Citation: Hassan, H. and Yankara, M.M. (2024). Salon Amfani da Karin Magana a Waƙa Bisa Fahimtar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya: Nazari Daga Wasu Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 24-32. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.004.
Salon Amfani da Karin
Magana a Waƙa Bisa Fahimtar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya: Nazari
Daga Wasu Rubutattun Waƙoƙin Hausa
Dr. Hussaini Hassan
07039283077
hussainihassan387@gmail.com
Department of Hausa, Federal College of Education, Pankshin
DA
Muhammad Musa
Yankara
08062367496
mymuhammad@fudutsinma.edu.ng
Department of Hausa, Federal University, Dutsin-Ma
Tsakure: Salon amfani da karin magana a waƙoƙin Hausa na baka, ko rubutattu, wani tsalli ne daga cikin salailan da
Yahya, (2001 da 2016), ya bayyana, ya kuma tsattsefe shi tare da zaratan
misalai. A wannan takarda an dubi wannan salo na amfani da karin magana, kamar
yadda ya kawo shi, kana aka yi nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa, sannan aka ɗora nazarin bisa wannan fahimta
ta Shehin Malamin. A fahimtar masanin, ya ce marubuta waƙoƙin Hausa suna amfani da karin magana ta hanyoyi guda
uku da ya haɗa da faɗaɗa karin magana, da gutsure karin magana da kuma ƙirƙirar karin magana. Har ila yau, sai ya nuna cewa
dukkan karin maganar da ake amfani da ita a waƙa ana yi ne
ko dai don yin ishara, ko ƙarin bayani ko nuna ƙwarewa a
harshen, ko kuma adana karin maganar. An zaƙulo misalai
daga waƙoƙinHausa da suke nuni ga faɗa ta wannan
masani, kuma Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, ta hanyar amfani da dabarar bincike ta bibiyar rubutattun
bayanai, da kuma sauraren waƙoƙin da aka
nazarta. A ƙarshen nazarin, wannan takarda ta ƙara tabbatar da wannan fahimta ta Shehin malamin na yadda marubuta waƙoƙin Hausa suke amfani da karin magana a cikin waƙoƙinsu, tare da sun sani ko ba su sani ba.
Fitilun Kalmomi: Salo; Karin Magana; Abdullahi Bayero Yahya; Rubutattun Waƙoƙin
Gabatarwa
Ɗangambo, (1984) da Zarruƙ, da
wasu (1987) da Yahaya da wasu (1992) da Gusau, (2003) da Mukhtar, (2005) da Sarɓi, (2007) da ‘Yar‘aduwa,
(2010) Yahya, (2013, 2016) da Auta, (2017) da sauransu da yawa sun bayyana waƙa da
magana ko lafazi wanda ake yi cikin tsarin da ya saɓa wa maganar yau da kullum.
Waƙa a duniyar Bahaushe kamar gishiri ne
cikin miya, domin, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba ga harkokin zamantakewarsu.
Hanya ce ta isar da manufofi da saƙonni ga jama'a, musamman kan abin da ya
shafi harkar ilimi ko faɗakarwa
kan sha’anin zamantakewa ko siyasa ko tarbiyya ko lamarin addini da
makamantansu. A kowane harshe na duniya, waƙa ita ce kan gaba wajen bunƙasa da
ɗaukakar adabin wannan
harshe, domin ita ke nashe dukkan sassa na rayuwar al’ummar da ke magana da
harshen. Waƙa
tana da tasirin gaske cikin jinin mutane. Don haka ne wasu lokuta mawaƙan
Hausa suke amfani da ita wajen cim ma burin duk wani al’amari da suka tunkara.
Masana da manazarta sun yi rubuce-rubuce
masu yawa kan abin da ya shafi salo a waƙoƙin Hausa, na baka da kuma rubutattu. Mafi
yawan rubuce-rubucen da aka yi, ba a cika ba salon amfani da karin magana
kulawar da ta da ce ba, kamar yadda Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya tsettsefe
cikin littafinsa na Salo Asirin Waƙa (2001, 2016).
Salon amfani da karin magana a waƙa,
fage ne da mawaƙa ke aiki da basira wajen yi wa waƙa kwalliya da sanya waƙa ta
yi armashi da daɗin saurare
a kunne. Duk da irin wannan matsayi da tagomashi na salon amfani da karin
magana, sai ga shi mafi yawan manazarta ba su faye ba fagen kulawa a nazarce –
nazarcensuna salo a rubutattun waƙoƙi ko na baka ba. Wasu masanan ma irin su
Gusau, (2003), da Bunza, (2009), da sauransu da dama ko kawo wannan salo ba su
yi ba, balle a ga inda suka sanya shi. Wannan ya ja hankali ga yin rubutu a kan
wannan salo domin ƙara fito da shi da jan hankalin masu nazari kan su riƙa kula
da shi saboda muhimmancinsa, musamman ma a yau da kusan mawaƙa na
wannan ƙarni
suka fi amfani da kare-karen magana sama da kowannen irin salo a waƙoƙinsu.
Salo
Ma’anar salo kamar yadda masana
suka bayyana shi ne “dabara ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya
kwarzanta ko ya bayyana.
