Ticker

6/recent/ticker-posts

Zuga Da Habaici a Wakokin Zamani: Nazari a Kan Wasu Wakokin Siyasa Na Muhammadu Buhari a Jumhuriya Ta Hudu – Manazarta Da Rataye

Cite this as: Ɗangulbi, A. R. (2024). Zuga Da Habaicia Wakokin Zamani: Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhammadu Buhari a Jumhuriya ta huɗu [Kundin digiri na uku wanda ba a wallafa ba]. Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria.

ZUGA DA HABAICI A WAƘOƘIN ZAMANI: NAZARI A KAN WASU WAƘOƘIN SIYASA NA MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUƊU

NA

ALIYU RABI’U ƊANGULBI 

A THESIS SUBMITTED TO THE SCHOOL OF POST GRADUATE STUDIES, AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA IN PARTIAL FULFILMENT OF THE REQUIREMENTS FOR THE AWARD OF DOCTORATE DEGREE IN AFRICAN LITERATURE (HAUSA) DEPARTMENT OF AFRICAN LANGUAGES AND CULTURES, FACULTY OF ARTS AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA, NIGERIA

SATUMBA, 2024

MANAZARTA

Abdullahi S. U. (1987), Gaskiya Dokin Ƙarfe. Kano: Printing Press Nigeria.

Abdulƙadir D. (1974). The Poetry, Life and opinions of Sa’adu Zungur,Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

Abdulƙadir D. (2008), Kwatanta Rubutattun Waƙoƙin Siyasa na Hausa Daga 1804-1899, da 1900-1966, Kundin Digiri na Uku, SashenKoyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Abdulƙadir D. (2007), Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa,Zaria. Amana publishers Ltd.

Abdulkarim M. M. [2014]. Politics without Bitterness, Sokoto: Madallah printing press.

Adeniyi O. [2005]. The Last 100 Days of Abacha, Lagos: The Bookhouse Company.

Afolalu, R. O. (1969),A History of West Africa A. D. 1000 to the Present Day.Ibadan.Onibonoje Press— Publishers,

Al-Mallah H. Y. [2011]. The Governmental System of the Prophet Muhammad. A Comparative Study in Constitutional Law; Lebanon: Dar Al-kotob AL-Ilmiyah.

Amfani A.H, (2012), Hausa da Hausawa: Jiya Da yau Da Gobe. A paper presentedin Honour of Dalhatu Muhammad, Department of African Languages and Cultures, Zaria : Jami’ar Ahmadu Bello.

Adamu M. (2014) Salon Tallata ‘yan takara a waƙoƙin jamhuriya ta huɗu:Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasar jamhuriya ta huɗu. Kundin digiri na biyu, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Aminu K. (1987) Tarihin Kafuwar Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya. Kaduna: Fisbas Media Service

Auta A. L (2008), Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Faɗakarwa a ƙarni na Ashirin. Kundin Digiri na Biyu. Sashen koyar da Harsunan Nijeriya; Kano: Jamiar Bayero

Bargery, G.P. (1993). A Hausa English Dictionary and English Hausa Vocabulary Second Edition: Zaria:Ahmadu Bello University Press Ltd.

Bagari, D. M.(1986),Bayanin Hausa Jagora ga Mai Koyon Ilimin Bayanin Harshe. Rabat-Moroc: Imprimerie El Maarif Al jadida.

Birniwa H.A. (1981). The Infiraji 1 – 5 of Aliyu Namangi, Unpublished M.A Thesis SOAS: University of London.

Birniwa H.A. (1987). “Conservatism and Dissent: A comparative Study ofNPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Political Verse from Cica 1946 – 1983” (Unpublished) Ph.D thesis, Department of Nigerian Languages, Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University

Birniwa H.A (2005), Tsintar Dame a kala: Matsayin Karin Magana a cikin Waƙoƙin Siyasa; Department of Nigerian Languages, Sokoto: UDUS

 Bunguɗu H.U.(2016).Nazarin Waƙoƙin Bara na Ƙarni na Ashirin da ɗaya a Zamfara,Kundin Digiri na uku, Department of Nigerian Languages,Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

Bunguɗu A.I. (2017). Tarken Rubutattun Waƙoƙin Siyasa Na Kabiru Yahaya Kilasik:Kundin digiri na biyu; Sashen koyar da Harsunan Nijeriya Kano: Jami’ar Bayero.

