Citation: Muhammad, H. (2024). Salon Amfani da Ƙissa a Wasu Rubutattun Waƙoƙin Siyasa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 589-597.
Salon Amfani da Ƙissa a Wasu Rubutattun Waƙoƙin Siyasa
Hassan Muhammad
Department of Nigerian Langauges, Sokoto State
University, Sokoto
Tsakure: A wannan nazari za a yi ƙoƙarin fito da
wasu ƙissoshin Alƙur’ani mai girma a taƙaice waɗanda wasu mawallafa rubutattun
waƙoƙin siyasa suka naɗe su a cikin wasu baitocin waƙa. Sanin kowa ne cewa rubutattun waƙoƙin siyasa ana
wallafa su ne don tallata jam’iyya ko ɗan takara ko ƙushe jam’iyyar hamayya ko wani abu makamancin waɗannan. Su waɗannan ƙissoshi da mawallafa waƙoƙin siyasa ke
amfani da su na daga cikin salailan da suke amfani da su wajen isar da wani saƙo wanda ya yi daidai da abin da wani ɗan takara ya aikata ko magoya bayansa suka aikata don ya zama abin koyi
idan wannan abin na ƙwarai ne, ko ya zama abin gujewa idan wannan abin mummuna ne..
Fitilun Kalmomi: Salo, Ƙissa, Rubutattun Waƙoƙi, Waƙoƙin Siyasa
1.0 Gabatarwa
Waƙa rubutacciya ko ta baka hanya ce ta isar da saƙo, musamman kan abin da ya shafi harkar ilimi ko faɗakarwa kan
sha’anin zamantakewa ko siyasa ko tarbiyya ko lamarin addini da dai sauransu da
dama. Waƙa a kowane harshe na duniya ita ce kan
gaba wajen bunƙasa da ɗaukakar adabin
wannan harshe, domin ita ke nashe dukkan sassa na rayuwar al’ummar da ke magana
da harshen. Waƙa takan yi ruwa da tsaki kusan a kowane
fanni na rayuwar al’umma. Ta yadda za a iya gyara al’umma ta zama mai kyawawan
halaye da ita, ko kuma a gurɓata ta da ita; ana iya tunzura mutane
ko a zuga su zuwa ga fusata ko kuma a kwantar masu da hankali da ita; ana iya
ba su ilimi cikin sauƙi har su gwanance ko kuma a jawo
hankalinsu zuwa ga muhimmin abu, a wayar musu da kai da ita.
Ƙissoshin Alƙur’ani ɗauke suke da
fa’idoji da yawa, saboda suna zuwa da labarun abubuwan da suka faru da daɗewa na gaskiya waɗanda ke sa idan
mutane suka ji su, za su hankaltu su daina
abubuwan da ba na kirki ba. Daga cikin
waɗannan ƙissoshi akwai na Annabawa kamar Annabi
Muhammadu (SAW) da sauran Annabawa ashirin da huɗu da aka ambaci
sunayen su cikin Alƙur’ani. Akwai ta sauran mutane waɗanda ba Annabawa
ne ba, akwai ƙissar wasu halittu waɗanda ba mutane ba.
An fara samun waƙoƙin siyasa tun
lokacin jihadin Mujaddadi Usmanu Ɗanfodiyo inda suke
yin amfani da su wajen yaɗa manufofin addinin Musulunci. Hiskett
(1977: 94) yana da ra’ayin cewa, waƙa a kowane lokaci
hanya ce ta yaɗa farfagandar siyasa a cikin Musulunci. A al’adar Bahaushe akwai shi da son
ya waƙe duk wani sabon al’amari da ya zo
masa. Wannan dalili shi ya sa lokacin da al’amarin siyasa na jam’iyyu ya zo
masa sai ya shiga waƙe su a inda yake bayyana yanaye-yanayen
tsarinsa tare da sigoginsa (Funtua, 2010).
2.0 Salo
Salo wani abu ne da ke bayyana saƙo kuma ya kai saƙon inda aka nufa
da shi. Salo dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta
ko ya bayyana. Idan kuwa za a yi wa wannan ma’ana gyara domin a bayyana salo a
cikin nazarin waƙa, ana iya cewa, salo yana nufin duk
wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda mawaƙi ya bi domin ya isar da saƙon da yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙa (Yahya, 2016: 29-30).
Idan aka lura da ma’anar salo da aka
bayar, to da wuya a iya ƙididdige tubalansa
abin nufi a nan shi ne, sai dai a kimanta faɗar abubuwan da
salo ya ƙunsa masu tabbatar da ingancinsa amma
ba a kawo su duka ba. Akwai muhimman tubalai takwas waɗanda masana da
dama suka lura da su, su ne mallakar kalmomi da ƙirar jumla da nau’o’in jumla da siffantawa da rauji da tsarin tunani da
jaddadawa da dangantakar tsari (Yahya, 2016: 30).
Shi kuma Sarɓi (2007: 128) ya
bayyana cewa salo da sarrafa harshe abubuwa ne guda biyu waɗanda aka ɗauka kamar tagwaye
ba faye rabe tsakaninsu ba a fagen nazari. Ya ce ana amfani da salo ne a
sarrafa harshe, sannan kuma iya sarrafa harshe na taimakawa wajen amfani ko zaɓar irin salon da
ya dace a yi amfani da shi. Ya ci gaba da cewa salo a fagen nazarin waƙa hanya ce da marubuta waƙoƙi ke bi wajen isar da saƙonus ga jama’a. Salo dabara ce mai wahalar bayyanawa, don
haka ne ya bambanta tsakanin marubuta. Wannan ya sa za a ga kowane marubuci da
irin nasa salon. Haka kuma ana iya samun marubuci ɗaya ya yi amfani
da salo daban-daban dangane da sha’awarsa ko lokaci ko yanayin da ya samu kansa
a ciki da kuma irin saƙon da yake son sadarwa ga jama’a.
