Tawayen Tabi’ai Da Manyan Malaman Muslunci

    Daga cikin shubuhohin masu rusa Ijma’in Salaf a kan haramcin tawaye wa shugaba fasiki akwai cewa; an samu daga cikin Tabi’ai da manyan Malaman Muslunci sun yi tawaye ma wasu shugabanni a zamaninsu.

    To, a rubutunmu na baya mun tabbatar da cewa; Hussaini (ra), da Abdullahi bn Zubair (ra) ba su yi tawaye ma kowane shugaba ba. Saboda haka a dunkule za a ce: babu Sahabin da ya yi tawaye ma wani shugaba. Don haka ya zama cewa; Sahabbai sun yi Ijma’i a kan rashin yin tawaye wa shugaba fasiki azzalumi. Kuma shi ya sa aka ruwaito da yawansu suna inkari ma wanda ya saba wannan Ijma’i, kamar yadda aka gani daga Abdullahi bn Umar (ra), Ibnu Abbas (ra) da sauransu. Shaikhul Islami yana magana a kan tsananin inkarin da Salaf suke yi ma wanda ya saba Ijma’i sai ya ce:

    "إن السلف كان يشتد إنكارهم على من يخالف الإجماع، ويعدونه من أهل الزيغ والضلال، فلو كان ذلك شائعا عندهم لم ينكروه، وكانوا ينكرون عليه إنكارا هم قاطعون به لا يسوغون لأحد أن يدع الإنكار عليه فدل على أن الإجماع عندهم كان مقطوعا به".

    منهاج السنة النبوية (8/ 354)

    Saboda haka inkarin da su Ibnu Umar (ra) suka yi ta yi a kan tawaye wa shugaba shi yake tabbatar da cewa; lallai Ijma’i ne tabbatacce. Don da a ce abu ne da aka samu wasu suna halastawa da ba su tsananta inkari a kai ba.

    Shi ya sa shi Ibnu Umar (ra) bayan ya yi Bai’a wa Yazidu, har tara iyalansa da jama’ar gidansa ya yi, yake musu gargadi mai tsanani a kan warware Bai’ar Yazidu:

    عن نافع، قال: "لما خلع أهل المدينة يزيد بن معاوية، جمع ابن عمر حشمه وولده، فقال: إني سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «ينصب لكل غادر لواء يوم القيامة»، وإنا قد بايعنا هذا الرجل على بيع الله ورسوله، وإني لا أعلم غدرا أعظم من أن يبايع رجل على بيع الله ورسوله ثم ينصب له القتال، وإني لا أعلم أحدا منكم خلعه، ولا بايع في هذا الأمر، إلا كانت الفيصل بيني وبينه".

    صحيح البخاري (9/ 57)

    Saboda haka wannan shi ne irin yadda Sahabbai suke tsananta inkari a kan yin tawaye wa shugaba, saboda hakan saba Ijma’insu ne, saba Ijma’i kuwa bata ne da tabewa.

    To saboda haka ita ma wannar shubuha za mu nazarce ta kamar yadda muka nazarci shubuhar jingina wa Hussain (ra) da Ibnu Zubair (ra) tawaye wa Yazidu.

    Wannar shubuha za mu raba ta kamar haka:

    (1) TAWAYEN MUTANEN MADINA WA YAZIDU

    Masu raya cewa; akwai sabani a mas’alar tawaye wa shugaba, don su rusa Ijma’in Ahlus Sunna a kan haramcin tawaye wa shugaba fasiki, daga cikin hujjojinsu suna raya cewa; ai Tabi’ai a Madina sun yi tawaye wa Yazidu, a “وقعة الحرة. Don haka suke ganin wannan hujja ne da za ta warware Ijma’in Salaf Ahlus Sunna a kan haramcin tawaye wa shugaba fasiki.