Bunza A.M (2009). Narambaɗa; Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre Limited.

CNHN (1977 da 1979). Waƙa a bakin Mai ita Kano: Jami’ar Bayero.Britannica Online Encyclopedia -----

CNHN (1987) Tarihin Kafuwar Jam’iyyu a Nijeriya daga Malam Aminu Kano, Kano: Jami’ar Bayero.

CNHN (2006),Ƙamusun Hausa, Kano: Jami’ar Bayero.

Crowder M. (1962), The Story of Nigeria,,London: Faber and Faber Limited.

CoLeman, J.S. (1958), Background to Nationalism. Barkelys and Los Angles: University of California Press

Dudley, B.J. (1968), Parties an Politics in Northern Nigeria. London: Frank Class and Co, Ltd

Dunfawa, A.A (2005) “Zambo da Habaici a cikin Rubutattun Waƙoƙin Addini”, Department of Nigerian Languages Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

Dumfawa, A.A.(2004),Zuga A cikin Waƙokin Fada, Department of Nigeria

Languages Series IV, Kano: B.U.K.

Umfawa A.A (2003) Waƙa a Tunanin Yara, Kundin Digiri na uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo

Ɗangambo, A. (1980) “Hausa Wa’azi Verse from C.A 1800 to (A 1970): A criticalStudy of form, Content, Language and Style” ,Kundin Digiri na Uku, London: Jami’ar SOAS.

Ɗangambo, A. (1984). Rabe- raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga RayuwarHausawa. Kano: Triumph Publishing Company.

Ɗangambo, A. (2007). Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Kaduna: Baraka Press andPublishers.

Ɗangulbi, A.R (2003). “Siyasa a Nijeriya”: Gudummawar Marubuta Waƙoƙin Siyasana Hausa ga Kafa Dimokuraɗiyya a Jamhuriya ta huɗu, zango na farko,”, Kundin Digiri na biyu, sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ɗangulbi, (1996) , Habaici da Zambo a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Sokoto: Takardar daaka gabatar a taron ƙara wa juna sani da aka gabatar a Kwalejin Ilim ta Shehu Shagari

Ɗangulbi A.R. (2013),Tasirin Habaici a cikin Waƙoƙin siyasa:Nazarin Waƙar SarkinYamman Sakkwato Alhaji Aliyu Magatakarda Wamako ta Alhaji Ibrahim Aminu Ɗandago,.Katsina: Federal College of Education.

Ɗangulbi da Wasu,(2022),Mazarƙwaila da Maɗi a Mahangar Al’ada da zamani. ISSN Print: 2708-6259/ISSN Online:2708-6267.Pp.56

Diso, A.H.(1997).Zambo da Yabo a matsayin Dabarun Jawo Hankali a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa na Hausa.Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harunan Nijeriya, Kano, Jami’ar Bayero.

Furniss, G. (1996). Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa Edinburgh:Edinburgh University Press Limited.

Funtuwa, A.I (2011). “Manufar Waƙa a siyasa: Ire-Iren Jigogin Waƙoƙin Siyasa na Hausa”, Kano: Bayero University.

Funtuwa A.I. (2003), Waƙoƙin Siyasa na Hausa a Jamhuriya ta uku,Yanaye-Yanayensu da sigoginsu” Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Gusau, S.M (2008). Waƙoƙin Baka a ƙasar Hausa, Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers

Gummi A. M.(1982): Alƙurani mai Girma da Tarjamar Ma’anoninsa zuwa Hausa.Lebanon: Darul Arabia

Garba S. (2011),Salon Sarrafa Harshe a waƙoƙin Aƙilu Aliyu, Kundin digiri na uku, Zaria: Ahmadu Bello University

Hiskett M. (1975) A History of Hausa Islamic Verse, London: SOAS,

Inuwa, T. (2012). “Nazarin Rubutattun Waƙoƙin Siyasa na PDP, Kundin Digiri naFarko, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Imam, A.(1937), Magana Jari ce Littafi na Biyu: Zaria: NNPC Ltd.

Idris, Y. (2016). Jigon Bijirewa a Rubutattun Waƙoƙin Siyasa a ƙasar Hausa 1903 – 2015, Kundin Digiri na uku, sashen Koyar da Harsunan Afrika da al’adu, Zaria: Jam’ar Ahmadu Bello.

