Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudummawar Rubutattun Wakokin Hausa Ta Fuskar Fadakarwa Wajen Kyautata Zamantakewar Hausawa

Citation: Salihi, T.M. (2024). Gudummawar Rubutattun Waƙoƙin Hausa ta Fuskar Faɗakarwa Wajen Kyautata Zamantakewar Hausawa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 117-122. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.014.

Gudummawar Rubutattun Waƙoƙin Hausa ta Fuskar Faɗakarwa Wajen Kyautata Zamantakewar Hausawa

Tijjani Muhammad Salihi

Hausa Department, Federal University of Education Kano/FCE Kano

09042398898

teesayy@gmail.com

Tsakure: Masu hikima na yin amfani da adabin baka wajen sarrafa harshen Hausa don sauran mutane masu magana da kuma amfani da harshen Hausa su saurara su kuma more wajen samun zantuttuka masu armashi da ke kawo nishaɗi da birgewa. A wannan takarda an yi amfani da ɗaya daga cikin waɗannan sassa na adabi wajen fito da wasu daga cikin tarin muhimmancin da suke da su ta fuskar kawo faɗakarwa don kawo gyara da ɗora al’umma a kan hanyar aikata abubuwan da suka kamata da gujewa munanan ayyuka. Don haka an yi amfani da rubutattun waƙoƙi don nuna irin tasirin da suke da su wajen faɗakarwa a waɗannan lamuran da suka danganci zamantaker Hausawa ta yau da gobe.

Fitilun Kalmomi: Rubutattun Waƙoƙi, Faɗakarwa, Zamantakewa, Hausawa

Gabatarwa

Wannan takarda, za ta yi bayani a kan yadda ake samun alaƙa tsakanin sassan adabi da sassan al’ada. Irin wannan alaƙa tana fitowa ne, idan aka dubi cewa ɗayan sashe na bayyana ɗan uwansa. An yi ƙoƙari wajen fito da wasu ayyuka na marubuta waƙoƙin Hausa ta nuna yadda waƙoƙin nasu suke bayar da gudummawa wajen faɗakar da al’umma, musamman Hausawa da kuma masu jin harshen Hausa; faɗakarwa ta fuskar yin nuni da kyawawan halaye da kuma nuna munin munanan halaye. Don ganin an fahimci wannan aiki yana da kyau a kawo ma’anar wasu sassa da suka taka rawar gani wajen fito da wannan aiki fili kamar haka:

Ma’anar Adabi

Umar (1987:5) ya bayyana adabin Hausa da cewa, “adabin Hausa shi ne sarrafaffen harshen Hausa mai ƙunshe da hikima ta musamman. Ana iya samun wannan ta baka a sigar tatsuniya ko karin magana ko waƙa ko almara ko wasannin kakkarya harshe ko gagara gwari ko kacici-kacici ko sauran nau’o’in zantukan hikima da suka fito daga bakin Bahaushe.”

Junaidu da ‘Yar aduwa (2007:66) sun bayyana ma’anar kalmar adabi kamar haka, “Adabi yana nufin wata hanya ta musamman wadda bil-adam (mutum) yake bi don sadar da abubuwan da suka shafi rayuwarsa da ta ‘yan uwansa. Abubuwa da yakan sadar ɗin kuwa mafi yawansu abubuwa ne da suka daɗaɗa masa rai watau annushuwa ko suka munana masa zuciya don nuna baƙin cikinsa da ƙin abin.”

A taƙaice, daga bayanan da suka gabata za a iya cewa, al’umma na sarrafa hikimomin da ke cikin adabinta wajen isar da wasu saƙonni ga jama’arta. Saƙonnin za su iya zama na kawo nisaɗi da farin ciki ko kuma don a nuna baƙin ciki ko ƙyamatar wani abu.

Ma’anar Al’ada

Ƙamusun Hausa (2006:9) ya bayyana al’ada da cewa, “hanyar rayuwar al’umma”.

