Ticker

6/recent/ticker-posts

Yabon Nasaba a Wakokin Narambada: Dangoginta da Dangantakarsu da Wanda ake wa Waka

Citation: Dunfawa, A.A. (2024). Title. Yabon Nasaba a Waƙoƙin Narambaɗa: Dangoginta da Dangantakarsu da Wanda Ake wa Waƙa. Ginshiƙin Nazarin Salon Waƙoƙin Hausa,93-98. www.doi.org/10.36349/djhs.2024.v03i01.011.

Yabon Nasaba a Waƙoƙin Narambaɗa: Dangoginta da Dangantakarsu da Wanda ake wa Waƙa

Atiku Ahmad Dunfawa
Sashen Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

Tsakure: Yabo a cikin waƙoƙin baka shi ne danganta wasu halaye da ɗabi’u kyawawa ga wani domin masu sauraren waƙa su ga girmansa da ɗaukakarsa a cikin al’umma. Ana yin haka ne ta hanyar amfani da kalaman koɗawa ko kambamawa ko cicciɓawa domin tabbatar da abin da aka ambata game da shi ga masu sauraren waƙar. Yabo shi ne abin da Tsoho (2013:1) ya kira shi yabau. A cikin rabe-raben yabo (yabau) da ya kawo akwai yabon dangantaka (nasaba), a wajen da ya nuna ana yaba mutum ta hanyar danganta shi da iyaye da ‘ya’ya da mata da ‘yan uwa da abokai da abokan arziki[1] da barwa[2] da sauransu Tsoho (2002:171-195). Irin wannan yabon na dangantaka (nasaba) shi ne maƙalar ke son ta duba a cikin waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa domin fitowa da matsayin waɗanda aka danganta wanda ake yabo da su.

Fitilun Kalmomi: Yabo, Waƙoƙin Baka, Ibrahim Narambaɗa

Gabatarwa

Yabon dangantaka (nasaba) wani muhimmin tubali ne da aka gina jigon yabo da shi a cikin waƙoƙin fada[3]. A yabon dangantaka, ana yaba mutum ta hanyar danganta shi da iyayensa ko ‘ya’yansa ko ‘yan uwa ko abokan aiki ko abokan arziki ko barori ko bayi. A waƙoƙin fada akan ambaci ɗa alhali ba ɗa ne na jinni ba, ko a ambace shi uba amma ba uba ne na jini ba. Haka ma akan danganta wani a matsayin aboki amma a kasa gane abokin aiki ne ko na zama tare ko na barantaka ko na bauta. A wanna maƙala za a dubi yabon dantantaka ta hanyar fayyace yadda ainihin dangantaka take tsakanin wanda ake yabo da waɗanda aka danganta shi da su. Za a yi amfani da waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa domin fito da misalai a kan abubuwan da aka ambata.

Kamar yada Tshoho (2002) ya faɗa, ana gina turken yabon nasaba ta amfani da iyaye ko ‘ya’ya ko mata ko ‘yan uwa ko abokai ko barwa, to a wannan tsarin ne za a ɗauki kowane rukuni na dangantaka a ga yadda Narambaɗa ya gina jigon yabo da shi tare da fayyace ainihi yadda dangantakar take tsakaninsu ta hanyar sharhin ɗan waƙar.

Dangantaka ta Jini

A irin wannan yabo ana ambaton iyaye ko kakannin wanda ake yabo a danganta shi da su ta hanyar amfani da lafuzzan ɗa ko jika ko gida. A wannan yabon ana iya kiran wanda ake yabo da lafazin ɗa ko da kuwa jika ne. Haka ma akan kira wanda ake yabo da ɗa ya Allah ko ɗan tsatsao ne ko na zumunta ko na zamantakewa ta abuta ko ta aiki, ana iya fahimtar haka ta sanin nasabar wanda ake yabo.