Isah, Z. (2013), Farfaganda a Waƙoƙin Fiyano na Hausa, 2003-2013,Kundin digiri na biyu, sashen koyar da Harsunan Afrika da al’adu, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Isiyaku M. (2016), Shugaba nagari a bakin mawaƙan zamani. Kundin digiri na farko, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Junju, M.H.(1980), Rayayyen Nahawun Hausa, Zaria:NNPC.

Koko H. S.(2014),Hausa-Cikin Hausa, Sokoto: Shehu Shagari College of Education

Kano, A. (1987), Tarihin Kafuwar Jamiyyun Siysaa a Nijeriya. Kano: CNHN

Lawal A. (edit) (1997), Stylistics in Theory and Practice, Ilorin: Paragon Books Ltd.

Leech G. P.(1968),A Linguistic Guide, to the Study of Poetry. London: Publishers.

Muktar I.(2005), Bayanin Rubutattun Waƙoƙin Hausa, Abuja: Countryside Publishers Ltd.

Muktar I. (2004),Introduction to Stylistic Theories, Practice and Criticism, Abuja: Countryside Publishers Ltd.

Muhammad A. L. (2011), Harshe da Siyasa: Nazarin salo a shirin Alƙawari kaya ne na sashen Hausa, Gidan Rediyo Tarayya Kaduna. Kundin digiri na biyu, sashen koyar da Harsunan Afrika da Al’adu. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

New Nigerian, 17-1-1966

New Nigerian,1-1-1984

The Democrat, 28-8-1985

New Nigerian, 1-11-1990

New Nigerian, 24-6-1993

New Nigerian, 17-6-1996

The Democrat, 13-3-1998

New Nigerian, 29-5-1999

Raft Constitution, (1996)

Draft Constitution, (1988)

Raft Constitution (1979)

Otite, O. and Ogionwo,W. (1979), An Introductiom to Sociological Studies,Ibadan.Heinemann Educational Books (NIG), LTD,

Phillips D. T. (1992), Lincoln On Leadership, Executive Strategies For Tough Times:America: First trade printing,

Sa’id, B. (1978). Gudummawar Masu Jihadi Kan Adabin Hausa, Kundin Digiri na biyu a sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Sa’id, B. (2002). Rubutattun Waƙoƙin Hausa na Ƙarni na Ashirin a Jihohin Sakkwatoda Kebbi da Zamfara, Kundin Digiri na uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Sani M. M (2012),“Tunanin Siyasa a Waƙoƙin Malam Hassan na Kutama” KundinDigiri na Biyu, sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Skinner N.C. (1980). An anthrology of Hausa Literature, Zaria: Northern NigeriaPublishers Company.

Tsoho M. Y. (1987), Tarkakken Matanin WaƘar Kanzil Azimi ta Aliyu Namangi,Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Afrika, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Tsoho M.Y. (2013) Adabi da harkokin siyasa; Bijirewa a WaƘoƘin Shegiyar UwaMai kashe ‘ya’yanta PDP ta Haruna Aliyu Ningi. Takardar da aka gabatar a taron Ƙarawa juna sani na farko a kan Harshe da Adabi da Al’adu, Cibiyar Nazarin Harunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Tsoho M.Y. (2002) Eulogues, the building Blocks of Hausa Praise song: A thematicand structural examination; Kudin digiri na uku a sashen koyar da Harunan Nijeriya da Afrika, Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

Usman B.B.(2008), Hikimar Magabata: Nazari a kan Rayuwar Malam (Dr) Umaru Nasarawa Wazirin Gwandu (1966-2000) da Waƙoƙinsa. Kundin Digiri na uku; Sokoto: UDUS

Yahaya, I.Y. (1988), Hausa a rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, Zaria:Northern Nigeria Publishers Company.

Yahya, A.B. (1987) “The Hausa verse category of Madahu with Special Reference totheme, style and Background of Islamic Sources and Belief” Kundin Digiri na uku, sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yahya A.B. (1997), Jagoran Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas Media Services

Yahya A.B (2003) Siffantawa Bazar Mawaƙa: Wani Salo Cikin Nazarin Waƙa Kano: CNHN BUK

Yahya, A.B. da Dunfawa, A (2010) “Waƙar Motar Siyasa: Saƙon Talakawa zuwa ga‘yan siyasar zamani. Department of Nigerian Languages, Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University,

Yahya A,B. (2001), Salo asirin waƙa, Kaduna. Fisbas Media Services.