Salo a nazarin waƙa kuwa
yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda mawaƙi ya bi domin isar da saƙon da
yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa
kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatu (Yahya 2016:29).
Salo yana nufin hanyoyi ko
dabarun da marubuci ya yi amfani da su wajen isar da wannan saƙo
nasa. Ya kuma ƙara da cewa za a iya fassara salo ta waɗannan siffofi da suka haɗa da: salo wani yanayi ne
da ya ƙunshi
zaɓi cikin rubutu ko
furuci, salo ƙari ne na daraja ko armashi a cikin rubutu ko furuci, salo ya
shafi kaucewa daidaitacciyar ƙa’ida, salo harshen wani mutum ne, wato
kowane mutum da irin yadda yake tunani kuma tunanin mutane biyu babu ta yadda
za a yi ya zama iri guda (Ɗangambo, 1982:1, 2007:37).
Salo wata dabara ce da za a iya
yi wa harshe ado da ita kuma hanya ce ta sarrafa harshe a jujjuya shi ta yadda
za a iya taƙaita
manufa ko a sakaya ma’ana ko kuma kaifafa tunani (Gusau 2003:54).
Ta duban waɗannan ma’anoni da aka kawo,
ana iya cewa salo dabara ce ta isar da saƙo ta hanyar amfani da kwalliya da sarrafa
harshe domin ganin an isar da saƙon cikin armashi da ban sha’awa.
Karin Magana
Wasu daga cikin masanan da suka
tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar karin magana sun haɗa da: Finnegan (1970) a
inda ta ce:
Karin magana jerin kalmomi ne mai
dubun hikima da zalaƙa wanda ke zuwa a gajarce, tare da ma’ana mai gamsarwa idan
aka tsaya aka yi sharhi.
Tudun wada (1982) yana ganin ba
wani abu ne karin magana ba illa, magana ce wadda ake lanƙwasa
ta, ta yi daɗin ji a
kunne ta kuma yi ma’ana.
Shi kuwa Bichi (1997) ya nuna
cewa:
Karin magana magana ce da take ƙunshe
da hikima a cikinta, kuma tana bayyana hoton rayuwa da tunanin al’ummar da ke
amfani da ita.
Gwammaja (2010) shi ma ya bayyana
ma’anar karin magana da cewa:
Salo ne na yi wa mutum nasiha a
kan wani abu da ya yi marar kyau, domin kada a fito ɓaro – ɓaro
a sanar da shi halayensa musamman idan akwai kunya a tsakaninsu.
Bugaje (2014) kuma sai ta bayyana
cewa:
Karin magana, magana ce mai tsawo
wadda aka dunƙule ta, ta zama gajera cikin hikima, da zalaƙa kuma
ta ƙunshi
ma’ana mai yawa in za a tsaya a warware ta.
A taƙaice za a iya cewa karin
magana tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaƙa tare
da bayar da ma’ana gamsasshiya mai faɗi,
mai yalwa, musamman in aka tsaya aka yi bayani daki-daki. Wato karin magana taƙaitacciyar
magana ce `yar ƙil wadda ta ƙunshi hikima da zantukan ma’ana.
Farfesa Abdullahi Bayero Yahya
Farfesa Abdullahi Bayero Yahya
wanda mafi yawan abokai da ɗalibansa
suka fi sani da Fafesa A.B. Yahya haifaffen garin Sakkwato ne a unguwar Giɗaɗawa. An haifi Farfesa a shekarar 1953. Kamar
yadda yake a al’adar ƙasar Hausa an tura shi makarantar allo yana da shekara uku
zuwa huɗu, a ƙarƙashin
malaminsu Malam Haliru. Lokacin da ya cika shekara bakwai sai aka sanya shi a
makarantar Firamare ta Waziri Ward Primary School, wadda daga baya aka sauya
mata suna zuwa Waziri Model Primary School, a inda ya yi shekara shida saɓanin bakwai da ake yi a
Firamare a wancan lokacin. Hakan ya faru ne a dalilin ciyar da shi gaba da aka
yi da ƙarin
aji guda, wanda galibi akan yi wa yara masu hazaƙa ko girma. A shekara 1967 ne ya samu
shiga makarantar Sakandirn gwamnnati da ke Birnin Kebbi, a inda ya kammala a
shekarar 1971. Da kammala makarantar sakandire sai ya fara aikin koyarwa a
farkon shekarar 1972, a inda ya fara aikin koyarwar a makarantar Firamare da ke
Kware, duk da cewa abokansa sun fi son da su haɗu
su nema gurbin karatu na fagen share shiga Jami’a a Bayero, wadda a lokacin ake
kira da Abdullahi Kwalejin Bayero, amma shi kuma ya fi sha’awar shiga Babbar
makarantar horon malamai Adɓance
Teachers College Sokoto, domin samun takardar Shaidar aikin Malanta. A cikin
shekarar ne kuwa ta 1972 a watan Oktoba ya samu gurbin karatu a Kwalejin Ilimi
Ta Shehu Shagari da ke nan Sakkwato, a inda ya kammala a shekarar 1975.
