Ticker

6/recent/ticker-posts

Zuga Da Habaici a Wakokin Zamani: Nazari a Kan Wasu Wakokin Siyasa Na Muhammadu Buhari a Jumhuriya Ta Huɗu – Babi Na Biyu

Cite this as: Ɗangulbi, A. R. (2024). Zuga Da Habaicia Wakokin Zamani: Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhammadu Buhari a Jumhuriya ta huɗu [Kundin digiri na uku wanda ba a wallafa ba]. Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria.

ZUGA DA HABAICI A WAƘOƘIN ZAMANI: NAZARI A KAN WASU WAƘOƘIN SIYASA NA MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUƊU

NA

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

A THESIS SUBMITTED TO THE SCHOOL OF POST GRADUATE STUDIES, AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA IN PARTIAL FULFILMENT OF THE REQUIREMENTS FOR THE AWARD OF DOCTORATE DEGREE IN AFRICAN LITERATURE (HAUSA) DEPARTMENT OF AFRICAN LANGUAGES AND CULTURES, FACULTY OF ARTS AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA, NIGERIA

SATUMBA, 2024 

BABI NA BIYU

BITAR AYUKKAN DA SUKA GABATA

2.1 Gabatarwa

Masana da manazarta sun yi bincike da nazari ta fuskar kimiyar harshe da al’adu da kuma adabi. Haka kuma sun yi wallafe-wallafe a waɗannan fannoni daban-daban, musamman a fannonin nazarin waƙoƙin Hausada suka shafi na siyasa. Wannan bincike ya waiwaya baya domin ya zaƙulo wani abu daga cikin ayyukan masana, waɗanda basu ce komi ba a kansa. Yana iya kasancewa kodon mantuwa irin ta ɗan’adam, ko kuma saboda rashin ɗaukar sa da muhimmanci. Saboda haka an gudanar da wannan bincike a fannin nazarin zuga da habaici a cikin waƙoƙin siyasar zamani da aka yi wa Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu.

Ɗangambo (1980), ya daɗa fayyace yadda waɗannan nazarce-nazarcen suka samo asali daga masana da manazarta fannin adabin Hausa tun lokacin da karatun harshen Hausa ya samu, kuma ya ɗaukaka a makarantun cikin gida da na ƙasashen duniya daban-daban. Sai dai tun wancan lokaci da aka fara bincike a kan waƙa, ba a yi wani aiki mai kama da nazarin zuga da habaici ba. Wannan bincike ya zurfafa cikin nazarin zuga da habaici ne, don zaƙulo yadda mawaƙan siyasar zamani da suka yi wa Muhammadu Buhari waƙa suka yi tasiri a fagen jawo hankalin mutane su fahimci saƙon da ake isarwa gare su na muhimmancin zaɓen mutum nagari a siyasa.

Dangambo (2007: 6), ya bayyana ma’anar waƙa kamar haka:‘Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar Ƙa’ida ta baiti, ɗango, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya) da sauran ƙaidojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba’’.

Yahya (1997:4 ), ya ce, ‘’ Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum ba’’. A nasa tunani, Birniwa, (2004: 67} ya bayyana cewa, maƙasudin marubuta waƙoƙin siyasa shi ne su yabi jamiyyarsu. A waɗansu lokuta ma, kushen da ake yi wa’yan jam’iyyar hamayya ba a kan shugabanni kawai yake tsawaita ba, har akan shigar da sauran mabiya.

Idris (2016) ya yi bincike ne a kan jigon bijirewa a waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa. Nazarin da ya yi bayanin irin yadda dangantakar masu mulki da waɗanda ake mulka da bijirewar da ake samu tsakaninsu.Binciken nasa bai ce komi ba a kan salon zuga da habaici ba.Don haka wannan bincike ya yi Magana ne a kan zuga da habaici da mawaƙan siyasar zamani suka yi amfani da su cikin waƙoƙin da suka yi waMuhammadu Buhari.

Birniwa [1987], ya yi magana a kan kwatanta waƙoƙin jumhuriyya ta farko da haɗa NPC da NEPU, da kuma na junhuriyya ta biyu.Wato,NPN da PRP, tare da bayyana aƙidar kowace jam’iyya da magoya bayanta. Sai dai gurbin da ya bari shi ne, nazarin salon zuga da habaici a cikin waƙoƙin siyasa.

Shi kuwa Abdulƙadir [2008], ya kwatanta rubutattun waƙoƙin siyasa na Hausa daga 1804-1966, nazari ne da ya shafi asali da ma’anar rubutacciyar waƙa da rabe-raben rubutattun waƙoƙin Hausa, da ma’anar waƙar siyasa,da halayyar waƙoƙin siyasa da kuma ire-iren waƙoƙin siyasa na Hausa. Ya kuma yi nazari da sharhin wasu waƙoƙin siyasa, waɗanda suka haɗa da; waƙar “Tsarin Mulkin Musulunci” da waƙar “Murnar Cin Birnin Alƙalawa” da waƙar “NEPU da waƙar “NPC” da sauransu. Ya kuma kwatanta waƙoƙin siyasar 1804-1899, da na 1900-1966, inda ya dubi jigo da salo da sarrafa harshe da kuma tsarin waƙoƙin. A cikin bayanansa malamin bai yi magana a kan salon zuga da habaici da mawaƙansiyasar zamani suka yi amfani da su ba cikin waƙoƙinsu. Don haka wannan giɓi da ya bari, shi ne wannan bincike yake ƙoƙarin cikewa saboda amfanin masu nazari su fahimci irin gudumawar da salon zuga da habaici suke bayarwa a fagen bunƙasa adabin Hausa da kuma harkokin siyasar zamani, musamman siyasar Muhammadu Buhari.

Abdulƙadir [1974], ya yi bayani a kan waƙoƙin Sa’adu Zungur ne, ya kuma yi sharhi a kansu, musamman waƙar maraba da soja da waƙar Arewa jumhuriyya ko mulukiya wadda ta yi tasiri ga wayar wa ‘yan siyasa kawunansu a kan mahimmancin gwagwarmayar neman ‘yanci.Ya dai sassarƙa zuga da habaici cikin waƙoƙinsa a matsayin jigogin faɗakarwa da gargaɗi ga al’ummar Arewacin Nijeriya domin su fahimci muhimmancin mulkin siyasa, wanda ke bai wa kowane ɗan ƙasa ‘yancinsa. Shi ma bai ce komi ba dangane da nazarin salon zuga da habaici ba. Wannan bincike zai cike katafaren giɓin da wannan masani ya bari a kan zuga da habaici da mawaƙan siyasa suke amfani da su wajen jawo hankalin masu sauraren waƙoƙinsu.

Mukhtar (2005), ya yi nazari ne a kan waƙoƙin komawa ga Allah ta malam Lawal Maiturare

Garba (2014) ya yi aikinsa a kan waƙoƙin siyasa a bakin sha’iri Nazifi Asnanic. Ya bayyana yadda mawaƙin ya yi amfani da zuga da habaici a matsayin dabarun jawo hankalin ‘yan siyasa da sauran al’umma su fahimci saƙon da waƙoƙinsa suke ɗauke da shi. Wannan aiki nasa yana da alaƙa makusanciya da wannan, domin ayyukan suna magana ne a kan salon jawo hankalin mutane su fahimci saƙon da ake isarwa gare su. Shi ma wannan aiki zai cike gurbin da ya bari dangane da zuga da habaici a matsayin jigo da salon sarrafa harshe da tubalin gina waƙa da ayyukan fasaha da sauransu.

Haka kuma,wannan bincike zai cike giɓin da sauran masana da manazarta irin su Dangambo, (1980), ya yi naari a kan waƙoƙi waazi waɗanda aka yi tun daga ƙarni na sha tara (19) har zuwa na ashirin. Malamin ya yi nazarin jigogi da zubi da tsari da kuma salo da sarrafa harshen waƙoƙiin.Y a nazarci waƙar Gargaɗi’ da ‘waƙar Halin duniya da waƙar Tuna mutuwa da waƙar alamomin bayyanar Mahadi da waƙar alamomin ƙiyama da waƙar bulaliyar zukata ga jamaa da kuma waƙar mari da sauransu.

Aikin nasa yana da alaƙa da wannan bincike domin aiki ne da aka yi nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa. Alaƙarsa da wannan bincike ita ce shi aikinsa a kan nazarin salon sarrafa harshe cikin waƙoƙin da ya yi nazari. Banbancinsu da wannan aiki shi ne nasa aikin a kan nazarin waazi waɗanda aka rubuta a ƙarni na 19 da na 20. Wannan bincike kuwa a kan nazarin zuga da habaici a cikin waƙoƙin siyasa da mawaƙan zamani suka yi wa Muhammadu Buhari.

 Dumfawa, (2003), ya yi bayani a kan yadda waƙa take da tasiri a tunanin yara. Ya danganta yadda tunanin yara yake karɓar waƙa da irin waƙoƙin da tunanin yara ke iya karɓa. Ya bayyana yadda tunaninsu yake da sauƙin karɓar waƙa wanda ya sa mafi yawa a gargajiyance ko a zamanance aka fi cusa tarbiya ga yara ta hanyar yin amfani da waƙa. Ya ba da misalai daga waƙoƙin baka da rubutattu na yara tare da fayyace irin yadda tsarinsu yake wanda ya saɓa wa na sauran waƙoƙi da ba na yara ba. Dangantakar aikinsa da wannan aiki ita ce dukkans suna nazari ne a kan waƙa, sai dai bambancin da ke tsakaninsu shi ne, aikinsa ya yi shi ne a kan waƙoƙin yara, shi kuwa wannan aiki a kan nazarin zuga da habaici da mawaƙan siysar Buhari suka yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu domin su faɗakar da al’umma game da muhimmancin zaɓen mutum nagari a muƙaman siyasa. Aikin nasa ai taimaka ma wannan bincike domin dukansua kan waƙa aka gudanar a su.

 Usman (2008), ya yi nazari a kan Rayuwar Malam (Dr.) Umaru Gwandu Nasarawa Wazirin Gwandu (1966-2000) da ‘Waƙoƙinsa. Ya yi bayanin jigogin waƙoƙin Malam Umaru Nasarawa, abin da ya shafi jigon yabo, da jigon siyasa, da jigon gargaɗi da faɗakarwa, da jigon addini da sauransu. Sannan ya dubi zubi da tsari da kuma salon sarrafa harshe na waƙoƙin. Wannan aiki nasa ya fito da bayanin salon kamantawa da siffantawa da mutuntawa da dabbantarwa da abuntarwa da alamtarwa da sauransu. Haka kuma ya yi bayanin zaɓen kalmomi da karin harshe da aron kalmomi da sauransu.

Har wa yau ya yi nazarin wasu waƙoƙinsa waɗanda suka haɗa da, waƙar, Tsuntsayen zamani, da waƙar ‘’Ba Madogara sai Allah da waƙar Marssiyyar Shehu Kangiwa. Wannan bincike ya yi makusanciyar dangantaka da wannan aiki domin an yi shi ne a kan rubutattun waƙoƙin Hausa na siyasa. Haka shi ma wannan bincike an yi shi ne a kan nazarin zuga da habaici a waƙoƙin siyasar Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu.

Auta (2008), ya yi bayanin jigon faɗakarwa tare da yin nazarin wasu rubutattun waƙoƙin faɗakarwa, inda ya yi bayanin jigoginsu da zubi da tsari da kuma salo da sarrafa harshe. Haka kuma ya yi bayanin wsu ƙananan jigogi waɗanda ya kasa su zuwa gida biyu. Kashi na farko shi ne, wayar da kai da kuma kashi na biyu shi ne na zamantakewa. A rukunin wayar da kai, akwai jigogin ilmi da gyaran hali a kiwan lafiya da sauransu. A ɓangaren zamantakewa kuma ya yi bayanin jigon aure da zaman lafiya da siyasa da sauransu.

Dangantakar aikinsa da wannan bincike ita ce,dukkansu suna magana ne a kan rubutattun waƙoƙin Hausa. Sai dai shi ya nazarci jigon faakarwa a cikin waƙoƙi daban-daban. Wannan aiki kuwa ya yi bincike a kan zuga da habaici a wasu waƙoƙin siyasar Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu. Aikin nasa ya zama jagora ga wannan aiki.

Tsoho (2002), ya yi bayani a kan ma’anar waƙa da samuwar waƙar baka da yadda ake shirya waƙa da kuma rabe-rabenta. Haka kuma ya yi bayanin jigogin waƙoƙin da suka shafi ƙarfi ko iko da tsoratarwa da girmamawa da haƙuri. Bugu da ƙari ya dubi siga da salon waƙoƙin. Aikin nasa yana da makusanciyar alaƙa da wannan bincike kasanccewar dukkansu an yi su ne a kan waƙa; sai dai bambanci da ke tsakaninsu shi ne, wannan aiki yana nazarin zuga da habaici ne a wasu waƙoƙin siyasa a mawaƙan zamani suka yi wa Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu.

Yahya (1987), ya yi nazarin rubutattun waƙoƙin Madahu, inda ya dubi jigo da salo da kuma tushen wakoƙin. Daga cikin waƙoƙin da ya yi nazari akwai; Waƙar Daliyya da waƙar Maamaare da waƙar Israi da waƙar Tsarabar Madina da sauransu.

Binciken nasa yana da alaƙa da wannan aiki ta fuskar nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa. Sai dai bambancin da ke tsakaninsu shi ne aikinsa ya shafi waƙoƙin Addini (madahu) shi kuma wannan aikin ya shafi siyasa,inda aka yi nazarin zuga da habaici a wasu waƙoƙin siyasa da aka yi wa Muhammadu Buhari a jumhururiya ta huɗu.

Gusau (1995), ya yi bayani a kan tarihin ginuwar nazari da feɗe adabin Hausa. A cikin littafin nasa ya bayyana yadda aka gina adabin Hausa da kuma nazarinsa. Har wa yau ya ƙara kawo mazahabobi da hanyoyin nazarin adabin Larabci da na Turanci, inda ya dubi tasirin tsohuwar hanyar nazarin Larabci da kuma sabuwar hanyar nazarin Larabci ga nazarin adabin Hausa. A al’adar Turawa kuma ya kawo hanyoyin zamani kamar su, hanyar nazarin asali da watsuwa zuwa sassa da hanyoyar nazari da tarihi da hayayyafa da hanyar nazari ra ra’i ko mazahaba, da hanyar nazarin gudummawar adabi ga al’umma da dai sauran hanyoyin nazarin adabin da dama. Bugu da ƙari ya dubi tarihin ginuwar nazari da feɗe shi a cikin Hausa, inda ya ya kawo lokuta kamar na maguzanci da lokacin da adinin Musulunci ya zo ƙasar Hausa. Haka kuma ya yi bayani dangane da lokacin daular Usmaniya, wato ƙarni na 19 da lokacin zuwan Turawa, wato, ƙarni na 20, da sauransu. Dangantakar da ke tsakanin aikin nasa da wannan bincike ita ce dukkan ayyukan biyu suna magana ne a kan adabi. Saboda haka aikin nasa ya taimaka ma gudanar da wannan aiki ha ya sami nasara.