Kakanni

Kakanni su ne waɗanda wanda ake yi wa waƙa ya fito daga tsatsonsu, na kusa ko na nesa. Jingina mutum ga wasu kakanni masu daraja waɗanda suka shuɗe kuma tarihi yake riƙe da gudummawar da suka bayar a cikin al’umma girmamawa ce. Wannan ya sa makaɗan sarauta ke danganta waɗanda suke yi wa waƙa ga irin waɗannan mutane domin a ga girman wanda ake yi wa waƙa a san jikan manyan mutane ne. Misali:

Jikan Shehu mai dubun doki ɗan Na-ammani,

Gawurtacce na magajin rafin Hausa.

            (Narambaɗa: Gwarzon Shamaki)

Batun da akai ga yau babu Sarki nan irinka,

Jikan Sanda arna suna shakkar haye ma.

            (Narambaɗa: Batun da akai ga yau)

A waɗannan ɗiyan waƙa da suka gabata, Narambaɗa ya yabi Sarkin Gobir Amadu ta hanyar danganta shi da kakanninsa na nesa da na kusa. Ya danganta shi da Shehu Ɗanfodiyo a matsayin kaka maɗaukaki, ya kuma danganta shi da Sarki Gobir Umaru a matsayin kaka na kusa. Duk wannan domin tabbatar da ɗaukakar Sarkin Gobir Amadu na Isa. Ga wani misali;

ƙi-garaje na Sardauna,

Mun taho mu ƙaru da jikan Hassan na Maishanu

            (Narambaɗa: ƙi-garaje Sardauna)

Haka ma a wannan ɗa da ke sama , Narambaɗa na yabon Sardaunan Isa ta hanyar danganta shi da Sarkin Musulmi Hassan ɗan Ma’azu a matsayin kakansa na kusa

Jikan Mamman Tukur,

Maza ba mata ba ne,

Ɗan namijin duniya,

A gaishe ka Guraguri

A wannan ɗa Narambaɗa na yabon Guraguri ne ta hanyar danganta shi ga kakansa na nesa, wato Mamman Tukur na Matuzgi. A wannan ɗa babu wani abu face Narambaɗa yana nuna dangantakar Guraguri da Mamman tukur ya kuma yabe shi ta hanyar wannan dangantaka (nasaba).

Gwabron giwa jikan Isau,

Maƙi-gudu baban ‘yanruwa[4].

            (Sarkin Ɓurmin Moriki)

A wannan ɗan ma Narambaɗa yana yabon Sarkin Ɓurmin Moriki ne ta hanyar danganta shi da kakansa Sarkin Ɓurmi Isau.

Duk a ɗiyan waƙar da suka gabata Narambaɗa ya nuna dangantakar waɗanda yake yabo da waɗanda ya danganta su da shi a matsayin kakanni suke gare su. Wannan ya nuna duk wajen da aka kira wanda ake yabo da jika to jikan ne kuma da lafazin jika ake amfani. To amma a waɗannan ɗiya da ke tafe ba da lafazin jika ya yi amfani ba, sai ya yi amfani da wasu lafuzza a maimakon lafazin jika. Ga abin da ya ce:

Shiri bajini Mamuda

Abu na Namoda shirarre

            (Narambaɗa: Shirin bajinin Mamuda)

Abu bajinin Namoda gagara dako na zagi,

Darzaza na Rafi baban yarin ƙaura.

            (Narambaɗa: Abu bajinin Namoda)

A waɗannan ɗiyan waƙa Narambaɗa bai kira Sarkin Kiyawa Abubakar da jikan Mamuda Ko jikan Namoda ba, a maimakon haka sai ya yi amfani da Kalmar bajini a matsayin jika, wato kiransa bajinin waɗannan shi ke nuna cewa kakanninsa ne. Lafazin bajini yana nuna wani ƙarfafan ɗa da aka samu daga zuruyyar wanda aka danganta wanda ake yabo da shi, shi ne Mamuda[5]. Wannan na nuna duk wajen da aka kira wanda ake yabo da bajijni gidan wani ko zakaran gidan wani to wanda ake yabo jika ne ga wanda aka danganta shi da shi. Kenan wajen danganta wanda ake yabo da kakanninsa ana iya amfani da bajini ko katakoro ka zakaran gidan wane su wakilci lafazin Jika.