Abdullahi ya yi gwajin koyarwa da ake tura ɗalibai
masu neman ƙwarewa
a fannin koyarwa a a Makarantar horon Malamai ta Gusau da kuma ta Bida a
shekarat 1974 da 1975.
Bayan kammala karatun da ya yi na
Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari sai ya fara aiki inda aka tura shi Sakandirin
Gwamnati ta garin Anka, inda ya zauna har zuwa shekarar 1978, a inda ya samu
gurbin karatu a jami’ar Bayero Kano. Farfesa ya kammala karatun digirinsa na
farko a fannin Hausa da Ilimin addinin Musulunci, a shekarar 1981, sannan ya yi
aikin yi wa ƙasa
hidima a shekarar 1982, wanda bayan ya kammala ya sake samun gurbin karatu a
Jami’ar ta Bayero domin karatun digiri na biyu a fannin Hausa. Farfesa ya fara
aiki a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo a shekarar 1983. Bai jima da soma aiki a jami’a ba ya
soma karatun digiri na uku. Wanda ya kasance cikin mutum uku na farko da aka
fara yaye wa a matakin digiri na uku a wannan sashe na Hausa, a shekarar 1987.
Tafiya ta yi tafiya, Farfesa
Yahya tun daga matakin Assistant Lecturer har ya kai Farfesa a shekarar 2003,
yau shekara ashirin ke nan. Shehin malamin ya riƙe muƙamai da dama tun a ciki da wajen ƙasar
nan. Daga cikin muƙaman har da shugaban Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da
Sakkwato. Farfesa ya ba da gudummuwa mai tarin yawa, ya yaye ɗalibai tun daga masu digiri
na uku, wanda yanzu haka daga ɗalibansa
akwai masu matakin farfesa da ma gwamnoni da ‘yan majalisu na tarayya da sauran
manyan ma’aikatan gwamnati a mataki daban-daban. A fannin rubuce-rubuce ya
rubuta littattafai da har zuwa yau ana amfani da su a duniyar ilimi, ban da
tarin maƙalu
masu dama, a shahararrun mujallu na ƙasa (Department of Nigerian Language,
UDUS 2023).
Salon Amfani da Karin Magana a
Waƙa
Shehin Malami Farfesa Abdullahi
Yahya ya bayyana cewa daga cikin salon da mawaƙa suke amfani da shi a waƙoƙinsu
har da amfani da karin magana. Ya nuna salo a matsayin wata dabara wadda mawaƙa suke
sarrafawa don isar da saƙonsu ga mai karatu ko sauraren waƙarsu ba tare da ƙosawa
ko gajiyawa ba. Akwai hanyoyi guda uku waɗanda
ya ce da a kan su ne mawaƙa suke ɗora
karin magana a cikin waƙarsu.Ga waɗannan
hanyoyi guda uku kamar yadda masanin ya bayyana.
Faɗaɗa Karin Magana
Kalmar faɗaɗa
tana nufin ƙara
wa abu faɗi (CNHN,
2006: 129). Mawaƙa suna amfani da karin magana a waƙa domin su faɗaɗa wannan karin magana, su kambama ta domin ya
zama sun ƙara
fito da saƙon
sarari yadda za a fahimta. Sai dai wani abin luara a game da wannan salo shi
ne, da yake idan Bahaushe ya tashi faɗaɗa abu yakan yabe shi ne ya
kururuta shi ya kuma kambama shi ya nuna ya fi kowanne, wannan ya sa maganar
takan zama tamkar kirari, amma idan aka ɗora
zancen bias faifan nazari, sai a ga karin magana ne, illa dai kawai an jirkita
ta sannan aka sarrafa ta wata sigar daban. Dubi misalin wannan baiti da Shehin
Malamin ya bayar a littafinsa:
Ana iya shafa kan mussa,
Na jibda ba ka farawa.
Ana iya kama ɗan buku,
Mijirya ba ka damƙowa.
Fura aka kwankwaɗa amma,
Kunu kam sai da kurɓawa.
Mutum in ya biɗo canji,
Abinai an na renawa.
(Alƙali Haliru Wurno: Ko ba ka Raƙumi ka
San Cau)
Baitukan cike suke da karuruwan
magana waɗanda suka yi
kama da kirari, amma ba kirari ba ne. Sannan dubi ƙarin wannan misalin wanda
ya yi kamada kirari, amma dai karin maganar tana nan a baitin:
Giwa du’abin da tah haifa,
Ai an shedi bai zamma taffa,
Domin ya wuce shiga kwalfa.
(Alhaji Garba Gwandu: Waƙar
Makaman Gwandu Balarabe)
Idan aka duba waɗannan misalai da ya Yahya,
(2016:14) ya kawo sai a ce wannan ai kirari ne a saboda siffofin kirari da ya
bayyana cikin baitin, amma abin da ya fito fili na karin magana shi ne ‘Ɗan
giwa, giwa ne’ wanda hakan ya yi kama da kirari. Wato dai karin maganar ita ce
ta faɗaɗa saƙon da ake son a isar. Wannan
kuwa ba wani abin mamaki ba ne, domin a cewar Zarruk da Alhassan, (1982:3-10),
akan iya canza karin magana a mayar da shi kirari, saboda lanƙaya
shi da mai yin kirarin yake yi ga kan sa. Misali:
4. Yaro da goriba sai lasa,
Ba gurgurar ta ko gutsura ba.
