TAMBAYA (62)❓
Assalamuh alaikum. Mlm ina da tambaya neh. Mene neh hukunchin mijih mai yin ball?
MIJI MAI YIN BALL
AMSA❗
Alhamdulillah
Ita kanta ball idan mutum yana yi bazaka ce sabo yake aikatawa ba,
saidai haramcin yana zuwa ne yayinda aka duba abubuwan da suke kewaye ball din
kamar yanda kowacce sana'a sabo zai iya kewayeta
Misali: lokacin sallah, azumi, gajeran wando saboda cinya tana fitowa
kuma cinya al'aurace
To amman babbar al'aurace qaramar al'aurace ?
Idan kabi fatawar Ibn Hazm to cinya ma ba al'aura bace hujjar hakan
shine; Sayyadina Usman RA ya ga cinyar Annabi SAW. Da ace babbar al'aurace da
Annabi SAW bazai bari Sayyadina Usman Bin Affan RA ya ga cinyarsa ba
Babbar al'aura itace: duwawu da kuma gaban mutum
Abin kiyayewa shine; wando yazo gwiwa, saman kuma ya wuce cibiya
Idan kika duba littafin mai ahlari yace: al'aurar namiji tana farawa ne
daga cibiya zuwa gwiwa
Sannan kuma sai azo batun kudin da yake samu (salary idan har ya maida
ita sana'arsa kenan) kuma yake ciyardake ya shayar dake ya kuma tufatar dake,
menene hukuncin wannan kudin, halak kuke ci ko kuma haramun ne ?
Anan za'a duba asalin tushen kudinne, bi ma'ana; idan ya zamana yasan
cewar kamfanin giya da makamantansa ne suka dauki nauyin kungiyar kwallon kafar
tashi to haramun yake ci idan kuma kamfanin kasuwanci ne ko kuma coach dinnasu
yana harkar kasuwanci ne yana zuba hannun jari to anan baza'a haramta abinda
yake samu ba indai har ya kiyaye dokokincan guda 3
Idan kuma yana yin ball dinne a matsayin motsa jiki wannan kada ki
takura masa indai har yana kiyaye wadancan matakan guda 3 domin kuwa wannan
motsa jikin yanada matuqar amfani ga lafiyar kowanne mutum namiji da mace
Sannan kuma abu na karshe shine yakamata ya dinga ball din a matsayin
exercise bawai a matsayin abin burgewa da koyi da yahudawa ba domin kuwa daman
asalinta sun kawota ne kasar Spain (Andalusia) suka rushe masallatai da
makarantun addininmu na musulunci suka gina stadium din ball don ganin sun
rabamu da addinin gaskiya
Alhalin Imamul Qurtubi (Malamin Tafsir dinnan) dan kasar Spain ne,
hakama Abbas Ibn Firnas da ake kirada Father of Aviation (Wanda ya bude kofar
yiwuwar qirqiro jirgin sama ta hanyar daure jikinsa da wasu abubuwa kamar
fuka-fukai ya hau saman bene ya fado yana shawagi kamar tsuntsu a sama) duk yan
kasar Andalusia ne, da sauran malaman musulunci wadanda lokaci bazai bawa
alqalami na damar zayyanosu ba
A binciken da masana sukayi duk cikin mutane 5 na kasar Spain da akwai
dan kwallo guda 1, kuma gashi an cusa mana aqidar kallon ball. Kamata yayi
yanda samari suke zuwa kallon ball su maida hankali wajen sanin addininsu da
hukunce hukuncensa a makarantu
Sun ja ra'ayin wasunmu kuma suna samun kudi damu a duk lokacin da muka
saka data muka kallesu ko kuma muka biya kudi muka shiga gidan kallo. Dr.
Bashir Sani Sokoto yace; shin ko mutane sun san cewar a binciken da masana
sukai na shekarar 2019 Real Madrid tanada a qalla 4.2 billion US dollars a
asusunta, Barcelona na da 4.02 billion dollars, Manchester United sunada 3.81
billion dollars. Magana ake ta tiriliyoyin nairori fa
Idan zaka hade jimullar kudaden clubs dake kasashen waje gaba daya,
idan da za'a siyar dasu, tareda stadium dinsu da yan ball din, sun doshi 24.094
billion US dollars. Wannan a bangaren wasannin iya football fa kenan shiyasa
suka fi jan ra'ayin samari a wannan bangaren. Kuma a haka akwai project da
Amurka sukayi na titin hawa (road) wanda ya ninninka wancan kudin har sau 3.