Yakasai S.A.da Sani A.U (2018), Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA).Sokoto: Unique Colours Publishers.

HIRA

Bello Muhammed Kwakwazo Gusau (Alƙalin ƙungiyar kanikawa ta jihar Zamfara)ɗan shekara 56,hira da shi a ranar Asabar 02/10/2023.

Rarara D. K. (Hira da shi a ranar 16, Maris 2023)

Ibrahim Yala Hayin Banki (Hira da shi a ranar 28, February 2022).

Kamilu Hussaini Adamu (Hira da shi a ranar Laraba 28, February, 2024).

Lawali Saraki (Zonal Director Education, Gusau) hira a ranar Alhamis 03/09/2022.

Mudassir Ƙasimu Jibril (Hira da shi ta whatsApp ranar 21, February, 2024).

Muhammed R. A (Hira da shi a ranar 26-2-2023)

Murtala Abdullahi Mamsa, (Hira da shi ta WhatApps ranar 20, February, 2024).

Salisu Zakari Bagega, (sarkin maqera),xan shekara 61; hira da shi a ranar23,Mayu,2022.

Yusuf Ibrahim Birnin Tsaba—Hira da aka yi da shi ranar 13/03/2021.

Rataye

Waƙar Aminu Ladan Abubakar Alan Waƙa: “IN HAR BA KA SAN GARI BA SAURARI DAKA”

Turke : (O’ O Dalilina for Buhari).

Jagora: In baka san gari ba saurari daka,

Ni hujjatarriqo ga turmin nan sha daka,

Don babu haɗin gami matar aure saxaka

Dan ya hana handama da ‘yan ɗauki akai baka

Don kishi kan qasarmu ai Arewa, kudun duka

Dan raya maraya har ma da ƙauyuka dulka,

GMB za mu baiwa ƙuri’unmu duka

To Baba Buhari ga dalilai na biya malka,

Na biya Maka,

Dalilai na biya mana.

Y/Amshi Dalili na kasata na figirmamawa

Ba zan je ga mahallaka ba

Dalili na

Ba zan yar da yaudara ba

Dalili na

Ba zan tura mahandama ba

Dalili na

 

Jagora: Buhari za mu zaɓa ba zan yarda

 Da maƙada ta ba

 

Y/Amshi Dalilina kasata na figirmamawa

Dalilina ba zan je ga mahallaka ba

Dalili na

Ba zan yarda da yaudara ba

Dalili na

Ba zan tura mahandama ba

Dalili na

 Buhari za mu zaɓa a 09

Muna kira sai a zaɓi Baba Buhari

 

Jagora: A haye dalilina noma da yaddawo Arewa

 Dalilina

Mun yi nomanmu sayarwa

Dalilina

Muna ci ko kuwa muna fitarwa waje

Dalilina

Talakkawa suna ta yin yalwa dalili na,

Dan ance mu yi shi muna tavawa

Dalilina

Wai tallafi ku jagurawa dalilina

Yan zu mi marsa mu ke ganowa dalilina

Mata maza duk mun riƙewa dalilina

A ‘yan Arewa.

Da rigata Arewa gar ku manta

 

Y/Amshi Dalilina kasata na figirmamawa

Da zan je ga mahallaka ba

Dalilina

Ba zan yarda da yaudara ba

Dalilina

Ba zan tura mahandama ba

Dalilina

Buhari za mu zaɓa a 09

Muna kira sai Baba Buhari

 

Jagora: A hayye zan baku dalili na,

 Da akwai da yawa ga kaɗan dalili na

Kai rayuwar ƙarya babu ga dalili na

Tsaya matsayinka a Gwabnatin dalili na

Gaskiya ta samu ga dalili na

Ba sani ba sabo cikin dalili na

Buhari na tallaka da mai kuɗi dalili na

Gaskiya dokin ƙarfe Buhari za mu zaɓa

A kwaimu da rawa muna kiɗi

Sai baba Buhari dalilina

 