Bunza (2006:xxv), ya bayyana al’ada da cewa, “a luggar Larabci, al’ada na nufin wani abinda ka saba yi ko ya saba wakana ko aka riga aka san da shi. Da wannan dalili ne wasu masanan furu’a ke gabatar da wani zancen hikima mai cewa, al’ada wata’ atul baladi kas sunna, ma’ana al’adar da gari ya saba da ita kamar sunna ce a bakuna wasu ɗalibai suna riya cewa hadisi ne… A harshen Hausa kalmomin da suka fi kusa da al’ada su ne kalmar ‘sabo’ da ‘gado’da ‘sada’ da ‘gargajiya.’

Bodley (2008:1), ya bayyana cewa, “bayani a kan al’adun al’ummma abubuwa ne da suka haɗa da yardarsu da tsarin ɗabi’unsu da harshensu da tsubbace-tsubbacensu da fasaharsu da kimiyyarsu da tsarin tufafinsu da hanyar samar da abinci da kuma sarrafa shi da addininsu da hanyar tafiyar da shugabanci tsakaninsu da kuma tsarin tattalin arzikinsu. Saboda haka ɗan adam ne kaɗai ke da al’ada, sannan kuma tana bunƙasa ne tare da al’umma.”

A taƙaice, za a iya bayyana al’ada da cewa, hanya ce ta gudanar da rayuwa musamman abubuwan da suka shafi ɗabi’u da jama’a suka amince da su.

Ma’anar Waƙa

Auta (2001) ya bayyana cewa “Dangane da ma’anar waƙa gaba ɗayanta an bayyanata da cewa, waƙa wata manufa ce da akan bayyana a rera ta hanyar amfani da amsa-amo ko kuma rerawar ta zama ta sautin murya mai zaƙi, wata sa’a da haɗawa da kiɗa da sauran salon jin daɗi ga mai sauraro dan jawo hankalinsa ga manufa; kuma takan sha bamban da maganar baka ta yan da kullum da zube da kuma wasan kwaikwayo.”

Mukhtar (2005:2) ya bayyana waƙa da cewa, “rubutacciyar wata hanya ce ta gabatar da wani saƙo a cikin ƙayyadaddun kalmomi da aka zaɓa waɗanda ake rerawa a kan kari da ƙafiya a cikin baitoci.”

Gusau (2003:Yahaya1976) ya bayyana waƙa da cewa: “Waƙa magana ce ta fasaha a cure wuri ɗaya a cikin tsari na musamman.”

Gusau (2003:Yahaya1984) ya bayyana waƙa kamar haka: “Waƙa wata maganar hikima ce da ake rerawa ba faɗa kurum ba wadda ke da wani saƙo da ke ƙushe cikin wasu kalmomi zaɓaɓɓu, tsararru kuma zaunannu.”

Ɗangambo (2007), ya bayyana waƙa kamar haka, “muna iya cewa waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya) da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓen su da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba.”

Sarɓi (2007) ya bayyana waƙa da cewa: “Wani saƙo ne da ake gina shi a kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti da ɗango da kari da amsa-amo da sauran ƙa’idojin da suka danganci daidaita kalmomi da zaɓar su tare da yin amfani da su a rubuce sannan a rera lokacin da ake buƙata.”

Daga waɗannan bayanai da aka ɗan tsakuro dangane da ma’anar waƙa, Bisa fahimta za a iya tsattsefe su da cewa, waƙa wata tsararriyar hanya ce da ake amfani da wasu zaɓaɓɓun kalmomi da aka ɗora su bisa wani yardajjen tsari da ake rerawa ko rubutawa don isar da wani muhimmin saƙo ga jama’a.