3.0 Waƙoƙin Siyasa
A cikin ƙamusun Larabci Almunjid Fil Lugah an bayyana kalmar siyasa da cewa
tana nufin kawo gyara ga talikai tare da shiryar da su zuwa ga wata hanya wadda
za ta kuɓutar da su duniya da lahira ta ɓangaren hukunci, da kuma aiwatar da
ayyuka da ke ƙarfafa daula na ciki da wajen ƙasa (Muhammad, 2019: 36).
Birniwa, (1987) ya bayyana cewa akan
tsara waƙoƙin siyasa musamman
don tallata jam’iyya da manufofinta da kuma kushe jam’iyyar hamayya tare da
shugabanninta da magoya bayanta.
Funtua, (2010) ya faɗi dalilai huɗu da yake ganin a
kansu ne ake shirya waƙoƙin siyasa, dalilan
su ne:
-
Akan shirya waƙoƙin siyasa domin yabo ga shugabannin
jam’iyyu da wasu fitattun ‘ya’yan jam’iyyun.
-
Akan shirya waƙoƙin siyasa domin tallata jam’iyyu da
‘yan takara.
Akan shirya waƙoƙin siyasa domin bayyana hamayya/adawa
tsakanin jam’iyyu.
Akan shirya waƙoƙin siyasa domin bayyana irin yanayin
rayuwar da al’ummar ƙasa suke ciki a sakamakon irin yadda
ake gudanar da mulkin ƙasa.
Ƙissa
Kalmar ƙissa Balarabiya ce, a luga tana nufin labarun da ake ruwaitowa. Haƙiƙa Allah maɗaukakin Sarki Ya
ambaci ƙissoshin waɗanda ya ba da
labari da su cikin littafinsa mai girma inda yake cewa “Kamar wancan ne Muke
labartawa a gare ka, daga labaran abin da ya gabata….” (Gummi sura ta 20: 99).
A wani wurin kuma Allah maɗaukakin Sarki yana cewa “Wancan yana
daga labaran alƙaryoyi. Muna ba ka labarinsu, daga gare
su akwai wanda ke tsaye da kuma girbabbe” (Gummi sura ta 11: 100). A wani wurin
Ya sake cewa “Mu Muna bayar da labari a gare ka, mafi kyawon labari (Gummi sura
ta 12: 13). Ƙissa a ma’ana ta ilmi ta malaman adabin
Larabci ba ta tabbatu a kan wani dalili iyakantacce ba, sai dai wani lokaci ana
amfani da ita don wani dalili da ya tattara ga wani fannin abin da ake ƙissantawa wanda ya game nau’o’i daban-daban na labari
kamar ruwaya da ƙissoshi da hikayoyi ko wani abin da
yake aukuwa can ba a rasa ba (Larabawa na kiran wannan abin nadir, ko kuma abin
da yake aukuwa lokaci-lokaci kamar mu’ujizar Annabawa (Yaƙub, ba shekara: 980). Nadir shi ne abin da bai cika faruwa ba a al’ada, sai
can ba a rasa ba, misali shi ne haihuwar da Allah Ya ba Annabi Zakariyya (AS)
yana da shekaru ɗari da ishirin (120), matarsa Hannatu na da shekara tis’in da takwas (98).
A harshen Hausa kuwa, ƙissa na ɗaukar ma’anoni daban-daban. A cewar
Sa’id, (2006: 282) ƙissa na da ma’ana biyu. Ta farko ita ce
ƙissa na nufin labari na musamman game
da Annabawa da sahabbai da mala’iku wanda yakan fito a cikin Ƙur’ani da sauran littattafan addini. Ma’ana ta biyu ita
ce labari.
Ɗangambo, (2011: 34) ya ba da ma’anar ƙissa da cewa
labari ne na gaskiya (ba almara ba) na wasu Annabawa. Labari ne wanda ya ƙunshi wani Annabi. Kuma labari ne wanda yake cikin Alƙur’ani mai girma. Misali, ƙissar Annabi Yusuf A.S. da matar sarkin Masar.
Muhammad (2019: 39) ya ce ƙissa na nufin duk wani labari da za a faɗa na gaskiya, ba ƙarya a cikinsa, kuma ya zama an kafa hujja da Alƙur’ani da hadisai ingantattu na Annabi Muhammad (SAW).
Duk labarin da ya cika waɗannan sharuɗɗa, to shi ake kira
da ƙissa.
4.0 Nau’o’in Ƙissa
Alƙur’ani mai girma ya zo da labarai masu yawa kan abubuwa daban-daban.
Labaran sun bambanta ta fuskar manufa, yanayi da kuma lokaci. Wannan ya sa aka
kasa ƙissoshi zuwa gidaje kamar haka:
-
Ƙissoshin Annabawa kamar Annabi Adamu da Nuhu da Ibrahim da sauransu amincin
Allah ya tabbata gare su baki ɗayansu.
-
Ƙissoshin mutanen kirki waɗanda ba Annabawa ba kamar Luƙuman da Zulƙarnaini da Uzairu
da Ɗaluta da sauransu.
-
Ƙissoshin mata kamar Hauwa’u matar Annabi Adamu (AS) da Asiya matar Fir’auna
da Maryama ɗiyar Imrana da matar Annabi Nuhu (AS) da matar Annabi Luɗu (AS)[1]
da sauransu.
-
Ƙissoshin wasu al’ummomi kamar irin Samudawa da Adawa da Mutanen Tubba’u da
Ashabul Kahfi da Ashabul Aikati da Ashabul Ukhdudi da Ashabus Sabti da Ashabul
Fili da sauransu.
