Ya Kwanta Da Matarsa Amman Bai...

    Ya Kwanta Da Matarsa Amman Bai...

    TAMBAYA (178)

    Assalamu alaykum malam tambayata miye hukuncin namiji da matarsa sunka konta a shinfida guda1 batarada sunyi mu amala ta aureba namiji yadau zakarinsa yahau saman farjin matarsa ba tare da yasaka acikin farJinta ba chin zasuyi wanka ko bazasuyiba

    AMSA

    Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

    Indai har ya shigeta to wanka ya wajaba akansa ko da ace baiyi releasing ba maana ko da ace bai kawo maniyyi ba indai har kaciyarsa ta buya a farjinta to wanka ya zama dole a gareshi

    Kamar yanda hadisin ya tabbata a cikin Musnad na Imam Ahmad Bin Hanbal da Kuma Sahih Muslim 526

    Haka Kuma an rawaito Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace: "Ruwa ya tabbata idan aka samu ruwa" ma’ana: Idan aka fitarda maniyyi to wanka ya wajaba

    Muslim 1/269 da Kuma Imam al-Baghawy a cikin Sharh al-Sunnah (2/9)

    Wadannan tambayoyin suna daga cikin dalilan da yasa muka bude sabuwar makarantar MU’AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI, wanda Online muke karatun a duk daren Lahadi, kenan kana daga gida zaka dinga karatun a wayarka cikin sauƙi

    A yanzu haka muna darasi na8️. Wanda yake da ra’ayi ko kuma yaji labarin wadanda aka saka musu rana (Engagement) to zai iya tallata musu. Dama ce ga Gwauraye, Tuzurai, Zaurawa, Masu Niyya da Kuma Ma’aurata. Mai ra’ayi sai yayimin magana ta priɓate a turo masa dokokin shiga

    (07035387476)

    Wallahu taala aalam

     Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    WALLAHU A'ALAM.

    https://t.me/TambayaDaAnsa

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.