Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakakken Aruli: Nazari a Bisa Bahaushen Kari Tare da Kafafuwansa Don Kwakulo Aruli na Hausa

Citation: Ibrahim, A. (2024). Waƙaƙƙen Aruli: Nazari a Bisa Bahaushen Kari Tare da Ƙafafuwansa Don Ƙwaƙulo Aruli na Hausa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa, 99-110. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.012

Waƙaƙƙen Aruli: Nazari a Bisa Bahaushen Kari Tare da Ƙafafuwansa Don Ƙwaƙulo Aruli na Hausa

Alhaji Ibrahim
Kesala Street, Misau, Bauchi State

Gabatarwa

1.      Manazarta ai nazari kan waƙa,

Domin nazari kan ma’aunin waƙa,

Shi ne ginshiƙin kimiyyar waƙa.

2.      Ma’aunin waƙa shi ke bambanta zube,

Idan ko an yo taliyo har gobe,

Aruli shi ne nahawunmu na waƙa.

3.      Idan ko waƙa ta ƙi amsa Aruli,

Tilas masana ku ji wannan ƙauli,

Mafita dai gun Malamanmu na waƙa.

4.      Cikin biyu dai dole a samo mafita,

A samo hujja wadda ta inganta,

Na tantance ƙafafu na wannan waƙa.

5.      Marubucin waƙa ya samar baiti,

Shi mai nazari shi yake li’irabi,

Ya sanya ƙafafu kan gaɓoɓin waƙa.

6.      Idan sun karɓa sunyi kan-kan-kan to,

A dukka karorin sun yi riga da gyauto,

Aruli ya inganta wannan waƙa.

7.      A dukka karorin fa idan sun ƙi su hau,

Cikin biyu tabbas ba guda wanda ya hau,

Ku ce musu zance bai zame war waƙa.

8.      Muna da ma’auni kan zuwan Larabawa,

Arulinmu yana nan na ‘yan Hausawa,

Da shi ne muka tantance dukkan waƙa.

9.      Saninsa muhimmi ne ga duk mai nazari,

Ya gane waƙa take, yanke sarari,

Shi ne ya bambance Ƙur’ani da waƙa.

10.  Kowane ilimi na da amfaninsa,

Ka bar ma’abutansa su je nazarinsa,

Ilimin ya zamto ribaɗin waƙa.

11.  Ga dukka gudanmu wanda ya yi wakilci,

Mu mar son barka ya tsare mana ‘yanci,

A kan wannan fannin kimiyyar waƙa.

12.  Idan kuma ba ɗai a cikin al’umma,

Da za yai magana gwargwado ma dama,

A bisa Aruli don kimiyyar waƙa.

13.  Masana ku fahimta da sauran aiki,

Ku faɗaɗa ilimi don ku kawo ɗauki,

A kan bigiren nan na Arulin waƙa.

14.  Masha Allah yanzu kam mun dace,

‘Ya’yan Hausawa a yau sun ƙwace,

Suke ta rubutun Arulin waƙa.

15.  Masana da yawa sun wuce ai gwalo,

Irin su Galadanci da Sheshi da Bello,

Sun yi rubutu kan Arulin waƙa.

16.  Magabata sun yi rubutu da yawa,

Irin su ubana Baba ɗan Dunfawa,

Da ya ba ni karatun Arulin waƙa.

17.  Don haka ne na ɗauki alƙalamina,

In tofa ɗan albarkacin bakina,

Don in yi waƙaƙƙen Arulin waƙa.

Waƙaƙƙen Ƙafafun Waƙa

18.  Muna da ma’auni wanda muka yi aro,

A gun Larabawa muka ɗauke shi aro,

Domin cuɗanya tsakaninmu da su.

19.  Mai nazari bi ni a sannu ka gan su,

Da ɗai-ɗai sai na fayyace su ka gan su,

Don manazarta sui ta labarta su.

20.  Fa-uu-lun shi ne dai ma’aunin farko,

Yana da gaɓobi uku, take a farko,

Guntu, sai dogo da dogo ga su.

21.  Ma-faa-ii-lun ne ya biyo shi a baya,

Gaɓa Huɗu ne, na farko ne guntayya,

Sai dogo, dogo da dogo ga su.

22.  Ma-faa-a-la-tun shi dai gaɓarsa biyar ne,

Gajere da dogo da gajere ku gane,

Sannan da gajere da dogo cikin su.

23.  Faa-i-laa-tun na nan biye masa shi ma,

Yana da gaɓoɓi har guda huɗu shi ma,

Dogo da gajere da dogo cikinsu.

24.  Sannan ga dogo cikon na huɗunsu,

Idan mai nazari yai biɗan ƙirgensu,

Huɗu ba ƙari take zai iske su.

25.  Faa-i-lun ma har gaɓa uku nasa,

Cikinsu da dogo da gajere ƙafarsa,

Gaɓarsa ta ƙarshe doguwa ce cikinsu.

26.  Mus-taf-i-lun na ma’aunin waƙa,

Gaɓoɓinsa huɗu kan ma’aunin waƙa,

Dogo, dogo da gajere cikinsu.

27.  Sannan sai dogo cikon na huɗunsu,

Idan an lissafa hakan a gan su,

Babu gaɓa ɗai da ta ƙaru cikinsu.

28.  Ƙafa ta bakwai sunanta Faa-i-laa-tun,

Bata zamto maimai ba Faa-i-laa-tun,

Haka nan tsarin yake gun samar su.

29.  Gaɓoɓinsa huɗu za na lissafa su,

Dogo da gajere kuna kallon su,

Sannan sai dogo da dogo cikinsu.

30.  Mu-ta-faa-i-lun shi ƙafa na takwas ne,

Gajere da gajere ga dogo zaune,

A ƙara gajere sai dogo ya biyo su.

31.  Maf-uu-laa-tu ne ƙafa ta tara,

Dogo da dogo ga shi nan zan tara,

Sannan dogo da gajere ga su.