-
Ƙissoshin ashararu kamar irin su Fir’auna da Ƙaruna da Jaluta da Samiri da Namarudu da sauransu.
-
Ƙissoshin dabbobi kamar tururuwa da alhudahuda na Annabi Sulaiman (AS) da
Saniyar Bani Isra’ila da hankakan ‘ya’yan Annabi Adamu da taguwar Annabi Salihu
da kifin da Annabi Yunusa (AS) ya yi zama a cikin cikinsa lokacin da ya faɗa ruwa da
sauransu.
Yanzu kuma kai
tsaye za a ci gaba da kawo gundarin wannan nazari wato wasu ƙissoshi a wasu waƙoƙin siyasa.
4.1 Ƙissar Ƙabila da Habila da Alu Yaƙub
Aƙilu Aliyu
shahararren mawaƙi ne kuma shugaban mawaƙa a lokacinsa a jihar Kano, kuma malamin addini ne
masanin Alƙur’ani. Wannan ne ya sa ya yi amfani da
hikimarsa ya gitto wani abu na ƙissar Habila da Ƙabila da kuma Alu Yaƙub a cikin wani baitin waƙarsa inda ya ce:
Mai hassada ni fa ban ce ka yi laifi
ba,
Ga ubanmu Adamu Shaiɗan ya yi tun a
gaba,
Ƙabila ma ya kashe Habila don jaraba,
Kuma babu wai, mun ji an yi wa Ali Yaƙuba,
In kai musu da faɗa ta, duba Ƙur’ani.
(Tauraron Zamani: Aƙilu Aliyu: Baiti na 23)
4.2 Ƙissar Ƙabila da Habila
Ƙabila wani mutum ne daga cikin mutanen farko-farkon duniya. Shi ɗa ne ga Annabi
Adamu (AS). Ya rayu tare da wani abokin haihuwarsa mai suna Habila inda ƙarshe Ƙabila ya kashe
Habila saboda ƙyashi da hassada kan matar aurensa
(Muhammad, 2019: 47-49).
Bayan Allah Maɗaukakin Sarki Ya
halicci Annabi Adamu (AS), Ya kuma halitta masa matarsa Hauwa’u daga awazarsa
ta sashen jikinsa na hagu, Ya yi nufin samar da zuri’a gare su, sai ya kasance
duk cikin da za a haifawa Annabi Adamu (AS) zai kasance ɗiya biyu ne mace
da namiji kuma yadda shari’ar wannan lokaci take dangane da al’amarin aure, shi
ne namijin da aka haifa a cikin farko shi zai auri macen da aka haifa a ciki na
biyu, yayin da namijin da aka haifa a ciki na biyu ya auri macen da aka haifa
ciki na farko. Ana nan a haka har aka haifi ‘ya’ya biyu ana kiran ɗaya Ƙabila ɗayan kuma Habila.
Ƙabila ya kasance manomi ne shi kuma Habila makiyayi. Ƙabila shi ne babba kuma tawainiyarsa kyakkyawa ce sosai bisa ga tawainiyar
Habila. Ana nan a haka sai Habila ya nemi auren tawainiyar Ƙabila sai ya ƙi yarda da hakan,
ya ce ai ita tare aka haife mu da ita kuma ta fi ‘yar uwar haihuwar ka kyawo
don haka ni nafi cancanta da in aure ta. Sai Annabi Adamu (AS) ya umurci Ƙabila da ya aurar da ‘yar uwarsa ga Habila amma sai ya ƙi, sai suka gabatar da abin ibada ga Allah maɗaukakin Sarki da
nufin duk wanda aka karɓi abin ibadarsa to shi ya fi cancanta
da ya auri macen da aka haifa kyakkyawa (wato tawainiyar Ƙabila). To a wannan lokaci Annabi Adam (AS) ba ya nan ya tafi Makka, wannan
ko ya faru ne a dalilin tambayar da Ubangiji (SWT) ya yi masa na cewa ko kasan
ina da ɗaki a bayan ƙasa? Ya ce a’a ban sani ba ya
Ubangijina. Sai Ubangiji (SWT) Ya ce lallai ina da ɗaki a Makka ka je
ka ziyar ce shi. To wannan shi ne dalilin tafiyarsa a Makka.
A lokacin da Annabi Adam (AS) zai tafi
sai ya ce da sama ga ɗana nan (Habila) ki kular mini da shi
cikin amana, sai sama ta ƙi, ya ce da ƙasa haka nan ita ma ta ƙi, ya ce da duwatsu haka nan su ma suka ƙi, sai ya ce da Ƙabila haka nan sai ya ce na’am zan karɓa kuma za ka je ka
dawo ka sami iyalinka yadda rayuwarka za ta yi daɗi. To a lokacin da
Annabi Adam (AS) ya tafi sai suka gabatar da abin ibadar da aka umurce su har Ƙabila ya kasance yana yi wa Habila bugun-gaba da cewa ni
na fi cancanta da in auri tawainiyata don ni ne babba bisa gare ka kuma ni
mahaifina ya bar wa wasiyya. A ya yin gabatar da abin ibada Habila ya gabatar
akuya ko tunkiya lafiyayya mai ƙiba, shi kuma Ƙabila ya gabatar da wasu zangarniyoyi na cikin abin da
yake nomawa sai ya samu wata zangarniya mai girma mai kyau a ciki, sai ya ɗauke ta ya ɓare ya ci. Lokacin
da wuta ta sauko daga sama, sai ta ci abin ibadar da Habila ya gabatar ta bar
na Ƙabila, a take sai ya yi fushi ya ce da
Habila lalle sai na kashe ka har ya kasance ba za ka auri tawainiyata ba. Sai
Habila ya ce da shi, ai da ma Ubangiji yana karɓar aiki ne daga
masu jin tsoronSa.
