الواقدي: فأتاه ابن الزبير فبايعه ليزيد وقال إني سامع مطيع غير أن الوليد رجل أخرق فكرهت جواره، ولقد خبرنا من معاوية ما لم نخبره من غيره، وإنما أنا عائذ بالبيت من أمر لا آمنه".

    أنساب الأشراف للبلاذري (5/ 307)

    Maganar Bai’ar Ibnu Zubair (ra) ga Yazidu Ibnul Jauziy ya tabbatar da ita, haka Ibnu Taimiyya.

    Ibnul Jauziy yana tarjama wa Ibnu Zubair sai ya ce:

    "ولم يزل مقيما بالمدينة إلى أن توفي معاوية، فبعث يزيد إلى الوليد بن عتبة يأمره بالبيعة، فخرج ابن الزبير إلى مكة، وجعل يحرض الناس على بني أمية، فوجد عليه يزيد إلا أنه مشى ابن الزبير إلى يحيى بن الحكم والي مكة فبايعه ليزيد، فقال يزيد: لا أقبل حتى يؤتى به في وثاق، فأبى ابن الزبير، وقال: اللهم إني عائذ ببيتك، وجرت حروب، وحوصر ابن الزبير، ثم مات يزيد، فدعى إلى نفسه، وسمي أمير المؤمنين، وولى العمال، واستوثقت له البلاد ما خلا طائفة من الشام فإنهم بايعوا مروان".

    المنتظم في تاريخ الملوك والأمم (6/ 137 - 138)

    Sai Ibnul Jauziy ya tabbatar da cewa; Abdullahi bn Zubair (ra) ya yi Bai’a wa Yazidu, ta hanun Gomnansa a Makka, Yahya bn Hakam, amma sai Yazidun ya ki amincewa; -wai- sai dai a zo da shi a daure. Shi kuwa ya ki yarda da hakan.

    5- Bayan mutuwar Yazidu Abdullahi bn Zubair (ra) shi ne Khalifa:

    Ya tabbata cewa; bayan mutuwar Yazidu sai dansa Mu'awiya bn Yazidu ya maye gurbinsa, amma bai dade ba ya rasu. Sai Marwan bn Hakam ya maye gurbinsa. To a wannan lokaci hatta kasar Sham sai da Abdullahi bn Zubair (ra) ya samu magoya baya:

    "وأقام الناس بدمشق، وخرج الضحاك إلى مسجد دمشق، فجلس فيه فذكر يزيد بن معاوية، فوقع فيه، فقام إليه شاب من كلب بعصا معه فضربه بها، والناس جلوس في الحلق متقلدي السيوف، فقام بعضهم إلى بعض في المسجد، فاقتتلوا، قيس تدعو إلى ابن الزبير ونصرة الضحاك، وكلب تدعو إلى بني أمية ثم إلى خالد بن يزيد، ويتعصبون ليزيد، ودخل الضحاك دار الإمارة، وأصبح الناس فلم يخرج إلى صلاة الفجر، وكان من الأجناد ناس يهوون هوى بني أمية، وناس يهوون هوى ابن الزبير".

    تاريخ الطبري (5/ 533)

    Wannan ya sa Abdullahi bn Zubair (ra) ya zama shi ne Khalifa bayan mutuwar Yazidu. Don sai da aka wayi gari Abdullahi bn Zubair (ra) ya mulki dukkan daular Muslunci in ban da Urdun.

    قال أبو بكر بن عياش: «ما بقي أرض إلا ملكها ابن الزبير إلا الأردن»

    السنة لأبي بكر بن الخلال (3/ 522 - 523)

    Wannan ya sa Abdulmalik bn Marwan shi ne ya yi tawaye wa Ibnu Zubair (ra) ba akasi ba. Malamai masu yawa sun tabbatar da haka. Daga cikinsu akwai Ibnu Qudama:

    "إن عبد الملك بن مروان خرج على ابن الزبير فقتله، واستولى على البلاد وأهلها، حتى بايعوه طوعا وكرها، فصار إماما يحرم الخروج عليه؛ وذلك لما في الخروج عليه من شق عصا المسلمين، وإراقة دمائهم، وذهاب أموالهم".

    المغني لابن قدامة (8/ 526 - 527)

    Ibnu Kasir yana magana game da Ibnu Zubair (ra) sai ya ce:

    "فإنه كان على صفات حميدة، وقيامه في الإمارة إنما كان لله عز وجل، ثم هو كان الأمر بعد موت معاوية بن يزيد لا محالة، وهو أرشد من مروان بن الحكم، حيث نازعه بعد أن اجتمعت الكلمة عليه، وقامت البيعة له في الآفاق، وانتظم له الأمر، والله أعلم".

