𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Tabbas muryar mace al’aura ce mun sani. Amma yanzu sai in ga mata suna wa’azi wanda kuma muryar za ta karaɗe duniya! To don Allaah, su waɗannan muryarsu ta halatta ne sauran maza su ji, ko yaya abin ya ke ne?
MURYAR MACE MAI WA’AZI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
A fahimtar malamanmu muryar mace ba al’aura ba ce, matuƙar dai ba sirara
muryar ko karairaya ta tayi ba, yadda wani namiji zai yi sha’awa har kuma ya karkata gare ta. Ubangiji Ta’aala ya ce:
{فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي
فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا}
To, kar dai ku yi karairaya da magana, sai wanda akwai cuta a cikin
zuciyarsa ya yi tsammani. Ku dai faɗi magana sananniya daidaitacciya. (Surah Al-Ahzaab: 32).
Abu ne sananne dai cewa: Tun tuni mata suna yin magana da maza a wurare
mabambanta, kamar a wurin ciniki da yin fatawoyi da neman ƙarin bayani a kan waɗansu al’amuran da suka shafi addininsu da
rayuwarsu. Abin da aka hana dai shi ne cakuɗa ko keɓantuwa a wanɗanda ba muharramai ba a wurin da ka iya haifar da munana zato, kamar a
duhu ko ɗaki ko ofishi ko mota da sauransu.
Amma yadda mata suke fita yanzu a cikkin taron jama’a maza da mata, ko
kuma a cikin kafafen yaɗa mabayanai na gargajiya da na zamani da sunan wa’azi ko faɗakarwa, wannan kam ba shi daga cikin ayyukan
mata a zamanin Sahabbai da Tabi’ai da sauran magabatan wannan al’ummar waɗanda aka yi musu shedar alkhairi. Kuma idan
da wannan abin da ake neman yayata shi a cikinmu a yau ɗin wani aikin alkhairi ne, to da kuwa matan
waɗanccan zamunnan da suka fi namu alkhairi sun
rigaye mu a kan hakan.
Muddin dai akwai mazan da za su iya yin wannan aikin, kuma suna yin
aikin yadda ya dace, kuma saƙonnin suna isa ko’ina kuma jama’a suna amfana yadda ya dace, to a gaskiya ba sai mata sun bar muhimmin
aikinsu na tarbiyya da kula da gidajen mazajensu, sun shigo wannan filin ba.
Ubangiji Ta’aala ya ce:
{وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ
تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى}
Kuma ku tabbata a cikin gidajenku, kuma kar ku yi fitar gayu, irin
fitar gayu na zamanin jahiliyyar farko. (Surah Al-Ahzaab: 33).
Wato dai ita mace cikin gida ne mazauninta, kuma tana fita ne kawai
idan fitar ta kama, zuwa ga abin da ya kama kaɗai.
Su dai waɗancan
matan salihai da suka gabata: Zama suke yi a cikin gidajen iyayensu ko na
mazajen aurensu, sai kuma ɗalibansu mata da yara su riƙa zuwa a lokutan da suka yanke musu, domin ɗaukar dukkan nau’uka fannonin ilimi a cikin
gidajen. Su kuma manyan mazan da ba muharramai ba, sai su riƙa sauraro daga bayan
shamaki. Kuma wannan ya isa kyakkyawan abin koyi ga na-bayansu, in sha’al Laah.
Amma yadda abin ya ke a yau, akwai tsoron kar ya zama mafari ko mabuɗi mai kai wa ga shigar da mata a cikin
ayyukan da Shari’a ba ta saka su a ciki ba, kamar shugabanci da waziranci ko alƙalancin gari ko jiha
ko ƙasa
da makamantansu. Ko kuma a shugabantar da ita a sallar jam’I da juma’a irin yadda ake ji da gani a wadansu garuruwan ƙasashen yamma da masu
sha’awar koyi da su. Wannan kuma duk a ƙarƙashin tsare-tsarensu
ne na siyasar dimokuraɗiyyar
zamani mai yayata maganarsu ta ƙarya cewa: ‘What a man can do a woman can do, even better!’ Wai: Duk wani abin da namiji ke iya yi, ita
ma mace za ta iya, har ma fiye!
Wannan fahimtata kenan a kan wannan al’amarin.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
+2348021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.