Tsoron Zama Da Kishiya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Slm. Malam Inada tambaya Dan Allah. shin mata zata iya addu’a Allah ya ciremata kishin mijinta. Cewa aure mijinta yake son ya kara. Kokuma addu’a kan Allah yabata ikon bayan dukkanin bukatar mijinta batareda ya karo auren ba? Shin zata iya? Toh kaji. Tunda Allah Mai iko ne kan lamuran bayinsa?

    Tsoron Zama Da Kishiya

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa’alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    To da farko dai yakamata ta san da cewar kishiya tana iya zama sharri hakama tana iya zama alkhairi.

    Tana iya zama sharri ne yayinda ta zamo barazana a zaman auratayya da kuma silar shigar abokiyar zamanta wuta kokuma mijin nata.

    A ɗaya bangaren kuma tana zama alkhairi yayinda ta kawo haɗin kai da zaman lafiya wa zaman auratayyar sannan kuma tazam silar shigar abokiyar zamanta Aljannah dakuma mijinta.

    Bawai laifi bane yin kishi to amman kishi ya rabu kaso 2, akwai kishi wanda addini ya halatta, akwai kuma kishi wanda mutum yake biyewa son zuciyarsa.

    Kishi wanda addini ya halatta shine yin kishi yayinda abokiyar zama tayiwa mijinta wani abin kirki ta yadda ke kuma zaki nuna kishi ta hanyar hanzarta yin irin aikin kokuma ma wanda yafi natan.

    Kishin son zuciya kuma, shine wanda mata suke bayyanashi da taimakon shaiɗan, ba abinda shaiɗan yake so samada ya raba hanyar da za’a samu yaɗuwar al’umma musulmai (auratayya kenan), hakan na faruwane yayinda mutum bai amfani da Mujahidatun nafs ba ma’ana yaƙi da son rai.

    Fargabar kada wata macen daga waje tazo ta mallake zuciyar miji ko kuma dukiyarsa ne yasa mata suke asiri don haukata wadda miji zai auro kokuma a mallake mijin sai abinda akace masa, wanda kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Yace "Duk wanda yaje wajen boka kuma ya gasgata zancensa to ya kafircewa abinda aka saukarwa da Muhammadu (Sallallahu alaihi Wasallam), kuma sai anyi kwana 40 a jere ba’a amsar sallar mutum",

     

    Alhamdulillah da ya zamana addu’a kike buƙata bawai sihiri ba, hakan ya nuna kinada Imani akasin wasu, Ko kin tuna abinda ɗaya daga cikin matan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam tace masa kafin ya aureta? Bayan mutuwar tsohon mijinta sai tayi tunanin bazata kara samun wani miji nagari samada shi ba, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam koyarda:

    اللَّهُمَّ أجُرْنِي فِي مُصِيْبَتي وأخْلِفْ لِي خَيْراً مِنْهَا

    Ta lazumci addu’ar a karshe sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da kansa ya tura neman aurenta. Bayan ta dan ja aji (irin na mata) saitace "Ya Rasulullah gaskiya ni macece mai kishi sosai " Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Yace zan roƙa miki Allah ya rage miki kishin naki. To kema anan ga amsarki ta fito, ki roƙi Allah akan ya rage miki kishi, ki dinga yawan sadaka dakuma yawan nafilfili da daddare tareda roƙon Allah yasa idan alkhairi ce a gareki da shi mijin tazo a zauna a samu nasarar cin jarrabawar shiga Aljannah wadda sai anbi Mijin sannan za’a samu, amma fa da wahala amman idan aka sa kai da addua za’a ga sauƙi.

    Sannan ki roƙi Allah akan indai ba alkhairi bace ya sa Mijin ya fasa auren gaba ɗaya, Allah Sami’un Basir ne "Mai Ji kuma Mai Gani" kuma Maji roƙon bawanSa ne, don haka kada kiyi wani kokwanto domin kuwa yafi kowa sanin daidai, idan zakiyi roƙon ki fara da:

    ▪️لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِالله

    ▪️حَسْبُنَا اللَّهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ

    ▪️يَا حَىُّ يَا قَيُّومُ

    ▪️لَّآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنتَ سُبْحَٰنَكَ إِنِّى كُنتُ مِنَ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Sai kawai ki roƙi duk abinda kike so.

    Target ɗin kowa dai shine samun Aljannah a sanadin zaman auratayya, to ki roƙi Allah akan indai zata zama silar shigarki da mijin to maraba akasin hakan wuta kenan to Allah yasa kada tazo.

    Wannan shine shawarar dazan iya baki, ina miki fatan nasara a rayuwar auratayya da kuma haƙurin jarrabawar zaman duniya.

    WALLAHU A’ALAM

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.