Y/Amshi Dalili na kun fi wannan shi ne

Dalilina kasata na figirmamawa

Da ba zan je ga mahallaka ba

Dalilina

Ba zan yarda da yaudara ba

Dalilina

Ba zan tura mahandama ba

Dalilina

Buhari za mu zaɓa a 09

Muna kira sai Baba Buhari

 

Jagora: Dalilina – dalilina

Toshe wawurar baitilmali

Dalili na daƙile gininkai da ya fi misali

Mutum ɗai ya wawushe kuɗin talakawa

A kai Turai can a makure babu dalili

A dalilin ga Buhari ya jawo balli

Dalilin yanzu anyi akawun ɗaya banki,

Batun rufe boda ya dawo wasu sun koka

 

Y/Amshi Muna duba yanzu muna gane dalili

 

Jagora: Um, ashe da tace yanzu barkatai mun gane

Y/Amshi: Muna duba yanzu, muna gane dalili

Jagora: Ashe daƙile cigaban ƙasa akai da haka

Y/Amshi Muna duba yanzu muna gane dalili

Jagora: Miyagun ƙwayoyi saffararsu ta haka

Y/Amshi Muna duba yanzu muna gane dalili

Jagora: Makamai ma ana shigo da su ƙasar ta haka

Y/Amshi Muna duba yanzu muna gane dalili

Jagora: A’a Buhari da lissafi, Baba Mai hangen nesa

 Tuni ya hango wannan

Ya sa a filan ɗinta

Masu jari hujja suke yaƙar wannan

 

Y/Amshi Muna duba yanzu muna gane dalili

Jagora: Dalili na kun ji wannan shi ne

Y/Amshi: Dalilina

Jagora: Ba zan je ga mahallaka ba

Y/Amshi Dalilina

Jagora Ba zan yarda da yaudara ba

Y/Amshi Dalilina

Jagora Ba zan tura mahandama

Y/Amshi Dalilina

 Buhari za mu zaɓa, a 09

 Muna kira sai Baba Buhari

Jagora: Kuma dakan xaka

Ta haɗu da mata ana shiƙar ɗaka

Zancen da nikai a yanzu ilimi ya haɓɓaka

Makarantu an gina mi zani daɗamaka

Ka zama Sarki Buhari kai dai sa aimaka

Na so a bani tamburra inta bugamaka

Na tabbata da kana mugunta da baka haka

Zamani mai tafi da kowa ba’a inxari

Gwanina ba zan wuce ba ni dai sai na faɗi

Farfesa Umar Garba na Xanbbata nike nufi

Y/Amshi NCC Bos amanar an jeho yacaɓe

 Dalili na ka yi ƙoƙari ka roshe ɓarnuka

Dalilina, kai ka baiwa al’umma ayukka,

Dalili na kai ka jawo noma an karkata

Dalili na kai ka hargatsata kamar haka

Dalilina ka mayar da ƙyauyukka burnuka

Dalilina kai ka soma samo muna martaba

 

Jagora: Buhari zani zaɓa ba zai yarda da ƙeta ba

Dalili na relewai tana zaga ƙasa

Dalilina nesa yanzu ta zamo kusa

Dalilina za a samu sauƙi a ƙasa

Dalilina suffuri da sauƙi a ƙasa

Dalilina titunanmu sun kawu ƙasa

Dalilina hasken lantarki ta haska ƙasa

Dalilina baba shi yake saita qasa

Dalili na yanzu babu tamkarsa ƙasa

Dalilina mun daɗe muna tona ƙasa

Dalilina yanzu munga canji a ƙasa

Baba zamu sake zaɓa

Dalilina nes lebul

Dalilina ba zan tai kwaɗayin dala ba

Dalilina ba zanje gun yaudara ba

Dalilina ba zan tallata wawuraba

Dalili na ni ba zan biku ina sani ba

Buhari zani zaɓa ban yadda da maƙatata ba

Dalilina kun ji wannan

 

Y/Amshi Dalilina

 

Jagora: Ba zan je ga mahallaka ba

Y/Amshi Dalilina

 

Jagora Ba zan tura mahandama ba

Y/Amshi Dalilina

Buhari za mu zaɓa a 09

Muna kira sai Baba Buhari

Dalilina shi zamu sake zaɓe Buhari

Hannunku sama ga wanda zai yi zaɓen Buhari yan ƙasata

Duk kaninmu sai Baba Buhari

Ahmadu Bello University Zariya 

Post a Comment

0 Comments