Ticker

6/recent/ticker-posts

Hotunan Wasu Shahararrun Mutane a Kasar Hausa

Waɗannan wasu jerin hotunan shahararrun mutane ne a ƙasar Hausa. An same su ta hannun Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji). A koyaushe kuna iya turo mana ire-iren waɗannan hotunan tarihi domin adanawa a taskar Amsoshi.
Muna Addu'ar Allah ya jiƙan magabatanmu.
Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III
Farko daga gefen hagu Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III ne tare da ɗan uwansa (Ƙanensa) Marigayi Mai girma Sarkin Sudan Na Wurno, Alh. Shehu Malami.
Da Mahaifin Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo Abubakar III, watau Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III da Mahaifin Marigayi Mai girma Sarkin Sudan Na Wurno Alh. Shehu Malami, watau Marigayi Mai girma Sarkin Sudan Na Wurno Mal. Muhammadu Bello, Mahaifinsu ɗaya, Mahaifiyarsu ɗaya, watau Modibbo Usman ɗan Mai Alfarma Sarkin Musulmi Mu'azu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi ne ya haife su. 
Allah SWT ya jaddadawa magabatanmu rahama, ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.
Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare
Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maiturare ɗan Sarkin Musulmi Ahmadu ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I /Atiku Mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi. Ya riƙe sarautar Marafan Sakkwato kafin ya zama Sarkin Musulmi.
Allah ya jaddada masa rahama, amin.
Marigayi Mai girma Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba
Marigayi Mai girma Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba ɗan Magajin garin Sakkwato Usman ɗan Magajin garin Sakkwato Abdulƙadir ɗan Magajin garin Sakkwato Malam Abubakar Haruna Ɗanjada Ba'allibe (Magajin garin Sakkwato na farko). Allah ya kyauta makwanci, amin.
Marigayi Mai girma Marafan Sakkwato Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi
Marigayi Mai girma Marafan Sakkwato Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi ɗan Alhaji Ali Bisije ɗan Dagacin Gasma ta Jihar Yobe, kuma jika ga Sarkin Kiyawan Ƙaura Namoda Malam zuriyar Muzaffar Muhammadu Namoda wanda shi ne (Muhammadu Namoda) ya ƙirƙiri Ƙaura Namoda a shekarar 1807. Allah ya kyauta makwanci, amin.
Sanata Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar Marafan Sakkwato
Mai girma Sanata Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar Marafan Sakkwato na yanzu ɗan Ƙayayen Mafara Abubakar jikan Abdu Yari ɗan Ƙayayen Mafara Ali Mayaƙi ɗan Ƙayayen Mafara na farko, Gurma.
Allah SWT ya ƙara imani da lafiya da nisan kwana mai albarka, amin.

Daga Taskar
Hon. Ibrahim Muhammad Ɗanmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya
08149388452, 08027484815
birninbagaji4040@gmail.com

Post a Comment

0 Comments