32.  Mus-taf-i-lun ne ƙafa ta goma,

Ita ma ba maimai ba ce ta goma,

Haka Allah ya ƙaddara a gan su.

33.  Dogo da dogo sai gajere ga su,

Sannan sai dogo da ke bi musu,

Haka tsarin nan ya kasance ga su.

34.  Goma cicif ne ga shi na kawo su,

Don manazarta sui ta aiki kansu,

Ko wani haske zai fito a gare su.

35.  Don bincike kam ba shi ƙarewa to,

Wannan magana babu ɗai mai rinto,

Ta haujin manazarta cikin ra’ayinsu.

Samfurin Ƙafafun Waƙa

36.  Wasu sun yi alamci da sifili sifili,

Suka alamta su da sifili sifili,

Zan muku samfur don ku gan su ku san su.

1.   0 0–0   0–0  Fa-uu-lun

2.   0 0–0   0–0  0–0 Ma-Faa-ii-Lun

3.   0 0–0   0  0   0–0 Ma-Faa-a-La-tun

4.   0–0 0    0–0 0–0 Faa-i-Laa-tun

5.   0–0 0    0–0  Faa-i-Lun

6.   0–0 0–0    0 0–0 Mus-taf-i-Lun

7.   0–0 0    0–0 0–0 Faa-i-Laa-tun

8.   0  0 0–0    0 0–0 Mu-ta-Faa-i-Lun

9.   0–0 0–0    0– 0   0 Maf-uu-Laa-tu

10.  0–0 0–0    00–0  Mus-taf-i-lun

37.  Wasu sun musu siffa da ba wannan ba,

Ita ma hanya ce da ba tababa,

Wadatar nazari ne ya dai samar su.

38.  Ku bi ni a sannun in bijirto da ita,

Da dai hanya ce wadda ta inganta,

Manazarta dukkansu sun yarda da su.

39.   Ba wani mai suka bare inkari,

Haka shi ke sanya ni ƙara kuzari,

Dajin ƙwarin guiwa wurin kawo su.

40.  Su ma ga nan yadda tsarin su yake,

Alamomi ne don na ƙarin haske,

Domin su kasance wakilai ne su.

1.                  v --  Fa-uu-lun

2.                  v  -  -   -  Ma-Faa-ii-Lun

3.                  v  - v v -  Ma-Faa-a-La-tun

4.                  -   v -  -  Faa-i-Laa-tun

5.                  v  -  Faa-i-Lun

6.                  -   - v -  Mus-taf-i-Lun

7.                  v  --  Faa-i-Laa-tun

8.                  vv –v -  Mu-ta-Faa-i-Lun

9.                  -   -   - v  Maf-uu-Laa-tu

10.              -   -   v-  Mus-taf-i-lun

41.  Waɗannan hanyoyi da aka bijirto,

Na ƙafafun waƙa fa ba kokwanto,

Masana sun karɓe su sun yarda da su.

42.  Kowanne guda da ka ɗauka a ciki,

Hanya ce yanke ta ƙare aiki,

Sanannu ne gun masana sun san su.

43. Ya rage naka sai ka zaɓa cikinsu,

A alamomin nan guda biyu ga su,

Ba wanda ya maka iyaka kan su.

44. Manazarci zaɓi ka darje ga su,

Duk fatawowin ga su mun kawo su,

Zaɓi na nan a gare ka gare su.

45. Maƙwanƙwashin gaɓa gajere “0” sifili,

Maƙwanƙwashin gaɓa dogo “0–0” su sifilai,

Misalinsu na bayar a ƙara ganin su.

46. Wanan samfur “Ɓ” shi ne misali na biyu,

Gajeren gaɓa ne bisa hanya ta biyu,

Da ya sami wakilcin gajeren cikinsu.

47. Wakilin dogo ga shi nan a sarari,

Siffarsa na kama “-” da karan ɗori,

Da su aka siffanta su don ku gan su.

48. Mun ƙare bayani a wannan fanni,

Mun kawo siffarsu dama da hauni,

Ya rage duk mai nazari ya biɗe su.

49. Ubangiji sauƙaƙa dukka fahimta,

Ga ɗaliban Ilmi su samu fahimta,

Bisa duk nau’in ilimi a gare su.

Ƙafafu ‘yan Asali

50. Za nai magana kan ƙafafun asali,

A cikin goma huɗu ne ‘yan asali,

Su ne ginshiƙan ma’aunin waƙa.

51. Fa-uu-lun wannan kam gaɓan asali ne,

Ma-faa-ii-lun ma to gaɓa ne zaune,

Cikin ‘yan asali na ƙafafun waƙa.

52. Ma-faa-a-la tun na cikin huɗun nan,

Faa-i-laa-tun ma na cikin huɗun nan,

Ƙafafun asali sun kammala na waƙa.

0    0–0    0–0    v --  Fa-uu-lun

0    0–0    0–0    0–0    v --    - Ma-Faa-ii-Lun

0    0–0    0  0    0–0    v – v    v - Ma-Faa-a-La-tun

0–0    0    0–0    0–0    v-    - Faa-i-Laa-tun

53. Waɗannan su ne fa ƙafafun asali,

Waɗanda ake tako da su tun asali,

Na Aruli ilmin kimiyyar waƙa.

54. Akwai bambanci ƙaɗa’an a gare su,

Turakunsu yana nan a farko gare su,

Wannan daraja ce a ma’aunin waƙa.

55. Kasancewar turkensu na nan farko,

Suka zamto ‘yan asali a farko,

Cikin tsarin nan a Arulin waƙa.

56. Hakan baya sawa a watsar sauran,

Ƙafafu ne su ma a wannan tsarin,

Suna da ajinsu a kimiyyar waƙa.

57. Kowa na nan na da nasa matsayi,

Cikin ƙafafun babu ɗai baibayi,

Haɗuwarsu ta samar ƙafafun waƙa.