Yahya (2002), ya yi bayani a kan siffantawa bazar mawaƙa wani saƙo ne cikin nazarin waƙa. A cikin mukalarsa ya yi bayanin maanar siffantawa da nauoinsa kamar kamantawa da jinsarwa da alamtarwa da kinaya da sauransu. Wannan muƙala ta zama jagora ga wannan bincike domin ta yi bayani yada za a yi nazarin waɗannan salailai a cikin nazarin waƙa. Bambancin muƙalarsa da wannan bincike ita ce shi wannan bincike yana magana a kan nazarin zuga da habaici a cikin waƙoƙin siyasar zamani da mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari suka yi amfani da su cikin waƙoƙinsu.

 Dangulbi, (2003), ya yi bayani a kan wasu jigogin wakoƙin siyasa na jumhuriya ta huɗu. Ya yi bayani dalla-dalla a kan jigogin faɗakarwa a yabo da tallata jam’iyya da ‘yan takara da jigon yabo da zambo da habaici da sauransu. Aikin nasa wani jagora ne ga wannan aiki domin ya yi bincike ne a kan gudummuwar marubuta waƙoƙin siyasa na Hausa ga kafa Dimokuraɗiyya a jumhuriya ta huɗu zango na farko. Wannan aiki yana bayani ne a kan nazarin zuga a habaici a wasu waƙoƙin zamani: Nazarin wasu waƙoƙin da aka yi wa Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu. Bambancin aikinsa da wannan aiki shi ne,wannan aikin an taƙaita shi a kan zuga da habaici cikin waƙoƙin zamani; yayin wancan aikin ya yi magana akan gudummuwar marubuta waƙoƙin Hausa na siyasa wajen kafa mulkin Dimokuraɗiyya a jumhuriya ta huɗu zango na farko.

Wannan bincike zai cike gurbin da suka bari a wannan fage na adabi, wato fagen nazarin zuga da habaici cikin waƙoƙin siyasar zamani da mawaƙan siyasa suka yi wa Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu. Wannan bincike zai nazarci salon zuga da habaici na waƙoƙin siyasar Muhammadu Buhari; domin gano irin tasirin da suka yi wajen cusa soyayyar Muhammadu Buhari a zukatan al’umma,ta hanyar faɗakar da al’umma game da kyawawan ɗabi’u da halayensa a cikin waƙoƙin siyasar zamani.

Diso (1997) ya yi magana ne a kan Zambo da Yabo a matsayin dabarun jawo hankali a rubutattun waƙoƙin siyasa na Hausa.A kundin nasa ya yi bayani a kan rubutattun waƙoƙin siyasa da haɓɓakar siyasar jam’iyya a Nijeriya, tare da kawo bayanin zambo da yabo a adabin Hausa.Ya kawo wasu misalan zambo da yabo a wasu waƙoƙin siyasar jam’iyya, waɗanda aka yi tun daga jumhuriya ta farko har zuwa shekarar 1996. Binciken nasa yana da alaƙa da wannan aikin, domin duka suna magana ne a kan waƙoƙin siyasa na Hausa. Sai dai bambancinsu shi ne, ya dubi zambo da yabo a rubutattun waƙoƙin siyasa, ya kawo misalai daga wasu rubutattun waƙoƙin siyasa na jumhuriya ta ɗaya da ta biyu da kuma ta uku. Wannan binciken yamaida hankali ne a kan salon zuga da habaici da mawaƙan siyasana Muhammadu Buhari suka yi amfani da su cikin waƙoƙinsu na wannan jumhuriya ta huɗu da muke ciki daga 2003-2022, domin su jawo hankalin masu saurare su fahimci muhimmancin zaɓen mutum nagari a mulkin siyasa wanda yin haka zai kawo cigaban kasa da zaman lafiya da tsaro a cikin ƙasa.

Isyaku (2016) ya yi aiki ne a kan shugaba nagari a bakin mawaƙan zamani. Ya yinazari ne, a kan rawar da mawaƙan zamani suka taka wajen bunƙasa adabin Hausa da al’ummar Hausawa. Ya nazarci tasirin zamani a nau’in shugabanci a ƙasar Hausa.Haka kuma ya dubi irin sauye-sauyen da aka samu a kan mawaƙan Hausa, musamman har ana yi wa wasu laƙabi da mawaƙan zamani saboda yin amfani da kayan kiɗa na zamani a cikin waƙoƙinsu na siyasa. Ya kawo misalan mawaƙan zamani kamar su Aminu Abubakar Alan waƙa da Mudassiru Ƙasim da Sadi Sidi Sharifai da Adam A. Zango da Naziru M. Ahmad (sarkin waƙa), da Nazifi Asnanic da Nura M Inuwa da Dauda Kahutu Rarara da Ibrahim Yala Hayin Banki da sauransu. Ya bayyana irin gudunmmawar da waɗannan mawaƙa suka bayar wajen faɗakar da mutane ga alfanun zaɓen shugaba nagari. Aikin nasa yana da alaƙa da wannan bincike domin yana nazarin salon zuga dahabaici da mawaƙan siyasa suka yi amfani dasu cikin waƙoƙin da suka yi wa Muhammadu Buhari.Wannan aiki zai cike giɓin da wannan bincike da Isyaku ya bari.

Adamu (2014), ya bayyana rawar da mawaƙan siyasa suka taka a jumhuriya ta huɗu, musamman ta fuskar tallata manufofi da aƙidun jam’iyyu (siyasu) ko ‘yan siyasa,masu nuna bijirewa ga jam’iyyun siyasa da manufofinsu. Ya nazarci tsarida salo a waƙoƙin siyasa da bambance-banbancen jigoginsu tare da sharhin wasu waƙoƙin jumhuriya ta huɗu.Misali, ANPP, da C.P.C da P.D.P.Aikin nasa bai yi magana a kan salon zuga da habaici kai tsaye ba. Wannan binciken zai cike wannan giɓi da manazarcin ya bari.

Isah (2013), ta yi bincike ne a kan nazarin hoton siyasar Nijeriya da tattalin arzikin ƙasa da kuma zamantakewa da addini kamar yadda suka bayyana a cikin waƙoƙin, tare da ayyana matsalolin da Nijeriya take fuskanta ta ɓangaren tattalin arziki, zamantakewa da siyasa da maslahar da marubutan suka kawo cikin waƙoƙinsu, domin ‘yan Nijeriya su farga, ko ci gaba da yin ɓarna ko kuma su gyara kamar yadda wasu waƙoƙin suka kawo mafita. Wannan aikin nata yana da makusanciyar alaƙa da wannan aiki, sai dai bambancisu shi ne wannan binciken zai yi nazarin salon zuga da habaici da mawaƙan zamani suka yi wa Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu tun daga 2003-2022.

A yunƙurin yin bita domin gudanar da wannan bincike an karkasa abubuwa da za a nazarta kamar haka:

2. 2. Siyasa

Siyasa wani salon mulki ne da wasu mutane ke jagorantar al’ummarsu bisa ga tsari irin wanda ke bai wa mutane damar faɗar albarkacin bakinsu (Democracy), wadda ake zaɓen shugabanni ta hanyar jefa ƙuri’a.

A harshen Larabci, “Siyasa’’ ta samo asali daga kalmar “Sa’asa”mai nufin “tsari”.Kuma daga wannan tushe sai kalmar ta koma “siyasatu”,wadda ke nufin “Tsari da tsayuwa kan al’amari [Al-Misbah al-Muniru Fi-garibi:362].A harshen Hausa, siyasa na nufin, wata dabara ce, wadda ake neman mutane su zama masu ra’ayi ɗaya domin su haɗa kai su zaɓi shugabanni da za su wakilce su a majalisu daban-daban na shugabancin ƙasa.Wato siyasa, wani tsari ne da ake jawo ra’ayin jama’a su aminta da zaɓen wani mutum don ya shugabance su, kamar yadda tsarin mulki ya tanada[Dangulbi:2003].

Harrap’s [1981], da Almunjid Abjada (Ƙamusun Arabic)sun bayyana cewa, siyasa nazari ne na yadda za a mulki ƙasa a ƙarƙashin zaɓaɓɓunwakilai a tutar jam’iyyu daban-daban.(Ƙamusun Larabci mai sun “Lisanul Arab),ya bayyana ma’anar siyasa da cewa, “Tafiyar da abu ta hanyar da zai yi daidai da abin”.Ya cigaba da cewa, “har ma idan aka ga mutum ya tsaya a kan dabbobi, kuma sun yarda da shi, sai a ce wane ya siyasance dabbobi. Ko kuma a ce shugaba ya siyasance talakawansa, idan an ji suna zaune lafiya.Siyasa mulki ne na farar hula wanda jama’a masu ra’ayi iri ɗaya za su haɗu su zaɓi wasu mutane don su shugabance su don a sami ingantacciyar al’umma da shiryar da su zuwa ga hanyar tsira ko a kusa ko a nesa.

.Bargery[1934] da Lawal[1983],da Gusau[1984],da Ƙamusun Hausa[2006],duk sun ba da ma’anar siyasa da cewa,”siyasa tana nufin,rangwame a farashin kowane abu ko kuwa tausasawa a cikin al’amurra.Wannan ya yi daidai da ra’ayin Abraham[1962] wanda ya bayyana cewa, siyasa tana nufin:

‘’Tafiyar da al’amurran jama’a tahanyarneman ra’ayinsu da shawarwarinsu.Wato,dabara ce ko wayo na iya hulɗa da jama’a’’.

Gusau(1984),ya bayyana cewa, siyasa na da ma’anoni biyu,ma’ana ta farko ita ce,siyasa na nufin gudanar da mulki ko tafiyar da mulkin jama’a daba wa kowa haƙƙinsa.Ma’ana ta biyu ya ce, idan Bahaushe ya ce, “wane ya yi mani siyasa”,to yana nufin:

i.Yaudara ko dabara ko wayo.

ii.Sauqi ko ramgwame.

iii.Lumana ko Lallami.

Sa’id [2002:172],yana cewa, siyasa wata hanya ce ta gudanar da zaɓaɓɓiyar gwamnati ta hanyar Dimokuraɗiyya a ƙarƙashin tsarin mulkin ƙasa, inda za a zaɓi shugabanni masu tafiyar da ita a ƙarƙashin kafaffun jam’iyyun siyasa. ya ƙara da cewa,siyasa tana iya ba da ma’anar ƙwarewa wajen iya tafiyar da jama’a da jure wa duk wata matsala tasu.Dar-el-mashreƙ[1960] ya ba da ma’anar siyasa,inda ya ce kalmar siyasa ta samo asali daga kalmar “saasa”.Bisa ga ƙa’idar tsarin nahawun Larabcisai takoma “siyaasa”. Ya bayyana ma’anar siyasa da cewa,”juyawa a kanwani lamari ko yarda da wani abu ko jiɓintar al’amarin al’umma tare da saninsu ko akasin haka.

A taƙaice siyasa tana nufin hanya ce ta gudanar da mulkin mutane a bisa tsarin mulkin gargajiya ta hanyar naɗi ko na zamani ta hanyar zaɓe, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Onigu Otite,Ogionwo W, (1979) sun ce,siyasa tana magana ne a kan shugabancin al’umma da ya shafi rayuwar zamantakewar al’umma a ɓangarori daban-daban.Sun ƙara da cewa, mulki shi ne damar aiwatar da wasu abubuwa ko wani aiki bisa ga tsarin doka da zai amfani al’umma.

2.3 Siyasar Gargajiya

Tsarin siyasar gargajiya shi ne, wanda ya shafi salon mulki irin na sarautun ƙƙgargajiya da kuma na addini. Irin wannan salon mulki ya samo asali tun kafin zuwan addinin musulunci. Ana sa ran cewa, an fara gudanar da mulki a duniya tun kafin musulunci ya bayyana. Al-Mallah (2011), ya bayyana cewa, a Ƙasar Arabiya babu wata tsayayyar hukuma da ke jagorancin alumma kafin zuwan musulunci. Ƙasar Arabiya tana da ƙabilu daban-daban tun a wancan lokaci.Kowace ƙabila tana bugun gaba da cewa, ita ta fi sauran ƙabilu kwarjini da ƙarfi. Duk da haka idan wani hatsaniya ko rikici ya tashi a tsakanin ƙabilun, sukan zauna da shugabannin kowace ƙabila daga cikinsu; su tattauna hanyar da za a shawo kan wannan matsala ko hatsaniya da ke tsakaninsu cikin sauƙi. Shugaban kowace ƙabila, da ake kira da suna Sayyid ko Shaykh, ana zaɓo shi ne daga iyali mafi alfarma daga cikin ƙabilun. Kuma ya kasance mutum mai kwarjini da ƙwazo ko jaruntaka, kuma wayayye. Yakasai, (2012, P.51), ya bayyana cewa, tsarin shugabanci a cikin kowace al’umma ya zama wajibi domin shi ne ke tabbatar da zaman lafiya da ƙaruwar tattalin arzikin ƙasa. Bargery, (1934, P. 944 ), ya bayyana shugabanci da cewa, muƙami ko matsayi ne na wakilcin jamaa da ake ɗora wa mutum ba ta hanyar yaƙi ba. Idris, (2016,P.128),ya ce, shugabanci wani abu ne da ya shafi muamula ta yau da kullum, a inda zai nemi taimako da goyon bayan sauran mutane domin sauke nauyin da yake kansa.

A siyasance kowane shugaban ƙabila shi ne ke da alhakin ɗaukar nauyin tafiyar da mulkin ƙabilarsa da ƙasarsa daidai da aladunsu da ra’ayoyinsu. Aikin kowane shugaba shi ne ya sasanta duk wata fitina da ta taso a tsakanin ƙabilun, tare da wakiltar jamaarsa wajen sulhu. Haka kuma, shi ne zaijagoranci yaƙi idan ya faru tsakanin ƙabilarsa da wata.A lokacin da addinin musulunci ya bayyana, kuma ya sami kafuwa a ƙasar Arabiya, sai salon mulki ya sauya daga gargajiya ya koma na addini.Manzon Allah (S. A W.) da sahabbansa sun gudanar da rayuwarsu kamar yadda tsarin musulunci ya zo da shi.Wannan salon mulki da addini ya zo da shi, ya ci gaba da yaɗuwa har ya zo ƙasar Hausa.

Yahaya (1988), ya bayyana cewa, muslunci ya shigo ƙasar Hausa tun wajajen ƙarni na 7, amma ba a samu waƙa ba, sai a ƙarni na goma sha shidda zuwa sha bakwai lokacin aka sami malamai da dama suka taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa addinin musulunci a ƙasar Hausa. Musulunci ya kawo sauyi ga salon mulkin gargajiya da ya taras Hausawa na gudanarwa. Mulkin ƙasar Hausa bai tashi daga hannun sarakunan ba, amma musulunci ya yi gyara ga yadda suke tafiyar da mulkin.