    البداية والنهاية ط هجر (12/ 206)

    6- Abin da ya faru tsakanin Ibnu Zubair (ra) da Yazidu fitina ce ba tawaye wa shugaba ba:

    Imamu Ahmad ya ruwaito:

    عن أبي الأشعث الصنعاني، قال: بعثنا يزيد بن معاوية إلى ابن الزبير، فلما قدمت المدينة، دخلت على فلان - نسي زياد اسمه - فقال: إن الناس قد صنعوا ما صنعوا، فما ترى؟ فقال: "أوصاني خليلي أبو القاسم صلى الله عليه وسلم: "إن أدركت شيئا من هذه الفتن، فاعمد إلى أحد، فاكسر به حد سيفك، ثم اقعد في بيتك"، قال: "فإن دخل عليك أحد إلى البيت، فقم إلى المخدع، فإن دخل عليك المخدع فاجث على ركبتيك، وقل بؤ بإثمي وإثمك، فتكون من أصحاب النار، وذلك جزاء الظالمين" فقد كسرت حد سيفي، وقعدت في بيتي".

    مسند أحمد ط الرسالة (٢٩/ ٥٠٢)، مسند البزار (٨/ ٣٠٤)

    Sahabin da aka manta sunan nasa shi ne Abdullahi bn Abi Aufa (ra), kamar yadda aka sarraha sunan nasa a riwayar al-Bazzar.

    Sai wannar riwaya ta nuna cewa; Sahabbai suna daukan abin da ya faru tsakanin Abdullahi bn Zubair (ra) da Yazidu a matsayin fitina ce, irin wacce ta faru tsakanin Sayyidina Aliyu (ra) da Mu'awiya (ra), da kuma bangaren A'isha (ra), Dalha (ra) da Zubair (ra), ba -wai- tawaye ba.

    Shaikhul Islami ya ce:

    "إن ابن الزبير لما جرى بينه وبين يزيد ما جرى من الفتنة، واتبعه من اتبعه من أهل مكة والحجاز وغيرهما، وكان إظهاره طلب الأمر لنفسه بعد موت يزيد، فإنه حينئذ تسمى بأمير المؤمنين، وبايعه عامة أهل الأمصار إلا أهل الشام. ولهذا إنما تعد ولايته من بعد موت يزيد، وأما في حياة يزيد فإنه امتنع عن مبايعته أولا، ثم بذل المبايعة له، فلم يرض يزيد إلا بأن يأتيه أسيرا، فجرت بينهما فتنة، وأرسل إليه يزيد من حاصره بمكة، فمات يزيد وهو محصور، فلما مات يزيد بايع ابن الزبير طائفة من أهل الشام والعراق وغيرهم. وتولى بعد يزيد ابنه معاوية بن يزيد ولم تطل أيامه، بل أقام أربعين يوما أو نحوها، وكان فيه صلاح وزهد، ولم يستخلف أحدا، فتأمر بعده مروان بن الحكم على الشام، ولم تطل أيامه، ثم تأمر بعده ابنه عبد الملك، وسار إلى مصعب بن الزبير نائب أخيه على العراق، فقتله حتى ملك العراق، وأرسل الحجاج إلى ابن الزبير فحاصره وقاتله، حتى قتل ابن الزبير، واستوثق الأمر لعبد الملك، ثم لأولاده من بعده".

    منهاج السنة النبوية (4/ 522 - 523)

    To da wannan zaka fahimci cewa; bai tabbata Abdullahi bn Zubair (ra) ya yi tawaye wa shugaba ba. Don haka jingina masa tawaye kuskure ne da Malamai da yawa suka afka cikinsa, a sakamakon wasu sun kirkiri karyar hakan, suka jingina ma wasu Sahabbai tawaye wa shugaba.

    Imamu Ahmad ya tabbatar da cewa: asalin jingina wa Sahabbai tawaye karya ce da mabiya son zuciya suka kirkira. Imam al-Zahbiy ya ce:

    "وقال المروذي في كتاب "القصص": عزم حسن بن البزاز، وأبو نصر بن عبد المجيد وغيرهما على أن يجيئوا بكتاب المدلسين الذي وضعه الكرابيسي يطعن فيه على الأعمش، وسليمان التيمي. فمضيت إليه في سنة أربع وثلاثين فقلت: إن كتابك يريد قوم أن يعرضوه على عبد الله، فأظهر أنك قد ندمت عليه.

    فقال: إن أبا عبد الله رجل صالح، مثله يوفق لإصابة الحق. قد رضيت أن يعرض عليه. لقد سألني أبو ثور أن أمحوه، فأبيت.

    فجيء بالكتاب إلى عبد الله، وهو لا يعلم لمن هو، فعلموا على مستبشعات من الكتاب، وموضع فيه وضع على الأعمش، وفيه: إن زعمتم أن الحسن بن صالح كان يرى السيف فهذا ابن الزبير قد خرج.

    فقال أبو عبد الله: هذا أراد نصرة الحسن بن صالح، فوضع على أصحاب رسول الله -صلى الله عليه وسلم".

    تاريخ الإسلام ط التوفيقية (18/ 56)

    To da wannan za mu kara tabbatar da cewa; jingina wa Salaf tawaye wa shugabanni, don a rusa Ijma’insu a kan haramcin tawaye wa shugaba fasiki shubuha ce wacce asalinta daga mabiya son zuciya take.

    Da wannan muke raddi wa matasan da suka fito suna rusa Akidar Ahlus Sunna da Ijma’insu, ta hanyar ikirarin cewa; -wai- Salaf sun yi sabani a game da mas’alar tawaye wa shugaba fasiki, don su ba da mafaka wa 'yan Ikhwan da 'yan Sururiyya, da Qudubawa Khawarijawan zamani.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.