Ƙafafu ‘yan Goyo

58. Bayani na ƙafafu da ke da goyo,

Zan yi a nan don fayyace ‘yan goyo,

Don ɗalibai sui nazari bisa waƙa.

59. Ƙafafu shida su ne ƙafa ‘yan goyo,

Ƙaunarsu ya sa har muke oyoyo,

Da kasancewar su ma’aunin waƙa.

60. Zan zo ni da su a cikin baitina,

Za su kasance a cikin waƙana,

Da-ɗai ɗai sai na bijiro su da waƙa.

61. Faa-i-lun dai na cikin ‘yan goyo,

Mus-taf-i-lun na cikin ‘yan goyo,

Da aka ƙidaya a ma’aunin waƙa.

62. Sai Faa-i-laa-tun na cikin ‘yan goyo,

Mu-ta-faa-i-lun na cikin ‘yan goyo,

Huɗu ‘yan goyo cikin ƙafafun waƙa.

63. Sun kankama ga shi na kawo su,

Saura biyu in zo da su ku gan su,

Cikon ‘yan goyo a ma’aunin waƙa.

64. Maf-uu-laa-tu na cikin ‘yan goyo,

Mus-taf-i-lun na cikin ‘yan goyo,

Ƙafa shida ‘yan goyo a nan muka sauƙa.

65. Kar fa ku manta kan ƙafa ‘yan goyo,

Sunansu biyu su ƙafa ‘yan goyo,

Sunan sun karɓu ga malamanmu na waƙa.

66. Kana da dama sai ka ce ‘yan rakiya,

Ya inganta ka ce ƙafa ‘yan rakiya,

Ba mai sukan ka kan ma’aunin waƙa.

0–0 0  0–0 - v -  Faa-i-Lun

0–0 0–0  00–0 - - v -  Mus-taf-i-Lun

0–0 0  0–00–0 - v --  Faa-i-Laa-tun

0  0 0–0  0  0–0 v v  -v-  Mu-ta-Faa-i-Lun

0–0 0–0  0–00 - -  - v  Maf-uu-Laa-tu

0–0 0–0  00–0 - - v-  Mus-taf-i-lun

67. Ku lura da kyawu kunga simfirin nan,

Su ne ‘yan goyo ‘yan alamomin nan,

Da aka alamta da ƙafafun waƙa.

Hanyar da Aka Bi aka Samar da Ƙafa ‘yan Goyo

68. Ga wani ɗan haske da za a ba ku,

Game da ‘yan goyo da za a ba ku,

To ɗalibai dai ya kamata ku zakko.

69. Ku ji bayani kan ƙafa ‘yan goyo,

Ta yadda ake samar ƙafa’yan goyo,

Da turakun nan waɗanda suka zo farko.

70. Da su ake kan sarrafa su a samu,

Ƙafa ‘yan goyo tun da sun zam namu,

Ku saurari bayaninsu ga shi a farko.

71.  (i) Ƙafa ta ɗaya ita ce ta rikiɗe,

Ta koma ta biyar kun ji kar ku ruɗe,

A dalilin turke da ya ƙaura a farko.

72.              Ya ƙaura a farko sai ya koma ƙarshe,

Ƙauran da ya yi har ya koma ƙarshe,

Shi ne ya sauya mar sifarsa ta farko.

1.      v –” “0  0–00–0” Fa-uu-lun

5. “-v- ” “0–0 0 0–0” Faa-i-Lun

73.              (ii) Ƙafa ta biyu ita ce ta rikiɗe,

Ta koma ta shida kun ji kar ku zauɗe,

A dalilin ɗaukewar turken a farko.

74.              Ya sauya wuri sai ka gan shi ƙarshe,

Wannan ƙaura da ta kai shi ƙarshe,

Shi ne ya sauya mar sifarsa ta farko.

75.              Ga hotonsu za na kawo su ƙasa,

Don su zamo hujja na kawo su ƙasa,

Ga nan misali ɗan’uwa na hasko.

2.   v -  - - ”     “0 0–0 0–0 0–0” Ma-Faa-ii-Lun

6. “- - v - ”    “0–0   0–0  00–0” Mus-taf-i-Lun

76.  (iii). Idan an ɗau turken ƙafa na biyu,

An kai shi tsakiya saɓanin na biyu,

Nan kuma sai a sami ƙafa ta bakwai.

2. “v - - -“     “0 00 0 0 0 0” Ma-Faa-ii-Lun

7. “-v--”     “0–0  0 0–0   0–0” Faa-i-Laa-tun

77.  (iv). Ƙafa ta uku ita ce ta rikiɗe,

Zuwa ta takwas har yanzu kar ku ruɗe,

Shi ma sanadin ɗauke turken farko.

78.              Ya ƙaura daga farko ya koma ƙarshe,

Yin ƙauran nan da ta kai shi ƙarshe,

Ƙafa ta takwas ta samu ba kadarko.

3.   v-v v-”     “0 0–00  0 0–0” Ma-Faa-a-La-tun

8. “v v - v-”    “0  0   0–0   0  0–0 ”Mu-ta-Faa-i-Lun

79.  (v) Ƙafa ta huɗu, ta rikiɗe ta juya,

Ta koma ta tara lokacin da ta juya,

Turke na ƙafan huɗu na nan ƙarshe.

80.  Da ya tashi a farko ya koma ƙarshe,

Dalilin da ya sa shi ya koma ƙarshe,

Shi ne ƙafa na tara tushensa ƙarshe.

4.      -v--”   “0–0 00–0   0–0 ” Faa-i-Laa-tun

9.   “- - -v”   “0–0    0–0  0–0   0” Maf-uu-Laa-tu

81.  (vi)Da an ɗauke turken ƙafa ta huɗu,

Daga farkonta ta ƙafarsa ta huɗu,

Zuwa tsakiya sai ƙafa ta goma.

