Sau da yawa mukan yi zaton cewa; ‘yan bidi’a halakakku ne, kawai da gangan suka saba ma Annabi (saw). A’a, ba haka abin yake ba, a cikinsu akwai wadanda suka nufi bin Annabi (saw); wato bin Alkur’ani da Sunna, amma sai suka kuskure, imma saboda jahilci ko rashin fahimtar Nassi ko shubha ko tawili da kuskure a Ijtihadi, ko wani sababin daban.
Shaikhul Islami ya yi cikakken bayani, inda ya ce:
فالبدع نوعان: نوع كان قصد أهلها متابعة النص والرسول، لكن غلطوا
في فهم النصوص، وكذبوا بما يخالف ظنهم من الحديث ومعاني الآيات؛ كالخوارج، وكذلك الشيعة
المسلمين، بخلاف من كان منافقا زنديقا يظهر التشيع، وهو في الباطن لا يعتقد الإسلام.
وكذلك المرجئة قصدوا اتباع الأمر والنهي، وتصديق الوعيد مع الوعد...
وأما الجهمية النافية للصفات، فلم يكن أصل دينهم اتباع الكتاب
والرسول؛ فإنه ليس في الكتاب والسنة نص واحد يدل على قولهم، بل نصوص الكتاب والسنة
متظاهرة بخلاف قولهم، وإنما يدعون التمسك بالرأي المعقول.
النبوات لابن تيمية (1/ 423 - 424)
"Bidi’o’i nau’i biyu ne; akwai nau’in da
manufar ma’abotansa shi ne Bin Nassin (Alkur’ani) da Bin Manzon Allah (saw),
amma sai dai sun yi kuskure wajen fahimtar Nassoshin, sai suka karyata abin da
ya saba ma zatonsu na Hadisai da ma’anonin Ayoyin Alkur’ani. Su ne kamar
Khawarijawa, da ‘Yan Shi’a Musulmai, sabanin wanda ya kasance Munafuki Zindiki
a cikinsu (Rafidha), wanda ya fake da shi’anci, alhali a cikin zuciyarsa bai
yarda da Addinin Muslunci ba.
Haka kuma Murji’a, su ma sun nufi bin umurnin
Allah da haninsa ne, da gaskata wa’adi da wa’eedi...
Amma Jahamiyya kam (ma’abota bidi’a nau’i ta
biyu), wadanda suke kore dukkan siffofin Allah, su asalin Addininsu ba su yi
nufin bin Alkur’ani da Manzon Allah (saw) ba. Wannan ya sa babu Nassi guda daya
a cikin Alkur’ani da Sunna da yake nuni ga ra’ayinsu. Kai, Nassoshin Alkur’ani
da Sunna masu yawa sun saba ma ra’ayoyinsu. Da ma su sun ce: hankali da ra’ayi
kawai suka rika".
Saboda haka, ba dadai ba ne ka dauka cewa; duk
wani dan bidi’a halakakke ne mai bin son zuciya, wanda ya nufi saba Alkur’ani
da Sunna.
Kuma a cikin wannan akwai raddi ga ‘Yan Kungiyar
Salafiyyun masu guluwwi a bidi’antarwa, ko masu guluwwi a mu’amala da hukunci
ga ‘yan bidi’a.
✍️ Dr Aliyu Muh’d Sani (H)
14 October, 2018
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.