 Iyaye

Yada ake yabon basarake ta hanyar danganta shi da kakanninsa haka ake yaba shi ta hanyar danganta shi da iyayensa. A waƙar fada ana iya yaba sarki ta hanyar danganta shi da ubansa mahaifi ko ɗan uwan ubansa wani lokaci har da abokon ubansa. A irin wannan dangantaka ana amfani da lafazin ɗa ne kawai. Ana iya bambanta uba mahaifi da ɗan uwan uba ko abokinsa kawai ta sanin tarihin wanda ake yi wa waƙa. Amma idan sunan da aka ambata sunan sarauta ne, to wanda ake yabo ɗan tsatso ne ko na zumunta ga wanda aka danganta shi gare shi. Misali Narambaɗa ya yabi Sarkin Gobir ta hanyar danganta shi da ubansa Alu. A nan ba yana nufin Alu ɗan Bello ba, yana nufin Sarkin Gobir Aliyu. Wanda yake jika ga Aliyu ƙarami ɗan Bello[6]. Ga abin da ya ce:

Amadu ɗan Alu gidanai na Isa,

Ya yi sarki kuma ga ɗiyan da yah haihwa nan sun yi.

Narambaɗa ya danganta Sarkin Gobir Amadu ga babansa domin yaba shi, ta nuna cewa shi ɗa ne na tsatso ga Sarkin Gobir Aliyu. Haka ma ya yabi Sarkin ƙayar Maradun ta irin wannan hanyar, ya danganta shi da mahaifinsa don ya yabe shi, ya ce:

Ya buwayi maza ginshiƙin tama na Amadu,

Garba ƙi-gudu ɗan Moyi[7] mai halin mazan jiya.

Ta hanyar irin wannan dangantaka ta iyaye na tsatso Narambaɗa ya yi ta ga sarakuna daban-daban. Misali:

Yai halin mazan jiya,

Ɗan Sanda mai Kwatarkwashi.

Ɗan Isiyaka makaye,

Jafaru mai halin mazan jiya,

Zamna da lafiya.     

Duka waɗannan ɗiyan waƙa da suka gabata Narambaɗa ya yabi sarakunan ne ta hanyar danganta su da iyayensu mahaifa. A wasu wurare kuwa danganta su ya yi ga wasu iyaye na zumunci waɗanda ba mahaifa na tsatso ba. Misali ya ce:

Jikan Shehu mai dubun doki ɗan Na’ammani,

Gawurtacce na Magajin Rafin Hausa

Ya buwai maza Salihu ko yanzu a bar wargi,

Ba su ima ɗan Inna[8] halin Ummaru na yayyo.

Na’ammani ba mahaifin Sarkin Gobir ba ne na tsatsao kamar yadda Inna ba mahaifiyar Sarki Salihu ce ta tsatso ba amma iyaye ne na zumunta aka danganta su gare su a matsayin iyaye don a yabe su.

Dangantaka ta ‘Ya’ya

Shi ma irin wannan yabon dangantaka a cikin waƙoƙin fada ba sai ɗa na tsatso za a danganta ga wanda ake yi wa waƙa ba a kira shi uban wane ba. Ɗa na iya zama na tsatso ko na zumunta ko na zamantakewa ta aiki ko ta abota ko ta barantaka ko ta abuta. Ita ma wannan dangantaka ana iya saninta ta hanyar sanin tsarin zamantakewar fada da tarihin wanda ake yi wa waƙa. Mafi yawa, duk wanda za ka ji an ambaci sunansa na yanka misali a ce uban Bello ko baban Sani, da sauransu to ɗiya ne na tsatso ko na ‘yan uwa ko na abokai. Misali:

Gwarzon Shamaki na Malam toron Giwa,

Baban Dodo ba a tam ma da batun banza.