82.  Ta samu ƙaɗan’an gun Arulin waƙa,

Manazarta ga dai ƙafafun waƙa,

Da jimillarsu ta kasance goma.

4.   “-v --”  “0–0 00–00–0 ” Faa-i-Laa-tun

10. “- -v- ” “0–0 0–0 0 0–0” Mus-taf-i-Lun

83. A nan za mu biɗa mu yi ƙarin haske,

Mun ɗauki ƙafafu huɗu mun turke,

Mun ce su ne huɗu turken asali.

84.  Dalilinmu a nan bisa wannan ƙauli,

Idan an yi wakurwa na neman asali,

An haifi shidan daga huɗu ‘yan asali.

85.  Idan an yi jimillarsu su ne goma,

Huɗu ga shida tara su su ne goma,

An samu shida daga huɗu ‘yan asali.

Ƙarin Bayani a Bisa Ƙafafun Waƙa

86.  Ƙarin bayani kan ƙafafun waƙa,

Bisa bayanin nan da muka sarƙa,

Don a fahimta kan ƙafafun waƙa.

87.  Bari mu kawo su duk ƙafafun waƙa,

A fahimci muhimmancin turken waƙa,

Da suke da kamanci ƙafafun waƙa.

88.  Ma’ana dai wanda ke kama da juna,

Don neman sauƙin fitar kari na-

Wanda yake sa sarrafawar waƙa.

89.  Muna da ƙafa ‘yan asali to ga su,

Za na taho da su a sake ganinsu,

Ga nan ƙafafun asali na waƙa.

1.   0 0–00–0”     “v --“  Fa-uu-lun

2.   0 0–00–0     0–0”     “v - - - ” Ma-Faa-ii-Lun

3.   0 0–00  0    0–0”    “v – v v -” Ma-Faa-a-La-tun

4.   0–0 00–0    0–0 ”    “- v    --” Faa-i-Laa-tun

90.  Waɗannan su ne fa ƙafa ‘yan goyo,

Barka da ganin su muna oyoyo,

Suna da muhimmanci ƙwarai gun waƙa.

5.      0–0 0 0–0     - v -  Faa-i-Lun

6.      0–0 0–0 0     0–0     -  - v     - Mus-taf-i-Lun

7.      0–0 0  0–0     0–0     -  v -     - Faa-i-Laa-tun

8.      0  0 0–0  0    0–0     v v    - v - Mu-ta-Faa-i-Lun

9.      0–0 0–0  0–0 0     -    - - v Maf-uu-Laa-tu

10.  0–0 0–0  00–0     -    - v  - Mus-taf-i-lun

91.  Waɗannan dai su ne ƙafafu goma,

Jimlace lissafa su za ka ga goma,

Su ne ginshiƙin kimiyyar waƙa.

92.  Huɗu ‘yan asali, shida ‘yan goyo ne,

Ƙafafun ke nan Ɗalibai kun gane,

Da su ake tsarge kimiyyar waƙa.

93.  Allahu sa sauƙi cikin nazarinsa,

Ka ƙara himma ga ɗalibin nazarinsa,

Ya zamo mahir kan kimiyyar waƙa.

Kashe – Kashe Ƙafafun Waƙa

94.  Idan muka duba zubin ƙafafun waƙa,

Duba na basira da kyau mawaƙa,

Ku kalle su da kyau ma’abuta waƙa.

95.  Muna iya sake taciya a cikinsu,

Ta hanyar kaso gida uku a cikinsu,

A bisa turaku masana na waƙa.

96.  Da ke a cikin ƙafafuwa ‘yan asali,

Da na ‘yan goyo waɗanda ba sa asali,

Ma iya sake kaso uku mawaƙa.

97.  Kaso na farko masu turke a farko,

Su huɗu ne masu turaku a farko,

Ƙafa ta ɗaya har zuwa ta huɗu mawaƙa.

98.  Turakunsu yana nan a farkon farko,

Kasancewar turkensu ya zo a farko,

Suka zamto ‘yan asali a waƙa.

99.  Ga shi ku gan su babu ja bisa wannan,

Ga samfur ya zo gare ku wurin nan,

Don kawo sauƙin kimiyyar waƙa.

1.      0 0–00–0”     “v --“  Fa-uu-lun

2.      0 0–00–0  0–0”     “v - - - ” Ma-Faa-ii-Lun

3.      0 0–00  0  0–0”    “v -v v - ” Ma-Faa-a-La-tun

4.      0–0 00–0   0–0 ”     “-v-   -” Faa-i-Laa-tun

100.          Kaso na biyu masu turke tsakiya,

Su biyu ne rak masu turke tsakiya,

A dai nazari kan kimiyyar waƙa.

101.          Ƙafa na bakwai ce tare to da ta goma,

Turakunsu sun zo tsakiya Gangama,

Haka tsarin yake gun Arulin waƙa.

102.          Ku gan su gani mai kyau da ba tababa,

Ba wani mai musu ya ce ba haka ba,

Mun kawo makwafinsu a cikin waƙa.

103.          Ga su ku gan su don ku ƙara fahimta,

Nazari tilas ga shi ya inganta,

Don tantancewar Arulin waƙa.

7.      “0–0 0 0–00–0 ”     “-ɓ-   -” Faa-i-Laa-tun

10. “0–0 0–0 0 0–0”     “- - ɓ   -“ Mus-taf-i-lun

104. Akwai wanda turkensu ya zo a ƙarshe,

Guda huɗu turkensu ya zo a ƙarshe,

Haka dai aka tsara a nazarin waƙa.

105. Ƙafa ta biyar da ta shida da ta takwas,

Sai ta tara ga dai su nan jere ragas,

A ƙarshe turken ƙafafuwan suka sauƙa.

106. Shi ma zan zo ma da samfurinsu,

Don yanke shakku a kan nazarinsu,

Ga ɗalibi mai nazari kan waƙa.