Turawan mulkin mallaka da suka zo ƙasar Hausa sun taras da Sarakunan ƙasar Hausa suna gudanar da mulkinsu daidai da tsarin mulkin musulunci. Turawa sun sauya salon mulkin ta yadda za su samu damar tsoma hannunsu cikin mulkin.Sun kawo salon mulki yadda zai dace da manufofins da buƙatunsu, inda suka yarda sarakuna su tafiyar da mulki,amma a ƙarƙashin kulawar Turawan mulkin mallaka.. Da tafiya ta yi tafiya, sai yan ƙasa masu kishin ƙasa suka fara gwagwarmayar neman yancin kai daga Turawan mulkin mallaka tun a wajajen shekara 1934 kamar yadda Idris (2016:45) ya cirato daga Yahaya (1988).

Aminu Kano (1987) ya bayyana yadda sarakunan gargajiya da alƙalai suke tafiyar da mulki a ƙasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka. Turawa sun yi haɗin gwuiwa da sarakuna suka gudanar da mulki wada ake kira ‘’mulki a kaikaice’’(Indirect rule). Wato, duk abin da za a yi dangane da wakilci a ƙasa,sai an bi ta hannun sarakunan gargajiya a zaɓi mutumin da zai wakilci al’umma a majalisa, bisa ga jagorancin Turawan mulkin mallaka.Tsoma hannu da Turawa suka yi a harkokin mulkin ƙasar Hausa, bai sa an daina bin wasu dokoki da tsarin mulkin gargajiya da na addinin musulunci ya zo da su ba.

2.4. Siyasar Zamani

Dudley (1968, p. 73-115) ya bayyana cewa a lokacin da Captain C. D. Morney ya iso arewacin Nijeriya ya bayyana cewa ya zo ne domin ya binciki shirin da ‘yan arewacin Nijeriya suka yi a siyasance na karɓar mulkin kai, kamar yadda ‘yan kudu suka buƙata daga Turawan mulkin mallaka.Amma ga dukkan alama ya fahimci cewa, ‘yan arewa ba su yi wani shiri ba,saboda mtsalar rashin jittuwar ra’ayoyin ƙungiyoyin da suka rayu a wancan lokaci.

A cikin shekarar 1934 ne, aka fara samun ƙungiyoyin siyasa suka kafu da gindinsu a kudancin Nijeriya, amma a arewacin Nijeriya ko labarinsu babu.

Siyasar zamani tana nufin mulkin dimokuraɗiyya wanda wani salon mulki ne ko tsari da aka kafa a kan wasu manyan gimshiƙai da suka haɗa da adalci da daidaito tsakanin jama’a da ‘yanci da walwalar al’umma.Haka kuma da biyar kadin yadda ake kashe kuɗin al’umma, da bayyana komai filla-filla cikin sha’anin tafiyar da shugabancin jama’a, [Hassan;2013]. Jama’a masu rinjaye su ne babban makamin dimokuraɗiyya ko akasin haka. Bunza [2013] ya bayyana cewa akan laɓe ƙarƙashin ƙungiyar jama’a da sunan ita ce ƙungiyar jama’a masu rinjaye don a jawo ra’ayin mutane su aminta da jam’iyyar da ake son mutane su karɓa.

Masana da manazarta sun bayyana wasu abubuwa da dama game da dimokuraɗiyya. Abraham Lincoln [1809-1865], ya fassara ma’anar dimokuraɗiyya da cewa “Gwamnatin jama’a, da jama’a suka zaɓa, kuma take aiki domin jama’ar.”Wato duk gwamnatin da jama’a ta zaɓe ta, kuma take yi wa jama’a aiki, ita ce dimokuraɗiya. Kamar yadda Skinner [1965] ya bayyana dimokuraɗiyya da cewa, “wata hanya ce ta mulkin ƙasa, wadda kowa ke da hannu a cikinta”.Wato, dimokuraɗiyya tsarin tafiyar da mulki ne da jama’a suke zaɓar shugabanninsu domin su yi wa jama’a aiki. Wannan bayani ya yi daidai da tunanin Oyediran da wasu [2001], cewa dimokuraɗiyya nau’in mulki ne wanda ‘yan ƙasa za su zaɓi wakilansu da za su yi musu jagora ta hanyar bayyanar da yardarsu. Shi ma Joyce [2003], cewa ya yi, “dimokuraɗiyya, ita ce, yadda al’umma gaba ɗaya suke fita domin su zaɓa wa kansu wanda suke so ya wakilce su. Haka kuma suke da damar tsige shi daga wannan wakilcin, idan sun ga ba ya yin abin da ya dace, ko kuma idan ba su gamsuss da abubuwan da yake yi ba”.

Nasir [2011] shi ma yana ganin cewa, ita dimokuraɗiyya kalma ce da aka samo ta daga harshen Girka, wadda take nufin gwamnati ta kowa da kowa wacce aka gina ta, ta hanyar jefa ƙuri’a. Wato zaɓe ta hanyar jefa ƙuri’a ko ta hanyar kai- da-halinka [ƙato-bayan-ƙato]. Shi ma Adamu [2013], cewa ya yi, dimokuraɗiyya ararriyar kalma ce wadda aka aro daga harshen Girkanci. A harshen ana kiran ta “Dimokratus”. A harshen Ingilishi tana nufin mulkin al’umma ta hanyar amfani da fararen hula ba sojoji ba; ta hanyar gudanar da zaɓe. Haka shi ma Hassan [2013], yake cewa, dimokuraɗiyya bayar da dama ce ga ‘yan ƙasa su zaɓi shugabanninsu da kansu, domin su jagorance su a gwamnatance. Wato yana nufin tsarin ya saɓa wa tsarin sarautar gargajiya wadda talakawa ba su da hannu ga zaɓen wanda zai shugabance su.

Har wa yau, Abdullahi [2013] ya bayyana dimokuraɗiyya cewa, wani tsari ne na shugabanci ko jagorancin jama’a ta hanyar ba su ‘yancin zaɓen mutumin da ake zaton an amince da jagorancinsa bisa ga wasu muhimman dalilai keɓaɓɓu. Dalilan kuwa sun haɗa da, kasancewar mutum ya zama mai kirki, mai riƙon amana, mai kyakkyawan asali da ɗabi’u nagari. Haka kuma akan buƙaci ya zama mai kyakkyawar hulɗa da mutane, wanda ba shi da wani tsalmi na abin kunya ko wani laifi ko tarihin tsoro a rayuwarsa. Duk wannan yana bayani a kan tsarin mulki wanda ake cewa, “Siyasa’’. Donald T. Phillips (1992) et, Abrahman Lincoln, cewa; Siyasa shugabanci ne wanda jam’a ke zaɓen shugabansu da kansu.

Ataƙaice, abin da ake nufi da siyasa a tawa fahimta, ita ce, tsari ne wanda ake gudanar da shugabancin al’umma ta hanyar zaɓen wakilai su wakilci jama’a da nufin aiwatar da manufofin gina ƙasa da al’umma baki ɗaya.Wato, mulkin siyasa yana nufin mulkin da ake zaɓen farar hula su shugabanci jama’ar ƙasa baki ɗaya. Ko jihohi ko ƙananan hukumomi da sauransu. Malam Umar Kwaren Gamba yana cewa:

“Farar fulla in suna da ilmi da basira,

Da niyyar hairi ga ‘yan ƙasa shi niƙ ƙara,

Suna iya jan ‘yan’uwa cikin tasu dabara,

A san hanyoyin da za a kauce ga hasara,

A tanadi kuma arzikin ƙasa har ya yi abki.

 

(Umar Kwaren Gamba; muhimmancin maida mulki hannun farar hula).

 

Bisa la’akari da gudummawar da masana da manazarta da mawaƙa daban-daban suka bayar dangane da siyasa, ana iya cewa, siyasa ita ce, hanyar da ake zaɓen shugaba bisa ga ‘yanci da walwala cikin ƙayyadadden tsarin da doka ta aminta da shi.Irin wannan salon mulki shi ke kawo wa talaka gwamnati kusa da shi, har ya sami damar faɗin albarkacin bakinsa, ba kamar mulkin soja ba. Ana samun irin wannan salon mulki ta hanyar kafa jam’iyyun siyasa a ƙasa.

2.5 Tarihin Ginuwar Siyasa (Damokuraɗiyya) a Arewacin Nijeriya Musamman Ƙasar Hausa

Dudley (1968, p. 73-115) ya bayyana cewa a lokacin a Captain C. D. Morney ya zo arewacin Nijeriya ya ce ya zo ne domin ya binciki shirin da ‘yan arewacin Nijeriya suka yi a siyasance na karɓar mulkin kai, kamar yadda ‘yan kudancin Nijeriya suka buƙata daga Turawa yan mulkin malaka. A lokacin da yake gudanar da bincikensa ya gano cewa ‘yan arewa ba su yi shirin komi ba, saboda matsalar rashin jittuwar ra’ayoyin ƙungiyoyin da suka rayu a wancan lokaci.

Ƙungiyoyin siyasa sun fara zama da gindinsu a shekarar 1934, a kudancin Nijeriya, amma a arewacin Nijeriya ko labarinsu babu, Aminu (1987, p. ). Malam Sa’adu Zungur da Malam Aminu Kano da wasu da dama sun yunƙura domin kafa wasu ƙungiyoyi ko jamiyyun siyasa a arewa waɗanda ɗaya daga cikinsu reshe ne na siyasr kudu tare da goyon bayan su Azikwe, Coleman (1958, p: 353). Kafin a kafa reshen jam’iyyar NCNC a kudu, a arewa akwai wasu ƙungiyoyi waɗanda ‘yan arewa suka kafa.

Daga cikin ƙungiyoyin da suka tattaru suka samar da jamiyyun siyasa a arewa akwai ƙungiyar Inganta Rayuwar Mutanen Bauchi (BGIU 1934) da ƙungiyar tattaunawa ta mutanen Bauchi (BC1944) da ƙungiyar zumunta ta Sakkwato (SYC 1948), akwai kuma ƙungiyar Matasa ta Kano (KYA 1948) da ƙungiyar Abokai ta Kano (FAK 1947). Akwai ƙungiyar ƙunyiyar malamai ta Arewa (NTA 1947) da ƙungiyar Matasan Zariya (ZYA 1948). Haka kuma akwai ƙungiyoyi da dama na ƙabilun Larduna daban-daban da suka rayu kafin da bayan saamun yancin kai, amma kusan duk waɗanda suka rayu kafin shekarun 1950, su ne suka cure a matsayin babbar jam’iyyar nan ta mutanen arewa, wato, NPC. Daga bisani wasu suka ɓalle daga NPC suka kafa NEPU.

Su kuma manyan jam’iyyun nan NEPU da NPC sun kafu ne a sanadiyar haɗewar da ƙungiyoyin da larduna suka kafa a wuri ɗaya, domin a samar da jam’iyya daya mai kare ‘yanci da martabar arewa.

2.5.1 Jumhuriya Ta Farko

 Jamhuriya ta farko ta soma ne a dalilin kafuwar qungiyoyin siyasa masu ra’ayin neman ‘yanci waxanda suka qunshi qungiyoyi daban- daban. Aminu (1987], ya bayyana cewa,waxannan qungiyoyi na qabilun larduna daban-daban, su ne suka cure wuri xaya suka kafa jam’iyyar mutanen Arewa ,wato NPC, da kuma jam’iyyar NEPP,wadda daga bisani ta canja suna ta koma NEPA, sannan kuma ta koma NEPU.

 Birniwa [1987], ya bayyana cewa shekarar 1950 ita ce shekarar da ta kasance mabuxin qofar siyasa a Nijeriya. A wannan jamhuriya ta farko, akwai jam’iyyu da suka fafata tsakaninsu, waxanda suka haxa da N.P.C,wadda ke da rinjayen kujeri a majalisar qoli. Ita kuma jam’iyyar N.C.N.C., tana biye da kujeru, yayin da sauran jam’iyyun NEPU da A.G. suke da rinjayen kujeru a jahohinsu. Jam’iyyar N.P.C., ita ke da firayin minista da ministan harkokin qasashen waje,Alhaji sir Abubakar Tafawa Valewa, da firimiyan jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Har wa yau akwai malam Zanna Bukar Dipcharima a matsayin ministan ciniki da masana’antu duk a qarqashin jam’iyyar N.P.C., da kuma Alhaji Muhammadu Ribaxo a matsayin ministan tsaro.

 Michael Crowder (1962), ya ce, a vangaren jam’iyyar N.C.N.C.,akwai wakilai da suka haxa da firayiministan qasa,sir Abubakar Tafawa Valewa da Dr Nnamdi Azikiwe a matsayin Gwamnan Tarayya na farko a ranar 16, ga watan Nuwamba 1960, wanda ya qunshi sassa uku na qasa. Wato Arewa da Gabas da kuma Yamma,da Lagos a matsayin babban birnin Tarayya. Haka kuma a kowace jiha akwai Firimiya da Gwamna masu kula da harkokin mulki. Sauran muqaman gwamnati kuwa an rarraba su ga jam’iyyun biyu masu riqe da mulkin qasa.Jam’iyyar N.P.C. tana qarqashin kulawar firimiyan jihar Arewa,sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato,da jam’iyyar N.C.N.C.,wadda ke qarqashin kulawar Dr Micheal Okpara a jihar Yamma.Ita kuma jam’iyyar A.G. da jam’iyyar NEPU,suka kasance jam’iyyun adawa.Bayan da Kamaru ta valle daga Najeriya sai jam’iyyar N.C.N.C. ta canja sunanta daga “jam’iyyar qasa ta Najeriya da Kamaru” zuwa “jam’iyyar qasa ta mutanen Najeriya”,wato “National Council of Nigerian citizens.”An qara daukaka darajar Dr. Nnamdi Azikiwe daga babban Gwamnan qasa zuwa ga matsayin shugaban qasa [President].

 A wannan jamhuriya ta farko, an sami marubutawaqoqin siyasa da dama sun taka rawar gani wajen yin amfani da azanci musamman zuga da habaici don su soki jam’iyar adawa da kuma tallata tasu jam’iyyar a idon mutane. Misali a cikin waqrsa ta NEPU, mai suna “Baqi uku sharrin NPC, Aqilu Aliyu yana zuga mutane da cewa:

 “Haba jama’a ku qi zaventa

 Saboda mu taru mu kashe ta

 Ta faxi da bayan bayanta

 Mu yarda da NEPU mu zave ta

 Mu huta masifar NPC.

 Aqilu Aliyu: Waqar NEPU}.

Haka ita jam’iyar NPC ta samu karɓuwa ga mafi yawan sarakunan ƙasar Hausa da masu hannu da shuni. Mawaƙa irinsu malam Muhammadu Giɗaɗo ya yi wa ‘ya’yan jam’iyyar NEPU habaici inda yake sukar maƙiya Sarauna. Yana cewa:

 In ban da jahilcinku NEPU maƙaryata,

 Wa za ya raina Firimiya Sardauna.

