𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum. Malam ina wuni? Yaya iyali? ALLAH YA kara maka lfy da nisan kwana, amin. Malam don ALLAH ya halatta wai mace ta yi taimama saboda an ɗaura mata lalle a hannu da kafa kuma a tsakanin salloli guda 2 ? Lalle irin na zamanin nan da ake yanka cellotape ɗin nan (gam). Wasu matan na cewa ai lalle ma sunnah ne. Sai su dinga barin lokutan sallah (farilla) na wuce su. Wasu kuma sukan haɗa salloli ba don komai ba, sai don wai su bari lallen nasu ya kama sosai.
Kuma ya halatta ta yi sallah a zaune in tana da
alwala saboda lallen?
Ya
Halatta Mace Ta Yi Taimama Saboda An Ɗaura Mata Lalle?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu
Ɗaura lalle ko wani nau’in ado, ba ya cikin uzurarrukan dake halasta wa
mutum yin taimama. Idan mace tayi taimama saboda wannan dalilin kuma tayi
sallah ahaka, gaskiya sallarta batayi ba. Wajibi ne taje tayi alwala ta sake
sallar.
Hakanan yin
sallah azaune saboda wannan dalilin shima bai halatta ba. Yin sallah azaune ta
majinyata ne waɗanda bazasu iya
yinta atsaye chak, ko kuma atsaye tare da jingino ba. Amma lafiyayyen mutum
idan yayi sallar farilla daga zaune, sallar batayi ba. Wajibi ne asake wannan
sallar tare da yin istighfari wato neman gafarar Allah saboda wannan gangancin
da akayi.
Haɗe salloli biyu
mabambanta wannan haramun ne. Babu wani uzurin da zai sa mutum yayi haka. Amma
idan akwai karbabben uzuri a shari’ance, ya halatta mutum ya haɗe azahar da la’asar, ko Magriba da isha’i.
Halastattun uzurarrukan nan sun haɗa da tafiya wato balaguro, sai jinya, ko ruwan sama, ko
kuma wani aiki daga ayyukan alkhairi waɗanda addini yake
umurni da yinsu. Misali kamar yin sulhu atsakanin wasu mutane waɗanda idan ka kyalesu ka tafi yin sallar, zasu iya watsewa
ba tare da cimma maslaha ba, to ya halatta ka tsaya ka sulhuntasu sannan kaje
kayi azahar ɗinka, koda ta shiga
lokacin la’asar babu komai. Saboda hadisin da aka ruwaito cewa Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam yaje yin sulhu atsakanin wasu mutanen madeena (Banu
Amr bn Auf) har lokacin la’asar ya shiga.
Amma jinkirta sallah bisa dalilin wani ado (make
up) ko lalle, wannan haramun ne kuma wasa da addini ne.
Allah (SWT) ya faɗa acikin suratu Maryam ayah ta 59:
فَخَلَفَ مِن بَعْدِهِمْ خَلْفٌ أَضَاعُوا الصَّلَاةَ وَاتَّبَعُوا
الشَّهَوَاتِ فَسَوْفَ يَلْقَوْنَ غَيًّا
"SAI WASU MUTANE SUKA MAYE GURBINSU WAƊANDA KE TOZARTAR DA
SALLAH KUMA SUKE BIYEWA SHA’AWOYI, DA SANNU ZASU HAƊU DA ASARA (MAI GIRMA)".
Abdullahi bn Mas’ud yace "GAYYU" sunan
wani rami ne mai mutukar zurfi, kuma mai mummunan wari, acikin wutar jahannama
acikinsa ne ake azabtar da masu wulakantar da sallolinsu.
Ƙataadah yace "Rami ne acikin wutar jahannama wanda ke kunshe da jini
da ruwan gyambo na ‘yan wuta (acikinsa za’a jefa masu haɗe salloli da gangan don son zuciya da lalaci).
Ibnu Jareer ya ruwaito hadisi ta hanyar Abu Umamah
cewar yaji daga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam makamancin haka.
Sa’eed ibnul Musayyab yace "Sune mutanen dake
jinkirta sallar azahar har sai lokacin la’asar ya shiga, ko su jinkirta magriba
har sai lokacin isha’i yayi. Ko su jinkirta sallar isha’i sai da asubahi ko su
jinkirta asubah har zuwa fitowar rana. Sune wadanda Allah yace zai jefasu
acikin gayyu (matattarar jini da ‘diwa da ruwan gyambon ‘yan wuta)".
Sa’ad bn Abi Waƙƙas yace "Na tambayi Manzon Allah Sallallahu
alaihi Wasallam game da ayar nan ta cikin Suratul Ma’un inda Allah yake cewa:
فَوَيْلٌ لِّلْمُصَلِّينَ الَّذِينَ هُمْ عَن صَلَاتِهِمْ
سَاهُونَ
"WAILUN (WATO RAMIN AZABA) YA TABBATA GA
MASU SALLAH, WAƊANDA KE RAFKANUWA GA BARIN SALLARSU".
Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yace
"Ma’anar wannan shine Jinkirtar da sallah daga kan lokutanta.
Allah shi kiyayemu daga afkawa azaba. Allah shi
hanar damu baki ɗaya, ya karbi
tubanmu Ameen.
WALLAHU A’ALAM.
DAGA ZAUREN FIƘHU 07064213990
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.