𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Idan ƙin bin umurnin iyaye a lokacin da ɗansu ke cikin bautar Allaah zai janyo masa shiga cikin jarrabawa a rayuwa kamar yadda ƙissar Juraiju ta nuna, to ya wajaba ga ɗan kenan ya aiwatar da duk abin da iyayen suka umurce shi da shi, ko da kuwa ya saɓa wa shari’a?
FIƘHUN ƘISSAR JURAIJU
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
[1] Da farko dai ƙissar Juraij sahihiyar ƙissa ce tabbatacciyar a cikin Sahih Al-Bukhaariy
(2482, 3436, 3466) da Sahih Muslim (2550), kuma ta auku ne in ji malamai, a
cikin Bani-Israa’ila bayan
wucewar Annabi Isaa (Alaihis Salaam) kafin zuwan Manzon Allaah Annabi Muhammad
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
Kuma wannan ƙissa ɗaya ce daga cikin
riwayoyin da suke tabbatar da annabtar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam), ta yadda yake bayar da labaran abubuwan da suke gabata alhali bai
halarci zamunan da suka auku ba, bai iya karatu ba balle a ce a wani wuri ne ya
karanto su, sannan kuma a cikin al’ummarsa babu wanda ya san su sai shi kaɗai da Allaah Ta’aala ya sanar da shi.
Sannan kuma wannan riwaya ta tabbatar da ɗaya daga cikin aƙidun da Ahlus-Sunnah Wal-Jamaa’ah su ke a
kansu, cewa: Lallai akwai waliyyan Allaah mai Rahama a cikin al’ummar duniya tun tuni, kuma cewa tabbas Waliyyai suna
karama. Sai dai kuma wannan bai ba su matsayin allantaka ko ubangijintaka ba,
balle har a ba su wani abu na ibadar da Allaah ne kaɗai ya cancance shi.
[2] Malamai da suka yi sharhin wannan hadisi sun
fitar da fa’idojin da ake iya samu daga cikinsa. Al-Haafiz Ibn Hajr al-Asƙalaaniy (Rahimahul Laah)
ya ambaci cewa:
وَفِي الْحَدِيثِ إِيثَارُ إِجَابَةِ الْأُمِّ عَلَى صَلَاةِ
التَّطَوُّعِ، لِأَنَّ الِاسْتِمْرَارَ فِيهَا نَافِلَةٌ وَإِجَابَةُ الْأُمِّ وَبِرُّهَا
وَاجِبٌ
A cikin wannan hadisin akwai muhimmancin fifita
amsa wa mahaifiya a kan sallar nafila. Domin cigaba a cikin sallar nafila ne,
amma amsa wa mahaifiya kuwa da yi mata biyayya wajibi ne.
Har zuwa inda ya ce:
وَالْأَصَحُّ عِنْدَ الشَّافِعِيَّةِ أَنَّ الصَّلَاةَ إِنْ
كَانَتْ نَفْلًا وَعُلِمَ تَأَذِّي الْوَالِدِ بِالتَّرْكِ، وَجَبَتِ الْإِجَابَةُ
وَإِلَّا فَلَا
Mafi ingancin magana a wurin malaman Shafi’iyyah
ita ce: Idan sallar nafila ce kuma ya san cewa mahaifin zai cutu idan bai amsa
ba, to amsawar ta zama wajiba. Idan kuma ba haka ba, to ba haka ba.
Sannan kuma ya ce:
وَعِنْدَ الْمَالِكِيَّةِ: أَنَّ إِجَابَةَ الْوَالِدِ فِي النَّافِلَةِ
أَفْضَلُ مِنَ التَّمَادِي فِيهَا
Kuma a wurin Maalikiyyah: Amsa wa mahaifi a cikin
sallar nafila shi ya fi cigaba a cikin ta. (Fat-hul Baariy: 6/482-483).
Shi ma As-Shaikh Muhammad Aliy Bn Adam Al-Ityoubiy
(Rahimahul Laah) ya ambaci irin waɗannan fa’idojin,
a inda ya fara da cewa: Daga cikin su akwai:
بَيَانُ عِظَمِ بِرِّ الْوَالِدَيْنِ، وَتَأَكُّدِ حَقِّ الْأُمِّ،
وَإِجَابَةِ دُعَائِهِمَا، وَلَوْ كَانَ الْوَلَدُ مَعْذُورًا، لَكِنْ يَخْتَلِفُ الْحَالُ
فِي ذَلِكَ بِحَسَبِ الْمَقَاصِد.
Bayanin girman al’amarin biyayyar iyaye, da girman
haƙƙin mahaifiya, da amsa wa
kiransu, ko da kuwa ɗan yana a cikin
wani uzuri ne. Sai dai kuma hakan yana saɓawa ne da
gwargwadon manufa. (Al-Bahrul Muheetut Thajjaaj: 47/248).