107. Ga su ka gan su masu turke ƙarshe,

Ka gan su ganin sheda, da ɗai koyaushe,

Ka gansu ka san matsayinsu a waƙa.

1.   0–0 0     0–0      - v -  Faa-i-Lun

2.   0–0 0–0  0 0–0     - - v - Mus-taf-i-Lun

3.   0  0 0–0   0 0–0     v v -   v - Mu-ta-Faa-i-Lun

4.   0–0 0–0  0–0 0     -  -  -    v Maf-uu-Laa-tu

108. Jadawali ukun idan an tara,

Za a ga goma sun cika ba rara,

Ƙafafuwa goma na kimiyyar waƙa.

109. An bi salo ne an fitar matsayinsu,

In mai nazari ya buƙaci ganin su,

Zai gan su cicif a buharin waƙa.

110. Allah don girmanka sa sauƙinka,

Cikin rawan da Ɗalibi zai taka,

Na binciken ilmi a fannin waƙa.

Ƙafa Cikin Hausa a Fatawar A. A. Dunfawa

111. Shehu Atiku Ahmadu Dunfawa,

Ya yi nazari ma’ana warkarwa,

Ya ce ƙafafun Hausa goma ne su.

112. Madalla da wannan batu dai nasa,

Gatanci ne yai wa harshen Hausa,

Na yin ma’auni bisa waƙoƙinsu.

113. Ya ɗalibi ban hankalinka ka gan su,

A cikin tsari daɗa zan kawo su,

Ga kuma samfur ɗin ƙafafun nasu.

114. ARAYYE Ita ce ƙafa ta farko a Hausa,

IYEENAAYEE sunan ƙafa ne a Hausa,

Ƙafa ce ta biyu a Hausa ya kawo su.

115. Ƙafa ta uku AYAARAAYEE su ka ba ta,

AYYARAAYEE ta huɗu ya inganta,

Ga huɗu dai na ba ku don ku gan su.

116. To YAARAYEE ita ce ƙafa ta biyar dai,

AYYAARAYEE ita ce ta shidanmu daidai,

In kuka lissafa hakan za ku gan su.

117. Ga YAARANAAYEE wadda ita ce ta bakwai,

Biyar a tara da biyu su ne fa bakwai,

Idan ko ka lissafa hakan za ka gan su.

118. RA’AYEENAYEE ita ƙafa ta takwas ce,

Haka dai aka tsaro su tartibi ce,

Mai nazarin waƙa ka zo to ga su.

119. Ƙafa ta tara ita ce AYYEEDIIDEE,

Waƙa sai an saka AYYEEDIIDEE,

Don samun dama wurin auna su.

120. AYYAARAYEE ce dai ƙafa ta goma,

Ita ce ma babba cikin ta goma,

Da ake tsarmawa a gano wassu.

121. Wannan gudumowa ce ta shehu Atiku,

Manazarci ne bisa waƙoƙinku,

A kimiyance yai batu ku san su.

122. Muna  godiya Malam da gudumuwarsa,

Da yai ijjitihadi kan ƙafafun Hausa,

Furofesa Dunfawa mun gamsu da su.

Samfurin Ƙafa Cikin Hausa Daga A.A. Dunfawa

1.      ARAYYE

2.      IYEENAAYEE

3.      AYAARAAYEE

4.      AYYARAAYEE

5.      YAARAYEE

6.      AYYAARAYEE

7.      YAARANAAYEE

8.      RA’AYEENAYEE

9.      AYYEEDIIDE

10.  AYYAARAYEE

Bayanin Ƙafa Cikin Hausa a Sabon Nazari

123. Shiru ba shi ne ci gaban Ilimi ba,

Nazari shi ne ci gabansa Abba,

Tare da hujja wadda za ta tsayar su.

124. Haƙiƙa dai na leƙa wannan fanni,

Ya kuma dace in yi ɗan bayani,

Kafafun Hausar nan a sake ganin su.

125. Da sauran rina fa a kaba in ji ni,

Mai nazari ya ci ka saurare ni,

Zan zo ni da hujjar da zai tarbe su.

126. Muna da ƙafafu fil azal a Hausa,

Mai nazari dage fa kar ka ƙosa,

Kai nazari domin ka gan su ka san su.

127. Kowa ya ga ɗan ɗinya da hula ya gan shi,

Shi fa Bahaushe duniya ta san shi,

Kafin baƙi ma su zo su gare su.

128. Suna rera waƙoƙinsu don nishaɗi,

Wasu ko don zambo su kai yai daɗi,

Adabin baka ya samu ne a gare su.

129. Za nai magana kan ƙafafun waƙa,

Na Hausa, domin ya zamo sassauƙa,

Don wani haske da na samu kan su.

130. Nazarin nan yai bincike mai faɗi,

Gwanin sha’awa gun masana zad daɗi,

Ƙarin haske ne a karin kan su.

131. Magana a ƙafar Hausa to yaya ta ke?,

Wassu masana suka ce goma suke,

Wannan nazari ya fa gano wassu.

132. Da ba a Magana bisa Karin kan su,

Rashin kawo su, zai iya sangartar su,

A ma mance, su ma ƙafafu ne su.

133. Da kyawu a nazarce su don a san su,

Ya zamto an taskace su don a gan su,

Rashin haka zai jawo a kasa sanin su.

134. Ƙafafun waƙar Hausa sha biyar ne,

A wannan nazari da ya zo kun gane,

Kuma ban ce ba, babu ƙari kan su.

135. Waɗannan ɗin dai ɗan’uwa na nazarta,

Tare da hujja wadda ta inganta,

Nazarin nan zai zo da su ku gan su.

136. Ya ɗalibi ban hankalinka ka gan su,

A cikin tsari daɗa zan kawo su,

Ga dai samfur ɗin ƙafafun nasu.