(Rabi’u Nguru: Faɗi Sosai)
A wannan baiti mawaƙin ya
yi amfani da karin maganar nan da Hausawa suke cewa “Yaro da goruba sai lasa”.
Bai bar karin maganar haka ba, sai ya faɗaɗa ta domin ya ga ya fito da
asalin ma’anar karin maganar. Faɗaɗawar a nan ita ce inda ya
yi ƙoƙarin
nuna cewa goriba gurgura akeyi, ko a gutsura idan an gurgura, amma a wajen yaro
marar haƙoƙi bai
iya gurgurar balle kuma ya gutsura. Wato dai mawaƙin ya yi amfani da wannan karin magana
wajen gwarzanta gwaninsa jagoran gwagwarmayarsu da kuma kambama shi, ta hanyar
kamanta yadda yaro marar haƙoƙi ba ya iya yin komai da goruba, in ba ya lasa ya bari ba,
haka maƙiya
abokan adawa ba za su iya yin komai da shi ba, balle su ci galaba a kan sa.
Dubi yadda kuma aka kawo wannan
salo a baitin da ke cewa:
Shiru an faɗa ai ba kwa tsoro ba ne,
Kamar ja wurin rago misalinmu ne,
Ku duba kunama ga ta ‘yar ƙanƙane,
Idan har ta harbi amale sai ka ga
yai makuwa.
(Mustapha Umar Baba: Fito – na –
Fito)
A wannan baitin kuma mawaƙin ya
sarrafa karin maganar nanne da Hausawa suke cewa “Shiru-shiru ba tsoro ba ne,
gudun magana ne” da kuma “Ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, shirin faɗa ne”. Mawaƙin ya
yi amfani da karin maganar ne wajen kambama masu gwagwarmaya da nuna cewa a bar
ganin suna ƙyale
duk wani abin da ake yi musu na musgunawa da zalunci, ba fa wai tsoro ba ne, ba
su da tsoro. Wataƙila, idan da a magana ce ta yau da kullum ake son faɗa wa wani ana iya ce mashi
ka bar ganin ana ƙyale ka, idan kayi zalunci, akwai abin da muke dubawa, amma
maimakon haka sai ya ce “ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, shirin faɗa ne” wannan zai sa abokin
adawa ya kaɗu ya shiga
tunanin ko wane irin mataki za su ɗauka
nan gaba. Har ma a a wani ɗango
na baitin yake kambama maganar da ba da misali da cewa ka dubi dai duk girma na
raƙumi
amma kunama sai ta sabauta shi, to su ma fa a bar ganin su ‘yan ƙalilan
yara, idan suka taso to sai sun sa abokin adawa ɗimuwa.
Har wayau dangane da amfani da
salon faɗaɗa karin maganam akwai:
Gobarar dare ta watan bakwai ga
rani kan kore,
Ta kama ta tsaya gidan su mai wa
Amo takkai.
(Audu Makaho: Waƙar Mai
wa Amo Takkai)
Nufin mawaƙin yin baƙar
addu’a ga abokin adawarsa kamar yadda baitin ya nuna. A maimakon haka, sai ya
yi amfani da karin magana nan na Hausawa da suke cewa “Watan bakwai, maƙarar
rani”. Ya yi hakan ne don ya kambama addu’ar tasa inda ya roƙi
Allah kan gobara ta taho ta kama gidan abokin adawarsa, kuma ya nuna yadda yake
son gobarar ta kasance mai muni; ta zo cikin dare kuma a watan bakwai. Shi kuwa
watan bakwai tsakiyar rani ne, ga ba isasshen ruwa a gulabe da tafkuna da za a
iya ɗiba a kai
gudummuwa domin a kashe, ga shi kuma lokacin rani lokaci ne na iskar bazara, da
ke kaɗawa. Ita kuwa
gobara da iska ba a shiri, ana kashewa ne, iska na ƙara yaɗa ta da rura ta.
Gutsure Karin Magana
Mawaƙasukan yi amfani da karin
magana a waƙa
ta hanyar gutsure shi. Za a samu cewa mawaƙi yakan faɗi
muhimman kalmomin da karin maganar ya ƙunsa ya bar sauran domin mai saurare ko
karatu ya cike su. Waɗannan
kalmomi da mawaƙi yake gutsurewa kan iya zama kalma ɗaya ko sama da haka, gwargwadon yadda ba zai
shige wa mai sauraro ko karatu duhu ba. Rubutattun waƙoƙin Hausa sukan zo da wani
abu makamancin haka, kamar yadda aka samuwani mawaƙi yana cewa:
9. Idan ko kun ƙi ji,
To wallahi kun shiga ukku.