Ga yadda ƙissar ta zo a Suratul Ma’ida (aya ta 27-31)
Kuma karanta musu (Ƙuraishawa ko kuwa al’ummarka) labarin ɗiya biyu (Ƙabila da Habila) na Adamu (AS), da gaskiya, a lokacin da
suka bayar da baiko, sai aka karɓa daga ɗayansu kuma ba a
karɓa daga ɗayan ba, ya ce: “Lalle ne, zan kashe ka”. (Ɗayan kuma) ya ce: “Abin sani dai, Allah Yana karɓa daga masu taƙawa ne. Lalle ne idan ka Shimfiɗa hannunka zuwa
gare ni domin ka kashe ni, ban zama mai shimfiɗa hannuna zuwa
gare ka ba domin in kashe ka. Lalle ne ni, ina tsoron Allah Ubangijin talikai.
Lalle ne ni, ina nufin ka koma da zunubina game da zunubinka, har ka kasance
daga abokan wuta. Kuma wannan shi ne sakamakon azzalumai”. Sai ransa ya ƙawatar masa kashewar ɗan’uwansa, sai
kuwa ya kashe shi, sa’an nan ya wayi gari daga masu hasara. Sai Allah Ya aiki
wani hankaka, yana tono a cikin ƙasa domin ya nuna
masa yadda zai turbuɗe gawar ɗan’uwansa. Ya ce
“Kaitona! Na kasa in kasance kamar wannan hankaka domin in turbuɗe gawar ɗan’uwana?”. Sai ya
wayi gari daga masu nadama.
Idan aka yi la’akari da wannan ƙissa, sai a fahimci cewa, Ƙabila ya saɓa wa umurnin Ubangiji, ya aikata sharri na kisan ɗan’uwansa saboda
hassada. Wannan batu ne ya sa Aƙilu Aliyu ya nuna
wanda ke hassada a yau, kafinsa ma wani mutum mai suna Ƙabila ya yi har ya kashe abokin haihuwarsa Habila.
4.3 Ƙissar Alu Yaƙub
Alu Yaƙub zance ne da yake nufin iyalin Annabi Yaƙub (AS), wanda labarinsu ya zo cikin suratu Yusuf wato sura ta 12 cikin Alƙur’ani. Kafin a fara bayani a kan yadda wannan ƙissar take akwai buƙatar a san wane ne
Ya’aƙub, kuma su wane Alu Yaƙub. Yaƙub amincin Allah
ya tabbata a gare shi Annabi ne cikin Annabawan Allah kuma yana ɗaya daga cikin
Annabawa 25 da aka ambaci sunayensu a cikin Alƙur’ani. Annabi Yaƙubu (AS) ɗa ne ga Annabi
Ishaƙa (AS) wanda yake shi kuma ɗa ne ga Annabi
Ibrahim (AS). Annabi Yaƙub (AS) shi ne wanda ake yi wa laƙabi da Isra’il, wadda ita wannan kalmar ta Isra’il daidai
take da ka ce Abdullahi a harshen Larabci wato bawan Allah (Albidaya Wannihaya
Vol. 1:40).
To, su waɗannan ‘ya’ya na
Annabi Yaƙub (AS) su ne ake kira Alu Yaƙub. Daga cikin su ne Allah Maɗaukakin Sarki Ya
zaɓi ɗaya ya yi masa Annabta shi ne Annabi Yusufu (AS), duk da yake akwai saɓanin malamai da
yawa game da ‘yan’uwan Annabi Yusufu (AS), wasu sun ce Annabawa ne, wasu sun ce
ba Annabawa ba ne, sai dai wannan bincike ba muhalli ne na tattauna dukkan saɓanin da malamai
suka yi a kansu ba, sai dai a ɗan faɗi kaɗan daga ciki.
Malaman da suka ce ‘yan’uwan Annabi
Yusuf (AS) Annabawa ne sun kafa hujja da faɗar Allah a cikin
Alƙur’ani a Suratul Baƙara aya ta 136 inda Yake cewa “Ku ce: “Mun yi imani da
Allah da abin da aka saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar zuwa ga Ibrahim
da Isma’ila da Ishaƙa da Ya’aƙubu da Jikoki da abin da aka bai wa Musa da Isa da abin da aka bai wa
Annabawa daga Ubangijinsu, ba mu rarrabewa a tsakanin kowa daga gare su, kuma
mu a gare Shi, masu sallamawa ne”. Hujjar malaman a wannan aya ita ce kalmar
Jikoki da aka ambata wadda da Larabci ake kira Asbaɗ. Amma Ibn Kasir
ya faɗa a cikin littafinsa Albidaya Wannihaya cewa “Annabi Ya’aƙuba (AS) yana da ‘ya’ya goma sha biyu maza kuma gare su
ne ake jingina kalmar Asbaɗ wato jikokin Bani Isra’ila dukkansu,
sai dai mafi ɗaukaka da girma da matsayi cikinsu shi ne Yusuf (AS), sannan mafi yawan
malamai sun tafi cewa babu Annabi cikinsu in ba Yusuf (AS) ba don babu wanda
aka yi wa wahayi cikin su, ya ce abin da ke ƙarfafa haka shi ne ayyukansu da maganganunsu. Waɗanda suka kafa
hujjar Annabtaka da ayar “Ku ce: “Mun yi imani da Allah da abin da aka saukar
zuwa gare mu da abin da aka saukar zuwa ga Ibrahim da Isma’ila da Ishaƙa da Ya’aƙubu da Jikoki…. ”Sun
raya cewa su ne jikokin da aka ambata a ayar, amma wannan ba hujja ce mai ƙarfi ba, saboda abin da ake nufi da jikoki a ayar su ne
dangin Bani Isra’il, kuma ba a samu wani Annabi ba cikin dangin da aka yi wa wahayi
daga sama” (Ibn Kasir, Albidaya Wannihaya ba shekara 1:197 – 220).