137. ARAYYE ita ce ƙafa ta farko a Hausa,

IYEENAAYEE sunan ƙafa ce a Hausa,

Ƙafa ce ta biyu a Hausa ta kawo su.

138. Ƙafa ta uku AYAARAAYEE su ka ba ta,

AYYARAAYEE ta huɗu ya inganta,

Ga huɗu dai na ba ku don ku gan su.

139. To YAARAYEE ita ce ƙafa ta biyar dai,

AYYAARAYEE ita ce ta shidan su daidai,

In kuka lissafa hakan za ku gan su.

140. Ga YAARANAAYEE wadda ita ce ta bakwai,

Biyar a tara da biyu shi ne fa bakwai,

Idan ko ka lissafa hakan za ka gan su.

141. RA’AYEENAYEE ita ƙafa ta takwas ne,

Haka dai aka tsaro su tartibi ne,

Mai nazarin waƙa ka zo to ga su.

142. Ƙafa ta tara ita ce  AYYEEDIIDEE,

Waƙa sai an saka AYYEEDIIDEE,

Don samun dama wurin auna su.

143. AYYAARAYEE ce dai ƙafa ta goma,

Ita ce ma babba cikin ta goma,

Da ake tsarmawa a gano wassu.

144. AYYEEYAARAYEE na cikin ƙafofi,

Ita ce ta sha ɗaya babu haufi,

Kogin nazari aka faɗa don su.

145. IYEENAANAAYEE ma ƙafa ce wannan,

Ƙafa ce mai ƙarfi ta sha biyu ke nan,

Da a kai lissafi wurin samo su.

146. Muna da ƙafa sunanta NAANAAYEE to,

Ta sha uku don sunanta NAANAAYEE to,

Haka dai suke fa babu ɗai mai musu.

147. AYYEEYAARAYEEDIIDE aboki ita ma,

Ƙafa ce ta sha huɗu kuma ba dama,

Nazari yau shi ya biyo ta kan su.

148. Ƙafa ta goma sha biyar ɗin ita ce,

IYEEDIIDEE kun ji ta ba ce-ce-ce,

Haka nan aka tsara su don nazarinsu.

Samfurin Ƙafa Cikin Hausa a Sabon Nazari

1.      ARAYYE

2.      IYEENAAYEE

3.      AYAARAAYEE

4.      AYYARAAYEE

5.      YAARAYEE

6.      AYYAARAYEE

7.      YAARANAAYEE

8.      RA’AYEENAYEE

9.      AYYEEDIIDE

10.  AYYAARAYEE

11.  AYYEEYAARAYEE

12.  IYEENAANAAYEE

13.  NAANAAYEE

14.  AYYEEYARAYEEDIIDE

15.  IYEEDIIDE

Karuruwan waƙoƙin Hausa a Balarabiyar Hanya na su Galadanci

149. To bincike ya tabbatar da wannan,

Su Larabawa da ka gan su ɗin nan,

Suna da ƙaida kan karorin waƙa.

150. Karuruwa har sha shida gare su,

Da Larabawa suka bijiro su,

Da su ake kan sarrafawar waƙa.

151. A waƙoƙin Hausa a wannan aiki,

Ga masu biyan sashin wannan tafarki,

A Hausa kari sha uku ne na waƙa.

152. Galadanci Nayintin sabinti fayif,

Da shi da Sa’id Nayintin ehti fayif,

Sun ɗauki wannan fatawa a waƙa.

153. Bello da Sheshe Tonti tatin su ma,

Suna nan bisa wannan tunanin su ma,

Na karorin nazarin kimiyyar waƙa.

154. Da bincike yai bincike a gare su,

Sun zurfafa kogin tunani kansu,

Suka samo sauran karorin waƙa.

155. Sai daga baya aka samar da uku,

Sai aka tara sha uku da uku,

Hausa ta tumfaye karorin waƙa.

156. A karori kam an yi kan-kan-kan to,

Dai dai wa daida malamai sun ce to,

Sun yi na’am bisa karorin waƙa.

157. Wannan, wani Ra’in masana ne wannan,

Akwai wasu Ra’i na daban a fannin,

Da suke magana kan kimiyyar waƙa.

Ga Yadda Ahmadu Bello ya tsara Karorin Waƙa a Balarabiyar Hanya.

158. Muna iya kawo duk karorin waƙa,

Don su zamo hujja a gun su waƙa,

Sun zama ginshiƙi a nazarin waƙa.

159. Ahmadu Bello ya zo da wannan tsari,

Ya zo shi da su a bisa wannan jeri,

Ya kuma karɓu gun su masana waƙa.

160. Ga su cikin baiti karorin waƙa,

Ku bi a sannu za a gan su a waƙa,

Yadda ya lissafo karorin waƙa.

161. Ɗawiil ya kira shi tokari na farko,

Ɗawiil ya gabatar nan ƙafa na farko,

Domin manazarta su sha shagalin su.

162. Madiid shi ne na biyu wannan tsari,

Sai Basiiɗ na uku wannan tsari,

A karorin shi ne na uku cikinsu.

163. Waafir na bi mi shi in kun gane,

A karori shi ne na huɗu ku gane,

A wannan tsari shi ya so ku san su.

164. Kaamil shi ne na biyar ku san su,

Hazaj shi an nan na shida cikinsu,

Rajaz na bakwai nan take na bijoro su.

165. Ramal na takwas ne a karorin waƙa,

Sarii’i na tara a karorin waƙa,

A jadawalin nan haka ya kawo su.

166. Na goma Munsarih ga shi an kawo shi,

Yana da kyawu ɗalibai ku san shi,

Karuruwan nan da na ambato su.

167. Karin Hafiif shi ne na sha ɗaya gun nan,

Shi Muƙtalib na sha biyu ne wannan,

Ba raba ɗaya biyu ga shi nan kun gan su.