Iya budget din Amurka na sati daya yafi budget din Nigeria na shekara guda. To
wadanne kudade kake tunanin Amurka ta ware don ganin ta rusa musulmai da
addininnamu na musulunci gaba daya ?. Iya budget din da Amurka tayi na 2015
yakai 3.7 trillion US dollars, a shekarar 2016 3.9 trillion US dollars, 2017
yakai 4 trillion US dollars. Idan da ace za'a siyarda dukkan clubs da ake dasu
a duniya bazasu kai 1 trillion US dollars ba, kai ba ma zasu kai 200 billion
dollars ba. Sannan a shekarar 2020 budget din Amurka yakai 4.8 trillion US
dollars
A iftila'in 9/11 (wato 9 ga watan September, 2001) kadai Amurka ta rasa
kudaden da zasu kai adadin da za'a iya siyan clubs irinsu Real Madrid guda 50.
Sun sako bombs a cibiyar kasuwanci ta duniya (World Trade Center dake birnin
New York) kawai don su dakushe musulunci kuma da suka tashi sai sukace ai Osama
Bin Laden ne ya sako bama-baman, amman a binciken qwaqwaf da akai an tabbbatar
da cewar Yahudawa ne suka tsara abin da taimakon gwamnatin Amurka dan dai kawai
a shafe musulunci kuma a sakawa mutane tsanar musulman duniya baki daya
A daidai kan wannan gabar yakamata na jefa qalubale ga matasa musamman
wadanda suke bata lokaci wajen asarar data suna kallon wasan kwallo live
A shawarce wadannan sune sunayen litattattafai guda 24 da yakamata mu
je mu karanta mu fahimcesu domin amfanuwarmu, domin kuwa na amfana dasu matuqa
kuma ina kwadayin yan uwa, iyaye da abokan arziqin dake wannan group na tambaya
da amsa su amfana dasu
Ga littattafan kamar haka;
1) Sifatu Salatin Naby PDF (Siffar yanda Annabi SAW yayi sallah,
wallafar Shaikh Muhammad Nasiriddin Albany (Rahimahullah)
Ya suffanta tare da kawo bayanai daki-daki akan yanda Annabi SAW ya
koyar da yanda ake sallah dogaro da hujjar hadisin "Sallu kama ra'ayta
muni usalli" bi ma'ana: "Kuyi salah kamar yanda kuka ga ina yi".
Don haka ya zama dole kowa ya koyi sallah irin yanda Annabi SAW ya koyar. Kamar
yanda muka sani cewar kowa yana cikin dayan biyu ne: immadai kana sallah ne a
al'adance (kamar yanda ka taso ka ga ana yi) ko kuma kana sallah ne a addinance
(yanda Ma'aiki SAW ya koyar)
2) Zaadil Ma'ad (Guzirin Alqiyama, wallafar Imam Ibn Qayyim al-Jauziyya
(Rahimahullah)
A cikin littafin mai suna "Guzurin Alqiyama" yayi bayani
daki-daki dangane da kyawawan dabi'u tare da ayyukan Annabi SAW. Zanso mu
mallaki littafin domin amfanuwa da ilimin da ya qunsa
3) Albidaya wan Nihaya (Farko da Karshe, wallafar Abubakar Alhafiz Ibn
Khathir (Rahimahullah)
Littafi ne wanda yayi bayani tun daga farkon halittar Alqalami,
Al-Arshi, Kursiyyu, Sammai da Kassai da tarihin Annabawa har zuwa shiga Wuta
(Allah ya tsaremu) ko Aljannah (Allah ya shigar damu), ya kawo bayananne da
hujjoji a cikin Qur'ani da Hadisai. Duk wanda ya karanta wannan littafi to
haqiqa zai kara sanin yanda rayuwa take kuma tunanin mutum zai canza saidai
idan mutum bai karanta littafin ba
4) Talbis iblis (Yaudarar iblis, wallafar Imam Abdurrahman Aljauzi
(Rahimahullah)
Yayi namijin qoqari wajen ganin ya ilimintar da mai karatu da koyar
dashi sanin hanyoyin da iblis yake bi yana kafa tarkonsa don batar da malamai
da jahilai. A wannan zamanin mai cike da qalubale da son abin duniya, ina
shawartar kowa ya karanta wannan littafin don ganin ka nesanta kanka daga
tarkon iblis
5) The Evils of Music: Devil's Voice and Instrument (Sharrin kade-kade:
sautin shaidan da kayan kidansa, wallafar Ibn Qayyim Aljauziyya (Rahimahullah)
A cikin littafin: "Sharrin kade-kade: sautin shaidan da kayan kidansa",
yayi bayani akan illar sauraren kida da kuma narkon azabar da Allah ya tanada
ga wadanda suka mutu suna jin kida basu tuba ba da kuma gargadi akan za'a hana