Su waɗannan ‘ya’yan ne
Allah Ya kawo bayanin wani lamari da ya auku tsakaninsu cikin ayoyi ɗari da sha ɗaya (111) na
suratu Yusuf. Kaɗan daga cikin ayoyin su ne:
A lokacin da Yusufu ya ce wa ubansa “Ya
baba! Lalle ne ni, na ga taurari goma sha ɗaya da rana da
wata. Na gan su suna masu sujuda a gare ni”. Ya ce, “Ya ƙaramin ɗana! Ka da ka faɗi mafarkinka ga ‘yan uwanka, har su ƙulla maka wani kaidi. Lalle ne Shaiɗan ga mutum haƙiƙa maƙiyi ne bayyananne. Kuma kamar wancan ne, Ubangijinka Yake zaɓen ka, kuma Ya
sanar da kai daga fassarar labarai, kuma ya cika ni’imominSa a kanka, kuma a
kan gidan Yaƙuba kamar yadda ya cika su a kan
ubanninka biyu a gabani Ibrahim da Ishaƙa, lalle
Ubangijinka ne Masani Mai hikima. (Gummi: Sura ta 12: 4 – 6)
Ku kashe Yusufu, ko kuwa ku jefa shi a
wata ƙasa, fuskar ubanku ta wofinta saboda
ku, kuma ku kasance a bayansa mutane salihai. Wani mai magana daga cikinsu ya
ce, ka da ku kashe Yusufu. Ku jefa shi a cikin duhun rijiya, wasu matafiya su
tsince shi, idan kun kasance masu aikatawa ne. Suka ce “Ya babanmu! Mene ne a
gare ka ba ka amince mana ba a kan Yusufu, alhali kuwa lalle ne mu, haƙiƙa masu nasiha muke ne a gare shi? Ka
bar shi tare da mu a gobe, ya ji daɗi kuma ya yi wasa, kuma lalle ne mu a
gare shi, masu tsaro ne”. Ya ce, “Lalle ne ni, haƙiƙa yana ɓata mini rai ku
tafi da shi. Kuma ina tsoron kerkeci ya cinye shi alhali ku kuwa kuna masu
shagala daga gare shi”. Suka ce, “Haƙiƙa, idan kerkeci ya cinye shi alhali kuwa muna dangin
juna, lalle ne mu a sa’an nan haƙiƙa mun zama masu hasara”. To a lokacin da suka tafi da
shi, kuma suka yi niyyar sanya su shi a cikin duhun rijiya, Muka yi wahayi zuwa
gare shi, “Lalle ne kana ba su labari game da wannan al’amari nasu, kuma su ba
su sani ba”. (Gummi: Sura ta 12: 9 – 15)
Bayan wannan ma, hassadar ta ci gaba
bayan shekaru masu yawa waɗanda a lokacin su ‘yan uwan na Yusuf
(AS) ba su da masaniyar yana raye, bayan har ya zama mai tsaron tattalin arziki
na ƙasar Masar gaba ɗaya. Yana wannan
hali ne aka yi shekaru bakwai na fari wanda yunwa ta samu jama’a har ‘yan’uwan
Annabi Yusuf (AS) suka zo neman abinci a garin. Lokaci na farko da Yusuf (AS)
ya gan su ya gane ‘yan uwansa ne. Bayan tattaunawa ta shiga tsakaninsu har ya
nemi da su zo masa da ɗan ƙaraminsu wato ɗan’uwansa da suke ɗaki ɗaya Binyaminu, ko
kuma ba za a sake sayar musu da abinci ba. To, bayan sun zo masa da ɗan ƙaraminsu ne, sai shi Yusuf (AS) ya yi dabarar riƙe ɗan’uwan nasa a hannunsa ta hanyar cewa
ya yi satar ma’aunin da sarki ke awo da shi. Wannan dalili ya sa Yusuf (AS) ya
riƙe Binyaminu a wurin shi. To, wannan
abin na faruwa sai su ‘yan’uwan Annabi Yusuf (AS) suka ce ai idan har ya yi
sata to ai ɗan’uwansa ya taɓa yi tun a da can (suna nufin Annabi
Yusuf (AS) ya taɓa sata) kamar yadda Allah ya hakaito hakan a cikin Alƙur’ani a cikin Suratu Yusuf aya ta 77 inda yake cewa:
Suka ce, “Idan ya yi sata, to lalle ne
wani ɗan’uwansa ya taɓa yin sata a gabaninsa”. Sai Yusufu ya ɓoye ta a cikin
ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce, “Ku ne mafi sharri ga wuri.
Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantawa”.[2]
A taƙaice wannan shi ne abubuwan da suka faru tsakanin Annabi Yusuf (AS) da ‘yan
uwansa, na irin hassada da suka nuna a gare shi.
Idan aka yi la’akari da bayanan waɗannan abubuwa, sai
a ga cewa, su ne Aƙilu Aliyu ya taƙaice a kalmar ‘Alu Yaƙub’.