Alaƙar Da Ake Samu Tsakanin Sassan Adabi Da Na Sassan Al’ada

Umar (1987:1) ya bayyana cewa, “an sami wasu masana a kasashen Afirka kamar su, Ruth da Finnegan da Albert B. Lord da wasunsu sun kai ga tunanin cewa adabi tamkar wata hanya ce da al’umma ke amfani da ita don bayyana al’adunta, watau dai ta nazarin adabin wata al’umma mutum zai iya samun tarihin rayuwar al’ummar ya gane irin dabi’ar jama’arta da basirarsu da yadda tunaninsu ke gudana da irin tsarin rayuwarsu…”

Bodley (2008:1), ya bayyana cewa, al’ada ita ce tsarin rayuwar al’uma, wanda take nuna ɗabi’u da tsarin tunanin al’ummar da ke zaune a wani sashe da suka keɓance kansu don gudanar da tsarin rayuwarsu da ya danganci koyo ko ƙirƙira bisa wani yardajjen tsari iri ɗaya. Ta hanyar al’ada ne ake iya gane wannan al’uma da waccan don kuwa kowace na da irin abubuwan da suka amince da su wajen gudanar da tsarin rayuwarsu ta yau da kullum.

Daga waɗannan bayanai za a tara da cewa, al’ada hanya ce da ke nuna mana tsarin rayuwar al’umma nagaba ɗaya, wato tun daga haihuwa har zuwa mutuwa. Haka zalika, tsarin rayuwar al’ummar Hausawa tsari ne, da ke ɗauke da gimamawa tsakanin na ƙasa da na sama. A nan ina son na bayyana cewa, ƙarami na girmama na gaba da shi ko da ba daga cikin gida ɗaya suka fito ba. Haka kuma mata na girmama mijinta. Irin wannan tsari shi ya haifar da makwabci ya ladabtar da ɗan makwabci. Sauyawar zamani sai ta haifar da samar da wani salon a irin wannan tsawatarwa, ko faɗakarwar da babba yake yi wa ƙarami ko na sama yake yi wa na ƙasa. Sabon salon da aka samar shi ne, ta hanyar amfani da hanyar zamani ta shirya ko wallafa waƙa a baka ko a rubuce don a gudanar da nazari a kan wannan waƙa, ko kuma a rinƙa karantawa a kafofin yaɗa labarai don jama’a masu sauraro su ji su amfana da saƙon da ake son ya isa gare su.

Ma’anar Faɗakarwa

Dangambo, (2002) ta bayyana faɗakarwa da cewa, “faɗakarwa na nufin nusar da mutum a kan abubuwan daya sani tuntuni, amma ya manta da su. Don haka ne ake yi masa tuni da yi masa hannunka mai sanda don ya dawo ya yi la’akari da su …Faɗakarwa na nufin yiwa mutum tuni a kan abinda ya rigaya ya sani, wato yana da masaniya a kan abin, sai dai a daɗa nusarshe shita yadda zai daɗa ratsa shi.”

Auta (2008:76) ya bayyana faɗakarwa kamar haka, “Ana tunatar da mutum ne a kan waɗansu al’amuran rayuwa domin ko dai ya aikata abubuwan nan saboda muhimmancinsu kuma ya amfana da su, ko kuma a lurar da mutum waɗansu al’amura munana domin ya guje su saboda illarsu.”

Halayyar waƙoƙin faɗakarwa sun dogare ne a kan abin daya shafi wayar da kai a kan gyaran hali, ko nuna muhimmancin neman ilimi ko kishin ƙasa ko kishin al’adu, ko na harshe ko kula da kiwon lafiya/tsabta da sauransu. Haka kuma ta wata fuskar, waƙoƙin sukan yi bayani ne a kan abubuwan da suka shafi maƙwabtaka, ko kyautata zamantakewa a gida ko kasuwa ko makaranta, ko wuraren sana’a ko zaman aure ko abokantaka.