mutum jin kida mai dadi a Aljannah. A wannan zamani na kide-kide ya zama kusan
dole mutum ya nemi wannan littafin ya karanta don katange kai daga fadawa
fushin Allah Azzawajallah
6) Music Made Me Do It (Jin Kide-kide ne sila, wallafar Dr. Gohar
Mushtaq)
Dr. yayi bayanai daki-daki akan yanda jin kida ya zama silar kurmancewa
da mutuwar masu saurare, yayi bayani akan illar jin kida ga lafiya da kuma
ruhin mutum. Yayi jan hankali akan jin kida yana haddasa munafurci kuma yana
kawo mummunan qarshe, ya kafa hujja da hadisai sahihai. Lallai yakamata mu nemi
wannan littafi sannan mu nusar da mawaqa masu saka kida a wakensu sharrin dake
tattare da saka wannan kidan
7) Natural blood of women (Jinin Mata, wallafar Shaikh Saleh
al-Uthaymeen (Rahimahullah)
Ya tattauna matsaloli akan jinin mata, kama daga jinin haila, haihuwa
da na ciwo. Yakamata kowacce mace tasan ilimi akan rabe-raben wadannan jinane
masu rikitarwa a dabi'ance tareda sauqin ganewa a addinance
8) Guidelines to intimacy in islam (Shiriya akan alaqar auratayya a
musulunce, wallafar Mufti Ahmad Ibn Adam Alkautary)
Yayi bayani sosai kuma daki-daki akan yanda Annabi SAW ya koyar da
al'ummarsa yanda ake rayuwar auratayya. Qalubale ga gwauro da gwauruwa wadanda
basuda ilimin sanin hakan kuma gashi suna da niyyar aure
9) Newborn baby guide (Shiriya ga Jarirai, wallafar Ibn al-Qayyim
Aljauziyya (Rahimahullah)
Ya rubuta littafinne a matsayin kyauta ga qanwarsa a lokacin da ba shi
da ko da riga daya da zai bata a matsayin tukwici a lokacin da ta haihu, sai
gashi Allah SWT ya albarka littafin ga shi muna amfana dashi. Yayi bayanai akan
yiwa jariri kiran sallah, sakawa jariri suna, yin aski, kaciya, yanka da sauran
bayanai dai da hujja a Qur'ani da sahihan hadisai, kai abin sai wanda ya
karanta dai
10) Ahkamul Jana'iz (Hukunce-hukuncen Jana'iza, wallafar Shaikh
Muhammad Nasiriddin Albany (Rahimahullah)
A wannan zamani wanda ake bidi'o'i kala-kala yayin aiwatarda ibada
Jana'iza, zakaga mutane suna abubuwan irin na zamanin jahiliyya a sakamakon
hakanne Malam Albany ya rubuta littafin da hujja a cikin Qur'ani da sahihan
hadisai akan yanda Annabi SAW ya koyar. Allah ya bamu ikon ilimantuwa
11) Evil eye is real (Kambun ido gaskiya ne, wallafar Ahmed
Abdurrahman)
Malamin ya tattaro bayanai a Qur'ani da hadisai akan sharrin kambun ido
da kambun baka. La'akari da mun tsinci kanmu a zamani na social media zakaga
musamman yanda mata suke dora hotunansu, yakamata mu karanta wannan littafi don
neman kariyar Allah SWT daga sharrin masu kambun ido
12) Reclaim your heart (Mallakar zuciya, wallafar Ustadha Yesmin
Mogahed)
Malama Yesmin tayi matuqar qoqari wajen janyo hankalin mutanen da
munanan dabi'unsa suka nesanta da kwaikwayon kyawawan dabi'un wasu. Na amfana
da littafin matuqa
13) Unchallengeable Miracles of the Quran (Mu'ujizozin Qur'ani,
wallafar Caner Taslaman)
Ban taba karanta littafi mai abin mamaki da dadi irin wannan ba, domin
kuwa mawallafin ya tattaro bayanai musamman na kimiyya ya fayyace su, haqiqa
ba'a taba littafi kamar Qur'ani ba haka kuma baza'a taba yi - domin kuwa shi ne
sha karatu
14) Reviving the Abandoned Sunnah (Dabbaqa sunnonin da aka qyale,
wallafar Abdulmalik Alqasim
Ya kawo sunnoni guda 45 da Annabi SAW ya koyar ga al'ummar sa. Na
amfana da wannan littafin kuma yakamata duk wanda yake son samun ladan koyi da
sunna to ya karanta wannan littafi
15) Jokes of the prophet in the Hadith (Barkwancin Annabi SAW a cikin
hadisi, thesis/program din wani dalibi ne daga jami'ar musulunci dake
Walisongo, Semarang)
Dalibin ilimin ya kawo hadisai akan yanda Annabi SAW yake barkwanci a
cikin wasu al'amuransa. Kamar labarin tsohuwar nan da Annabi SAW yace mata
tsofaffi basa shiga Aljannah, ta fara kuka, sai yace mata ai yana nufin sai an