4.4 Ƙissar Annabi
Ibrahim (AS)
Annabi Ibrahim (AS) wanda ake yi wa laƙabi da Khalilullahi wato Badaɗayin Allah, ya yi
lokaci da Sarki Namarudu wanda yana ɗaya daga cikin mutane huɗu da suka mallaki
duniya tunda maɓullar rana har zuwa mafaɗarta. A lokacin wannan sarki mutanensa
na bautar gumaka kuma shi Annabi Ibrahim ya ƙyamaci hakan. Abubuwa da yawa sun faru a wannan ƙissar sai dai ambatonsu a wannan wuri ba muhallin yin hakan ne ba. A ƙarshe dai mutanen sun yi nasarar kama Annabi Ibrahim suka
jefa shi a cikin wuta wanda a wannan lokaci ne Ubangiji ya yi umurni ga wuta da
ta zamo mai sanyi da aminci ga Annabi Ibrahim (AS). Ƙissar Annabi Ibrahim ta zo a surori da dama cikin Alƙur’ani amma a wannan nazari za a taƙaita da kawo ƙissar da ke cikin Suratul Anbiya’i daga aya ta 51 zuwa ta
73 wadda ita ce Muhammadu Bello Giɗaɗawa ya naɗe a wannan baitin
da ke tafe:
Ka duba can ga jefa Khalilu Naran, Haƙiƙan ya shige ta cikin salama.
(Waƙar Jam’iyyar Salama, M. B. G.: Baiti na 14) Annabi Ibrahim A.S. yana ɗaya daga cikin
manyan Annabawan Allah da ya aiko zuwa
ga bayinsa, sannan ma shi ne na biyu daga cikin Annabawa biyar da ake ce wa
ulul azmi minar rusuli. Ƙissar Annabi
Ibrahim tana ɗaya daga cikin ƙissoshi masu darasi da ƙawatarwa a cikin Alƙur'ani wanda ayoyi
da surori da dama suka zo da bayaninta ta siga daban-daban. Labarin karya
gumakan da Annabi Ibarahim ya yi yana ɗaya daga cikin muhimmin abu a wannan ƙissa. Annabi Ibrahim tun yana saurayi matashi ya gabatar
da wannan aiki muhimmi na karya gumaka da kuma tattaunawa da ya yi da ɗan’uwan babansa
wato Azara dangane da bautar gumaka da kawo masa dalilai da ya yi a kan rashin
cancantar gumaka wajen bauta. Alƙur'ani ya ba da ƙissar Annabi
Ibrahim (AS) inda ya yi amfani da kalmar Baba wajen ɗan’uwan mahaifin
Annabi Ibarahim domin Larabawa sukan yi amfani da kalmar Baba wajen ɗan’uwan Uba. Don
haka ne waɗansu a nan sukan ce wai Azara Baban Annabi Ibrahim ne alhali kuwa ba
mahaifinsa ba ne, wasu malaman tafsiri sun yi amfani da wannnan kalma ne Ta "ab"
a matsayin Baba. Duk da yake bincike ya tabbatar da saɓanin hakan, wato
cewa ba mahaifinsa ba ne.[3]
Ga yadda ƙissar ta zo:
Kuma lalle haƙiƙa Mun kawo wa Ibrahim shiryuwarsa daga
gabani, kuma Mun kasance Masana gare shi. Ya ce wa ubansa da mutanensa mene ne
waɗannan mutum mutumai waɗanda kuke masu lazimta a kansu? Suka
ce: Mun sami Ubanninmu masu lazimta a kansu. Ya ce: Lalle, haƙiƙa, kun kasance ku da Ubanninku a cikin ɓata bayyananna.
Suka ce: Shin ka zo mana da gaskiya ne, ko kuwa kai kana daga masu wasa ne? Ya
ce: a’a, Ubangijinku Shi ne Ubangijin sammai da ƙassai, wanda Ya ƙaga halittarsu. Kuma Ni ina daga masu
shaida a kan haka. Kuma ina rantsuwa da Allah, lalle zan yi wani shiri ga
gumakanku a bayan kun juya kuna masu bayar da baya. Sai ya sanya su guntu-guntu
face wani babba gare su, tsammaninsu suna komawa zuwa gare shi. Suka ce: Wane
ne ya aikata wannan ga gumakanmu? Lalle shi, haƙiƙa, yana daga azzalumai. Suka ce: Mun ji
wani saurayi yana ambatar su, ana ce masa Ibrahim. Suka ce: To, ku zo da shi a
kan idanun mutane, tsammaninsu za su bayar da shaida. Suka ce: Shin kai ne ka
aikata wannan ga gumakanmu? Ya Ibrahim! Ya ce: a’a, babbansu, wannan, shi ya
aikata, shi. Sai ku tambaye su idan sun kasance suna yin magana. Sai suka koma
wa junansu suka ce: Lalle ne ku, ku ne azzalumai. Sa’annan kuma aka sunkuyar da
su a kan kawunansu suka ce, lalle, haƙiƙa, ka sani waɗannan ba su yin magana. Ya ce: Shin to,
kuna bauta wa abin da, ba ya amfaninku da kome kuma ba ya cutar da ku bancin
Allah? Tir da ku, kuma da abin da kuke bauta wa, bancin Allah! Shin to, ba ku
hankalta? Suka ce: Ku ƙone shi kuma ku taimaki gumakanku, idan
kun kasance masu aikatawa. Muka ce: Ya wuta! Ki kasance sanyi da aminci ga
Ibrahim. Kuma suka yi nufin wani mugun shiri da shi, sai Muka sanya su mafiya
hasara. Kuma Muka tserar da shi da Luɗu zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta ga talikai. Kuma Muka ba shi
Is´haka da Ya’aƙuba a kan daɗi alhali kuwa
dukkansu Mun sanya su salihai. Kuma Muka sanya su shugabanni, suna shiryarwa da
umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alheri da tsayar da
salla da bayar da zakka. Kuma sun kasance masu bauta gare Mu. (Alƙur’an, Sura 21: 51-73).[4]
4.5 Ƙissar Fir’auna
Fir’auna wani mutum ne daga cikin
mutanen da suka rayu a zamanin Bani Isra’ila. Ya yi mulki a zamanin Annabi Musa
(AS), kuma Allah ya ba shi ƙasaita, abin da ya
sa shi girman kai da bai wa kansa matsayin abin bauta. Wannan mutum ne Aƙilu Aliyu ya naɗe ƙissarsa cikin baitin waƙarsa inda yake
cewa:
Wani fasiƙi baƙi mai iya shirya lalata,
Fa da yag ga wawa ya ce masa, ‘zo ka
arzuta,
Kamin wata ɗaya kai ma sai ka
sai mota,
Ya nuna wauta da jahilci da ƙasaita,
Fa irin ta Fir’auna, tarayya da
Rabbani.