 Muhammadu Giɗao: Waƙar npc;yabon Sardauna)

 

 Rikicin siyasar Najeriya ya haddasa wa wasu rasa gidajensu da barin garuruwansu na haihuwa da dukiyoyinsu. Wasu kuma sun shiga gidan kaso saboda banbancin siyasa. Wannan salon mulkin kama-karya da shugabanni suka yi, ya jawo hankalin qasashen duniya su tsoma bakinsu cikin rikicin siyasar Najeriya. Ministocin qasashe renon Ingila sun gudanar da babban taro a Lagos, babban birnin tarayya a ranakun 14-15 ga janairu 1966. Bayan kammala taron ne, a daren 15, ga janairu wasu ‘yan tsirarrun matasan sojoji suka yi yunqurin kifar da gwamnatin siyasa ta farko. Manjo Chukuma Nzeogwu Kaduna ya jagoranci juyin mulkin da ya yi sanadiyar rasa rayukan firimiyan jihar Arewa sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da firayin minista sir Abubakar Tafawa Valewa, da firimiyan jihar yamma Chief Samuel L. Akintola da sauran wasu manyan hafsoshin soja ‘yan asalin Arewa. Wannan juyin mulki na ranar 15, ga watan janairu 1966, ya kawo qarshen mulkin siyasa a jamhuriya ta farko.

 2.5.2 Mulkin Soja

 Bayan da soja suka kifar da gwamnatin siyasa ta jamhuriya ta farko, sai aka naxa kanar Yakubu Gowon ya ja ragamar mulkin Najeriya a 1966. Ya riqi qasa har tsawon shekara tara, inda ya yi fama da matsalolin da suka haxa da zanga-zanga daga wasu ‘yan Najeriya da ke da ra’ayin vallewa su kafa tasu qasa wanda ya haddasa yaqin basasa da ya yi sanadiyar rasa xinbin rayuka da dukiyoyi. Gwamnatin tarayya ta yi qoqarin shawo kan wannan bore cikin shekaru uku, wato daga 1967-1970.

Gwamnatin soja ta Yakubu da ta janar Murtala da Obasanjo ta taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin qasa.Lokacin mulkinsa ,Janar Obasanjo ya yi alkawarin mai da mulki ga hannun farar hula a shekarar 1979. Bisa ga haka sai ya duqufa wajen shirye-shiryen samar da kundin tsarin mulki da ya halatta wa ‘yan Najeriya kafa jam’iyyun siyasa da gudanar da zavuka na qasa.A sanadiyar wannan qoqari da Obasanjo ya yi sai aka gudanar da zaven wakilai daga ko’ina cikin qasa domin su zauna su tsara kundin tsarin mulki.An sanya wannan kundi tsarin mulki cikin doka a ranar 21,ga Satumba 1978 [Draft constitution 1976:299]. An fara aiki da shi a ranar 1, ga Oktoba,1979.

2.5.3 Jumhuriya Ta Biyu

 Bayan kammala zaven qasa da aka yi wanda ya xora Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari bisa mulki a matsayin shugaban qasa mai cikakken iko a qarqashin inuwar Jam’iyyar N.P.N., xaya daga cikin jam’iyyun siyasa biyar da suka fi fice a Nijeriya a ranar 1st Oktoba,1979. Chief Olusegun Obasanjo ya miqa ragamar mulki ga sabon shugaban qasa na farar hula a jamhuriya ta biyu. Jam’iyyun N.P.N.,da G.N.P.P.,da U.P.N.,da N.P.P.,da kuma P.R.P, su ne suka fafata a tsakaninsu (Shagari:2000:66). A qarshen zango na farko na jamhuriya ta biyu an yi wa wata jam’iyya rijista mai suna “Nigerian Advanced Party”, (NAP) wadda Tunji Braithwait ya shugabanta. Bayan miqa mulki ga farar hula da Obasanjo ya yi, sai soja suka koma bariki suka ci gaba da sa ido ga yadda ‘yan siyasa suke tafiyar da mulki.

Gwamnatin Shagari ta fuskanci matsalolin tavarvarewar tattalin arzikin qasa da ya haddasa tsuke bakin aljihunta.Wannan ya ba wa soja damar sake karve mulki daga hannun ‘yan siyasa a ranar 31, ga Augusta 1985 [The Democrat, 28 August 1985:1].

A wannan jamhuriya ta biyu mawaqan siyasa sun taka muhimmiyar rawa wajen yin amfani da zuga da habaici don tallata jam’iyyunsu daban-daban. Misali, Muhammadu Sulaiman Xunxaye mawaqin jam’iyyar N.P.N, ya yi amfani da zuga da habaici yana sukar jam’iyyar P.R.P. domin ya zuga jam’iyyarsa ta N.P.N. a cikin waqarsa mai suna “Yan santsi kun zama kaya”, yana cewa:

 “Ku guje wa ‘yan PRP,

 Jam’iyyar ta cika haufi

 Da yawan cewa su sun fi

 Kowa sun mai sai wofi

 Bayan kuma sun gigita.

 (Xunxaye: Waqar NPN).

 

2.5.4 Jumhuriya Ta Uku

Bayan karve mulki sai aka naxa Janar Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin shugaban qasa. Tun daga wannan lokaci soja suke jan ragamar mulki har zuwa lokacin da shi Babangida ya yi nufin miqa mulki a hannun farar hula, amma zai cire kakin soja ya tsaya takarar shugaban qasa a tutar jam’iyyar siyasa. Saboda haka sai ya kafa kwamitin sake tsara kundin mulki wanda zai halatta wa kowane xan qasa damar tsayawa takarar zave a shekarar 1988. A sakamakon rahoton da kwamitin sake shirya kundin tsarin mulki ya bayar, an buqaci ‘yan Nijeriya su kafa jam’iyyun siyasa.’Yan Nijeriya sun amsa kiran shugaban qasa ta hanyar qirqiro jam’iyyunsu daban-daban, amma daga qarshe shugaban qasa bai amince da su ba. Sai ya qirqiro nasa jam’iyyu guda biyu, wato N.R.C. da S.D.P. Gwamnatin Babangida ta shirya gudanar da zave daki- daki ta yadda za ta yi nasarar miqa mulki a hannun farar hula cikin lumana kamar yadda ya yi alqawari. Marubuta waqoqin siyasa irin su Garba Gashuwa, wanda ya tallata jam’iyyun N.R.C da S. D.P, ya yi wa ‘ya’yan jam’iyyun habaici yana cewa:

 

     Bana an hana yin daba da banga tuni da ma

 Su ma kuma yanzu kai kaxan ma su tsaya ma

Domin an sha su sun fa warke tuni da ma

Sai wawa sai mahaukaci shi ka tsaya ma,

 Domin manufarku xai ba za kuma a musa ba.

  (Garba Gashuwa: Waqar NRC da SDP).

 An gudanar da zaven qananan hukumomi a ranar 8, ga Disamba 1990. Shugabannin qananan hukumomi da aka zava sun yi aiki tare da zavavvun gwamnoni da ‘yan majalisun dokoki na jahohi a qarqashin gwamnatin soja ta Babangida har tsawon shekara uku [1990-1993].

 Matsalar tashin hankalin da ‘yan Nijeriya suka faxa ta sa ala tilas shugaba Babangida ya miqa mulki ga hannun Chief Ernest Shonekan a Augusta 1993. Bayan wasu ‘yan watanni da Shonekan yake riqe da mulki, sai Janar Sani Abacha ya karve mulki a ranar 17, ga Nuwamba 1993.

Shi ma janar Abacha ya yi alqawarin miqa mulki ga hannun farar hula kamar yadda takwaransa janar Ibrahim Babangida ya yi. Don haka shi ma sai ya fara shirye- shiryen gudanar da zave a qarqashin tutar jam’iyyun siyasa. Saboda haka sai janar Abacha ya bai wa ‘yan Nijeriya dama su qirqiro nasu jam’iyyun da kansu.’Yan siyasa sun qirqiro jam’iyyu da dama, amma gwamnati ta amince da yi wa jam’iyyu biyar rijista. Jam’iyyun da aka ba da sanarwar an yi wa rijista a ranar 30, ga watan Satumba 1996 su ne: Jam’iyyar N.C.P.N., da U.N.C.P., da D.P.N., da G.D.M., da kuma C.N.C. Mr Chief Sumnner Dagogo-Jack shi ne ya ba da wannan sanarwa a matsayinsa na shugaban hukumar zave ta qasa [NECON].

 Gurin Janar Sani Abacha shi ne, ya tuve kakin soja ya tsaya takarar kujerar shugaban qasa a qarqashin jam’iyyar U.N.C.P. An gudanar da zavuka daban-daban kafin a gudanar da na shugaban qasa. Manufar janar Sani Abacha ita ce ya cire kakin soja ya sa rigar farar hula, amma gurinsa bai cika ba. Abacha ya rasu a ranar 8 ga watan Yuni, 1998, kafin a gudanar da babban zave na shugaban qasa. Mawaqa kamar Garba Gwandu ya taka rawar gani wajen yi wa jam’iyyar U.N.C.P. waqa don tallata ta ga jama’a ta hanyar yi wa wasu ‘yan siyasa na wata jam’iyya habaici. Ga abin da yake cewa:

“ Patin duk da manyanshi ba su da hanquri,

Ba su kashe wuta sai su hazguxa tunzuri,

Kar ku shige shi malam Bala ka tsaya wuri,

Xau patin da kwana kaxanna da hamzari,

Qasar ga ta zo ta bunqasa, zo ka bi Garkuwa”.

 

Bayan rasuwar janar Abacha, sai aka naxa Abdulsalam Abubakar ya gaje shi. Bayan rantsar da shi, sai shi ma ya xauki alqawarin miqa mulki ga hannun farar hula. Abdulsalam ya himmantu wajen shirye-shiryen miqa mulki ga farar hula. An shirya kundin tsarin mulki a 1998, wanda ya fara aiki a 1999. Wannan ya kawo qarshen jamhuriya ta uku da ba ta yi nasara ba.

2.5.5 Jamhuriya Ta Huxu

Bayan kammala dukkan shirye-shiryen kudin tsarin mulki, sai Abdulsalam ya xage takumkumin siyasa.Ya buqaci ‘yan Nijeriya su qirqiro jam’iyyun da suke so. A wannan karo jam’iyyu uku kawai aka yi wa rijista daga cikin jam’iyyu da yawa da aka qirqiro. Jam’iyyun su ne, jam’iyyar A.D da A.P.P da kuma P.D.P., waxanda Hukumar zave mai zaman kanta ce ta yi wa waxannan jam’iyyu rijista. An gudanar da zave a matakai daban-daban a faxin tarayyar qasar nan domin tabbatar da mulkin dimokuraxiyya ya samu zama da gindinsa a Nijeriya. Jam’iyyar P.D.P. ce ta lashe zaven kujerar shugaban qasa, wadda Chief Olusegun Obasanjo ya zama zavavven shugaban qasa na farko a jamhuriya ta huxu. Sauran jam’iyyun, A.P.P da A.D., kowacensu ta sami wakilai a majalisun tarayya da na jahohi da kuma ƙananan hukumomi daban-daban. Bayan kammala zave, sai shugaban qasa na soja, wato Abdulsalam Abubakar ya miqa ragamar mulki ga zavavven shugaban qasa na farar hula da ‘yan majalisar tarayya a ranar Asabar 29, ga watan Mayu,1999. Rantsar da zavavven shugaban qasa Olusegun Obasanjo shi ya kawo qarshen mulkin soja da kuma jamhuriyya ta uku da ba ta yi nasara ba. Sannan ya zama farkon jumhuriya ta huɗu zango na farko. Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya share shekara takwas (8) yana mulki, wato daga 1999- 2007. Umar Musa ‘Yar aduwa ya yi shugaban ƙasa na tsawon shekara uku, Allah ya karɓi ransa.Sai goodluck Johnethan ya gaje shi ya cika wa’adi mulkin ‘Yar aduwa, kafin a sake zaɓen sa ya yi shekara huɗu a karagar mulki, 2010-2015. Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashe zaɓen 2015, wanda ya tabbatar masa zama shugaban ƙasar da alummar Nijeriya suke ɗoki a kai. Mawaƙan Buhari sun taka muhimmiyar rawa wajen tallata shi ga jamaa har ya sami karɓuwa aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2015.

Wannan aiki zai ci gaba daga inda manazarta suka tsaya ko kuma inda ba su ce komi kai tsaye ba.Wato ɓangaren nazarin zuga da habaici da marubuta waqoqin siyasar zamani suka yi amfani da su cikin waqoqinsu da suka rera ma Muhammadu Buhari, musamman a wannan jamhuriya ta huxu da muke ciki, domin su jawo hankalin jama’a su yarda da zaɓen Buhari a matsayin shugaban ƙasa a 2015.

2.6. Zuga

Hausawa sun aro wannan kalma ta zuga daga waɗannan zuga-zugi, suka riƙa amafni da ita a wurin zabrar da mutum ko ingiza shimutum ya aikata wani abin bajinta, ko wani aikin alheri da zai amfani al’umma.Masana sun yi cece-ku-ce wajen bayyana abin da ake nufi da zuga. Yahya (1997:131), ya ce, ana amfani da kalmomin yabo ga wanda ake yi wa zuga ta hanyar ambaton wasu kyawawan ɗabi’u ko halaye da iyaye da kakanninsa suka taɓa yi a lokacin rayuwarsu, sai a danganta su da shi wanda ake zugawa. Bargery (1934, p: 1144), ya bayyana zuga da cewa, “kambamawa ce, wadda ake tura wanda ake yi wa waƙa domin ya aikata wani aiki wanda idan yana cikin hankalinsa ba zai yi ba”. A cikin zuga ana ambaton wani abu mai kyau ko mai nagarta ko na bajinta da iyaye da kakannin wanda ake zugawa suka taɓa aikatawa a lokacin rayuwarsu.Wato akan danganta wanda ake yi wa zuga da bajintar da na gaba da shi suka taɓa aikatawa, don shi ma, a tura shi ko a zuga shi ya koyi kyawawan ɗabi’u ko bajinta da iyayensa da kakanninsa suka yi.

Bunza (2009, p: 147), ya ce, ‘’zuga da kirari ɗan juma ne da ɗan jumai wajen taka muhimmiyar rawa a fagen isar da saƙo’’. Wato dukkansu bori guda suke yi wa tsafi a matsayinsu na manyan jigogi a waƙoƙin Hausa. Ita dai zuga wani salo ne da mawaƙan Hausa ke amfani da shi domin su jawo hankalin masu sauraro su fahimci saƙon da waƙarsu take ɗauke da shi. Sannan kuma jigo ne a cikin waƙa da ake amfani da shi don a wayar wa masu sauraro kawunansu cikin nishaɗi su fahimci saƙon da ake isarwagare su. A tunaninsa, koyaushe kirari ya haɗu sosai, ba za a rasa zuga a cikinsa ba. Wato, zuga wani babban jigo ne da ke da alaƙa da kirari ta hanyar kambama wanda ake yi wa shi ya ji cewa ba tamkar shi a fagen bajinta. Ana amfani da shi wajen isar da muhimmin saƙo ga jamaa.

Malamin ya ƙara da cewa, “ita zuga wata dabara ce ko salon isar da saƙo da mawaƙa ke amfani da shi ta hanyar yin amfani da kalmomi masu nuna siffa ko kamanceceniya da wani abu mai rai ko maras rai; domin su ɗaukaka darajar mutum sama, su ingiza shi, ko kambama shi ya aikata wani abun bajinta ko akasin haka. Wato, a ce, ya yi wani abu, ko ya saba yin wani abu, ko zai iya yin gani ko karo da wani mawuyacin abu”. Mawaƙan Hausa sukan yi amfani da zuga, musamman na sarauta, da na maza, da kuma na siyasa domin su ingiza ko harzuƙa wanda suke yi wa waƙa ya aikata wani abu da hankali bai ɗauka. Wato ya aikata abin da ba zai iya aikatawa ba idan yana cikin hankalinsa. Irin wannan salo na amfani da zuga a matsayin dabarar isar da saƙo, shi ne mawaƙan siyasa suke amfani da shi a cikin waƙoƙinsu domin su isar da saƙo ga al’umma cikin gaggawa.