(Abdullahi Lushi: Laƙad
Ja’al haƙƙu)
Wannan karin maganar ba ta cika
ba, mawaƙin
ya katse ta, bai ƙarasa ta ba, da niyyar mai saurare ya ƙarasa. Karin maganar nan
ce da Hausawa suke cewa “In an ƙi ji, ba a ƙi gani ba”. A wannan baiti mawaƙin ya
yi amfani da karin maganar ne domin jan kunnen ‘yan sanda waɗanda a waƙar ya
ce su ne ake tura wa suna dukansu idan suna tarurrukansu ko wa’azozinsu na
addini. Wato yana gargaɗinsu
da cewa ranar da za su fara rama dukkan abin da suke yi masu, to su ma sun
shiga uku, don kuwa ba za su sassauta masu ba.
Ƙirƙiro Karin Magana
Mawaƙa suna amfani da ƙirƙirarrun
karin magana a waƙoƙinsu domin nuna ƙwarewa da iya sarrafa harshe gami da naƙaltarsa.
Irin waɗannan karin
magana sun samu ne daga baya sakamakon wayewa ta cuɗanya da wasu al’ummu. Mawaƙan
sukan ƙirƙire su
ne domin su dace da manufar waƙar ko kuma baitin waƙa. Ga
wasu misalai kamar haka:
43. Allah shi ne yai badame
sannan yai bahago,
Ba ka tanƙwaruwa kwamandan yaƙi
gamji go,
Ga jirgin tsira yana ta sanarwa I
will go,
In ba san banza ba wane ne zai
hau jirgin salula.
51 Dubi halittar doki Allah ne
yai ba wani ba,
Dubi irin sukuwarsa bai sa mai
shak – zoba ba,
Duba yadda yake gudu kuma ba da
karan-shaf ba,
Ba sitiyari babu hon motar ƙudurar
Allah ta’ala.
(Mustapha Umar Baba: Waƙar
Tauhidi)
Abin lura a waɗannan baituka shi ne, mawaƙin ya
yi amfani da wasu karin magana guda biyu da a iya cewa ƙirƙirarru ne, kuma domin su
dace da saƙon
da yake so ya fitar cikin baitocin. A baiti na43, mawaƙin ya yi amfani da karin
maganar da ya kira ‘son banza mai sa a hau jirgin salula’. Ma’anar abin da mawaƙin ke
nufi da jirgin salula ya fito a ɗango
na uku, wanda ke nufin shi jirgin salula kishiya ne na jirgin tsira. Wannan
kuwa ya yi canjaras da hikimar Hausawa da suke cewa motar ƙwaɗayi ba ta da masauki sai
tashar walaƙanci,
shi kuwa kwaɗayi da
son banza duk tushensu ɗaya
ne, Ɗanjuma
ne da Ɗanjummai.
Haka abin ya kasance abaiti na 51
inda ya yi amfani da ƙirƙirarriyar karin magana domin ta yi daidai da manufar waƙarsa,
wato inda ya ce “Ba sitiyari babu hon motar ƙudurar Allah ta’ala”. A zahiri wannan
magana ce a dunƙule, wanda in an fassara za a samu faffaɗar ma’ana. Mawaƙin ya
yi amfani da wannan magana wajen nuna ƙudura ta ubangiji, yadda ya halicci doki
ake amfani da shi tamkar yadda ake amfani da mota abin hawa. Sai ma ya nuna shi
ya fi ma mota, domin shi ba sitiyari ba karan – shaf da sauran abubuwa da in
suka lalace mota za ta tsaya.
A gaba an samu baitin da ke ɗauke da wannan salo kamar
haka:
7. Kasuwa da gida gun kwanciya
duk kuna jin tsoro,
In ka hau mota tsautsayinka kake
sauraro,
To barejirgin sama makarar sama
ce jirgin Nijeriya.
(Nura
Shahidi: Waƙar
Talakan Nijeriya)
Mawaƙin ya yi amfani da zance
na hikima a dunƙule da take ɗauke
da wata ɓoyayyiyar
ma’ana, wanda shi ne abin da ake nufi da karin magana. Wannan magana da za a
iya cewa ƙirƙira ya
yi, ita ce inda ya nuna jirgin sama ba komai ba ne ga talakawan Nijeriya face
akwatin gawar su, wato“makarar sama ce jirgin Nijeriya”. Mawaƙin
yana nuna irin taɓarɓarewar tsaro a ƙasar
Nijeriya, wanda yawan haɗarin
da jirage suke yi a saboda rashin gyara ko nagarta tamkar mutum ya shiga
makararsa ta mutuwa ce. Wato ke nan idan jirgin sama ya yi hatsari akan ce
wannan jirgin sama ne kuwa ko dai makarar sama.
Dalilan Amfani da Karin Magana
Ta wannan ɓangare kuwa, Shehin Malamin ya bayyana cewa
ana amfani da karin magana a waƙa a saboda wasu dalilai da suka haɗa da yin ishara da ƙarin
bayani da nuna ƙwarewa ga harshe da kuma adana karin magana. Da yawan marubuta
waƙoƙi suna
amfani da karin magana saboda waɗannan
dalilai da ya bayyana, kamar yadda aka tsinakayi misalai daga waƙoƙi.