(Tauraron Zamani Aƙilu Aliyu: Baiti na 20)
Fir’auna wani azzalumin sarki ne da ya
yi mulki a ƙasar Masar. Sunansa na yanka Mus’ab bn
Walid, Fir’auna kuwa sunan sarauta ne ta ƙasar Masar. Magana
mafi inganci shi ne Fir’auna ba sunan sarauta ne ba, sunan yanka ne dalili kuwa
shi ne an ambaci sunansa sau 74 cikin Alƙur’ani kuma duk a
Fir’auna suka zo ba Alfir’aunu ba, don haka Fir’auna sunan yanka ne ba laƙabin sarauta ba, hujjar da ke ƙara ƙarfafa wannan ita ce sarkin da ya yi
zamani da Annabi Yusuf (AS) an kira shi da Almaliku a wurare biyar cikin Alƙur’ani, kuma duk a ƙasa ɗaya ce ta Masar.
Fir’auna ya yi ɓarna a cikin ƙasa, ya bautar da Bani Isra’ila, ya kuma sa an yanka
jarirai maza da yawa na ‘ya’yan Bani Isra’ila domin kawai an gaya masa cewa za
a haifi yaro cikinsu wanda zai yi sanadin rushewar mulkinsa. Bayan duk waɗannan abubuwa sun
faru Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko Annabi Musa (AS) da ɗan’uwansa Annabi
Haruna (AS) zuwa ga Fir’auna domin ya kira zuwa ga kaɗaita Allah da
bauta. Bayan Annabi Musa (AS) ya kira shi ga bauta wa Allah sai ya ƙi, ya yi girman kai ya ƙaryata dukkan hujjojin da Annabi Musa ya je masa da su, daga ƙarshe ma sai ya yi da’awar cewa shi ma Ubangiji ne abin
bauta.
Ubangiji (SWT) Ya ambaci ƙissar Annabi Musa (AS) da Fir’auna a wurare da dama cikin
Alƙur’ani. Kaɗan daga cikinsu su
ne:
Muna karantawa a kanka daga labarin
Musa da Fir’auna da gaskiya domin mutane waɗanda suke yin
imani. Lalle ne Fir’auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutanenta ƙungiya-ƙungiya, yana raunanar da wata jama’a daga gare su; yana
yanyanka ɗiyansu maza kuma yana rayar da matan su, lalle ne ya kasance daga masu ɓarna. Kuma Muna
nufin Mu yi falala ga waɗanda aka raunanar a cikin ƙasar, kuma Mu sanya su shugabanni, kuma Mu sanya su
magada. Kuma Mu tabbatar da su a cikin ƙasar, kuma Mu nuna
wa Fir’auna da Hamana da rundunoninsu abin da suka kasance suna sauna daga gare
su. (Gummi: Sura ta 28:3 – 6)
Kuma Fir’auna ya ce, “Ya ku mashawarta!
Ban san kuna da wani abin bautawa baicina ba, saboda haka ka hura mini wuta, ya
Hamanu! A kan laka (domin a yi tubali), sa’an nan ka sanya mini bene,
tsammanina zan ninƙaya zuwa ga Ubangijin Musa, kuma lalle
ne ni, haƙiƙa ina zaton sa
daga maƙaryata.” Kuma ya kangare, shi da
rundunoninsa, a cikin ƙasa, ba da haƙƙi ba, kuma suka zaci cewa su, ba za a mayar da su zuwa
gare Mu ba. (Gummi: Sura ta 28:38 – 39).
Shin labarin Musa ya zo maka? A lokacin
da Ubangijinsa Ya kiraye shi, a cikin rafi mai tsarki, wato Ɗuwa? Ka tafi zuwa ga Fir’auna, lalle ne shi ya ƙetare haddi. Sai ka ce masa, ‘Ko za ka so ka tsarkaka,
kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronsa? Sai ya nuna
masa ayar nan mafi girma. Sai ya ƙaryata, kuma ya saɓa (umurni). Sa’an
nan ya juya baya, yana tafiya da sauri. Sai ya yi gayya, sa’an nan ya yi kira.
Sai ya ce, “Ni ne Ubangijinku mafi ɗaukaka.” Saboda haka Allah Ya kama shi,
domin azabar maganar ƙarshe da ta farko. Lalle ne a cikin
wannan haƙiƙa akwai abin kula
ga wanda yake tsoron Allah. (Gummi: Sura ta 79:15 – 26).
Idan an dubi yadda tsarin waɗannan ƙissoshi suka zo a cikin ayoyin Alƙur’ani, za a ga kowace cikinsu ta zo da irin maganganu na girman kai da ƙetare iyaka da Fir’auna ya yi ga Ubangijinsa, amma biyu
daga cikinsu, su suka fi nuna wautarsa da jahilcinsa da ƙasaitarsa daidai da yadda Malam Aƙilu ya faɗa, wato inda ya
nuna shi ma abin bauta ne, cikin Suratul Ƙasasi da Suratun
Nazi’at.
Kenan a nan Aƙilu Aliyu ya nuna wanda yake yi wa habaici ya ƙetare haddi irin na Fir’auna.
Ƙetare haddin da ake nunawa shi ne arzurtawa wanda aiki ne na Allah. Wanda
ya ce yana arzutawa ya yi tarayya da Allah cikin ayyukansa.