maida ita budurwa, sai tayi dariya. Zanso mu karanta wannan littafin domin kuwa
na amfana dashi matuqa musamman ta fuskar barkwancina ga yan uwa da abokan
arziqi da nake zama tare dasu
16) Looking into the eye of the Dajjal (Ganin idon Dajjal a ilimance,
wallafar Abu Muhammad Ibn Dawood)
Na amfana da karanta wannan littafin domin kuwa mawallafin yayi bayani
sosai akan sharrin da yake tattare da bayyanar Dajjal, cewar tun da aka halicci
Annabi Adam AS ba'a taba wani bala'i sama da bayyanar Dajjal ba, mu sani cewar
duk wanda neman kudi ne abin son sa fiyeda addini to tabbas zai wahala ya
qetare fitinar Dajjal. Mafita shine karanta addu'ar da Annabi SAW ya koyar
bayan kowacce Tahiyya kafin sallama. Allah yasa mudace
17) Prophet's Wudoo (Alwalar Annabi SAW), fassarar Dawud Durbank)
Ya kawo bayanai daki-daki akan yanda Annabi SAW yake yin alwala da
hujjoji a cikin sahihan hadisai. Munsan dai babu sallah ga wanda ba shi da
cikakkiyar alwala
18) World of The Jinn and Devils (Duniyar Aljanu da Shaidanu, wallafar
Dr. Umar S. al-Ashqar)
Ya kawo bayanai akan yanda Aljanu da shaidanu suke rayuwa da kuma yanda
suke hidima ga shugabansu wato iblis, da hujjoji a cikin Qur'ani da sahihan
hadisai. Na amfana da littafin sosai
19) Ranking of the 100 Most Influential Persons in History, by Michael
H. Hart - Prophet Muhammad No. 1 (Mutane 100 da suka fi kowa daraja a tarihin
duniya, Annabi Muhammad SAW shine na 1, wallafar Michael H. Hart
Duk da cewar mawallafin ba musulmi bane ba amman yace Muhammad SAW
shine mutum na farko a cikin shahararrun mutane 100 da suka fi daraja da samun
daukaka a tarihin duniya. Littafin ya janyo cece-kuce, yace ni kaina Christian
ne amman na tabbata Muhammad (SAW) ya fi Jesus komai. Allahu Akbar ! Daman tuni
Allah SWT yace "Wallahu ya'asimuka minannasi". Zanso mu karanta
wannan littafin domin hakan zai kara mana son masoyinmu Annabi Muhammad SAW
20) The Day of Judgement Preparing for the Hereafter (Ranar lahira,
shirye-shiryen alqiyama, wallafar Shaik Muhammad al-Wasaabee)
Yayi bayanai daki-daki akan bala'o'in da suke tattare da ranar
alqiyama, da kuma shirye-shiryen da ya kamata mumini yayi don ganin ya samu
dacewa da gidan Aljannah
21) Purifications of the heart (Tsarkake zuciya, wallafar Shaikh Hamza
Yusuf Hanson)
Ban taba karanta littafin da yayi bayani sosai akan yanda zaka tsarkake
zuciyarka ba sama da wannan littafin. Abin dai sai wanda ya karanta kuma ya
fahimta
22) Signs of the Last Day (Alamomin tashin alqiyama, wallafar Harun
Yahya)
Yayi bayanai akan alamomi manya da kanana da suke da alaqa ta kai tsaye
da tashin alqiyama. Saidai na cewa masu karatu - Allah ya bada ikon amfana da
ilimin da ke ciki
23) The Soul Journey (Tafiyar Ruhi, wallafar Ibn al-Qayyim Aljauziyya
(Rahimahullah)
Yayi bayani akan yanda mala'iku suke rejistar ruhin musulmi a saman
bakwai a littafin illiyyin (Na yan Aljannah) - Allah yasa muna ciki, yayinda
kafirai kuma ake rejistar sunansu a kasan bakwai a littafin sijjin (Na yan
wuta) - Allah ya tsaremu. Na qaru matuqa silar karanta wannan littafin
24) Aljannah wan Nar (Aljannah da Wuta, wallafar Imam al-Qurtubi
(Rahimahullah)
To anan ne fa da ni dakai mai karatu zamu tsinci kanmu, ko dai a wuta
(Allah ya tsaremu ba don halinmuba) ko kuma a Aljannah (Allah ya dawwamar damu
a ciki ba don halinmu ba
Wadannan sune littattafan da naga ya dace na danyi tsokaci akan
yakamata da ke da mai gidanki da sauran ma'aurata ya kamata su karanta a
maimakon su bata lokaci wajen kallo ko kuma buga ball
Wallahu ta'ala a'alam
Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta,
astaghfiruka wa'atubi ilayk
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.