Ticker

6/recent/ticker-posts

Diniyar Yau - Abubuwan Mamaki Da Suke Faruwa a Duniya

Duniya tana da faɗi matuƙa. Wannan jerin wasu abubuwan mamaki ne da suka faru ke suke faruwa a duniya a cikin shekarar 2024.

Abubuwan Mamaki Da Suke Faruwa a Duniya

Wasu masana kimiyya suna bincike kan yadda yi wa sararin samaniya allurar ƙurar lu'ulu'u (diamond) zai iya magance ɗumamar yanayi. Matsalar ita ce, aikin zai ci kuɗin da ya kai dalar Amurka tiriliyan ɗari biyu!

Abubuwan Mamaki Da Suke Faruwa a Duniya

 

A Amurka, wata uwa ta kai ƙarar wani AI da waɗanda suka samar da shi bisa tuhumar cewa AI ɗin ne ya yi sanadiyyar ɗanta ya kashe kansa. Har yanzu ba a sanya tsauraran matakai a duniya ba game da AI da kafafen sada zumunta saboda an kasa samun ƙwararan hujjoji game da illolinsu ga al'umma (duk da kuwa akan ci karo da illolin a bayyane lokaci zuwa lokaci).

 Abubuwan Mamaki Da Suke Faruwa a Duniya

Koriya Ta Kudu ta ware dala miliyan 326 domin yaƙar 'kaɗaitaka' (loneliness) da yake janyo ƙaruwar kisan kai a tsakanin al'ummarta. Cigaban zamani da na'urarori suna ƙara janyo kaɗaitaka tsakanin mutane a duniya! Hausawa su gode wa Allah tare da riƙo da abin da ya rage musu na zumunci bisa koyarwar addini da kyawawan al'adu.

 

Bincike ya nuna cewa, sakamakon intanet, kasuwar caca a duniya ta kai $773.7BN. Tallace-tallacen caca suna son haura yawan kowane nau'in talla a kafafen intanet da manhajoji. Bincike ya gano cewa, caca ta yi wa kimanin mutane miliyan 450 illa a duniya. Har ta kai ga kashe kai da mutuwar auratayya da munanan rashin lafiya!

 

China ta tura mutane uku zuwa duniyar wata. Sun kasance mafiya ƙarancin shekaru a waɗanda suka taɓa zuwa a duk duniya. Za su yi watanni shida a can. China da Amurka suna zazzafan gwagwarmayar kasancewa kan gaba wajen fara amfani da albarkatun da suke duniyar sama. Mutane biyu da aka tura duniyar sama daga Amurka a ranar 05/06/2024 sun maƙale a can sakamakon matsalar da jirginsu ya samu. Kamfanin SpaceX yana shirin ɗauko su a Fabarairun 2025.

 

Afirka Ta Kudu tana ƙoƙarin janye waɗansu takunkuman da suka hana binciken kiwon lafiya a fannin sauya ƙwayoyin halittar ɗan'adam. Sauya su zai bayar da damar samar da "Designer Babies", wato yaran da aka tsara ƙwayoyin halittarsu cikin siga ta daban saɓanin gadaddu daga zuriyarsu. Canza ƙwayoyin halitta yana nufin sauya halaye da ɗabi'u da yiwuwar kamuwa ko rashin kamuwa da cututtuka da kuma yanayin jiki da damar iya sabo da muhallai da yanaye-yanayen ɓangarorin duniya.

 

Wata kotun Rasha ta ci tarar kamfanin Google $20,000,000,000,000,000,000,000,000,000,000,000,000 ($20 decillion) wato dalar Amurka desiliyan ashirin. Ya fi jimillar kuɗaɗen da suke duniya gaba ɗaya. Hakan ya biyo bayan kulle wasu tashoshin YouTube masu goyon bayan Rasha da aka yi.

 

Yau farashin Bitcoin ɗaya ya kai kimanin dalar Amurka dubu saba'in da biyar ($75,000). A kuɗin Nijeriya zai kama kimanin miliyan ɗari ɗaya da ashirin da tara da dubu ɗari uku da saba'in da biyar (129,375,000). A shekarar 2010, farashinsa bai fi naira hamsin (50) ba.

 

A 1986 ne NASA ta tura jirgin bincike zuwa duniyar Uranus. Tazarar duniyar daga Earth ta kai kilomita biliyan biyu da milliyan ɗari takwas (2.8b km). Ya isa cikin shekaru tara (9). Ta ƙuduri aniyar sake tura jirgin bincike cikin shekaru goma (10) masu zuwa saboda ya bayyana cewa binciken baya yana da rauni.

 

Akwai kimanin gidaje miliyan tara (9,000,000) waɗanda babu kowa a ciki a Japan. Wasu ƙananan garuruwa sukan jejjera mutum-mutumi (sanye da tufafin mutane) masu yawa a gefen hanya da makarantu da sauran wurare don su kasance tamkar mutane - tsabar rashin al'umma a yankunan.

Post a Comment

0 Comments