𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wai yaya ake yin ta’aziyyar yaro ƙarami ne wanda alƙalami bai hau kansa ba?
TA’AZIYYAR
ƘARAMIN YARO:
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
Da farko, malamai sun yarda cewa, mustahabbi ne a
yi wa ƙaramin yaro sallah ta
jana’iza, saboda maganar Manzon Allaah (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
«وَالسِّقْطُ يُصَلَّى عَلَيْهِ، وَيُدْعَى لِوَالِدَيْهِ بِالْمَغْفِرَةِ
وَالرَّحْمَةِ»
Jaririn da aka yi ɓarin shi [a wata riwaya: ƙaramin yaro] ana yi masa sallah, kuma a roƙa wa iyayensa gafara da
rahama. (Abu-Daawud: 3180, da At-Tirmiziy:1031, da Ibn Maajah: 1507 suka
riwaito shi, kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi).
A nan sai aka keɓance iyayensa da addu’ar neman gafara da rahama. Domin
kamar yadda malaman suka ce: Yaro ƙarami ba a fara rubuta masa laifi ba, balle har a je nema masa gafara a
kansu.
A cikin bayanin Sallar Jana’iza Al-Imaam Ibn Ƙudaamah ya ambaci cewa:
(1563) فَصْلٌ: وَإِنْ كَانَ الْمَيِّتُ طِفْلًا، جَعَلَ مَكَانَ الِاسْتِغْفَارِ
لَهُ: اللَّهُمَّ اجْعَلْهُ فَرَطًا لِوَالِدَيْهِ، وَذُخْرًا وَسَلَفًا وَأَجْرًا،
اللَّهُمَّ ثَقِّلْ بِهِ مَوَازِينَهُمَا، وَأَعْظِمْ بِهِ أُجُورَهُمَا، اللَّهُمَّ
اجْعَلْهُ فِي كَفَالَةِ إبْرَاهِيمَ وَأَلْحِقْهُ بِصَالِحِ سَلَفِ الْمُؤْمِنِينَ
Fasali: Idan kuma mamacin yaro ne ƙarami, a maimakon
istighfari sai a musanya da cewa: Ya Allaah! Ka sanya shi ya zama magabaci, da
guzuri, kuma da lada ga iyayensa. Ya Allaah! Ka nauyaya mizaninsu da shi, kuma
ka girmama ladansu da shi. Ya Allaah! Ka sanya shi a cikin kulawar Annabi Ibrahim,
kuma ka sada shi da magabata na ƙwarai daga cikin muminai. (Al-Mughnee: 2/365).
Amma a wurin ta’aziyya, mafi kyau shi ne lafazin
da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi amfani da shi, a
lokacin da ya aika wa ‘yarsa da hakan a sakamakon rasuwar ɗanta:
«إِنَّ لِلَّهِ مَا أَخَذَ، وَلَهُ مَا أَعْطَى، وَكُلُّ شَيْءٍ
عِنْدَهُ بِأَجَلٍ مُسَمًّى، فَلْتَصْبِرْ وَلْتَحْتَسِبْ»
Haƙiƙa! Na Allaah ne abin da
ya karɓa, kuma nasa ne abin da ya bayar. Kuma komai a wurinsa da
ma yana da ajali ne ambatacce. Don haka sai ta yi haƙuri kuma ta nemi sakkayar Allaah. (Sahih
Al-Bukhaariy: 1284).
A nan ma bai yi batu a kan nema wa jaririn gafara
ba.
Idan kuma an buƙatu ga yi wa mamacin addu’a a wurin ta’aziyyar domin daɗaɗawa da farantawa
ga iyayensa da sauran makusanta - kamar yadda aka saba - to, sai a maimaita waɗancan addu’o’in da aka yi a wurin sallar jana’izarsa.
Su ma dai babu batun neman gafara ga jaririn a
cikinsu.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad abdullaah Asslafiy
+2348021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.