Baban Maiwurno bas su can sun yi zancen banza,

Mai ga-noma bai yi ƙwazon mai gona ba.

Toya matsahwa sadauki na Abdu,

Baban Isa baban Buwai,

In don na ka gama lafiya.

Duka waɗannan misalai da suka gabata suna nuna waɗanda aka ambata na iya zama ɗiyan tsatso ko na ‘yan uwa ko na zamantakewar aiki ko ta abota. Saidai idan aka kira Sarki baban wane kuma ya zam wanen nan sunan wata sarauta ne ta ‘yan sarki, to shi wannan ɗa ne na tsatso ko na ‘yan uwa amma ba na abota ko na zamantakewa ba. Misali:

Ya hana wargi na Malam,

Tausau baban Durumbu.

Durumbu sarauta ce ta ‘ya’yan sarki, kiran sarkin babansa na nuna ɗansa ne na tsatso ko na ‘yan uwa.

Dangantaka ta Zumunta

A irin wannan yabon dangangantaka a kan danganta wanda ake yi wa waƙa da yayyensa ko ƙannensa. Sai dai fahimtar yaya ne ko ƙane ne sai ga wanda ya san gidan sarautar. Za a danganta basarake ga wani yaya nasa ko ƙanensa a yaba shi ta wannan fuska, sai dai kamar yadda aka faɗa mai saurare ba ya iya gane yaya ne ko ƙane ne sai in yana kusa ga gidan sarautar. Misali:

Hawo da shirin yaƙi ,

Na Sambo marinjayi.

Ginshimin Ɗanjeka,

Ni na sani daɗai bai yi sake ba,

Na taho murna ga Muhamman na Rafi ya tabbata Sarki.

Tattaki maza ɗan Shehu na Babba,

Kamda’aren[9] Salau mazan ƙwarai.

Ya buwayi maza ginshiƙin tama na Amadu,

Garba ƙi-gudu ɗan Moyi mai halin mazan jiya.

Duk waɗannan da ka danganta su da waɗanda ake yi wa waƙa suna matsayin yayye ne ga sarakunan ko kuma ƙanne, saidai tantance yaya ne ko ƙane sai ga wanda ya san zumuntar.

Dangantaka ta Mata

Dangantaka ta fuskar mata akan ambaci sunan mata ko matan da wanda ake yi wa waƙa ke aure wanda aka saba da shi. Wani lokaci mawaƙa kan ɗora kansu a matsayin mata ga wanda suke yi wa waƙa ko kuma su kira shi miji ta la’akari da ɗawainiyar da ake yi masu tamkar yadda ake wa matan da ake aure. Sai dai wannan yabo na danganta sarki da matansa bai cika yawa a waƙoƙin Narambaɗa ba. Ga misali:

Mijin Nana Yalwa ɗan Sanda,

Gulbi ka wuce kwalhewa.

Narambaɗa ya danganta Sarkin Zazzau da matarsa don yaba shi ta hanyar kiran sa mijin ita Yalwar.

Dangantaka ta Aiki

Wannan ita ce dangantar basaraken da ake yi wa waƙa da wasu abokan aikinsa, kamar masu sarautu (da ke ƙarƙashinsa ko masu zaman kansu) ko ‘yan majalisarsa. Misali:

Jikan Shehu mai dubun doki ɗan Na’ammani

Gawurtacce na Magajin Rafin Hausa

Ai in na so kiɗi gidanka nikai shi yah hi,

Na Magajin gari na Jekada Abdu,

Ga gidan Sarki ban zuwa gidan wani mai ‘yag garka.

Ginshimin Ɗanjeka,

Ni na sani daɗai bai yi sake ba,

Na taho murna ga Muhamman na Rafi ya tabbata Sarki.

Ibrahima na Guraguri,

Mai Shinkafi bajinin Zagi,

Mu dai Allah ya bar muna kaya.