168. Na sha uku Mujtath a wannan tsari,

Ga Mutakaarab na sha huɗu da sauri,

Ahmadu Bello haka ya jero su.

169. Mutadaarak na sha biyar a gare shi,

Mudaari’ii, na sha shida a gun shi,

Ahmadu Bello haka ya kawo su.

170. Ahmadu Bello haka ya tsaro su,

Da Ɗawiil shi ya fara ƙirge kan su,

Ya ƙare da Mudaari’ii a ƙidayar su.

171. Haka bai sa tsarinsu ya sauya ba,

Suna nan bisa aikinsu ba tababa,

Shi dai haka nan ya biɗa ya zubo su.

Ga Yadda A.A. Dunfawa ya Tsara Karuruwan Waƙa a Balarabiyar Hanya.

172. Nazari farko ke da shi ba ƙarshe,

Haka nan yake gun masana ko yaushe,

Sui nazari har ma su samar fatawa.

173. Cimar wani dai to gubar wani ne fa!,

A bar masana Ilmi su toshe ƙofa,

Manazarta suke ta fafatawa.

174. Domin su toshe mana sauran giɓi,

Mun miƙa wuya gare su ba wani zaɓi,

Mun sallama a gare su sallamawa.

175. Ga yadda Dunfawa ya zo da nasa,

A cikin Littafi ya zo da nasa,

Ma’aunin waƙa na A.A. Dunfawa.

176. A nasa tsarin Mutaƙarab na farko,

Shi ya gabatar bisa farkon farko,

Zaz sha’awa tsarin karorin waƙa.

177. Ɗawil shi ne na biyu wannan tsari,

Hazaj na uku ga shi nan a sarari,

A wannan tsari na karorin waƙa.

178. Wafir shi ne na huɗu ku gane,

A wanga tsari ‘yan uwa ku gane,

Bisa tsarin Dunfawa baharin waƙa.

179. Na biyar Mutadarak fa ba tababa,

Fatawar nan ta ƙara ɗumbin haiba,

Da kuzari gun manazarta waƙa.

180. Rajaz na shida jama’a ku gane,

Shi kuma Basiɗ yana kari na bakwai ne,

Wannan tsari na Mazhabar Dunfawa.

181. Shi Munsarih ya zo a kari na takwas,

Fatawar ta inganta komai fes-fes,

Nazarin ya karɓu gun kimiyyar waƙa.

182. Ramal yana nan a kari na tara,

Har yanzu dai na san da sauran rara,

Na jimillan ƙirgen karorin waƙa.

183. Madid na goma yake a karin waƙa,

Hafif na sha ɗaya a karorin waƙa,

Na sha biyu Kamil kamilin waƙa.

184. Sai Muƙtalib na sha uku a ƙidaya,

Na sha huɗu Mujtass karin kimiyya,

Da ake nazari kan kimiyyar waƙa.

185. Na sha biyar Sari’i sarin waƙa,

Mudari’i na a karorin waƙa,

Shi ne na sha shida a karorin waƙa.

186. Nan muka zo ƙarshensa wannan bahasi,

Na Dunfawa da yai mana ba ko sisi,

Domin mu ƙwarance kimiyyar waƙa.

Faɗaɗa Nazari

187. Fatawar Dunfawa ta yi dogon zango,

Ta ƙi tsayi kan karin Oro dai Gago,

Ya yi wakurwa kan karin Hausawa.

188. Ya samo sakamakon wakurwa,

Da yai a bisa kan karin Hausawa,

Don nemowan karuruwan Hausawa.

189. Dunfawa ya ce muna da namu na Hausa,

Ba na aro ba namu ne na Hausa,

Don Larabawa sun tarar Hausawa.

190. Suna da waƙoƙinsu don tarbiyya,

Suna da waƙoƙinsu na nishaɗi,

Akwai karorin da suke aunawa.

191. Domin ɗiyan waƙa ya zo a tsari,

Sauƙa da hawa, amo su zo a tsari,

Ba wani ɗan tasgaru bare guncewa.

192. Dunfawa ya ce kari bakwai gare su,

Ya bi kiɗa ne sanda zai nemo su,

Buri ya cika car wurin wakurwa.

193. Ku bi a sannu ga shi zan bijiro su,

Don ɗaliban waƙa su samu ganin su,

Cikin fatawar Sheikh Atiku ɗan Dunfawa.

194. Cikakken kari shi ne na farko a Hausa,

Kari mai Dungu Ɗaya ne na biyunsa,

Haka dai aka samu ga ɗan Dunfawa.

195. Kari mai Dungu Biyu shi ne na uku,

‘Ya’yan Hausawa ku dai san na uku,

Haka dai ya fi kyawu gida zas sha’awa.

196. Kari mai Wushirya ya zame na huɗunmu,

Kari mai Cassawai yana nan a namu,

Shi ne na biyar a wurin Hausawa.

197. Kari mai giɓi gaba shi ne na Shida,

Awurin Hausawa dai, shi ne na shida,

Mun gode sosai da wagga wakurwa.

198. Kari mai Gibi Baya shi an na bakwai,

Karorin Hausawa iyakarsu bakwai,

A dai fatawar Shek Atiku ɗan Dunfawa.

199. Ga yadda karin Hausa tsarinsu yake,

Manazarta waƙa ku bi ku tarke,

Cikin wannan Ra’i na Shek Dunfawa.

Sunan Karuruwan Hausa Alamcinsu

Cikakken Kari   - - - -

Kari Mai Dungu Ɗaya v - - -

Kari Mai Dungu Biyu  v v - -

Kari Mai Wushirya  - v v -

Kari Mai Cassawai  v - v -

Kari Mai Giɓi Gaba  - v - -

Kari Mai Giɓi Baya  - - v -

Sakamakon Sabon Bincike

200. Ilmi shi bai gaji yin shiru ba,

Ƙarin bincike shi ya fi ba tababa,

Daga inda wasu su ka ja su ka tsaya,

201. Wasu daga nan ne za su ja su ɗora,

Su faɗaɗa nazari gwargwadon basira,

A samo wani haske da zai buwaya.