A kan wannan gaɓa Auta (2008:77) ya bayyana cewa, a duk waɗannan rukunai biyu wato zamantakewa da wayar da kai a waƙoƙin faɗakarwa, na da wasu siffofi ko sigogi da suke tattaruwa su tayar da babbar manufa daga cikin wannan sigogi akwai:

i.        Nuna muhimmancin abu

ii.      Nuna muni ko illar abu

iii.    Jawo hankali zuwa ga manufa

iv.    Kula da abin

v.      Nasiha domin aiwatar da gujewa abin

Idan aka duba waɗannan sigogi na sama, za a ga cewa wannan aikin ya fi karkata kacokam a kansu, don ƙoƙarin fito da manufar da aka sa a gaba. Misalan wasu daga cikin rubbutattun waƙoƙin Hausa da suke na faɗakarwa a kan kyautata zamantakewar Hausawa su ne kamar haka:

Ta Fuskar Wa’azi

A al’adance kowa ya yarda da cewa akwai mutuwa, don haka ne mawaƙa suke ta famar rubuta waƙoƙi don tunatar da mutane ita don ko su gyara halayensu, misali waƙar Tukur Babura ta Gargaɗi ga Jama’a:

Bt. 6 - Mala’ika ya fa kama fa ranka ya zare,

Dukkan jijiyoyin jikinka fa ya bi yasare,

Ya bar ka kwance cikin bargo ka taɓare,

Wa’adinka ya cika yau kwananka ya ƙare,

            Mata da yara, su ɗau kuka a kan gawa.

Bt. 7 - An wo kiran jama’a sunzo wurin sutura,

Da ɗunke littafani kuma sai aje a tura,

Da gwarwashi da turare dole an hanƙura,

Da an yi sallah a kai rami a je a zuba,

            In kafiri ne ya hallaka ba ruwan kowa.

(Tukur Babura: Waƙar Gargaɗi ga Jama’a)

Ta Fuskar Illar Jahilci

Marubuta waƙoƙi masu tarin gaske da suke gargaɗin jama’a a kan su nemi Ilimi don su kaucewa jahilci. Zama cikin jahilci yana haifar, da kuma lalata tsarin zamantakewar al’umma har ma ya kai ga rushewar wannan al’umma.

Bt.3– Zalunci gami da lalaci,

Duka mai haddasa su jahilci.

Bt.4 – Yawan rikici da cin bashi,

Duka mai haddasa su jahilci.

 

Bt.5 – Sata da fashi da yin caca,

Duka mai haddasa su jahilci.

Bt.7 – Rashin haɗa kai, yawan hargitsi,

            Duka mai haddasa su jahilci.

(Mu’azu Haɗeja: Waƙar ta Ilimi)

Ta Fuskar Illar shaye-shaye

Marubuta waƙoƙi da dama, sukan yi waƙa a kan illar da ke tattare da shaye-shayen miyagun kayan maye. Sukan fito da tarin illolin da mashayi yake haifarwakansa da kuma jama’a tare da nuna irin wahalar da zai sha a nan duniya da kuma gobe ƙiyama idan har bai bar wannan halayya ko ɗabi’a ba, wato bai tuba ba.Misali,

Bt. 3 - Farko wanda zai ƙi ka Allah,

In ka zamo mashayin giya.

Bt. 4 - Sannan shugaban Musulmi,

Annabi tun a nan duniya.

Bt. 5- Lakkan zai ƙi ka, ramin wuta,

Ya tabbata nan ga mai shan giya.

Bt. 10 -Ko kun haɗu kar ka kuskura kai,

Hannu da mutum mashayin giya.

Bt. 11- Baa saye wuri nai haka nan,

Ba a sayarwa mai shan giya.

Bt. 12 - Baa ba mashayi ɗiya,

Ba a auren ɗiyar ɗan giya.

