TAMBAYA (179)❓
Assalama alaikum barka da warhaka malam Allah saka
da alkhairi ameeen
Wata makociyata taɗomin da wata mgn daɗu nace ɗanyi tanbaya
Su 2 ne agun mijin tou tunkawo amarya ran aikin
amarya sai yaɗiwa uwargidan da bukatar
ɗai kwanta da ita sai taki tace bace a ah itakan yabari
sai kwananta yaɗo sun sha fada
dashi akan haka ammah takiyi
Tou yanɗu sai ran kwanan
uwar gida kuma yaje gun amarya tasha fita ran girkinta uwar gida sai ta iskeshi
dakin amarya har gidansu taje ita uwar gida akan haka ammah yaki Dena wa Don
ita amaryar in yaje gunta ran girkin uwar gida taba hanashi kanta
Yabin yadami uwar gida har yanɗu itama inya ɗo mata ran kwanan amarya itama tafara yada dashi tabar korarsa tou tanbaya anan ɗasu iya ci gaba dahan ko dai tadena yada dashi in ba ran girkintaba. Don Allah muna neman mafita Allah sah mudace ameeen
Yana Kwana A Dakin Kishiyata Alhalin Ba Ranar Kwananta Ba Ne Ba
AMSA❗
Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu
Ya halatta miji ya shiga dakin matarsa yayi mu’amalar
auratayya da ita ko da ace baa dakin nata yake ba domin kuwa na farko dai matar
shi ce
Domin kuwa munada hadisi cikin Sahihul Bukhari
wanda aka rawaito cewar Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya kasance watarana
ya kwana a dakin Hafsat Bintu Umar (Radiyallahu anha) lokacin da ta tafi anguwa
sai Annabi ya kira Mariya (Radiyallahu anha) ya kwanta da ita a kan gadon
Hafsat
Lokacin da Nana Hafsat ta dawo ta fahimci abinda
ya faru sai tayi ta bata rai, har sai da Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya
bata haƙuri yace na haramtawa
kaina Mariya (Dayake daman ita Mariya baiwa ce). Nana Hafsat taji dadin wannan
mataki da ya dauka takaiwa Nana Aisha rahoto sukaita jin dadi, nan take Allaah
(Subhanahu wata’ala) ya saukar da ayar:
( يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ لِمَ تُحَرِّمُ مَا أَحَلَّ اللَّهُ
لَكَ ۖ تَبْتَغِي مَرْضَاتَ أَزْوَاجِكَ ۚ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ )
التحريم (1) At-Tahrim
Yã kai Annabi! Don me kake haramta abin da Allah
Ya halatta maka, kanã nẽman yardar mãtanka, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
Daganan sai Annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
yayi kaffarar wannan rantsuwar domin cika umarnin Allaah Azzawajallah inda
yace:
( قَدْ فَرَضَ اللَّهُ لَكُمْ تَحِلَّةَ أَيْمَانِكُمْ ۚ وَاللَّهُ
مَوْلَاكُمْ ۖ وَهُوَ الْعَلِيمُ الْحَكِيمُ )
التحريم (2) At-Tahrim
Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima.
Allaah Azzawajallah ya bamu labarin abinda ya faru
ƙarara Kamar haka:
( وَإِذْ أَسَرَّ النَّبِيُّ إِلَىٰ بَعْضِ أَزْوَاجِهِ حَدِيثًا
فَلَمَّا نَبَّأَتْ بِهِ وَأَظْهَرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ عَرَّفَ بَعْضَهُ وَأَعْرَضَ
عَن بَعْضٍ ۖ فَلَمَّا نَبَّأَهَا بِهِ قَالَتْ مَنْ أَنبَأَكَ هَٰذَا ۖ قَالَ نَبَّأَنِيَ
الْعَلِيمُ الْخَبِيرُ )
التحريم (3) At-Tahrim
Kuma a sã’ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri
zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya
bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani
sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: "Wãne ne ya gaya
maka wannan?" Ya ce: "Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini."
Daganan sai Allaah Azzawajallah ya ce musu (Hafsat
da Aisha - Radiyallahu anhum):
( إِن تَتُوبَا إِلَى اللَّهِ فَقَدْ صَغَتْ قُلُوبُكُمَا ۖ وَإِن
تَظَاهَرَا عَلَيْهِ فَإِنَّ اللَّهَ هُوَ مَوْلَاهُ وَجِبْرِيلُ وَصَالِحُ الْمُؤْمِنِينَ
ۖ وَالْمَلَائِكَةُ بَعْدَ ذَٰلِكَ ظَهِيرٌ )
التحريم (4) At-Tahrim
Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã’iku a bãyan wancan, mataimaka ne.
( عَسَىٰ رَبُّهُ إِن طَلَّقَكُنَّ أَن يُبْدِلَهُ أَزْوَاجًا
خَيْرًا مِّنكُنَّ مُسْلِمَاتٍ مُّؤْمِنَاتٍ قَانِتَاتٍ تَائِبَاتٍ عَابِدَاتٍ سَائِحَاتٍ
ثَيِّبَاتٍ وَأَبْكَارًا )
التحريم (5) At-Tahrim
Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya
musanya masa waɗansu mãtan aure
mafiya alhẽri daga gare ku,
Musulmai mũminai mãsu tawãli’u, mãsu tũba, mãsu ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da
‘yammãta.
Sai Kuma gargadi ya biyo baya:
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا قُوا أَنفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ
نَارًا وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ عَلَيْهَا مَلَائِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ
لَّا يَعْصُونَ اللَّهَ مَا أَمَرَهُمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ )
التحريم (6) At-Tahrim
Yã kũ waɗanda suka yi
ĩmãni! Ku kãre wa kanku (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu
ne. A kanta akwai waɗansu malã’iku
mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin
da ake umunin su
Wannan kenan
Haka Kuma dai ya tabbata cewar Sunnah ce mai karfi
Miji ya kwana 7 a dakin amarya daga ranar da ya auro ta ita Kuma bazawara kwana
3 ne
Don haka anan abinda aka fi so shine, bayan sati
guda dincan Mijin ya Kamanta Adalci idan ya kwana daya a dakin uwargida to sai
ya kwana 1 a dakin amarya don gudun jayayya wanda ka iya haifar da gaba a
tsakaninsu
Idan kuma amarya ta tafi anguwane kuma sunyi dashi
zata kwana can kuma sai wani dalilin yasa ta dawo to amaryar zata haƙura ne da wannan daren
tunda baa yi tunanin dawowarta ba. Haka kuma idan akasamu akasi ya kwana a
dakin amarya sai kuma ya bayya na ba ranar girkin ta ba ne to ya kamata yayi
adalci ya biya uwargida kwanan da aka sadaukarwa da amaryar
Don haka idan miji ya kwana a dakin wadda yaga
dama to anan wata Sunnah ce ta musamman ya raya. Saidai Kuma baace ya wuce
makadi da rawa ba. Yace zai fifita amarya akan uwargida domin kuwa ana jiye
masa tsoron kada ranar Lahira ya tashi da cutar barin jiki (Paralyzed) saboda
rashin adalcin da yake nunawa a tsakaninsu
Irin wadannan matsalolin duk mun wuce babinsu a
cikin karatun da muke ONLINE a sabuwar MU’AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI. Ga
wanda yake son shiga zai iya yimin magana ta Priɓate sai a turo masa dokoki da tsare tsaren makarantar
(07035387476)
Wallahu taala aalam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla’ilaha
illa anta astaghfiruka wa’atubi ilayk
Amsawa:
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur’ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.