202. A wannan fanni wanda zai inganta,

Madalla da wannan batu a rubuta,

In dai nazari ne a fannin kimiyya.

203. Karin Hausa takwas ne a wannan nazari,

To bincike ya tabbatar da ƙari,

Nazari ya inganta kan kimiyya.

204. Manazarta ga naw sabon alƙawari,

Da a kai nazari kan tsohon alƙawari,

Ya haifar haske a bisa kimiyya.

205. Zan zo da karin nan takwas manazarta,

Na kimiyyar waƙa da ya inganta,

Don Ilimi ɗan bincike ne duniya.

206. Ku fara ƙidaya za na lissafa su,

Don ɗaliban waƙa su gan su su san su,

Bai ƙarewa bincike a kimiyya.

207. Cikakken kari ya zo kari ne na Ɗaya,

Mai bi masa kari mai Dungu na ɗaya,

Karin waƙar Hausa ne cikin kimiyya.

208. Kari na uku kari ne mai Dungu Biyu fa,

Zan zo da siffar su ku gan su yau fa,

Hujja ce mai kau da dukkanin jayayya.

209. Kari na huɗu shi ke kari da Wushirya,

Kari mai Wushirya ya fi kai wa ƙurya,

Don matsayinsa da yake a kimiyya.

210. Kari mai Cassawai kari ne shi ma,

Shi ne na biyar kun ji hauni da dama,

Babu guda ɗai wanda zai jayayya.

211. Kari na shida ba ɗai da ke tababa,

Kari na shida shi ne mai Giɓi a Gaba,

Ilimi ne tsantsa Arulin kimiyya.

212. Kari na bakwai shi ne da Giɓi Baya,

Kari mai Giɓi Baya ya buwaya,

Ya mai nazari kar ka juya baya.

213. A sabon nazari ga shi yadda ya zo shi,

Karorin Hausa yadda aka samo shi,

Nazari ya tabbatar shi ba jayayya.

214. Shifa Gadai Bago kari na takwas ne,

Nazari shi ne ya binciko shi ku gane,

Hujja shi ke kore duk jayayya.

215. Sauti na kiɗa shi yake nuƙusani,

Sanda mawaƙi harshensa yai saɓani,

Zare na tunaninsa take zai ja baya.

216. Sai sautin ganga ta sam nuƙusani,

Kari na Gadai Bago nan ya samu sukuni,

Har ya yi tasiri ake jin ɗuriya.

217. Wannan hujjar madogara ce Malam,

Na fitar da Gadai Bago ƙaɗa’an sarmadam,

Kari ne shi ma a fagen kimiyya.

 

Sunan Karuruwan Hausa Alamcinsu

Cikakken Kari   - - - -

Kari Mai Dungu Ɗaya v - - -

Kari Mai Dungu Biyu  v v - -

Kari Mai Wushirya  - v v -

Kari Mai Cassawai  v - v -

Kari Mai Giɓi Gaba  - v - -

Kari Mai Giɓi Baya  - - v -

Gadai Bago   v - - v

Kammalawa

1.      Komai ya yi farko ka san zai ƙarshe,

Wannan nazari yanzu ya zo ƙarshe,

Ma’ana to dai kammalawa ce nan.

2.      Sunana Alhaji Ibrahim ni,

A Misau nake nan Bauchi ba saɓani,

Tataji Misau inkiya ta ke nan.

3.      Nai ɗan bahasi kan Arulin waƙa,

Shauƙi ya ɗebe ni na yi da waƙa,

Allah sa sauƙin fahimtar wannan.

4.      Matani da a kai bincike kan waƙa,

Ban zurfafa ba don ya zam sassauƙa,

Ya sa manazarta su nazarce shi tunin.

5.      Kafin sauran binciken in fitar shi,

Manazarta waƙa ku dakwance shi,

Gaba ba da jimawa ba za ku ga wannan.

6.      Cika mini burina Tabaraka Allah,

Mu fid da Aruli don isarka Allah,

Na Hausa tsagwaro da za a yi gaban nan.

7.      Ina neman ɗaukinku ya Malamaina,

Ku ƙara mini ƙarfi cikin bincikena,

Don mu game ƙarfi da ƙarfe gun nan.

8.      Mu samar da Arulinmu ba tababa,

In har muka samar shi, mu ke da riba,

Mun san na aro, daɗa ga namu sannan.

9.      Mun ribaci ilmi ta kowane hauji,

Ga dai tunanin ɗalibinku kun ji,

Tataji Misau da kake ji ɗin nan.

10.  Matsa lamba kan bincike bisa waƙa,

Zai samar mana Arulin waƙa,

Na Hausa in mun zurfafa a fagen nan.

11.  Gyaɗa sai an matsa ta za ta yi mayi,

Wuta ce matakin farko don ta yi mayi,

Manazarta don kuna sau maganan nan.

12.  In dai za ai magana na Aruli,

Dole manazarta ku dai baje koli,

Da hakan dai har za mu samar namun.

13.  Rashin tsagawa, rashin jini in ji Hausa,

Rashin tonawa, rashin Arulin Hausa,

To ɗalibai ƙalubalenku fagen nan.

Manazarta

Galadanci, M.K. M (1975) The Poetic Marriage between Arabic and Hausa, Harsunan Nigeria (pp 1 – 16) BUK.

Bagari, D. M. (1987) Zangarniya (Waƙoƙin Hausa). Rabat – Morocco.

Dunfawa, A.A. (2003) Ma’aunin Waƙa. Sokoto: Garkuwa Publishers.

Bello, A. (2015) Arulin Hausa a Faɗaɗe. Zariya: Ahmadu Bello Uniɓersity Press Ltd.

Post a Comment

0 Comments