(Mu’azu Haɗeja: Waƙar Giya)

Ta Fuskar Kira ga kama Sana’a

Wasu marubuta waƙoƙin Hausa sukan shirya waƙoƙinsu ne a kan jama’a da su kama sana’ar yi, su bar zaman banza. Haka kuma a wasu lokutan akan ware wasu sana’o’in a waƙe don nuna irin muhimmancin da suke dashi. Misali:

Bt. 3 - Ƙasarmu ta noma Allah Ya bamu,

Saboda mu noma abinci Ya ba mu,

A domin mu shuka, mu noma mu samu,

Ruwan sama na nan, da Allah Ya bamu,

A dukkan ƙasarmu ta Nijeriaya.

Bt. 4 - Mu koma ga noma mu sami halali,

Mu zam cida kanmu, mu cida iyali,

Mu gan mu da mota da babur da rali,

Kaɗan dai muna so, mu sami hali,

Mu gaskata nomada ban gaskiya.

Bt. 6 - Mu watsar da neman kuɗi na haramun,

Mu bar duniyar nan salamun salamun,

Mu sani nasiha a ranar ƙiyamun,

Mu san rahama nan ga sarki Rahimun,

A gobe ƙiyama gaban Rabbiya.

(Tukur Baɓura :Waƙar Noma)

Ta Fuskar Riƙe Amana

Akan sami wasu marubuta waƙoƙin, suna nuna yadda masu mulki suke riƙe da ragamar tafiyar da jama’a, kamar yadda tsarin zmantakewa yake a ƙasar Hausa wanda dalilin haka akan shirya waƙa don shugabanni su riƙe jama’arsu da gaskiya. Misali:

Bt. 95 - Manufarmu bayyana danguna,

 Na ƙabilu ban da tsirariya.

Bt. 96 - Don akwai wasu a sarakuna,

 Mun barsu da ayar tambaya.

Bt. 97 - Haƙƙin jama’a na kansu duk,

             Su riƙe igiyarsu da gaskiya.

(Sa’adu Zungur: waƙar Arewa Jumhuriya ko Mulukiya)

Ta Fuskar Kula Da Rayuwar Duniya

Haka kuma, marubuta waƙoƙin Hausa na rubuta waƙoƙi don faɗakar da jama’a a kan halin rayuwa na yadda yakamata mu tafiyar da rayuwarmu. Misali:

Bt. 6 - Ku san duniya na da ruɗi da dama,

Halinta shi ne fa zan zayyana ma,

Masoyana ne suka zan yin nadama,

            Aboki ka gane ta baki ɗaya.

Bt. 7 - Sunanta karuwa mai ƙyalƙyalawa,

Tana yaudarar wanda baya kulawa,

Sai ya gaza sai ta maishe shi wawa,

            Ta koma wuri ɗaya tai dariya.

Bt. 8 - Takenta ne gata nan gata nan ka,

Ka cinci ka cinci tana nuna shirka,

Sharrinta shi za na ƙirga maka,

Sai kai tunani cikin zuciya.

Bt. 9 - Mai yaudara duniya tsohuwa ce,

Kamarta kamar walƙiya da maraice,

Misali nake maka don kar ka mance,

            Ka bata amanarka baki ɗaya.

Bt. 10 - In tai kirari tace ba kamarka,

Haƙiƙa ba za a sami kamarka,

In dai ta aure ka zan gargaɗe ka,

            Kar ka yi nuni da sharholiya.

Bt. 11- In kuma ka ƙi fa za kai nadama,

Sai ta naɗa ka ta sa kai ta koma,

Aikinta ne don a nan ta fi himma,

            Ta koma ta raɓe tana dariya.

(Adamu Sandalo Sudawa: Waƙar Duniya mai Yaudara)

Ta Fuskar Kira ga Magidanta

A wasu lokutan, marubuta rubutattun waƙoƙin Hausa na yin kira da magidanta dasu riƙe amanar da ke hannunsu ta aure kada a nuna bambanci a tsakanin mata ko kuma a wulaƙanta su. Yin haka zai haifar da samun zaman lafiya da al’umma ta gari, kamar yadda “Waƙar Aure” ta Tukur Ɓaɓura ta bayyana.

