Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Hadisan Manzon Allah (SAW)

Waɗannan wasu jerin hadisan Manzon Allah (SAW) ne. Allah ya ba mu ikon koyi da koyarwar addini, ya sa mu gama da duniya lafiya.

Hadisan manzon Allah (SAW)

Hadisan manzon Allah (SAW)
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Dangane da duk wani kuɗi da ka kashe a bisa tafarkin Allah, ko 'yanta bawa, ko a matsayin sadaka ga mabuƙata, ko domin tallafa wa iyali, to wanda ya fi kawo lada shi ne wanda ka kashe a kan iyalanka." (Sahih Muslim: 995)


Manzon Allah (SAW) ya ce: "Dukkan ayyuka suna tare da niyya. Duk abin da mutum ya yi niyya shi yake samu. Duk wanda ya yi hijirarsa saboda samun duniya, to zai same ta - ko wata mata da yake son aura, to sakamakon hijirarsa yana ga abin da ya yi hijira dominsa." (Sahih Al-Bukhari: 1)

Hadisan manzon Allah (SAW)
Manzon Allah (SAW) ya ce: "Babu wani Musulmi da yake da 'ya'ya mata guda biyu, kuma ya kula da su biya tarbiyya mai nagarta, face zai shiga aljanna." (Al-Adab Al-Mufrad: 77)

Hadisan manzon Allah (SAW)
A'isha (RA) ta ce: Na ji Manzon Allah () yana addu'a a cikin gidana: "Ya Allah, ka ƙuntata wa waɗanda suke ƙuntata wa al'ummata yayin shugabantar su, sannan ka sassautawa waɗanda suke sassauta wa al'ummata yayin shugabantar su.""
(Muslim: 1828)


Manzon Allah () ya ce:" Kada ɗaya daga cikinku ya yi salla alhali yana sanye da tufafi ɗaya wanda bai rufe kafaɗunsa ba."
(Sahih Al-Bukhari: 359)

Hadisan manzon Allah (SAW)
Manzon Allah (SAW) yakan ce: "Mafi munin abubuwa su ne waɗanda aka ƙirƙira (da sunan addini); duk wani abin da aka ƙirƙira bidi'a ne, sannan duk wata bidi'a ɓata ce, kuma duk wata ɓata tana wuta.
(Sunan An-Nasa'i: 1578)


Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lallai Allah ba ya dubi zuwa ga fuskokinku ko dukiyoyinku, sai dai yana dubi ne zuwa ga zukatanku da ayyukanku."
(Sahih Muslim: 2564)


Manzon Allah () ya ce: “Allah ya gafarta wa al’umma ta munanan abubuwan da zukatansu suka raya musu idan dai ba su aikata su ko furta su ba, sannan ya gafarta musu abin da aka tilasta su aikatawa.”


Manzon Allah () ya ce: “Kada ɗayanku ya yi tafiya (da ƙafafunsa) yayin da yake sanye da takalmi sawu/wari ɗaya; ko dai ya sanya takalma biyu, ko kuma kada ya sanya takalmi kwatakwata.”
(Sahih Al-Bukhari: 5856)


A'isha (RA) ta ce: Hannun Annabi (SAW) na dama ya kasance ne domin wankansa da abincinsa, hannun hagunsa kuma domin tsarkinsa ne da kuma (kawar da) ƙazanta."
(Sahihu Abi Dawud: 33)

Post a Comment

0 Comments