Magajin Gari da Magajin Rafi ‘yan majalisar Sarkin Musulmi ne ake danganta Sarkin Gobir das u a matsayin yabo. Shi ko Rafi basarake ƙarƙashin Sarkin Ɓurmin Moriki. Yayin da Guraguri yake ɗan majalisar Magajn Shinkafi. Narambaɗa ya danganta waɗanda yake yabo da waɗannan mutane don zamansu abokan aiki.

Bayi da Barwa

Ana yabon Sarki ta hanyar danganta shi ga wasu bayinsa ko barwansa. Ita iri wannan dangantaka tana ɗaukar fuska biyu; wani lokaci a ɗauki baran ko bawan a matsayin abokin aiki ga sarki sai a ce na wane, wani lokaci kuma a ɗauki baran ko bawan amtsayin ɗa ga sarki, sai a kira sarkin da uban wane cewa da bawan ko baran. Ana yin haka ne saboda bawa ko bara na iya zama matsayin ɗa ko matsayin abokin aiki. Shi ya sa kake jin duk wani wanda ke riƙe da wata sarauta ta bayi ko ta barori wani lokaci mawaƙi ya kira sarki ubansa ko ya kira sarki nasa. Misali:

Sardauna shirarre na Shamaki,

Ci-fansa na Malam tsakin tama.

Ai baban Shamaki karo sai rago

Bunsuru kau da gabanka ka’ a ji ma bakin banza.

Ruwa da kada baban Mandede.

Baban Shamaki manyan daga.

Shamaki sarauta ce ta bayin sarki, shi ya sa wani lokaci ake cewa sarki na Shamaki a matsayin abokin aiki wani lokaci a ce masa uban Shamaki ta la’akari da zamansa bara ko bawa. Haka ma abin yake ga sauran sarautu irinsu kamar sarutar yari. Wani lokaci a kira sarki na yari wani lokaci uban yari. Misali:

Amadun bubakar gwarzon Yari,

Dodo na Alkali.

Ubangijin Shamaki Sadauki,

Na yari tattaki masu ja ma.

Abu bajinin Namoda gagara dako na zagi,

Darzaza na Rafi baban yarin ƙaura.

Narambaɗa ya kira sarki a matsayin abokin aikin yari, a wani waje kuma ya kira shi a matsayin uaba ga Yari.

Sarautar Jekada sarautar barorin sarki ce, ita ma Narambaɗa ya yi amfani da ita ta fuskokin biyu ya ce:

Ai in na so kiɗi gidanka nikai shi yah hi,

Na Magajin gari na Jekada Abdu,

Ga gidan Sarki ban zuwa gidan wani mai ‘yag garka.

Bai ɗau wargi ba na Jekada,

Na ma-ji-kira baban ‘yankwana[10].

Baban Jekadiya,

Ruwa da yawa maganin fari

Jakada sarautar barori ce, ita taw aɗannan fuskokin biyu Narambaɗa ya yi amfani da su wajen danganta su ga yabon sarakunansu. To haka abin yake ga suran sarautu irinsu, kamar Sarkin Zagi ko Ajiya.

Naɗewa

Bayanan da suka gabata sun nuna yadda fuskokin yabon dangantaka a waƙoƙin fada suke da kuma lafuzzan da aka fi amfani da su a irin wannan yabon. An nuna lafuzzan jika ko gwarzo ko bajini ko ginshiƙi duk sukan zo ne domin nuna basaraken da ake yi wa waƙa jika ne ga waɗanda aka danganta shi da su.

Shi kuma lafazin ɗa ana amfani da shi ne a matsayin basaraken da ake yi wa waƙa ya kasance ɗa na tsatso ko na zumunta ka na zamantakewa ga wanda aka danganta shi gare shi.

Lafazin baban wane, yakan tuzgo ne ta fuska biyu. Idan sunan yanka ko laƙabi ne aka ambata, to zai zama ɗa ne na tsatso ko na zumunta ko na zamantakewa. Amma idan sunan sarauta ne, to ba ɗan zamantakewa ba ne, ɗa ne na tsatso ko na zumunta. Ta dangangantakar mata kuwa, to ba a danganta sarki da wata mata idan ba matarsa ta aure ba.