    To sai dai wannar shubuha ce ba hujja ba, saboda abubuwa kamar haka:

    1- Mun tabbatar a baya - a game da tawayen da ake jingina wa Hussain (ra) da Ibnu Zubair (ra) - cewa; mutane a Makka da Madina da ma Hijaz, har Iraqi ba su hadu a karkashin mulkin Yazidu ba. Ba su yi masa Bai’a sun yarda da Mulkinsa ba. Saboda haka abin da ya faru da manyan Tabi’ai a Madina ba sunansa Tawaye ba, sunansa fitina, kamar yadda bayani ya gabata a baya, a magana game da fitinar Ibnu Zubair (ra). Don haka asali mutanen Madina mafi yawansu ba su yi Bai’a wa Yazidu ba. Ibnu Taimiyya yana magana a kan Yazidu sai ya ce:

    "وأما ما فعله بأهل الحرة، فإنهم لما خلعوه وأخرجوا نوابه وعشيرته، أرسل إليهم مرة بعد مرة يطلب الطاعة، فامتنعوا، فأرسل إليهم مسلم بن عقبة المري، وأمره إذا ظهر عليهم أن يبيح المدينة ثلاثة أيام".

    منهاج السنة النبوية (4/ 575)

    Su mutanen Madina wa Ibnu Zubair (ra) suka yi Bai’a:

    "وعلا أمر ابن الزبير بمكة، وكاتبه أهل المدينة، وقال الناس: أما إذ هلك الحسين ع فليس أحد ينازع ابن الزبير".

    تاريخ الطبري (5/ 475)، البداية والنهاية ط هجر (11/ 599)

    Saboda haka asali ba za a ce mutanen Madina sun yi Tawaye wa Yazidu ba.

    2- Idan kuma akwai wadanda suka yi Bai’a a karon farko daga cikinsu, amma daga baya suka warware Bai’ar. Kuma ko da an samu wadanda suka warware Bai’ar, to sabawarsu ga Ijma’in Sahabbai abin zargi ne, ba zai taba zama hujja ba, don saba Ijma’i abin zargi ne, bata ne da tabewa, kamar yadda ya gabata daga Ibnu Taimiyya, da kuma yadda yake a Littatafan “Usulul Fiqh”, inda suke bayanin hukuncin wanda ya saba Ijma’i.

    (2) TAWAYEN MANYAN MALAMAI A FITINAR IBNUL ASH’ATH:

    1- Amma manyan Malamai da suka shiga cikin fitinar Abdurrahman bn al-Ash’ath, suka yi tawaye wa Abdulmalik bn Marwan, wannan ma ba hujja ba ne, saboda Ijma’in Sahabbai ya gabaci tawayen nasu, ba za a yi la’akari da sabanin nasu ba. Don haka sabaninsu ba zai warware Ijma’in Sahabbai ba.

    2- Kuma bayan haka, hasali ma sun yi nadama sun tuba. Ibnu Sa’ad ya ruwaito ya ce:

    أخبرنا سليمان بن حرب قال: حدثنا حماد بن زيد قال: ذكر أيوب القراء الذين خرجوا مع ابن الأشعث، فقال: «لا أعلم أحدا منهم قتل إلا قد رغب له عن مصرعه، ولا نجا فلم يقتل إلا قد ندم على ما كان منه»...

    قال: أخبرنا عفان بن مسلم، وسليمان بن حرب قالا: حدثنا حماد بن زيد، عن أيوب، عن أبي قلابة أن مسلم بن يسار صحبه إلى مكة قال: فقال لي وذكر الفتنة: «إني أحمد الله إليك أني لم أرم فيها بسهم، ولم أطعن فيها برمح، ولم أضرب فيها بسيف» قال: قلت له: يا أبا عبد الله، فكيف بمن رآك واقفا في الصف؟ فقال: «هذا مسلم بن يسار، والله ما وقفت هذا الموقف إلا وهو على الحق فتقدم، فقاتل حتى قتل» قال: «فبكى، وبكى حتى تمنيت أني لم أكن قلت له شيئا».

    الطبقات الكبرى ط دار صادر (7/ 188)، المعرفة والتاريخ (2/ 86 - 87)، تاريخ دمشق لابن عساكر (58/ 146 - 147)

    Khalifa bn Khayyad ma ya ruwaito ya ce:

    حدثني عبد الرحمن قال نا حماد عن أيوب قال: "ما صرع مع ابن الأشعث أحد إلا رغب له عن مصرعه، ولا نجا منهم أحد إلا حمد الله الذي سلم".