Yin Ishara
An bayyana ma’anar Ishara da cewa
“An Illustration; indication; adɓice;
fore-warning” (Bargery, 2016: 480). Wato daidai ne ace tana nufin misali, ko
nuni ko kuma shawara mai kyau ko hani. An kuma ƙara bayyana ma’anar kalmar ishara da cewa
tana nufin nuni, ko sanarwa (CNHN, 2006:208). Wato abin nufi shi ne nuni zuwa
ga wani abu, la’alla abin da ake gani ne kurum ko ake iya taɓawa, ko nuni ga wata magana
ko zuwa ga gaskiya. Misali:
69. Burazas ku sa ƙaimi
haba ‘yan uwa,
Haƙa ta yi nisa tun da ta kai ruwa,
Haƙiƙa akwai nasara da ba makawa,
Ku dage ku cije babu shakkar uban
kowa.
(Mustapha Umar Baba: Waƙar
Fito-na-fito)
A wannan baiti mawaƙin ya
yi amfani da karin maganar da ke cewa “haƙa ta cim ma ruwa” wajen yin ishara ga
abokan gwagwarmayarsu a kan su ƙara tashi tsaye su ƙara ƙoƙari
kuma su zage damtse domin kuwa burinsu ya soma cika, nasara za ta samu a wannan
fafutika da suke yi. Wato dai kai ka ce wani albishir ne mawaƙin
yake yi wa ‘yan gwagwarmayarsu.
Sannan kuma akwai:
11. Ai ƙofar Allah da yawa take
ta ma fi ƙofar
cali,
Don mun riƙe Allah ake bugunmu ana
ta cin zali,
Ya ‘yan uwa kui haƙuri
Allah shi ne fa alƙali,
In mun tsaya gaban kotun Allah ma
gane mai raki.
(Mustapha Umar Baba: Maganin
Mayu)
Karin maganar Hausawa da suke
cewa “ƙofar
Allah ta fi ƙofar
cali yawa” ita ce ta zama ƙumshiyar wannan baiti. Shigowarta cikin baiti shi ya nuna
ishara ce mawaƙin yake kan cewa duk wata musgunawa da azzalumai suke yi musu
saboda sun ce Allah za su bi, to mabiya su yi haƙuri akwai ranar sakayya. Ka da su ɗauka kamar wannan abu da
ake yi musu ya wuce a banza, a’a yana musu ishara da cewa akwai ranar da
azzaluman za su koka, ranar da za su tsaya a kotun Allah wanda ba a afil.
Ga yadda misalin ya sake bayyana
a gaba:
27. In da rabon a sha dukabari ba ta maganin
komai,
Ɗan tsako ya sami abinci sai ya guje wa
dangi nai,
Sai ran da shirwa ta yi mamaya ya
ga za ta dai cim mai,
Zai zo gurin uwarsa yana ki rufe
ni na tuba na biki.
(Mustapha Umar Baba: Maganin
Mayu)
Nan kuma mawaƙin ya
yi amfani da kare-karen magana guda biyu da nufin yin ishara ga waɗanda suka fita daga cikin
gwagwarmayarsu suka musu tawaye. Su ne mutanen da suke ce musu ‘yan tawayiya.
Kare-karen maganar su ne “mai rabon shan duka ba ya jin bari sai ya sha”. Sai
kuma“Ɗan
tsako samu ka ƙi dangi”.Wato dai mawaƙin yana sanar da abokan gwagwarmayarsu
cewa ka da su damu waɗannan
da suka yi tawaye, rana tana zuwa da za su yi nadama, wataƙila ma
ranar da nadamar ba za ta yi amfani ba. Don kuwa Hausawa suna cewa wanda bai ji
bari ba to zai ji hoho.
Ƙarin Bayani
Ana amfani da karin magana a
cikin baitocin waƙa domin ƙarin bayani ga babbar manufar baiti ko baitocin da ya fito.
Karin maganar kan iya fitowa kamin ko bayn ko kuma cikin baitocin da ya fito.
Marubuta waƙoƙin
gwagwarmaya suna amfani da irin wannan salo a inda sukan yi amfani da karin
magana domin ƙarin bayani a kan saƙon da yake son ya isar. Duba wannan
misalin:
3. Dalilin tsara ƙasidar yanzu asirin zan yaye,
Kwanan can mun kai ziyara wani baƙin ƙauye,
Sai na ji suna faɗin su ma sun zam ‘yan
tawaye,
Kai nasu ya waye sun daina biyar ƙatti
sun amsa saƙo.
Da jin haka ke da wuya da ɗai a kujera na kimtse,
Sai na yi farat nai firgigi har
na rantse,
Ina faɗa ko yau kasuwa ta zamto ta watse,
Shi dai ɗan koli da ribar nan da yac ci yake ta taƙo.
(Abdullahi Lushi: Ya sharafuddini
Haƙiƙa Mun
Shaida ka ida saƙo)
Duba da abin da baitin ya ƙumsa,
mawaƙin
ya yi amfani da karin maganar nan na Hausawa da suke cewa “ko yau kasuwa ta
watse ɗankoli ya ci
riba”. Mawaƙin
ya yi amfani da karin maganar ne wajen fito da bayani na baitin da ya gabaci
wannan, a inda ya nuna cewa ya ji daɗi
ya yi murna ya kuma yi farin ciki yadda ya ga cewa bukatarsu na kiran al’umma
kan su yi wa gwamnatin da ba ta Allah ba tawaye, to ya yi nasara, haƙa ta
cimma ruwa, tun da ga shi har a cikin ƙauyen ƙayau, an samu wasu sun fahimci abinda
suke kira a kan sa. Wato dai wannan karin magana mawaƙin ya yi amfani da ita
wajen bayyana abin da baiti na sama ya ƙunsa.