Bt. 11- Ku mazaje ku daina wasa da aure,

Mui ta kwazon riƙe shi dam-dam ya kyaure,

Mu da matanmu sai mu cije mu daure,

 Mui ta roƙon Ubangijin hakilina.

Bt. 12 - Ku mazajen da ba ku tsoron Ilahu,

Wanda matar gida, abincinta ahu,

‘yan uwa kunji masu saɓon Ilahu,

             Don a saɓon Ubangiji sun yi suna.

Bt. 15 - Ai mazajen ƙasarmu mun san halinsu,

Masu mata suna zuwa gantalinsu,

Su ko matan gida a ɗau alhakinsu,

 Duk gwaninta ga karuwai za su nuna.

(Tukur Ɓaɓura: Waƙar Aure)

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, za a gace akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin adabin al’umma da kuma al’adun al’umma don kuwa, ana yin amfani da adabi wajen bayyana sassan al’ada. Wannan aiki da aka kawo ya yi ƙoƙari wajen kawo, irin rawar da saasan adabi ke takawa wajen bayyana sassan al’ada. A nan an yi amfani da ɓangaren rubutataccen adabi ne musammaman ma ɓangaren waƙa, inda na kawo wasu al’amura da ke cikin tsarin rayuwar Hausawa ta yau da kullum. An kuma yi duba ga rubutattaun waƙoƙin da suke faɗakarwa a kan waɗannan fuskoki. An zaɓo wasu daga cikin waƙoƙin faɗakarwa, da kan yi nuni ga wasu masu aikata munanan halaye da kuma kawo irin sakamakon da kan biyo baya ga wanda ya aikata wanda wannan sakamako yakan zama mara kyau.

Manazarta

Auta, A.L. (2001). “Tarihin Rubutattun Waƙoƙi A Ƙasar Hausa.” Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies Vol. 1, No. 1. Kano: Department of Nigerian Languages

Auta, A.L. (2008). “Rubutattun Waƙoƙin Hausa Na Faɗakarwa a Ƙarni Na Ashirin.” Kundin Digiri Na Uku. Kano: Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

Babura, T. (1987). Waƙoƙin Tarihi Da Gargaɗi. Kano: RUKHSA Publications

Bodley, J.H. (2008). Culture. Retrieved from http://Microsoft_Encarta/culture.com

Bunza, A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Lagos: Tiwal Press Nigeria Ltd. C.S.N.L (2006)

Ƙamusun Hausa. Kano: Bayero University Kano.

Dangambo, H. A. (2002). “Salon Sanin Jigo A Adabin Baka Na Hausa: Nazari Kan Jigon Fadakarwa.” Kundin Digiri Na Biyu. Kano: Jami’ar Bayero

Dangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Kano: KDG Publishers Ltd.

Gusau, S.M (2003). Jagoran Nazarin Waƙar Hausa. Kano: Benchmark Publishers Ltd.

Haɗeja, M. (2010) Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja. Zaria: Amana Printing & Adɓert Ltd.

Junaid, I. da ‘Yar aduwa, T.M. (2007). Harshe Da Adabin Hausa. Ibadan: Spectrum Books Ltd.

Mukhtar, I. (2005). Bayanin Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Abuja: Countryside Publishers Ltd.

Yahaya, I.Y. da Ɗangambo, A. (1989). Jagoran Nazarin Hausa. Zaria: N.N.P.C. Ltd.

Sarɓi, S.A. (2007).Nazari Waƙen Hausa. Kano: Samarib Publishers Ltd.

Umar, M.B (1987). Dangantakar Adabin Baka Da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishing Company.

Zungur, S. A. (2008) Waƙoƙin Sa’adu Zungur. Zaria: N.N.P.C. Ltd.

Post a Comment

0 Comments