MANUFAR BUDE USMANNOOR ONLINE ACADEMY❗
Usmannoor_Assalafy
Assalamu alaikum, Warahmatullahi, Wabarakatuhu
Dalilin da yasa na yi tunanin bude USMANNOOR ONLINE ACADEMY shi ne: don na zama silar gyaruwar Ibadar al'ummar musulmi baki daya, a maimakon yanda muke maida hankali a Media Platforms muna asarar Data dinmu a al'amuran Dunya sai naga ai a ɓangaren Gyaran addini ya kamata mu dinga amfani da data dinmu, riba biyu: ga lada ga Kuma wayewar addini
Ni ba malami baneba, kamar yanda wasu suke tunani, ni dan
qaramin dalibin ilimi ne don haka manufata shi ne na dora mutane akan hanyar da
za ta sadasu zuwa ga malaman Ahlus Sunnah ta yanda zasu koyi cikakkiyar Ibadah
musamman Sallah, kamar yanda Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar. Don
Haka idan na yi kuskure ya kamata ku karbi uzuri na a matsayina na Dan Adam
Wanda ba Ma'asumi ba.
Daga 12 August, 2024 zuwa yanzu haka (da kake karanta wannan
saqon) mun samu sababbin dalibai Mata da maza (Hausawa) sama da 2,800 da sukai
Online Registration daga qasashe sama da 10: (Saudi Arabia, Makkah, Nigeria,
Niger, Ghana, Cote de voir, Cameroon, Libya, Togo, Mali, Burkina Faso, Algeria,
and still counting. Alhamdulillah). Manufata itace: a dinga dabbaqa Sunnar
Manzon Allaah Sallallahu alaihi wasallam a dukkan al'amuran da muke gudanarwa
na yau da gobe domin kuwa rashin koyi da fiyayyen halitta ne yasa muka tsinci
kanmu a halin da muke ciki a yanzu. Wanne irin sauyi kake tunanin zaka samu
idan kana dabbaqa abinda muka karanta a cikin karatun SUNNONI 1,000 din can❓
Muna karatun littafin (THE 1,000 SUNAN by Shaikh Khalid
Husaynaan) SUNNONIN MA'AIKI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM guda 1,000 wanda za'a
dinga gabatar da guda 3 ko sama da haka a duk daren Alhamis sannan Kuma a
amfana da karatun littafin: SIFATU SALATIN NABY (THE DESCRIPTION OF THE
PROPHET'S PRAYER by Shaikh Nasiriddin al-Albany) wato SIFFAR YANDA ANNABI YAKE
SALLAH, a daren Juma'a da Kuma littafin KIMIYYA DA AL'AJABAN QUR'ANI a daren
Asabar. In Sha Allaah (Wannan Kuma bincike nane saidai ban Kai ga wallafa littafin
ba)
Registration: N2,000 (Ko Kuma Sefa jaka 5 ga maqotanmu
musamman NIGER)
Opay/Moneypoint Account;
Usman Danliti
7035387476
Ko
Zenith Bank
Usman Danliti
2118853750
NITA: 0023407035387476
Sannan Kuma duk karshen wata zaka turo monthly contribution
(N500 ko sama da hakan ga masu niyya) don gudanar da karatuttukan da akeyi
laakarida siyan DATA da sauran gudanarwa. Sannan Kuma ko da gudunmawa ko babu,
zamu ci gaba da karatuttukan in Sha Allaahu. Fatanmu shi ne Allaah yasa mu gudu
tare mu tsira tare, Ya sa Kuma mu dinga aikin da ikhlasi yakuma rabamu da riya
Muna roqon Allaah ya bamu ikon amfana da ilimin muyi aiki
dashi har ma wasu su amfana musamman Sallah. Allaah Azzawajallah yace:
( الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ
الصَّلَاةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ )
البقرة (3) Al-Baqara
Waɗanda
suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka
azurta su suna ciyarwa.
( وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ
وَارْكَعُوا مَعَ الرَّاكِعِينَ )
البقرة (43) Al-Baqara
Kuma ku tsayar da salla; kuma ku bãyar da zakka; kuma ku yi
rukũ'i tãre da yin rukũ'i.
Annabi {Sallallahu alaihi wasallam} yace: "Idan Allaah
Yana son bawa da alkhairi sai ya fahimtar dashi addini"
Bukhari da Muslim
Zaku iya sharing saqon (batareda kun canza harafi ko guda 1
ba) domin kuwa duk Wanda ka zama silar gyaruwar addininsa to zaka samu share na
ladan da zai samu. Bonanza akan Bonus kenan
✍️ADMIN: ZAUREN TAMBAYA DA AMSA:
Founder/Proprietor: USMANNOOR ONLINE ACADEMY
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
©️Copyright
Contact School Management through WhatsApp number:
07035387476
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.