Haka kuma a gaba an samu cewa:
25. Maƙi gani sai ka kau da idonka don kuwaga
shi nan,
Ya fito ga shi nan kuma ras har
kun ji yai magana,
Ina su kulɓa ina su kurege? ‘Yan dakon fitina?
Marmaza ku naɗe tabarma don ko ga mai
gurin ya dawo.
26. Malaman fada maƙiya to yaya ranku yake,
Kun yi sharrin kun ɓatancin duk a banza yake,
Kun ta kushe malam ga jama’a ta
son sa suke,
Ku ƙara yin himma don sharrin naku ma jama’a
ya kirawo.
27. Kun rubuta takardu kar a sake
shi kun yi kira,
Ahaf! Ulama’us su’i ai fa kun
makara,
Duk ku gane idan Allah ya nufaci ɗan zakara ,
Zai yi cara sai ya yi ko da
muzuru shaho suna kai kawo.
(Tabarmar Kunya: Mustapha Umar
Baba)
Waɗannan
baitoci cikin su mawaƙin ya yi amfani da karin magana wajen ƙarin bayani game da
manufar da yake son ya isar. Karin maganar ita ce inda Hausawa suke cewa “Mai
guri ya zo mai tabarma ya naɗe”,
da kuma karin maganar nan ta Hausawa “Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana
muzuru ana shaho sai ya yi. A baitukan mawaƙin ya nuna cewa shugaban gwagwarmayarsu
yana da maƙiya,
da suka yi ta ƙulle–ƙulle na kar a sake shi lokacin da gwamnati ta ɗaure shi. To da ya fito shi
ne mawaƙin
ya yi amfani da wannan karin magana na nuna cewa to mai guri ya zo fa mai
tabarma sai ya naɗe. Sannan
ya ƙara
fito da manufarsa ta waccan baiti na farko da wata karin maganar a baiti na
gaba da cewa duk wannan makirce-makirce da ake masa in Allah ya nufa, to lallai
ba makawa sai ya kai ga cin nasara. Wato zakaran da Allah ya nufa da ya yi cara
ko ana muzuru dashaho sai ya yi.
Nuna Ƙwarewa ga Harshe
Ana gane ƙwarewar mai amfani da harshe
ta yadda yake amfani da karin magana da sarrafa ta yadda yake so. Waƙar da
aka yi amfani da kare-karen magana takan ba mai sauraro sha’awa, takan kuma yi
armashi. Sannan shaida ce ta nuna cewa mawaƙin ya laƙanci harshen da al’adun masu harshe. Dubi
waɗannan misalai:
Don ana taƙamar ɗinki ai ba a fasa ƙwarya
ba,
Don hangen hadarin nesa ai ba a
yi wanka da kashi ba,
Wanda ya ƙyale malam ban ga abin da
zai kama kuma ba,
Don haka mu komai wuya muna nan
bayanka Zakzaky.
In da rabon a sha duka bari ba ta
maganin komai,
Ɗan tsako ya sami abinci sai ya guje wa
dangi nai,
Sai ran da shirwa tai mamaya ya
ga za ta dai cimmai,
Zai zo gurin uwarsa yana ki rufe
ni na tuba na bi ki.
(Mustapha Umar Baba: Waƙar
Maganin Mayu)
Lokaci guda a cikin baiti ɗaya kacal mawaƙi ya
yi amfani da karin maganabiyu, wanda wannan ba ƙaramar burgewa ba ce da nuna ƙwarewa.
A baiti na 24, da na 25, ya kawo waɗannan
kare-karen magana na Hausawa da suka haɗa
da:“Ba a fasa ƙwarya don taƙamar iya ɗinki”,
da kuma “Ka da hangen hadari ya sa ka wanka da kashi”.Dukkan waɗannan karin maganganu sun
zo a waƙar
ne da nufin nusar da mutane cewa abin da bai wadace ka ba, ko bai zamo naka ba,
ba za ka yi saurin sakin na hannunka ba, kamar dai yadda mutum ba za ya ɗebo kashi ya yi wanka da
shi don ya hangi hadari ba. Ko kuma ya fasa ƙwaryarsa don yana taƙamar
ya iya ɗinki ba.
Wato dai manufar mawaƙin shi
ne yi wa masu da’awar tawaye ga kiran malaminsu jagorar gwagwarmayarsu shaguɓe da cewa sun saki reshe ne
fa sun kama ganye, wato sun bar tsira sun nufi halaka.
Haka abin ya kasance ga baitina
gaba wato na 25, inda ya sake amfani da wasu kare-karen maganar su ma guda biyu
a jere don ƙara
nuna ƙwarewa
ga harshe. Waɗannan
karin magana su ne inda Hausawa suke cewa “Idan da rabon a sha duka, bari ba ta
magani” da kuma “Ɗan tsako samu ka ƙi dangi”. A wannan baiti mawaƙin ya
ida warware zancensa da ya ƙullo a baiti na baya wato na 24, da cewa duk yadda za a nuna
wa mutum tsira, to fa idan ba shi da rabo, ba za ya bi ba, wato idan da rabon a
sha duka, to bari ba ta magani. Kuma idan har mutum ya bar danginsa to ba wayau
ya yi ba, lallai wata rana zai yi da–na–sani, har ya zo neman gafara.