Oxford Dictionary (9th edition: ), ya bayyana cewa, zuga kambamawa ce ta hanyar amfani da kalmomin ƙarfafa zuciya ga wanda ake yi wa, ya ji ba kamarsa, musamman a fagen yaƙi ko wani aiki na nuna bajinta. A nan, zuga tana a matsayin wani jigo da mawaƙa ke isar da saƙon waƙarsu ga masu sauraro. Sannan ana amfani da kalmomin da suka dace idan ana son a zuga mutum ta fuskar yaƙi. Wato, zuga tana taka rawa a matsayinsa na salon sarrafa harshe da mawaƙa ke amfani da kalmomi masu ƙunshe da hikima da kuma ƙaidojin harshe. Misali kalmomi irin su mai bindigar yaƙi, ko takobi, ko garkuwa da mashi, kalmomi ne na siffanta wanda ake yi wa waƙa da wasu siffofi na tsoratar da abokan hamayyarsa. Haka kuma akwai kalmomina zuga, irin su maƙetaci, mugu ko mugunta, gwarzo ko gwarzaye, bahago, ko shago, ko ɗibgau, ko wandara da sauransu. Mawaƙa suna amfani da dabarar kawo irin waɗannan kalmomi na zuga cikin waƙoƙinsu domin su bayyana wa jamaa cewa, wanda suke zugawa buwayayye ne a fagen yaƙi ko wani abu mai kama da haka.

Mawaƙan Hausa, musamman na siyasa suna amfani da wasu zaɓaɓɓun kalmomi, su tsara su, sannan su sassarƙa su cikin ɗiya ko baitocin waƙoƙinsu domin su isar da saƙo zuwa ga jama’a. Zuga yana daga cikin dabarun jawo hankalin masu sauraren waƙoƙi da mawaƙan Hausa ke amfani da su,musamman mawaƙan siyasar zamani domin su wayar wa jama’arsu kai ga wani abu da ake so su sani ko su aikata.

A taƙaice zuga tana nufin zaburar da wani mutum, ko ingiza shi ya aikata wani abu da ba zai iya yin sa ba, idan yana cikin hankalinsa. Mawaƙan siyasa suna amfani da wannan dabara ko salo domin su kambama ɗan siyasa ya ji ƙarfin guiwar karawa ko gogayya da abokan adawarsa. Ko kuma ya yi wata kyautar ƙasaita ga mawaƙinsa, ko ga wasu mutane da aka jingina su gare shi. Wato, baya ga kasancewar zuga a matsayinsa na babban jigo a cikin waƙoƙin Hausa, haka kuma wata dabara ce ta jawo hankalin wanda ake harzuƙawa ya ji cewa, ba kamarsa a fagen yaƙi ko kyauta ko bajinta ko wani abu da mutane ke aikatawa. Saboda haka, zuga wani jigo ne a cikin waƙoƙin Hausa, musamman na siyasa da ke isar da saƙo ga masu sauraro. Har wa yau, zuga salon sarrafa harshe ne da mawaƙa ke amfani da shi domin su nuna ƙwarewarsu ga harshen da suke rera waƙa a cikinsa. Wato, harshen Hausa wanda suke sarrafa kalmomi cikin ƙaidojin nahawun Hausa da dokokin da waƙa ta tanada na zubi da tsari.

Mawaƙan siyasar zamani a jumhuriya ta huɗu; musamman waɗanda suka yi wa Muhammadu Buhari waƙa, sun taka rawar gani wajen amfani da zuga su isar da saƙon waƙoƙinsu cikin harshe mai armashi. Ta hanyar yin amfani da zuga da mawaƙan zamani suka yi cikin waƙoƙin siyasar da suka yi wa Muhammadu Buhari; ya ƙara fito da kwarjininsa da kyawawan ɗabi’unsa ga jama’a da su kansu mawaƙan siyasar da suka zuga shi.

Zuga wata magana ce, wadda mawaƙan Hausa na baka ko rubutacciya ke amfani da ita domin su ingiza ko su zabura mutum ya aikata wani abu wanda idan yana cikin hankalinsa ba zai iya aikatawa ba. A wata hira da aka yi da sarkin maƙeran Bagega, Malam Salisu Zakari Bagega, (ɗan shekara 57), ranar 23/09/2022, ya ce, zuga ya samo asali ne daga zuga-zugi da maƙeran gargajiya suke amfani da su wajen hura wuta; domin su gasa ƙarfe ya yi laushi kafin su sarrafa shi zuwa wani abin amfani; kamar kwashe ko galma ko laushe ko makafci ko wuƙa da sauransu. Zuga-zugi wasu fatun awaki ne da ake ɗinkawa a yi masu baki tare da kwarkwaro na ƙarfe, wanda ake liƙawa a bakin zuga-zugin domin ya ba da iska kai tsaye ga gawai da aka saka a ramin maƙera don a gasa ƙarfe. Wannana bayani ya fito daga Salisu Zakari Bagega, Sarkin Maƙera ɗan shekara 57, a wata hira da aka yi da shi ranar 23/09/2022.

Ana riƙe zuga-zugin da yatsun hannuwa biyu, ana ɗaga su sama su ja iska sannan a hura iskar ga ramin maƙera domin ta hura wuta.Wannan zuga, wato hura wuta tana gasa ƙarfe sai ya yi ja, sannan a ciro shi da wani almakashi da ake kira ‘awartaki’, sai a ɗora a uwar maƙera a riƙa dukar sa har sai ya zama abin amfani da ake buƙata.

Domin tantancewa da tsettsefe bayanai a kan matsayin zuga a waƙoƙin Hausa, musamman na siyasa an nazarci matsayin zuga kamar haka:

2.6.1.Nau’o’in Zuga

Masana da masu nazarin adabin Hausa, musamman a kan nazarin waƙar baka ko rubutatta sun yi ƙoƙarin binciko wasu hanyoyi da ake iya yin amfani da zuga domin a cimma nasarar isar da saƙon a ake nufin isarwa ga jamaa. Misali, Dumfawa, (2004, P.223-231), ya karkasa zuga zuwa gida uku kamar haka:

2.6.2. Zuga kumburau

Zuga kumburau shi ne wanda mawaƙan Hausa musamman na siyasa ke amfani da shi domin su kumbura wanda suke yi ma waƙa har ya ji yana cika yana cika yana batsewa tamkar dai ana hura shi da zuga-zugi. Duk wanda ake yi ma irin wannan zuga zai ji zuciyarsa na kumbura, ya ji ya kai wani matsayi na daraja ko ɗaukaka, har zuciyarsa ta riƙa yi masa wasu saƙe-saƙe, (Dunfawa, 2004). A wannan hali, masu sauraren waƙar sun san ba haka abin yake ba. Misali:

 Ga Buhari Uba babba,

 Jarumi Gwarzo babba,

 Janar Buhari mazan fama,

 Kin ji gaskiya dokin ƙarfe.

 (Yala: Waƙar APC.

 

A nan mawaƙin ya yi amfani da zuga kumburau domin ya zaburar da Buhari, inda ya danganta darajarsa da ta Babban uba. Ya kuma nuna cewa duk wanda ke da uba babba kai tsaye yake isa ya gan shi ba sai an yi masa iso ba.Haka kuma ya kamanta Buhari a jarumi gwarzo, wana baubu wani mutum da zai iya fuskantar sa sai ya shirya. Wannan zuga ne kumburau mawaƙin ya yi amfani da shi domin ya ƙara bayyana wa alumma irin martabar da Muhammadu Buhari yake da ita a idon mutane. Don haka mawaƙin ya zuga Buhari domin ya nuna ‘yan siyasa cewa darajarsa ta zarce sauran ‘yan siyasar Nijeriya.

2.6.3. Zuga kambamau ko Kariyau

Shi kuwa zuga kariyau wata irin zuga ce da mawaƙan fada, har da na siyasa ke amfani da ita don su kambama da kuma kare martabar wanda suke yi wa waƙa daga hawan ƙawarar abokan hamayya (Dunfawa, 2004). A wani lokaci kuma don a kare wanda ake yi wa waƙar daga waɗanda yake wa shugabanci a kan ka da su kuskura su yi wata jayayya da shi. A cikin irin wannan zuga mawaƙa kan riƙa bayar da tsoro game da shi ta hanyar nuna wa yan adawa cewa wanda suke yi wa waƙar gagarau ne wandara. Sukan nuna a cikin waƙar tasu cewa, duk wanda ya yi jayayya da gwarzonsu, to zai sha wahala, domin duk wanda ya ja da shi, to shi ne ƙasa.Wani lokaci mawaƙan kan riƙa ambaton wasu nasarori da ɗan siyasa ko shugaba ya taɓa samu a kan wasu abokan hamayyarsa. Misali:

Ga zakaran da Rabbana Sarki yan nufa,

Dole a ƙyale maigida koko a rankwafa,

Don haka gar ku ja da shi balle ku zurfafa,

Yau Allah yana a bayan mai gaskiya.

 (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

 

 

A wannan baiti da ke sama, mawaƙin yana tsorata mutane ko yan adawa game da Muhammadu Buhari, wanda yake zugawa. Wannan nau’i na zuga rawa biyu yake takawa. Na farko yana tunatar da wanda ake yi wa waƙa cewa yanzu fa ya kai wani matsayi da ba a iya jayayya da shi. Wannan zuga ce kambamau. Na biyu kuma yana shaida ma mutane yana kuma ba su tsoro game da wanda yake yi wa waƙar a kan ka da wani ya kuskura ya faɗa masa ko jayayya da shi domin ya wuce a buge shi ko a tsananta jayayya da shi domin Allah yana bayansa saboda gaskiyarsa, wannan kuwa kariya ce yake yi wa Buhari domin ka da ‘yan adawa su ga damar faɗa masa. Waɗannan abubuwa biyu da aka bayyana su ne suka bai wa wannan zugar suna zuga mai kariya, saboda akwai zuga tare da kariya a cikinta.

2.6.4. Zuga Ingizau

Zuga ingizau shi ne wanda mawaƙa ke amfani da shi domin su tunkuɗa ko su ingiza wanda suke yi wa waƙa ya aikata wani abu, wanda da ba don zugar ba, da ba zai aikata shi ba. Wannan abun yana iya zama wata babbar kyauta ce ko kuma wani abu daban, (Dunfawa, 2004) . Haka kuma ta wajen irin wannan zugar ana iya ingiza ɗan siyasa ko shugaba ya ƙi yin wani abu da kafin zugar ya yarda zai aikata shi. Wani lokaci ana danganta irin wannan zuga da wani abun tarihi, sai ta zama kamar an fama wa wanda aka yi wa ita wani rauni da ya yi baya ya kusa warkewa. Misali,

 Ba batu na zuga ba, mai son karo ya zo ga rago a kara,

 Ka ji giwa bukkar daji, kin wuce harbi koko tokara,

 Sannu maliya ba ki ƙafewa dukkan ruwa a cikin ya tattara,

 Jam’iyar talakawa APC mun amince ‘yan Nijriya.

  (Murtala Mamsa: Gaskiya ta zo,APC).

 

A cikin wannan baiti da ke sama, mawaƙin ya zuga jam’iyyar APC ce, cewa, ta ƙara shirin faɗa ka da ta ji tsoro domin ta riga ta mamaye dukkan sassan Nijeriy. Saboda haka ta fito kai tsaye ta mulki Nijeriya domin talkawa suna goya mata baya. Mawaƙin ya zuga jam’iyar APC da masu mara mata baya su jajirce wajen yaƙin neman mulkin ƙasa domin dukkan jamiyyun da ke nema babu wadda ta kai ta yawan jamaa. Duk da yake ba yaƙi ake yi ba a wannan zamani, jam’iyyar za ta ji tana ciccika (‘yan siyasa) kamar dai a tafi yaƙin domin kowane lokaci a shirye suke.

 An samo waɗannan rabe-raben zuga ne a cikin muƙalar da Dumfawa ya gabatar a cikin ALGAITA, (2004), a cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano

Malamin ya yi bayaninsa ne a kan zuga a cikin waƙoƙin sarakuna ko fada, inda ya kawo misalai domin ya kare kansa. Amma wannan aikin ya kalli kashe-kashen zuga a waƙoƙin siyasar Muhammadu Buhari domin fito da rawar da zuga take takawa wajen faɗakarwa da ilmantar da al’ulmma game da muhimmancin zaɓen shugaba nagari a mulkin siyasa.

Zuga da Kirari suna da alaƙa da juna ta ƙud-da-ƙud domin dukkansu suna ƙunshe da kalmomin yabo. Zarruƙ da Alhassan (1976, P. 1) sun bayyana cewa kirari wasu kalmomi ne da ake furtawa domin a koɗa wani mutum ko wani abu, a yi masa washi ko talla ko zuga. Kuma akan yi nuni ta hanyar kirari, a yi wa mutane hannunka-mai-sanda. Sun ƙara da cewa, kirari ba ya inganta sai da azancin magana domin zance ne ginanne wanda ake ɗebowa daga rumbum adabi da ake kuma ƙawata adabin da shi. Gusau (1988:38), ya ce, kirari shi ne faɗin wasu kalmomi ga kai ko ga wani wanda za su iya sa a jidaɗi ko cim ma wani girma a idon jama’a. Kamar yadda Ibrahim (1985:228) ya ce kirari wasu kalmomi ne na azanci waɗanda Hausawa suke amfani da su domin yabo ko zuga ko ba’a ko kuma yabon wata kyakkyawar al’ada ko kuma sukar wata mummuna.

Bisa ga waɗannan bambance-bambancen ra’ayoyi dangane da kirari, za a iya cewa, akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin zuga da kirari kamar yadda Bunza (2009, P.147) ya ce, zuga da kirari ɗan juma ne da ɗan jumai, wato dukkansu bori guda suke yi wa tsafi. Ya ƙara da cewa, idan zuga ya haɗu ba za a rasa jin amon kirari a cikinsa ba. Shi zuga wata dabara ce ta ɗaukaka darajar abu sama, a iza shi ko a tura shi, a ce ya yi wani abu, ko ya saba aikata wani abu, ko zai iya yin karo ko ganin wani mawuyacin abu. Shi kuma Yahya (1997, P. 67), ya bayyana zuga da cewa, magana ce mai ƙunshe da kalmomin ingiza mutum ya ji cewa yana iya fuskantar kowace irin barazana ta abokan hamayya ko gaba ko ‘yan adawa.