[3] Wato dai ba a cikin kowane irin hali ne ake
amsa wa kowace mahaifiya ba, ko da kuwa a cikin sallar nafila ce ba ta farilla
ba. Idan aka fahimci mummunar manufa ce a ɓoye a cikin kiran, kamar tana son fitinar yaron a cikin
addininsa ne, da ƙoƙarin lalata masa
ibadarsa ga Ubangijinsa, to a nan ba zai amsa mata ba.
A wannan wurin sai ya tuna da ayar nan da Allaah
Maɗaukakin Sarki yake cewa:
{وَإِنْ جَاهَدَاكَ لِتُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ
فَلَا تُطِعْهُمَا}
Idan kuma su (iyayen biyu) suka yi matuƙar ƙoƙari domin ka yi tarayya da Allaah kan wani abin da ba ka da ilimi a kansa,
to kar ka yi musu ɗa’a. (Surah
Al-Ankabuut: 8).
Da kamar wannan ayar da a cikinta yake cewa:
{وَإِنْ جَاهَدَاكَ عَلَى أَنْ تُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ
بِهِ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا}
Kuma idan suka yi matuƙar ƙoƙarinsu a kan wai sai ka
yi tarayya da ni abin da kuma ba ka da ilimi a kan shi, to kar ka yi musu ɗa’a. (Surah Luƙman: 15).
Sai kuma ya tuna da irin maganarsa (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam):
« لَا طَاعَةَ لِمَخْلُوقٍ فِي مَعْصِيَةِ اللهِ عَزَّ وَجَلَّ »
Babu ɗa’a ga wani
mahaluki a cikin saɓon Allaah
Mabuwayi Mai Girma. (Ahmad: 1095, kuma Al-Arnaa’ut ya sahhaha isnadinsa).
Don haka, har iyaye uwa da uba da sauran manya ma
ba a yi musu ɗa’a ko biyayya a cikin
aikin da ya ke na saɓon Allaah Ta’aala
ne, ko na saɓon Manzonsa ne (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
[4] Kodayake ba a yarda a yi musu ɗa’ar a cikin saɓo ba, kamar haka
kuma ba a yarda a yi musu duk wani abin da ke nuna wulaƙanci ko tozarci a gare su ba. Allaah Ta’aala ya ce:
{وَوَصَّيْنَا الْإِنْسَانَ بِوَالِدَيْهِ ، حَمَلَتْهُ أُمُّهُ
وَهْنًا عَلَى وَهْنٍ وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ ، أَنِ اشْكُرْ لِي وَلِوَالِدَيْكَ
إِلَيَّ الْمَصِيرُ . وَإِنْ جَاهَدَاكَ عَلَى أَنْ تُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ
عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا ، وَصَاحِبْهُمَا فِي الدُّنْيَا مَعْرُوفًا ، وَاتَّبِعْ
سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَيَّ ، ثُمَّ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُمْ بِمَا
كُنْتُمْ تَعْمَلُونَ}
Kuma mun yi wasiyya ga mutum game da iyayensa biyu
- Mahaifiyarsa ta ɗauke shi cikin
rauni a kan rauni, kuma yayensa a cikin shekaru biyu ne - cewa: Ka yi godiya
gare ni kuma ga iyayenka. Makoma gare ni ta ke. Kuma idan suka yi matuƙar ƙoƙarinsu a kan wai sai ka yi tarayya da ni abin da kuma ba ka da ilimin shi,
to kar ka yi musu biyayya. Kuma ka zauna da su da kyautatawa a cikin duniya,
kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al’amari gare ni.
Sannan zuwa gare ni ne makomarku, sai kuma in ba labarin duk abin da kuka
kasance kuna aikatawa. (Surah Luƙman: 14-15).
Kuma Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:
{وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ، وَبِالْوَالِدَيْنِ
إِحْسَانًا ، إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِنْدَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا
تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ ، وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا . وَاخْفِضْ
لَهُمَا جَنَاحَ الذُّلِّ مِنَ الرَّحْمَةِ ، وَقُلْ رَبِّ ارْحَمْهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي
صَغِيرًا}
Kuma Ubangijinka ya hukunta cewa: Kar ku yi bauta
ga kowa sai dai gare shi kaɗai. Iyaye biyu
kuma ku kai matuƙa wurin kyautata musu. Idan ɗayansu ko su
duka biyun suka kai girma a tare da kai, to kar ka ce musu: ‘uff!’ Kuma kar ka
tsawace su. Amma ka gaya musu magana ta darajawa. Kuma ka sassauta musu gefen
sassauci domin tausayawa gare su, kuma ka riƙa cewa: Ya Ubangijina! Ka yi musu Rahama, kamar
yadda suka rene ni a halin ina ƙarami. (Surah Al-Israa’: 23-24).
Allaah ya sa mu iya sauke dukkan haƙƙoƙin da su ke a kanmu kafin zuwan ajalinmu.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.