Dokokin Shiga Makarantar "Mu'amalar Auratayya a Musulunci"

DOKOKIN SHIGA MAKARANTAR "MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI"

Da akwai dokoki guda 3 ga duk wanda yake son zama halastaccen member na makarantar "MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI":

Maida hankali wajen bibiyar karatun da ake a kowanne daren Lahadi, bayan sallar Isha' (ana iya sauke karatuttukan da akayi Kai tsaye na littafin: "GUIDELINES TO INTIMACY IN ISLAM" ma'ana "MU'AMALAR AURATAYYA A MUSULUNCI" wallafar Shaikh Mufti Abdurrahman Adam Alkauthary, wadanda zamu dinga hadasu da videos na karatuttukan malamai don a kara fahimta). Littafin PDF ne mai dauke da Pages 123

Za ka iya zama member ne kadai ta hanyar yin Registration:

📌KUDIN REGISTRATION: N2,000 (Idan ka bayarda sama da hakan ma zamu karba)

(Ko Kuma Sefa jaka 5 ga maqotan qasashenmu kamar su NIGER)

Mata da miji zasu iya shiga wannan makarantar saboda a gudu tare a tsira tare. Wadanda suke da niyyar aure kuma yanada kyau su sanar da iyayensu batun wannan makarantar kafin su shiga. Saboda abin ya tafi akan tsari sai muka fitarda Class din Maza daban, Class din Mata shima daban

3️Duk qarshen kowanne wata akwai monthly contribution, shi kuma N500 (Idan ka bada sama da hakan za'a karba) a matsayin tuition fees domin da wannan ne zamu dinga kula da kuma gudanar da karatuttukan har a kammala littafin, kamar irinsu saka DATA da dai sauransu

A yanzu haka da akwai wadanda suka bada gudunmawarsu ta shekara daya (Watanni 12), idan mutum ya ga dama zai dinga badawa duk karshen wata, ko ka dunqule ka bayar da na watanni, gwargwadon ikon ka. Ba takurawa. Kuma ko da gudunmawar ko Babu zamu ci gaba da gudanar da karatun, in Sha Allaah

Bayan mun kammala littafin da akwai "CERTIFICATE OF APPRECIATION" wato shaidar cewar ka halarci wannan makaranta, wadda mutum zai je CAFÉ a cire masa a matsayin RECORD

Zaka iya tura gudunmawar ta Opay ko Zenith Bank kamar haka:

Opay/Moneypoint Account;
Usman Danliti
7035387476

Ko

Zenith Bank
Usman Danliti
2118853750

Masu amfani da Sefa Kuma zaku turo zuwa Kano ta NITA: 07035387476

A turo evidence of payment (shaidar an turomin: receipt ko screenshot)

Bayan kayi Registration, hukumar makaranta a shirye take da ta turo maka link wanda za ka yi joining haka kuma idan kana buqata za'a turo maka karatuttukan da suka wuceka

Babbar manufarmu itace mu gyara ibadar da muke musamman ta mu'amalar aure, muyi koyi da Sunnah don rabauta fiddunya wal akhira

Daga fara karatun littafinnan, bansan adadin mutane nawa na zama silar gyaruwar aurensu ba, kaga anan ai an bawa shaidan kunya kam

Muna roqon Allaah ya bamu ikon amfana da ilimin muyi aiki dashi har ma wasu su amfana

Ku sanar da sauran mutane gameda wannan sabon program din ku kafa musu hujja da maganar Uwar Muminai, Nana Aisha (Radiyallahu anha) da tace: "Madallah da matan Madina wadanda kunya bata Hana su yin tambaya gameda addininsu"

Annabi {Sallallahu alaihi wasallam} ya ce: "Idan Allaah Yana son bawa da alkhairi sai ya fahimtar dashi addini"

Bukhari da Muslim

Kamar yanda hukumar wannan makaranta ta tsara: 📌 GAMEDA MONTHLY CONTRIBUTION, N500 ne, idan ka bayarda sama da haka, kyautatawa ce

Jazakumullahu khayr

 ✍️ADMIN: ZAUREN TAMBAYA DA AMSA:
Founder/Proprietor: USMANNOOR ONLINE ACADEMY
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
©️Copyright

Contact School Management through WhatsApp number: 07035387476

Dokokin Shiga Makarantar "Mu'amalar Auratayya a Musulunci"

Post a Comment

0 Comments