Mawaƙan siyasa da sauran mawaƙan Hausa suna amfani da waɗannan kalaman azanci a cikin waƙoƙinsu domin su kambama wanda suke yi wa waƙa ya aikata wani abu da ba zai iya aikata shi ba muddin yana cikin hankalinsa.Saboda haka amfani da waɗannan kalmomi na yabon wasu kyawawan ɗabi’u da iyaye da kakanni suka aikata a lokacin rayuwarsu, wata dabara ce da ake amfani da ita wajen jawo hankalin mutane su harzuƙa su aikata wani abin alheri ko akasin haka. Da wannan dalili ne ake ganin cewa zuga da kirari tawayen kalmomi ne da mawaƙan Hausa, musamman na siyasa suke amfani da su domin su kambama wanda suke yi wa waƙa ya ji a ransa cewa ya fi kowa a fagen siyasa. Misali, Murtala Mamsa yana cewa:

 Ba batu na zuga ba, mai son karo ya zo ga rago a kara,

 Ka ji giwa bukkar daji, kin wuce harbi koko tokara,

 Sannu maliya ba ki ƙafewa dukkan ruwa a cikinki ya tattara,

 Jam’iyyar talakawa APC nmu mu amince ‘yan Nijeriya.

 (Murtala Mamsa: Gaskiya ta zo, APC)

 

Wannan zuga yana ƙunshe da kalmomin kirari a cikinsa. ‘sannu maliya ba ki ƙafewa da ka ji giwa bukkar daji kin wuce harbi koko tokara. Dukansu kalmomi ne na kirari da mawaƙin ya yi amfani da su domin ya zuga wanda yake yi wa waƙa. Wannan ita ce dangantakar zuga da kirari ta fuskar kambama mutum ya aikata abin bajinta cikin farin ciki da annashuwa. Yayin da mahassadansa ko ‘yan adawa suke cikin damuwa da ɓacin rai.

2.7. Habaici

Bergery (1993) da Ɗangambo (1984) da Ɗangulbi (1996), sun ce, “habaici magana ce mai ɓoyayyar manufa”. Akan yi magana ce gajeruwa da nufin isar da wani saƙo ko wani abu ga wanda aka yi maganar dominsa.Wato akan yi habaici a cikin sigar karin magana don a gargaɗi wani mutum ko a yi masa hannunk- mai- sanda ko shaguɓe ga wani abu maras kyau da yake aikatawa domin ya ji, ya daina.

Calvin (1990), ya bayyana cewa, habaici magana ce a kaikaice zuwa ga wani ba tare da fitowa fili an ambaci sunansa ba. Ya ce, an fi amfani da siffar wanda ake yi wa habaici ko ɗabi’unsa; saboda a ɓoye sirinsa a idon mutane. Amma shi wanda ake yi da shi ko ya ji, ya san da shi ake.Saboda haka, sai ya yi ƙoƙarin gyara ɗabi’unsa da ake zarginsa da su.

Malumfashi da wasu, (2014, Pp. 24), sun bayyana cewa, habaici kan faru a lokacin da abu biyu ko fiye suka nuna ƙaunarsu a kan abu ɗaya. Wato bisa ga al’ada irin ta ɗan adam, baya son ya haɗa, ko ya yi tarayya da wani a kan abu ɗaya da wani. Wannan ne ya sa Bahaushe yake amfani da kalmar habaici don ya nuna rashin amincewarsa ga tarayya ga abin da yake so da wani mutum. Umar (1987) ya ce “an fi samun habaici a tsakanin mata masu kishin juna, wato, a tsakanin mata masu kishi da juna aka fi samun habaici. Kamar yadda Koko (1989) ta ce, habaici tsoro ne kuma yakan zo cikin sifar takala da kuma ramuwa a fakaice. Koyaushe habaici yana tafiya tare da arashi da ke nuna shakku ko razana ta mai magana zuwa ga wanda yake yi wa maganar a cikin sigar karin magana. Misali; “wanda ya gani shi ka faɗi”.

Swift ed (2023) Encyclopaedia Britannica, ya bayyana cewa habaici wata magana ce a fakaice ta shaguɓe da ake yi wa wani don a zolaye shi ko a yi masa hannunka- mai sanda. Ya bayyana cewa waɗanda ake yi wa habaici su ne ‘yan adawa ko abokan hamayyar siyasa ko sarautar gargajiya.

Habaici wata magana ce da ake furtawa zuwa ga wani mutumko wasu mutane a matsayin hannunka- mai –sanda ko shaguɓe ko gugar-zanadon wanda aka yi wa, ya ji ya gyara halayensa ba tare da an ambaci sunansa ba. Masana da manazarta sun yi bayanai daban-daban dangane da ma’anar habaici.

Habaici wani babban jigo ne a cikin waƙoƙin Hausa, musamman na siyasa, sannan kuma salon jawo hankalin mutane ne su fahimci saƙon da ake isarwa gare su cikin sauri da mawaƙan Hausa ke amfani da shi cikin waƙoƙinsu na Hausa. Mawaƙa na amfani da habaici cikin waƙoƙinsu domin su isar da wani muhimmin saƙo ga jamaa. Haka kuma yakan zamo salon sarrafa harshe da dabarar jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da ake son isarwa zuwa gare su. Wannan bincike ya yi ƙoƙarin ƙirƙiro wasu nauoin habaici dangane da bayanai da ya ci karo da su waɗanda masana suka kawo na ma’anonin habaici daban-aban. Misali; gargaɗau, daga gargadi wanda ake amfani da karin magana. Haka shaguɓau daga shaguɓe, da sakayau daga sakaya da sauransu. An ciro kalmomin lamiri da Dauda Bagari (1986) da Junju (1980) suka yi amfani da su a cikin littattafansu na Rayayyen Nahawu da Bayanin Hausa. Haka kuma binciken ya duba aikin Bashir Abdullahi (2012) wanda a cikinsa aka ciro kalmomin tsigalau. Duba da yadda aka yi amfani da kalmomi daban-daban wajen gina habaici ya sa wannan bincike ya yi ƙoƙarin karkasa nauoin habaici guda tara da kuma yadda ake sarrafa su a cikin waƙoƙin siyasa da aka yi wa Muhammadu Buhari.

2. 8.Nau’o’in Habaici

An karkasa habaic har zuwa nau’o’i guda tara, kamar haka: Habaici- Gargaɗau da Habaici-Shaguɓau da Habaici-Nunau da Habaici-Sakayau da Habaici- Miƙau da Habaici-Ƙasƙantau da Habaici-Gama-gari da Habaici-Keɓantau da kuma Habaici- Kaikaitau. Misali:-

2.8.1.Habaici-Gargaɗau

 Habaici-Gargɗau shi ne wanda ake amfani da karin maganganu da suka ƙushi nasiha ko waazi domin a gargaɗi mutum ya bar aikata wasu miyagun halaye ko ɗabi’u da yake yi; domin ya samu karɓuwa a cikin al’ummarsa. A cikin habaici gargaɗau an fi yin amfani da karin magana, domin Bahaushe ya ɗauki karin magana a matsayin wata hanya da yake gargaɗin ‘ya’yansa ko mutane wajen kange ko hana su aikata duk wani aiki da zai iya kawar musu da mutunci a idon mutane. Mawaƙan siyasa suna amfani da wannan nauin habaici domin su gargaɗi ɗan takara ko ‘yan siyasa ko shugabanni su gyara ɗabi’unsu da halayensu domin su samu karɓuwa ga jama’a. A ɓangaren sauran jama’a kuma ana gargaɗin masu saurare ko magoya bayan wasu ‘yan siyasa ko jam’iyyu su kauce wa zaɓen mutanen da ba su cancanta ba saboda rashin kyawawan ɗabi’u ko halaye nasu da suka bayyana a fili. Misali, Aminu Alan waƙa yana cewa:

A yau ‘kan mage ya waye’,

Talaka ka san matakanka.

(Aminu Ala:A.P.C. guguwar sauyi).

Wannan baiti na waƙar Aminu Ala, habaici ne mawaƙin ya yi wa wasu yan siyasa da ke amfani da kuɗi wajen saye ƙuriun talakawa domin su cimma gurinsu na lashe zaɓe, amma daga baya idan suka sami nasarar lashe zaɓe sai su yi watsi da talakawan. Saboda haka ne ya sa mawaƙin yake gargaɗin talakawa tare da nuna wa ‘yan siyasa cewa, yanzu kan mage ya waye, don haka ba za su sake yaudarar su da kuɗi ba domin su jefa musu ƙuriu ba. Saboda haka a ba su yan kuɗi ƙalilan don su sayar da yancinsu na zaɓen mutumen da bai dace ba ya ƙaura. Wani misalin habaici gargaɗau shi ne, inda Yusuf Fasaha yake cewa:

Mai son tsira ya taki gaskiya,

In ka ƙi kai za ka sha wuya.

(Yusuf Fasaha:mu bi A.P.C.al’ummar ƙasa).

 

Shi ma wannan ɗan waƙa yana ɗauke da karin magana wadda ke nuna wa al’umma cewa ana gargaɗin ‘yan siyasa da su kasance masu gaskiya domin ita ce ke sa mutum ya samu tsira da kariyar mutuncinsa a nan duniya da kuma gobe ƙiyama. Sai mawaƙin ya yi habaici ga duk wanda ya ƙi gaskiya cewa, shi zai sha wuya domin kuwa tun a nan duniya zai tozarta, kuma gobe lahira ya sha azaba. Wannan habaici ne gargaɗau zuwa ga ‘yan siyasa don su kasance masu gaskiya a cikin tafiyarsu ta siyasa, wanda yin haka shi zai kuɓutar da su daga tozarta a nan duniya da lahira. Ya ce duk wanda ya ƙi gaskiya shi zai sha wuya domin mutane ba za su aminta da takararsa ba. Wajibi ne ga kowane mutum ya kasance mai sassauci da tausayi ga dabbobi da tsirrai, balle ma ga ɗan Adam domin ya tabbatar da gaskiyarsa mutum nagari mai riƙon amana ga duk muamular da ke tsakaninsa da abokan muamularsa (Abdulahi 1987:11-12).

2.8.2. Habaici -shaguɓau

Habaici shaguɓau yana nufin ɓaci da ake yi wa wni a fakaice ta fuskar tsokana. Wato, ana amfani da kalmomin lamiran dangantaka kamar, wanda, wadda, waɗanda,(Bagari:1986:114) domin a gina habaici shaguɓau. Mawaƙan siyasa suna amfani da waɗannan lamiran dangantaka su gina habaici domin su yi wa wasu mutane ko ‘yan siyasa da ke da alaƙa ko kusanci da siyasa ko jamiyyar da ake yi wa waƙa. Akan fara kawo kalmar lamirin dangantaka kafin a faɗi maganar da ake son a faɗa ga wanda ake yi wa habaici. A tsarin nahawun Hausa, ana amfani da kalmar ‘wanda ko wadda domin a danganta mai aiki da irin aikin da ya yi. Misali, Musa, wanda ya shigo yanzu ya fita a guje. A tsarin waƙa duk inda wannan kalma ta wanda ko wadda ta fito za ka taras ana yin habaici ne ga wani ko wata domin a yi masa ko mata shaguɓe ga aikin da tyake ko take aikatawa maras kyau tare da tunatar da shi ko ita su gyara. Misali, Dauda Adamu Kahutu Rarara yana cewa:

Wanda duk ke haushinka

Bai halin ‘yan sunnah ba.

(Rarara: Baba tsoho ya sauka A.P.C.).

Mafi yawan habaice-habaicen da mawaƙan Hausa ke yi, musamman na siyasa sukan yi ƙoƙari su yi wa wanda suke yi wa habaici shaguɓe domin su kaucewa zargin masu saurare cewa sun ci wa mutumen da suke yi wa habaici fuska.Saboda a fito fili a bayyana sunan wanda ya aikata wani abu da bai dace ba. Hakan yana iya kawo rashin zaman lafiya da tayar da fitina tsakanin magoya bayan ɗan siyasar da aka yi wa habaici da wasu ‘yan adawa ko magoya bayan wata jam’iyya da ba tasu ba.Wani misali na habaici shaguɓau shi ne inda Ibrahim Yala yake cewa:

Wanda ya ja da kai Buhari zai sha wuya,

Domin ka fi wane mai halin ‘yan giya,

Mai fuska kamar ana murjin taliya,

Kai hango shi ba ya ƙaunar Nijeriya.

(Ibrahim Yala: Waƙar A.P.P. 2003)

A wannan misali da mawaƙin ya kawo dangane da ɗabi’un wani ɗan takara ya yi amfani da habaici-shaguɓau ne a layi na farko, inda ya kawo lamirin ‘wanda’, domin ya yi wa wannan ɗan takara shaguɓe. Haka kuma a layi na biyu mawaƙin ya yi amfani da habaici miƙau, inda ya yi amafani da lamirin ka domin ya ɓoye sunan mutumin da yake magana a kansa; kuma ya sifanta wanda yake yi wa habaicin da habaici-ƙasƙantau ta hanyar amfani da kalmar ƙasƙanci ta ‘yan giya’. A layi na uku, mawaƙin ya kawo habaici keɓantau don ya bayyana wata sifa ta wanda yake yi wa habaici a idon mutane. Faɗar kalmar ‘mai’ a wannan layi ta nuna cewa a keɓance akwai wanda ake yi wa habaicin wanda da zarar mutane sun ga ko ji haka za su iya tunanin cewa ga wanda ake yi wa habaicin kai tsaye. A ƙarshe ya jawo hankalin mutane da su kalli wanda yake yi wa habaicin wanda ya ce yana da fuskar yan giya, wanda mutane za su yi saurin gane da wanda yake yi w`a habaici. Haka kuma Murtala Mamsa Jos yana cew:

 Kuma duk haɗamar mai haɗama,

 Wallah bai iya ɗaukar duniya,

 Mai yawan bacci in ya sha hura ku duba

 Kar ku yi tambaya,

 Wadda ya yi biyayya haƙƙin uwa, uba ya zauna lafiya

 Akasin haka illa ce ‘yan ƙasa ku duba yan Nijeriya.

 (Murtala Mamsa: sabuwa ta zo)

2.8.3. Habaici –Nunau

Habaici nunau yana nufin ɓaci da za a yi wa wani a fakaice ta hanyar ishara ga wani abu ko wasu abubuwa da yake aikatawa. Shi wannan nau’in habaici ana amfani da lamiran nuni ne domin a bayyana zahirin abin da yake faruwa ga wanda ake yi wa habaicin da lokacin da ake yin habaicin ko wurin da ake yin habaicin. Wato, ana amfani da kalmomin lamirin nuni na kusanta ne domin a gina habaici nunau. Kalmomin da ake amfani da su sun haɗa da: Wannan, wancan, wanga, wagga, waɗannan da waɗancan. Misali, Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana cewa:

Wanga fati kun yi batun banza,

Don kun ce kun ga ɗiyan ƙarya.

(Kamilu :Waƙar APC).