Adana Karin Magana
Za a ƙarƙare bayani da bayyana
cewa ana amfani da karin magana a waƙoƙi domin ya zama an adana da taskace karin
magana. Wato ke nan waɗannan
kare-karen magana da aka kawo aka ba da misalai da su a wannan takarda sun samu
takaskacewa, kuma za su zama masu amfani gaba tun da har zuwa yanzu suna nan
cikin waƙoƙin,
wanda hakan ne ma ya ba da dama har aka same su aka yi nazarin irin matsayin da
suka fito da irin amfanin da aka yi da su, da moruwar da aka samu daga gare su.
Kammalawa
A wannan takarda kamar yadda aka
gani, kuma bayani ya gabata, an dubi yadda masani Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin
Hausa, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya bayyana yadda ya kamata a yi amfani da
salon amfani da karin magana ne, a waƙoƙin Hausa, a inda aka gwada duba wannan
hanya, aka yi amfani da misalai daga wasu waƙoƙin Hausa wajen bayar da misalai. Sai dai
an gano cewa baya da waɗannan
salalai da Shehin Malamin ya bayyana, na yadda ake amfani da karin magana, an
gano cewa mawaƙa suna amfani da karin magana a waƙoƙinsu ta hanyar sarrafa
karin maganar ya zama kirari. Idan mutum ya siffanta kansa da wani karin
magana, to wannan karin maganar ya zama kirari ke nan.Wannan ma salo ne.
Manazarta
Auta, A. L. (2015). Faɗakarwa a rubutattun waƙoƙin
Hausa, Kano: BUK Press
Bunza, A.M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic
Publication Centre Ltd.
CNHN, (2006). Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero, Zaria: Ahmad Bello University Press.
Department of Nigerian Language,
(2023). Flier for call of paper, for A Festschric in hounor of Professor
Abdullahi Bayero Yahya, Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin
Hausa.Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.
Ɗangambo, A. (1982). “Rikiɗar Azanci: Siddabarun Salo
da Harshe Cikin ‘Tabarƙoƙo’ Tahamisin
Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin
Hausa da muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa, Kano: Triumph Publishing Company
Limited.
Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar
Gadon Feɗe Waƙa,
Kaduna: Amana Publishers Limited.
Gusau, S.M (2003). Jagoran
Nazarin Waƙar
Baka Kano: Benchmark Publishers Limited.
Hassan, M.B (1982). “Karin Magana
da Salon Maganar Hausawa”, Nazari a kan Harshe, da Adabi, da Al’adu. Cibiyar
Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Koko, H. S. (2011). “Hausa Cikin
Hausa”. (ba maɗaba’a).
Lawal, N. (2016). Tarƙaƙƙen
Nazarin Rubutattun Waƙoƙin Noma Na Gasar Argungu Ta 1982.Kundin digiri na Uku. Kano:
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Malumfashi, I. da Ibrahim, M.
(2014). Ƙamusun
Karin Magana. Kaduna: Makarantar Bambadiya Publishers.
Mukhtar, I. (2005). Bayanin
Rubutattun Waƙoƙin Hausa. Area 7 Garki Abuja: Country Side Publishers Limited.
Sarɓi
S.A (2007). Nazarin Waƙen Hausa, Kano: Samrib Publishers.
T/wada, Y. Y. (1982). “Tsari da
Ma’ana a Karin maganar Hausa”, Nazari A Kan Harshe, da Adabi, da Al’adu.
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Omar, S. (2013). Fasahar Mazan
Jiya: Nazari a Kan Rayuwa da Waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja.Sokoto: Garkuwa Media Services Ltd.
Umar, M. B. (1987). Dangantakar
Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishers.
Yahya, A.B. (2007). Jigon Nazarin
Waƙa,
Kaduna: Fisbas Media Services.
Yahya, A.B. (2016). Salo Asirin
Waƙa.
Sokoto: Guaranty Printers.
Yahya, A.B. (2002). “Siffantawa
Bazar Mawaƙi:
Wani Shaƙo
cikin Nazarin waƙoƙi”. Studies In Hausa Language, Literature and Culture the
Fifth Hausa International Conference, Centre for the study of Nigerian
Language, Bayero University Kano.
‘Yar’aduwa, T.M, da Junaidu, I.
(2007). Harshe da Adabin Hausa A kammale Don Manyan Makarantun Sakandire.
Ibadan: Spectrum Books Limited.
Zarruk, R. M. da Wasu (1987). Sabuwar
Hanyar Nazarin Hausa Don Kananan Makarantun Sakandire. Littafi Na Ɗaya –
Uku. Ibadan: University Press PLC.
Zarruk, R. M. da Alhassan, H.
(1982). Kirarin Duniya 222. Zaria: Ganuwa Publishers Limited.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.