Ta’addanci Mafi Girma Da Aka Yi Wa Addinin Muslunci

    Akwai wasu gungun mabiya ra’ayi da ake kira da sunan "Mutakallimun", wadanda suka hada da Mu’utazila, Asha’ira da Maturidiyya, wadanda tun da dadewa suka illata al’ummar Musulmi suka bata musu Addininsu, suka cire musu ganin girman Sunnar Annabi (saw) a zukatansu, suka yi watsi da Sunnar suka gabatar da hankulansu a kanta. Babu wanda ya tsira daga wannan sharri sai kadan da Allah ya tabbatar da su a kan tafarkin Salaf mabiya Sunnar Manzon Allah (saw).

    Su wadannan "Mutakallimun" din sun shiga cikin ilimin "Usulul Fiqhi" sun lalata shi, sun kawar da shi daga tafarkinsa na farko, wanda Imamu Shafi’iy ya fara rubutu a kansa, suka zuba munanan ra’ayoyinsu a cikin ilimin, wadanda suka gada daga ‘Yan Falsafa masu yakar tafarkin Annabawa.

    Da suka zo magana a kan Nassoshin Alkur’ani da Hadisan Annabi (saw) sai suka kalle su ta fiskoki biyu;

    1- Tabbacin Nassin ta hanyar isowarsa (الثبوت).

    2- Nassi ta fiskar kafa hujja da shi (الدلالة).

    A fiska ta farko sai suka kasa Nassosahin zuwa gida biyu:

    1- Tabbatattu a yanke ba shakka (قطعي الثبوت), su ne Alkur’an da Hadisai Mutawatirai.

    2- Tabbatattu bisa zato (ظني الثبوت), wato Hadisai Ahaad.

    Ta fiskar kafa hujja ma sai suka kasa su kashi biyu:

    1- Hujja a yanke babu shakka (قطعي الدلالة).

    2- Hujja a bisa zato (ظني الدلالة).

    To a wannar fiska ta biyu ne suka yi watsi da Alkur’ani da Hadisai a Babin Aqeeda, suka ce: ba a daukar Aqida sai daga dalili yankakke (قطعي الدلالة), su kuma Alkur’ani da Hadisai dalilai ne na lafazi, su kuma babu yakini a cikinsu, don haka ba dalilai ne na yankan shakku wajen kafa hujja ba. Saboda haka ba za a kafa hujja da su a Aqeeda ba, wato babin sanin Allah da Siffofinsa da sanin gaskiyar Annabi, sai dai a kafa hujja da dalilai na hankali, -wai- hankali shi ne yakini, abin da ya yi nuni gare shi ne ilimi da babu shakka a cikinsa. Amma Alkur’ani da Sunna kam ba sa nuni ga ilimi da yakini, suna nuni ne ga zato.

    Subhanallah!

    -Wai- Maganar Allah da Manzonsa ne ba sa nuni ga yakini sai zato!!!

    Dukkan Malaman Mu’utazila da Asha’ira da Maturidiyya a kan wannan suke, irinsu Alkali Abduljabbar da Fakhruddeen Al-Raziy da sauransu. Kuma shi Raziy ya fi su bushewar ido a wannan babi. Ga irin abin da yake fadi:

    "إن الدلائل اللفظية لا تفيد إلا الظن" .

    المطالب العالية (9/ 118)

    "Dalilai na lafazi (Alkur’ani da Hadisi) ba sa nuni ga dalili na yakini sai zato".

    Kuma ya ce:

    "التمسك بالدليل الظني في المطلوب اليقيني باطل قطعا" .

    المطالب العالية (9/ 118)

    "Riko da dalili na zato a mas’alar yakini (Aqida) batacce ne a yanke".

    Da irin wadannan ra’ayoyi suka cika littatafansu na "Ilmul Kalam" da na "Usulul Fiqhi". Shi ya sa duk wanda ya karanci "Usulul Fiqhi" a mummunan hanu to wannar kwamacalar kawai ya koyo da sunan Addini!

    Amma Imamai cikin Salaf da mabiya tafarkinsu, su Imamu Malik, Imamu Shafi’iy, Imamu Ahmad da su Ibnu AbdilBarr su kam sun saba ma tafarkin wadancan, Ibnu AbdilBarr ya hakaito fafarkinsu kamar haka:

    وعلى ذلك أكثر أهل الفقه والأثر وكلهم يدين بخبر الواحد العدل في الاعتقادات ويعادى ويوالى علها ويجعلها شرعا ودينا في معتقده على ذلك جماعة أهل السنة

    التمهيد لما في الموطأ من المعاني والأسانيد (1/ 8)

    "A kan wannan mafi yawan Malaman Fiqhu da Hadisi suke, kowannensu yana aiki da Hadisi Ahaad da aka ruwaito daga adali a mas’alolin Aqida, kuma yana kulla soyayya da kiyayya a kansu, kuma yana sanya su a matsayin Shari’a da Addini a Aqidarsa, a kan wannan Jama’ar Ahlus Sunna suke".

    Amma abin mamaki, Raziy har Ijma’i ya hakaito a kan wannan mummunan ra’ayi nasu!

    To wane irin Ijma’i ne a Addini wanda babu su Imamu Malik, Shafi’iy, Ahmad a cikinsa?!

    Saboda haka, duk malami ko Dr. da ka ji yana cewa; ba a kafa hujja da Hadisi Ahaad a Aqeeda, ko yana cewa; Hadisi Ahaad zato ne to ka sani ba a kan tafarkin Ahlus Sunna yake ba, ko da kuwa Babansa ne ya kafa Izala.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh’d Sani (H)

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.