 

A nan mawaƙin yana nuna wa jamaa a zahiri cewa, abu ne mai wuya a ce bishiyar ƙarya ta yi yaya. Gaskiyar karin maganar Hausawa da suke cewa, ƙarya fure take yi, ba ta yaya. Amma sai ga wasu yayan wata jamiyya sun ce, sun ga ɗiyan ƙarya.To, yaya gaskiyar waccan karin magana da ke cewa ƙarya fure take yi ,ba ta ƙarya? Wannan habaici da Kamilu ya jefi yan jamiyyar PDP da shi ya nuna wa masu saurare cewa har abada itaciyar ƙarya ba za ta taɓa yin ‘ya’ya ba. Saboda haka mawaƙin ya yi amfani da wannan habaici domin ya tozarta yayan jamiyyar PDP, dangane da furicin da suke yi na cewa jamiyyarsu kaɗai ce ta fi cancanta ta ci gaba da mulkin ƙasa. Don haka wannan magana da suka faɗa, maganar banza ce, domin sabuwar jam’iyyar APC ita ce wadda ta fi sauran jam’iyyu cancanta ta mulki Nijeriya.

Ibrahim Yala hayin banki ya yi wa azzaluman shugabanni habaici waɗanda suka yi ɓarna ta hanyar sace dukiyar al’ummar ƙasa domin ya nuna wa Buhari cewa, idan ya hau mulki dole ne ya hukunta azzaluman yan siyasa da suka sace dukiyar alumma bisa ga hainci da zalunci. Misali yana cewa:

Wancan lokacin farar hula sun gudu,

Domin sun yi ɓarna dole su zan gudu,

Yanzu idan ka hau dole wancan na gudu,

Zai tsere ya bar ƙasar don bai gaskiya.

(Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

 

Mawaƙin yana jawo hankalin Muhammadu Buhari ne tare da faɗakar da shi cewa, a wancan lokacin baya da farar hula suka yi mulki an sami azzaluman shugabanni sun yi facaka da dukiyar ƙasa ba bisa ƙaida ba; saboda haka yana kira ga Buhari ya sa ido ga irin mutanen da zai yi tafiya tare da su a cikin gwamnatinsa; domin ka da ya maimaita abin da wasu shugabanni da suka gabata suka yi na tafiya tare da azzaluman mutane a gwamnatinsu. Wato ya ɗauki mutane masu gaskiya da riƙon amana waɗanda za su taimaka masa ya cimma gurinsa na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da hana cin hanci da rashawa da satar dukiyar al’umma da samar da zaman lafiya da tsaro a cikin ƙasa.Ya yi wannan habaici ne ga gwamnatocin farar hula da suka gabata suka yi amfani da ƙarfin mulkinsu suka saci dukiyar ƙasa, suka shaƙata da ita, alhali sauran talakawan ƙasa suna cikin mawuyacin halin rashin abinci da rashin tsaro da sauransu.

Har wa yau Ibrahim Yala ya ƙara kawo wani misali na habaici-nunau yana cewa:

 Allah wadaranku masu halin salmaniya,

 Wannan ɗan baƙin da ƙira ta yan giya,

 Tun da ya hawo yake halin danniya,

 Mugun in ka gan shi ka san bai gaskiya,

 (Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya)

2.8.4.Habaici -Sakayau

Habaici sakayau yana nufin habaicin da ake sakaya ko ɓoye sunan wanda ake y wa habaicin. A wannan habaici-sakayau ana amfani da kalmomin sakaya ko ɓoye sunan wanda ake yi wa habaici, a bar mutane su yanke ma kansu hukunci wajen ƙoƙarin gano wanda ake yi wa habaicin da kansu. Dukkan habaici a ake yi ana ɓoye suna ne domin a isr da saƙo a fakaice, sai wanda ya san dalilin da ya sa aka yi habaici kaɗai zai fahimci wanda ake yi wa. Ana amfani da kalmomi kamar haka: Wani, wata, wasu, ko waɗansu domin a gina habaici zuwa ga ‘yan siyasa ko jam’iyyar siyasa ko ɗan adawa, wanda ba a son a ambaci sunansa ƙarara. Siyasa abu ce mai tafiya da raayi da kuma zamani, saboda haka kowane ɗan siyasa yana ƙoƙari ya ga cewa tafiyarsa ta yi daidai da zamanin da ake ciki ta hanyar yin abubuwan da zamani da mutanen zamani ke buƙata. Habaici kan iya sa masoyan ɗan takara ko ɗan siyasa su ƙaurace wa zaɓen wanda ɗabi’unsa da halayensa suka saɓa wa aƙida da manufar jamiyyarsu ko alummarsu. Sannan sukan dubi matsayin shugaba ko ɗan siyasa da ya kasa aiwatar da mulki daidai da tafiyar zamani saboda rashin ilimi ko ƙwarewa ga hulɗa da jama’a su jefe shi da habaici da ya yi daidai da abin da yake aikatawa a bayyane. Misali, Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana cewa:

Wani ya hau mulki ba ilimi,

Ya ruɗe an mashi Turanci.

(Kamilu: Runhu an furen banza).

Rashin ilimi matsalace mai girma ga wanda yake neman matsayi na jagorancin jama’a.Domin duk mutumin da ba shi da ilimi ba zai san abin da mutane ke so ba, balle ya yi masu abin da ya dace. Ilimi shi ne tushen samar da kyakkyawar hulɗa tsakanin shugaba da waɗanda yake shugabanta, ko waɗanda suka zo domin su yi hulɗa da shi ko da ƙasarsa da yake shugabanta. A baitin da ke sama mawaƙin ya bayyana irin illar da rashin ilimi take da shi ga shugaba domin yakan kasa gudanar da kyakkyawar hulɗa tsakaninsa da waɗanda yake shugabanta, ko wata hulɗa ta siyasa, ko ta cinikayya ko makamantan haka da su. Yin magana da wani harshe na daban da ya banbanta da harshen ƙasa, dole sai an koye shi, sannan a iya magana da masu jin wannan harshe.Wannan dalili ne, ya sa mawaƙin ya yi wa wani shugaba habaici domin ya yi ƙoƙari ya koyi harshen Turanci don ya taimaka masa wajen gudanar da hulɗa tsakaninsa da ƙasashen Turawa da kuma waɗan da ke jin Turanci. Rashin jin harshen Turanci babbar illa ce ga shugaba domin ba zai iya jawo hankalin mutane su fahimci abin da gwamnatinsa ke so ba. Saboda haka, wannan illar zaɓen mutumen da ba shi da ilimi a kowane irin muƙamin gwamnati, ta jawo hankalin mawaƙan siyasa su riƙa amfani da habaici wajen ƙasƙanta shugabanni ko yan siyasa a idon jamaa. Mulkin siyasa da yake buƙatar mutum mai ilimi da ƙwarewa a harshen Turanci da shaanin mulki. Misali, Ibrahim Yala yana cewa:

Duk wani wanda ba ya jin tsoran Rabbana,

To mun daina girmama shi ya cuta mana,

Mai rawani da jiniya Allah isar mana,

Za mu buga da ku bana faɗin Nijeriya.

(Ibrahim Yala: Waƙar APP/ANPP 2003).

 

Shi ma da yake jefa habaici ga wata jam’iyya Murtala Mamsa yana cewa;

Wani fati ya mutu mun gano,

An je zaɓen duka gwamnoni.

(Murtala Momsa:Waƙar A.P.C.).

A ɗan waƙa na farko mawaƙin ya yi amfani da habaici shaguɓau don ya muzanta ‘ya’yan jam’iyyar adawa bisa ƙaryar da suka yi wa alumma na taimaka masu ga samun abubuwan more rayuwa da ayyukan cigaban ƙasa, amma suka kasa.Ya nuna cewa saboda ƙarya da suka yi wa jamaa shi ya sa fatin ya mutu, sannan ya ɓace su da cewa sun yi ƙarya da suka ce sun ga ɗiyan ƙarya. Kowa yasan Hausawa na cewa ƙarya fure take yi ba ta yaya, saboda haka,wannan habaici ya yi wa yan jamiyya mai mulki shaguɓe domin su sauya salon tafiyarsu ga al’amarin siyasa wal’alla ko za su samu fatinsu ko jam’iyyarsu ta dawo da darajarta.

Shi ma da yake ba da misali na habaici-sakayu, Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana cewa:

An yi gwaba don mu sha zaƙi,

Wata ga ta da ɗan karen tsami

(Kamilu:Karen bana maganin zomo A.P.C.)

Wannan ɗan waƙa yana yi wa mulkin soja habaici ne domin ya bayyana wa mutane muhimmancin mulkin farar hula wajen bai wa talakawa ‘yanci da walwala da kuma samar masu da abubuwan more rayuwa. Sabda haka mawaƙin ya yi wa mulkin soja haaici cewa, mulki ana yin sa domin amfanin jama’a, to, amma sai ga shi mulkin soja ba ya bai wa talakawa damar walwal balle su faɗi albarkacin bakinsu idan sun ga ba a yi daidai ba.Wannan dalili ne ya sa mawaƙin ya yi wa mulkin soja habaici domin ya soki wannan salon mulki irin na kama karya. To a nan mawakin ya yi wa jam’iyyar APC ta Muhammadu Buhari waƙa domin ya tallata ta ga jamaa su goya mata baya da kuma shi kanhi ɗan takararta.

2.8.5. Habaici -Miƙau

Habaici-miƙau yana nufin habaicin da ake jifar wani ko wasu ta hanyar amfani da lamirin suna miƙau.Wannan nau’in habaici yana ɗauke da kalmomin lamirin miƙau wanda galibi yana aikin miƙau ne ga abokin magana ka/kai, ke’ ‘ku’ ‘su’ ‘mu’(Bagari, 1986: p:113), waɗanda ke nuna maganar da ake yi, shi ko su ake faɗa wa, ta fi shiga jikinsa bisa ga ya zam labari ake ba shi ta hanyar amfani da lamirin ga’ibi, wato wanda ba ya nan. Misali, ’ya’. Rarara yana cewa:

Ku kuka hau hanyar bori,

Ya kyautu ku nemo mai gurmi.

(Rarara: Maraba da tsoho oyoyo).

Mawaƙin ya yi wannan habaici ne don ya soki yan siyasar da ke da aƙidar biyar bokaye da matsafa ko matsibbata domin neman biyan bukatarsu ta siyasa.Wannana ɗan waƙar ya bayyana wa masu saurare irin miyagun ɗabi’u da ‘yan siyasa marasa dogaro ga Allah suke yi wajen biyar gidajen bokaye suna neman sihiri don su ci zaɓe. Duk masu irin wannan ɗabi’a ta amfani da bokaye wajen neman biyan buƙata, su ne suka mayar da mulki, ‘a mutu ko a yi rai’. Haka kuma da zarar sun kai ga mulkin, sai rashin tausayi da jinƙai ya fice daga zukatansu. Hakan kan sa, su riƙa yin abin da suke so da dukiyar alumma a satar kuɗi suna arzita kansu. Hakan kan kawo su wawashe dukiyar ƙasa domin su saka talakawa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi, da fatara da yunwa da rashin aikin yi ga matasa. Ibrahim Yala ya dubi haka, sai ya soke su da habaici yana cewa:

Kun ga halinsu ya sa mu mun koma bara,

Don haka nik kiram mutane kui hattara,

Kan zancen da nai walla ba na ƙirƙira,

Sai mu zage mu zaɓi mai kishin gaskiya.

(Ibrahim Yala: A.P.P 2003).

Kamar yadda mawaƙin ya bayyana a ɗa na farko,ya yi amfani da habaici miƙau ne domin ya faɗakar da al’umma cewa waɗannan mutane da yake maganar da su ,su ne suka sace dukiyar ƙasa, suka jefa mutanen Nijeriya cikin halin talauci da yunwa. Yanayin da shugabannin jamiyyar P.D.P suka jefa yan Nijeriya ya kai su ga faɗawa barace-barace a titunan ƙasar nan, da kuma yawon raraka da maula a gidajen yan siyasa da masu hannu-da-shuni, da kuma yawon tallace-tallace barkatai da yan mata da sauransu ke yi a Titunan ƙasar nan don neman abin saka wa bakin salati..Mawaƙin ya ƙara ba da wani misali dangane da halayen shugabannin da suka gabata na jamiyyar P.D.P a kan wawashe dukiyar ƙasa da suka yi, wanda ya jefa yan Nijeriya cikin mawuyacin halin da suke ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin aikin yi da tsaro a ƙasa baki ɗaya. Ibrahim Yala yana cewa:

Ku da kuke ta sukar Buhari uban ƙasa,

Ku ne kun ka kwashe Fetur da kuɗin ƙasa,

Don tsabar rashin mutuncinku cikin ƙasa,

Har ma dukiyar marayu kun murɗiya.

(Ibrahim Yala; Waƙar A.P.P. 2003).

 

Wato mawaƙin ya nuna wa jamar ƙasa cewa waɗannan ‘ya’yan jam’iyya mai mulki,wato, jam’iyyar P.D.P su ne ummul haba’isin shiga duk wani mawuyacin halin da ‘yan Nijeriya suke ciki. Saboda haka ne yake sukar tafiyar waccan jam’iyya tare da kiran mutane su dawo rakiyar ta,su rngumi jam’iyyar A.P.P, wadda Muhammadu Buhari ke takarar kujerar shugabancin Nijeriya a ƙarƙashin inuwarta.Har wa yau, malamin ya ci gaba da yi wa shugabannin P.D.P habaici yana cewa:

Mun gano ku masu mulkin Nijeriya,

Kun maishe mu jahilai ba mu da tarbiya,

Ku kun tura ‘ya’yanku Turai gaba ɗaya,

Ku kun ba mu gariyo mui muku kariya,

(Ibrahim Yala: A.P.P 2003).

A wannan fagen mawaƙin yana yi wa shugabannin Jamiyyar P.D.P. habaici dangane da halayyarsu ta tura yayansu ƙasashen waje su yo ingantaccen karatu, yayin da suke sayen miyaguun makamai suna bai wa yayan talakawa, suna ba su kariya. Wato, sun mayar da yayan talakawa yan bangar siyasa, wanda suke kare su daga duk wata fitina da ka iya tasowa ta same su ko ta halaka su.

Shi ma da yake yi wa ‘ya’yan jam’iyyar P.D.P mai mulkin ƙasa habaici Dauda Rarara yana cewa :

 

Ku gaya wa ɓarayin can su gudu,

Mun san kanwa ku ke da gami.

(Rarara: sai baba Buhari A.PC)

Da yake faɗar albarkacin bakinsa wajen yi wa shugabannin jam’iyya mai mulki habaici dagangane da zalunci da wawushe dukiyar al’umma da ha’intar dukiyar talakawa, Ibrahim Yalayana cewa:

Su suka sanya rasshawa yau tay yo yawa,

Su suka tsaida arzikin ‘yan Nijeriya,

Su ke kulle kamfani don har sun saya,

Sun raba tallaka da aiki ‘ya’yan tsiya.

(Ibrahim Yala; A.P.P. 2003)

Mawaƙin ya yi wa shugabannin da ke kan gadon mulki habaici domin ya nakasa kwarjinin da suke da shi a idon yan Nijeriya. Wannan dalili ne ya sa ya yi amfani da habaici miƙau inda ya ce, su suka sanya rasshawa yau tay yo yawa, domin ya faɗakar da jama’a game da taɓarɓarewar tattalin arziki yake ciki a sanadiyar cin hanci da rashawa da shugabannin jam’iyya mai mulki suka yi. Saboda haka, sai ya soke su da wannan ɗabi’a ta cin hanci da rashawa domin mutane su guje wa sake zaɓen su a zaɓe na gaba.