5.0 Sakamakon Bincike
Wannan nazari ya fito da cewa ƙissoshi labaru ne da ake ruwaitowa, sannan ƙissa a adabin Larabci ba ta tabbatu a kan wani dalili
iyakantacce ba, sai dai wani lokaci ana amfani da ita don wani dalili da ya
tattara ga wani fannin abin da ake ba da labari a kai wanda ya game nau’o’i
daban-daban na labari kamar ruwaya (wato samo labari daga wani wuri a watsa
shi) da ƙissoshi (wato labarai na gaskiya waɗanda suka shafi
Annabawa da sahabbai da mala’iku da sauransu). A adabin Hausa kuma ƙissa na nufin labari, ko kuma wani labari na musamman
game da Annabawa da sahabbai da mala’iku wanda yakan fito a cikin Alƙur’ani da sauran littattafan addini.
Haka nazarin ya ƙara fito da cewa waƙoƙin siyasa na da
can da na yanzu, ba wai waƙoƙi ne kawai da ake yi don tallata jam’iyya da manufofinta
ba ko kushe jam’iyyar hamayya tare da shugabanninta da magoya bayanta ba, a’a
waƙoƙi ne da ake samun
abubuwan koyarwa waɗanda suka shafi addinin Musulunci, ciki
kuwa har da ƙissoshin Alƙur’ani waɗanda ke zuwa a naɗe don gargaɗi ga al’umma ko faɗakarwa ko kuma
kafa hujja daga Alƙur’ani. Haka ma na yanzu su ma akwai
abubuwan da suka shafi addini cikinsu, amma dai suna da ƙaranci bisa ga na wancan lokaci.
6.0 Kammalawa
A wannan maƙala an yi taƙaitaccen nazari ne kan abin da ya shafi
ƙissa a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa wanda wannan yana cikin
salailan da wasu mawaƙa ke amfani da shi don isar da wani
muhimmin saƙo ga al’umma. Nazarin ya zo da taƙaitaccen bayani kan abin da ya shafi salo da waƙoƙin siyasa da ƙissa. Ƙissoshin da aka tattauna a wannan
nazari sun haɗa da ƙissar Ƙabila da Habila da ƙissar Alu Yaƙub da ƙissar Annabi Ibrahim (AS) da ƙissar Fir’auna waɗanda aka samo cikin waƙoƙi biyu, su ne waƙar Tauraron Zamani ta Malam Aƙilu Aliyu da waƙar Jam’iyyar Salama ta Muhammadu Bello Giɗaɗawa. An rufe
wannan maƙala da kawo sakamakon bincike da
bayanin kammalawa.
Manazarta
Birniwa, H. A. (1983). “The Influence of Qur’an and Hadith Texts on Hausa
Literate Poems”. A Seminar Paper Presented at International Seminar on Hausa
Studies. Sokoto: University of Sokoto.
Birniwa, H. A. (1987). “Conservatism and Dissent: A comparative Study of
NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from ca 1946 to 1983. Kundin Digiri
na Uku. Sokoto: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Birniwa, H. A. (2002). “Salon Riwayar Hadisi a cikin Waƙoƙin Infiraji na Dr. Aliyu Namangi”.
Takardar da aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani.
Sakkwato: Sashen Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Birniwa, H. A. (2004). ‘Siffantawa a Cikin Waƙoƙin Siyasa’, Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies vol. 1 No1. Sokoto: Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ɗangambo, A. (2011). Rabe-raben Adabin
Hausa (Sabon Tsari). Kano: K. D. G. Publishers.
Funtua, A. I. (2010). ‘Sigogin Waƙoƙin Siyasa Na Hausa A Jamhuriya Ta Uku’, Himma Journal of
Contemporary Hausa Studies. Katsina: Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua.
Gummi, A. M. (1979). Fassarar Al-Ƙur’ani Mai Girma.
Madina: Rabiɗatul Alam el-Islam.
Hiskett, M. (1977). An Anthology of Hausa Political Verse. London.
Ibn Kasir I. U. (2009). Albidaya Wannihaya. Beirut Dimishqa: Daru Ibn
Kasir.
Muhammad, H. (2019). “Ƙissoshin Alƙur’ani a wasu Waƙoƙin Siyasa na Malam Aƙilu Aliyu”. Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya.
Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sa’id, B. (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello
University Press.
Sarɓi, S. A. (2007). Nazarin Waƙen Hausa. Kano:
Samrib Publishers.
Yahya, A. B. (2016). Salo Asirin Waƙa. Sokoto:
Guaranty Printers.
[1] A cikin Tafsirul Jalalaini na Imamul
Muhalli da Imamus Suyuɗi a
tafsirin aya ta goma cikin Suratut Tahrim an faɗi cewa sunan matar Annabi Nuhu (AS) Wahilatu, ita kuma
matar Annabi Luɗu (AS)
Wa’ilatu.
[2] Domin samun cikakken bayani game da
wannan ɓangare na ƙissa wato zuwan ‘yan’uwan Annabi Yusuf (AS) ƙasar Masar a
dubi Suratu Yusuf aya ta 43 zuwa aya 83 wadda ta fara daga lokacin da Sarkin
Masar ya yi mafarkin shanu bakwai masu ƙiba da wasu bakwai ramammu da
zangarniyoyi bakwai kore-kore da wasu bakwai ƙeƙasassu. Haka kuma Ibn Kasir a
cikin Albidaya Wannihaya mujalladi na ɗaya shafi na 213 ya faɗi cewa, satar da
suke cewa Yusuf ya yi ita ce sace gunkin kakansa na wajen uwa da ya yi ya
kakkarya shi ko kuma abincin gida da yake ɗauka yana fitar da shi waje yana
ciyar da talakawa, wasu kuma sun faɗi wanin waɗannan.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.