    وحدثت عن محمد بن طلحة قال رآني زبيد مع العلاء بن عبد الكريم ونحن نضحك فقال لو شهدت الجماجم ما ضحكت ولوددت أن يدي أو قال يميني قطعت من العضد وأني لم أكن شهدت"...

    قال الأصمعي وحدثني عثمان الشحام قال لما أتى الحجاج بالشعبي عاتبه فقال الشعبي: "أجدب بنا الجناب، وأحزن بنا المنزل، واستحلسنا الخوف، وخبطتنا فتنة، لم نكن فيها بررة أتقياء، ولا فجرة أقوياء". فقال له: "لله أبوك".

    تاريخ خليفة بن خياط (ص: 287 - 288)

    Wadannan su ne wadanda suka yi Tawaye, alhali sabawarsu ba hujja ba ce, saboda abubuwa guda biyu:

    (1) Ijma’in Sahabbai ya rigayi sabawar tasu, don haka ya zama saba wa Ijma’i. Don haka ba sabawa ne abin lura ba.

    (2) An ruwaito nadamarsu da tubansu.

    A takaice, wadannan su ne manyan shubuhohin masu rushe Ijma’in Salaf Ahlus Sunna, a kan haramcin tawaye wa shugabanni, inda suke raya cewa; -wai- an samu sabani, don haka ba za a zargi wanda ya yi tawaye wa shugaba fasiki ba. Kuma wannan sabani shi zai ba da dama ma wanda yake ganin halascin tawaye shi ma ya yi tawayen.

    To cikin abin da ya gabata mun tabbatar da cewa; lallai babu Sahabin da ya yi Tawaye wa shugaba fasiki. Hussaini (ra) bai yi tawaye ba, Ibnu Zubair (ra) bai tawaye ba, haka sauran Sahabban da suke tare da su.

    Haka kuma su ma mutanen Madina ba su yi tawaye ba. Wadanda kuwa suka yi tawayen - wato mutanen Ibnul Ash'ath, da ire-irensu - sabawarsu ba abin lura ba ce, ba zai warware Ijma’in Sahabbai da ya gabaci sabawar tasu ba.

    Kuma ko da an yi sabanin, ta yaya mujarradin sabani ya zama dalilin halasta aiki?!

    Ai mujarradin sabani ba dalili ba ne, kuma ba kowane sabani ne yake abin lura ba, musamman a wannar mas’ala ta Akida, wacce Hadisai masu yawa sun zo a kan hani ga tawaye wa shugaba. Imam al-Shadibiy yana tsoratarwa a kan bin sabani bisa son rai, sai ya ce:

    "وقد زاد هذا الأمر على قدر الكفاية؛ حتى صار الخلاف في المسائل معدودا في حجج الإباحة، ووقع فيما تقدم وتأخر من الزمان الاعتماد في جواز الفعل على كونه مختلفا فيه بين أهل العلم، لا بمعنى مراعاة الخلاف؛ فإن له نظرا آخر، بل في غير ذلك، فربما وقع الإفتاء في المسألة بالمنع؛ فيقال: لم تمنع والمسألة مختلف فيها، فيجعل الخلاف حجة في الجواز لمجرد كونها مختلفا فيها، لا لدليل يدل على صحة مذهب الجواز، ولا لتقليد من هو أولى بالتقليد من القائل بالمنع، وهو عين الخطأ على الشريعة، حيث جعل ما ليس بمعتمد متعمدا، وما ليس بحجة حجة".

    الموافقات (5/ 92 - 93)

    Saboda haka da wannan za ka tabbatar da cewa; Ijma’in Salaf Ahlus Sunna a kan Haramcin Tawaye wa Shugaba Fasiki yana nan daram, saboda sabanin da ake rayawa daga wasu Sahabbai bai tabbata ba. Sabanin da aka ruwaito daga wasu Tabi’ai da Malamai kuwa, shi ma bisa ka’ida bai tabbata ba, saboda an ruwaito Taraju’insu. Kai, ko da ba su yi Taraju’i ba, sabanin nasu ba abin lura ba ne, saboda sabani bayan Ijma’in Sahabbai ba shi da wani amfani.

    Allah ya shiryi masu rusa Akidar Ahlus Sunna da Ijma’in Salaf.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.