A ɓangaren dangantakar aiki kuwa, mafi yawan waɗanda ake danganta sarki da su masu riƙe da wasu sarautu ne ya Allah a ƙarƙashin sarkin da ake yi wa waƙar ko a wasu wurare. Kamar yadda aka gani ga Magajin Rafi da Magajin Gari ko Rafi da Guraguri da wasunsu.

Danganta sarki ga bayinsa ko barwansa kuwa, mafi yawa yakan kasance ga bayi ko barwa masu riƙe da wata sarauta irin tasu, kuma yakan ɗauki fuska biyu ne; ko dai a danganta shi ga baran nasa a matsayin uba ko a danganta shi gare shi a matsayin abokin aiki. Irin waɗannan su ne kamar Yari ko Zagi ko Sarkin Dogarai ko Ajiya ko Jekada ko ‘Yankwana da sauran sarautu da suka danganci bayi da barwai.

Manazarta

Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa, Ibrash Islamic Publication Centre LTD, Adelabu Street, Surulere, Lagos.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa Da Gudummawarsa Ga Rayuwar Hausawa, Triumph Publishrs, Kano.

Dunfawa A.A. (2003) Ma'aunin Waƙa, Garkuwa Media Services, Sokoto, ISBN 978-36144-9-5

Dunfawa, A.A. (2004) "Zuga A Waƙoƙin Fada" in Algaita Journal of Dept. of Nigerian Langs. Bayero University, Kano, No 3 Vol.1, ISBN 978-36905-2-3, page 223-233.

Finnegan, R. (1977). Oral Poetry: It’s Nature, Significance and Social Context, Cambridge University Press.

Gusau, S. M. (2003). Jogon Nazarin Waƙar Baka, Benchmark Publishers Limited, No. 29 AKCC Busuness Complex, Aminu Kano Way, Kano.

Gusau, S. M. (2008). Waƙoƙin Baka A ƙasar Hausa: Yanaye- Yanayensu Da Sigoginsu,

Sami, S. (2007). Traditional Titles in Northern Nigeria, Na-Hweraka Resources LTD, No. 12 UMCA Shop, Zuru.

Tsoho, M. Y. (2013). “Bayanin Yabau A Matanin Waƙar Ummaru Ɗan Ɗanduna Na Gwandu, Ta (Dr) Mamman Shata Katsina, in Ɗunɗaye, Journal of Hausa Studies, Dept of Nig. Languages, UDU, Sokoto.

Yahya, A. B. (1997). Jigon Nazarin Waƙa, Fisbas Media Services, Kaduna.

Yahya, A. B. (1999). Salo Asirin Waƙa, Fisbas Media Services, Kaduna.



[1] Su ne abokai wa]anda ban a aiki ba wa]anda wata hul]a ta daban ta ha]a ku.

[2] Su ne barori ko bayi da ke a gidan sarauta.

[3] Akwai irin wannan yabo ko ba a wa}o}in fada ba, amma a nan wa}o}in fada aka damu das u.

[4] ‘Yanruwa sarauta ce wadda mai ri}e da ita shi ke kula da albarkatun rowan masarauta

[5] Mamuda shi ne Sarkin Kiyawa na biyu kuma }ane ga Namoda wanda ya kafa ƙauran Namoda

[6] Aliyu }arami ]an Sarkin Musulmi Bello ne, Shi ne Sarkin Isa na farko a cikin Torankawa

[7] Sarkin ƙaya Moyi ]a yake ga Mu’alle]I ]an Bello wanda ya kafa ƙayar Maradun

[8] Innar Gobir uwa take ga Sarkin Gobir, amma ba uwa mahaifiya ba

[9] Ma’anar kamda’are daidai take da gwarzo

[10] ‘Yankwana shi ne shugaban bayin sarki masu kula da kulle }ofar da ke shiga wajen iyalan sarki kuma sub u]e da safe.

Post a Comment

0 Comments