Barkwanci...
Ka yi budurwa 2, a ce maka mayaudari.
Ta yi samari 10, a ce mata mai farin jini.
Wai babu hukumar kare haƙƙin maza ne? 🤷♂️
Barkwanci...
Mijinta a fusace ya ce: "Ki tattara duk wani abin da
mallakinki ne, ki fice daga wannan gidan."
Matar ta suntume shi a kafaɗa
ta yi waje. 🤓
Barkwanci...
Abokinmu ya koka mana cewa matarsa ta raina shi, kuma tana
masa rashin mutunci iri-iri.
Mun je mata nasiha kawai ta zubo mana ɗanwake. Muka kalle shi muka
ce: "Ba ka da gaskiya." 🤓
Barkwanci...
Duk sun rikita ƙasar! Ɗazu wani tsoho 👨🏽🦳
yake faɗa mini cewa
idan ya girma yana so ya zama lauya.
Barkwanci...
Kai adashe ɗaukar
farkon duniya ce. Na ba da 2k, an ba ni 50k. 😳
Ni kam na fita ma. 😎 Allah ya sa su kammala
lafiya. 🙏
Barkwanci...
Misalin karin magana mai "wai" da
"inji": "Da sauran aiki a gabana, wai Tulumbu ya ga talaka da
tumbi." 🫃
Barkwanci...
Waɗanda
za su sake mining Hamster Season 2, tabbas za su iya zaɓen Tulumbu a 2027. 👨🏽🦳🏃♂️
Barkwanci...
Tun da ka ga MTN, Airtel, GLO da bankuna ba su tura wa
mutane "happy independence" ba, kai ka san akwai matsala a ƙasar
nan.
Jokes...
9ja Wahala!
A professor of 'Peace and Conflict Resolution' divorced his
wife yesterday. 😳😳
Barkwanci...
A wane mataki ka/kike?
1. Shegen mai kuɗi
(500m zuwa sama)
2. Mai arziki (100 - 500m)
3. Mai kuɗi
(20m - 100m)
4. Kwanciyar hankali (1m - 20m)
5. Talaka (100k - 900k)
6. Ba sauƙi (50k - 100k)
7. Akwai Allah (10k - 50k)
8. Mun gode Allah (5k - 10k)
9. Kai jama'a! (500 - 1k)
10. Hayya-hayya (10 - 50)
Jokes...
Book of Relationship, chapter 81 verse 64 says: "He who finds a girlfriend in Africa has adopted an orphan." 😅🤭
Barkwanci...
A faɗa wa NEPA 💡🔦 ba mu mutu ba. Har yanzu muna nan ɓulɓul. 😒😏
Barkwanci...
SA: "Jagaban, 'yan Lanjeriya fa sun cika intanet da
zancen yaran nan."
T-Pain: "Lallai a hana kowa caji yau." 🔌🔌
SA: "Okay, Sir!"... "Hello, gidan
wuta..." 💡🔦
Barkwanci...
Ki aure miji ɗan NEPA, daga kin fito a riƙa nuna ki kamar ɓarauniya.
Barkwanci...
Miji ya saya wa matarsa sabon janareta da firjin da pure
water leda 50 sannan ya ba ta 20k ta yi jarin zoɓo
da fresh milk domin sana'a.
Wata rana mijin ya ga littafi an rubuta "Sunayen 'Yan
Bashin Pure Water." Da ya duba, sunansa ne na 3.
Barkwanci...
Wai Bargo ne 30k? 🤔
Ai gwara na cika 20k na auro bazawara ta zo min da shi 🤌😂
Barkwanci...
An kawo amaryar aka yi kuskure aka shiga da ita wani gida na
daban.
Matar gidan yanzu sumarta bakwai. 🤓🤓
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.