Wasiyya Mai Tsada Daga Ibnu Mas'ud (RA)

    Aliyu bn Ja'ad da Abu Nu'aim sun ruwaito:

    عن عبد الرحمن بن عبد الله بن مسعود، عن أبيه قال: أتاه رجل، فقال له: يا أبا عبد الرحمن علمني كلمات جوامع نوافع قال:

    «اعبد الله ولا تشرك به شيئا، وزل مع القرآن حيث زال، ومن جاءك بالحق فاقبل منه، وإن كان بعيدا قصيا، ومن جاءك بالباطل فاردده، وإن كان قريبا حبيبا».

    مسند ابن الجعد (ص: 326)، حلية الأولياء (1/ 134)

    Daga Abdurrahman bn Abdullahi bn Mas'ud (ra) daga Babansa ya ce: Wani mutum ya zo masa sai ya ce: Ya Baban Abdurrahman, ka koyar da ni wasu kalmomi wadanda suka tattara manyan ma'anoni masu amfani, sai ya ce:

    ((Ka bauta ma Allah kar ka yi masa shirka, ka gusa tare da Alkur'ani duk inda ya gusa, duk wanda ya zo maka da gaskiya to ka karba daga gare shi, ko da kuwa ya kasance a nesa da kai sosai. Haka duk wanda ya zo maka da karya ka jefar da ita ko da kuwa ya kasance makusacinka ne masoyi)).

    A nan Sahabin Annabi Ibnu Mas'ud (ra) yana umurni ne da Tauhidi da nisantar Shirka, da riko da Alkur'ani da binsa, da kuma karban gaskiya daga kowa, da jefar da karya daga kowa.

    Alal hakika wannar magana fadakarwa ce a kan abubuwa masu girma sosai. Abin da kalma ta karshe ta kunsa fadakarwa ne ga abin da muka wayi gari a cikinsa a yau, na ta'assubanci da kungiyanci, ta yadda mutane da yawa ba sa karban gaskiya daga abokan sabaninsu ko abokan husuma, kuma suke yarda da karyar da ta zo daga wadanda suke kan kungiya daya da fahimta daya, da kokarin ba ta kariya ido rufe.

    Alal hakika duk wanda yake neman tsira zai yi riko da wadannan kalmomi, ya yi aiki da su yadda ya kamata.

    ✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani

    Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.