Wane Lokaci Ne Mutum Ya Kamata Ya Kusanci Iyalisa A Cikin Wata?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Malam dan Allah wane lokaci ne mutum ya kamata ya kusanci iyalisa a cikin wata, saboda wayensu na nuna cewa: 1 ga wata 15 ga wata bai kamata a kusance su ba. meye karin bayani?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa’alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

    Wannan zancen ba gaskiya bane, cewa ba’a kusantar iyali a farkon wata ko karshen wata. Bamu samu wani zance ingantacce ba da yake nuni da hani akan saduwa da iyali a farkon wata ko karshen sa. Kuma bamu san wani hadisi ba da yazo lafazin hani a hakan.

    Ya halasta miji ya sadu da matarsa a kowane irin lokaci bukatar hakan ya taso. Amma haramun ne Miji ya sadu da matarsa a lokacin da ɗayansu (Miji ko Mata) yake cikin ihraam na aikin hajji ko Umrah, ko kuma ɗayansu yana azumi da rana, amma zasu iya saduwa da dare bayan sun buɗa baki. Haka kuma haramun ne Miji ya sadu da matarsa a lokacin da take cikin haila har sai ta samu tsarki tayi wanka. Haka kuma haramun ne saduwa da mace idan tana cikin jinin Nifaas. Bayan waɗannan lokuta, toh babu wani lokacin da aka hana saduwar ma’aurata matuqar suna lafiya kalau.

    WALLAHU A’ALAM.

     Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.