2.8.6. Habaici-Ƙasƙantau

Habaici- ƙasƙantau nauin habaici ne da ake yi wa wani domin a ƙasƙanta shi a idon jamaa ta hanyar faɗar wata sifarsa ko aasalinsa da sauransu. Shi irin wannan habaici ana amfani da kalmomin tsigalau ne waɗanda suka haɗa da, ‘ɗan’ ‘yar’ da ‘yan da sauransu. Bashir, (2012, P.16) , Tsigalau wata kalma ce da ake amfani da ita a matsayin ɗafa-goshi da za a iya haɗa ta da wata kalma domin a gina wata kalma da za ta ba da suna, ko asali ko sifa. Misali, ɗan Nijeriya, ɗan sokoto, ɗan neja, ɗan Minna da sauransu. Haka kuma akwai sifa, misali ɗan baƙi, yar baƙa. ko ɗabi’a ta wani ko wasu mutane. Misali, ɗan caca, ɗan damfara, ‘yar damfara da sauransu. Ana amfani da waɗannan kalmomi na tsigalau domin a muzanta ‘yan adawa ko wasu shugabanni da suka kasa aiwatar da ayyukan raya ƙasa a lokacin da suke kan karagar mulki. Haka kuma ana samar da kalmar aikatau ko suna-aikatu duk a cikin kalmar tsigalau,. Mawaƙan Hausa na zamani, musamman na siyasa da ake magana a kansu suna amfani da kalmomin tsigalau ‘ɗan’, ‘yar’, da ‘yan da sauransu, domin su gina habaici zuwa ga masu wata ɗabi’a ko sifa ko asali domin a yi masa ko musu gyara ko gargaɗi su daina aikata wani abu mai muni da ya saɓa wa ra’ayin al’umma ko shari’a. Haka kuma, a ƙasƙanta asali ko ɗabi’ar wanda ake yi wa habaici a idon mutane, wnda yin haka ya zama al’adar mawaƙan siyasa na ƙasƙanta yan siyasa da ba su raayi da su.

Akan yi amfani da waɗannan kalmomin tsigalau don a yi wa namiji ko mace ko jam’in mutane habaici dangane da wata ɗabi’a, ko asali, ko halin rashin kunya da suke aikatawa da ya saɓa wa buƙata ko tunanen alumma. Wannan dalili ne ya sanya aka kira wannan nauin habaici da habaici ƙasƙantau; domin ana amfani da waɗannan kalmomi don a bayyana mummunan halin wani mutum ko asali, ko sifa ta ƙasƙanci domin mutane su fahimci saƙon da ake son su sani game da wanda ake yi wa habaici. Misali, ɗan iska, ɗan giya ɗan caca, da ‘yar iska, ‘yar tasha, ‘ya giya da sauransu. Akwai ɗan baƙi yar baƙa, ɗan damfara,‘yan damfara da sauransu (Junju, 1980, P. 15). Mawaƙa sukan haɗa waɗannan kalmomin tsigalau da suna, domin mutane ba za su iya gane wanda ake yi wa habaicin ba, sai fa idan suna da tarihin taƙadadamar da ke tsakanin mai yin habaicin da wanda ake yi wa. Ko kuma sun san sifar ko asalin wanda ake yi wa habaicin. Mawaƙan siyasa sukan riƙa amfani da waɗannan kalmomin tsigalau a cikin waƙoƙinsu domin su gina habaici ga abokan adawa ko jamiyyun adawa don su muzanta wani ko wata ko wasu gungun mutane da suka zama ƙarfen-ƙafa a harkokin siyasarsu. Misali, Murtala Mamsa yana cewa:

Riƙon amana ba ɗan kishiya,

Wanda yai haka sai ya kassara.

(Murtala: Sabuwa ta zo, A.P.C).

 

A ɗan waƙa na farko mawaƙin ya yi amfani da kalmar ɗan kishiya’ don ya ƙasƙanta da ko ya muzanta wanda yake yi wa habaici a idon jamaa ko masu sauraron waƙarsa. Saboda a aladar zamantakewar Hausawa suna ƙarfafa ƙiyayya ga mutumen da ba uwarsu ɗaya ba, amma uba ɗaya, wato ɗan kishiya; wanda wasu ke kira ‘ɗan uba’. A sanadiyar kasancewar ɗan kishiya ba ya biyar wanda ba su fito ciki guda da shi ba da alheri, sai Hausawa su danganta wannan matsala da cewa ba a bai wa ɗan kishiya amana. Duba da haka ne ya sa mawaƙin ya yi habaici ga wani ɗan jam’iyyar da ba A.P.C ba, cewa, duk wanda ya ba shi (ɗan kishiya) amana, to sai ya kassara, wato sai ya kariya. Sannan ya kawo habaici shaguɓau domin ya bayyana wa masu saurare cewa duk wanda ya bai wa ɗan kishiya amana to, sai ya kassara.

A siyasance mutane sukan yi ƙoƙarin neman haƙƙoƙinsu da aka tauye, sai dai abin ban takaici shi ne, shugabanni ba su kan kula da ƙorafe-ƙorafen talakawa.Yya bayyana cewa, har a makarantu ana samun hainci ta ɓangaren malamai idan suka ƙi shiga cikin aji su koyar, ko su karɓi kuɗi ga ɗalibai da iyayen yara domin su gyara masu sakamakon jarabawarsu. Bugu da ƙari, su ma ɗalibai da ke satar jarabawa ko maguɗin jarabawa duk ɗabi’u ne na ha’inci. Idan ‘yan siyasa ko ‘yan takara suka yi amfani da kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe ko lokacin jefa ƙuria don a zaɓe su, ko da ba su cancanta da a zaɓe su ba; yin haka ya zama ha’inci.

Da wannan dalili ne ya sa marubuta waƙoƙin siyasa da na sauran fannoni sukan duƙufa wajen yi wa shugabanni gargaɗi tare da jawo hankalinsu da su daina yin amfani da kuɗi don mutane su zaɓe su. Domin yin haka shi zai sa a sami shugabanni marasa adalci, masu ƙarfafa cin hanci da ha’intar dukiyar al’umma.Misali Ibrahim Yala ya yi irin wannan habaici na ƙasƙantau zuwa ga tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, wanda ya so ya cire kakin soja ya saka hula ta farar hula. Ya yi wa gwamnatin Babangida da shi kansa habaici ƙasƙanta domin mutane su fahimci irin illar da hainci ya haifar wajen taɓarbarewar tarbiyar al’’umma a Nijeriya lokacin da Babangida yake mulki. Mawaƙin ya kawo misali da zaɓen 1993 da aka yi, inda aka yi amfani da kuɗi daƙarfin mulki aka ci zaɓe, amma Babangida ya soke. Yin haka ya jawo tashin hankali da hasarar ɗinbin dukiyoyi da rayukan mutane. Wannan mataki na soke zaɓen ‘June Twelve’ shi ne tushen tashe-tashen hankula da yin ƙaura da mutanen kudancin ƙasar nan suka yi. Sanadiyar haka ya an yi hasarar dukiyoyi da rayuka ta hanyar haɗarukkan motoci da ya yi ta faruwa saboda yawan zirga-zirgar mutane dag arewacin Nijeriya zuwa kudancin Nijeriya. Mawakin ya yi wa Ibrahim Babangida habaici na ƙasƙanci, yala yana cewa:

Duk wahalar da muke ciki yau to ɗan Minna ya saka mu fama,

Wai burinsa ya wanke laifi na ‘june twowel’ a wurin na yamma,

Yau son kanka ya samu halin da za a daɗe babu warwarewa,

Dubi halin da ya sa Arewa ya mance takara zai yo wa,

Wai Baba me ka bari haƙiƙa da za mu bari har kayo wucewa,

Koma ka ƙare yaƙin gidanka gwamnanka zai kai ka kushewa.

(Ibrahim Yala: Waƙar CPC Canji).

A irin yunkurin da gwamnatin mulin soja ta wancan lokaci ta yi na neman zarcewa ga mulki ta hanyar kafa jam’yyun siyasa, da ita kanta ta kafa su. An gudanar da zaɓuka daban-daban har da na shugaban ƙasa. A zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar M. K.O. Abola shi ne ya ci zaɓe, amma saboda zargin maguɗin zaɓe da aka yi, sai gwamnatin Babangida ta ba da sanarwar cewa ta soke wannan zaɓe. An sami matsalolin hasarar dukiyoyi da rayukan jama’a da dama, wanda ya sa mutane suke ƙora-ƙorafe a kan haka. Daga cikin mutanen da suke ganin abin da ya faru shi ne ya haddasa abubuwan da suka wakana.Dalilin haka ya sa mawaƙin ya jefi Janar Ibrahim Babangida da habaici ƙasƙantau ta hanyar kiran sa da suna ɗan Minna’.

Allah wadarannku masu halin salmaniya,

Wannan ɗan baƙin da ƙira ta yan giya,

Tun da ya hawo yake halin danniya.

   (Ibrahim Yala: A.P.P, yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya)

Mawaƙin ya yi amfani da kalmar ɗan baƙi don ya bayyana wa mutane sifar shugaban ƙasa da ya mayar da dukiyar ƙasa abir wasoso, ya hana kowa ya more sai dai shi da mutanensa. Domin ya ƙara bayyana shi ga alumma su gane wanda yake yi wa habaici,sai ya ƙara muzanta shi da wata ɗabi’a da sifa irin ta ‘yan giya ta yadda masu saurare za su iya saurin fahimtar wanda yake yi wa habaicin. Wato mutum ne mai ƙirar sifar yan giya.Ya nuna wa mutane cewa, shi wannan shugaba da yake yi wa habaici, koyaushe cikin maye yake. Wato ya sifanta shi da ɗabi’a ta mashaya giya domin ya muzanta shi a idon mutane da duniya baki ɗaya.Ya ce, tun lokacin da wannan shugaba ya hau mulki bai yi wa talakawa akin komai ba, sai satar dukiyar ƙasa da danne haƙƙin jamaa da aka ba shi amana na kula da martaba da dukiya da mutunci ko rayukan alummar ƙasa.

2.8.7. Habaici -Gama-gari

Habaici gama-gari yana nufin ɓaci a kaikaice da ake yi zuwa ga kowane jinsi na mutane Wannan nau’in habaici yana ɗauke da kalmomin lamiri gama-gari da suka haɗa da kowa, kowane, kowace, kowaɗanne da sauransu. Mawaƙan siyasa suna amfani da wannan habaici domin su isar da saƙo kai tsaye ga ilahirin jamaa ko yan adawa ko masu ƙulle-ƙullen sharri don ganin shugaba ko wanda ake yi wa waƙa ya samu matsala ga tafiyar siyasarsa. Mawaƙan Hausa, musamman na siyasa suna amfani da waɗannan lamiran gama-gari domin su ƙulla habaici a cikin waƙoƙinsu da nufin su isar da saƙon ɓatanci ga ‘yan siyasa ko ‘yan adawa. Misali,Kamilu ɗan almajirin mawaƙa yana cewa:

Mu bi Allah kar mu ɗau boka,

Mu yi shanawa kamar kowa

(Kamilu: Karen bana maganin zomo).

Wannan ɗan waƙa yana ɗauke da habaici kamar yadda ya bayyana ‘mu yi shanawa kamar kowa’ habaici ne da ke bayyana wa masu saurare cewa, yanzu mutane sun bar biyar bokaye sun koma ga Allah wanda yake shi ke ba da mulki ga wanda yake so. Idan mutum ya bi Allah ga dukkan al’amurransa, sai ya sami walwala, wato, ya shana kamar yadda duk wanda ya dogara ga Allah yake yi.Wato duk mutumin da ya bi Allah ga dukkan al’amarin rayuwarsa sai ya sakata ya wala, babu wani abu da zai tayar masa da hankali. Ibrahim Yala yana cewa:

Kowa ya ƙi A.P.C. jamaa,

Gaskiya kam ya zuba ganganci,

 (Ibrahim Yala: Waƙar Maja A.P.C.).

Wannan nau’in habaici gama-gari ya faɗakar da mutane gaba ɗaya cewa babu keɓewa ga wani mutum, duk wanda ya yarda ya ƙi biyar jamiyyar A.P.C. maja, gaskiya ya yi babban kuskure. Wato ba ƙaramin ganganci ya yi ba, domin za a yi tafiyar nasara ba da shi ba. Ya ƙara da cewa, jiki magayi ne baba janarwato idan Buhari ya hau mulki zai fatattaki masu ƙiriniya.

2.8.8.Habaici -Keɓantau

Habaici keɓantau shi ne ɓaci da ake yi zuwa ga wni ko wasu masu wata ɗabi’a hali na musamman su kaɗai ke da irinsa. Wannan nau’in habaici yana tafiya ne da kalmomi masu bayyana keɓabbar sifar wani abu a aikace ko mutum, domin a jawo hankalin masu sauraro su yi ƙoƙarin gano wanda ake yi wa habaicin ta hanyar abin da yake aikatawa. Kalmomin su ne ‘mai’ da ‘maras’‘masu’ ‘marasa', waɗanda ake liƙa su ga suna ko aiki ko sifa su ba da wani suna ko aiki ko wani hali ko sifa ta mutum ko mutane da suke aikata wani abun assha. Mawaƙan siyasa suna amfani da wannan naui na habaici domin su soki ko tozarta wanda suke yi wa shi; domin su faɗakar da shi game da halin da ake ganin sa yana aikatawa da ya saɓa wa ra’ayin mutane ko shari’a ko al’ada. Misali Yusuf Fasaha yana cewa:

Mai son tsira ya taki gaskiya,

In ka ƙi kai za ka sha wuya.

 ( Yusuf Fasaha: Mu bi A.P.C. al’ummar ƙasa).

Wannan ɗan waƙa ya keɓanta ne ga mutane ko mutumin da yake muradin ya ga an yi rashin gaskiya ko maguɗi ga zaɓe. Mawaƙin ya yi wannan habaici domin ya jawo hankalin yan adawa su sa tsoron Allah a cikin ransu, musamman a lokacin zaɓe saboda yin haka shi zai sa a yi zaɓe na gaskiya.Rashin gaskiya ga dukkan al’amurra shi ne ke jefa mutane cikin mawuyacin hali, su ɗara faɗin da-sun-sani a lokacin da suka tsinci kansu cikin wahala.

Mawaƙin ya yi amfani da wannan kalma ta maidomin ya sifanta duk mutumen da ke ƙin gaskiya cewa shi ka shan wuya. Saboda haka wanna habaici sifatau yan bayyana mutane da ba su son gaskiya a harkokin siyasa cewa kodayaushe ka gan su suna cikin wahala har ta kai su ga neman ceto idan ba su samu ba sai neman wurin gudu kamar yadda Mudasiru Ƙasimu yake cewa:

Masu kashe Nijeriya za su kau,

Ko sun ƙi ko sun fuffuka.

  (Mudassiru: Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari).

Mawaƙin ya sifanta azzaluman shugabanni da cewa su ne masu kashe Nijeriya.Saboda haka yake sukar su da cewa ko sun ƙi ko sun so sai sun fuffuka sun bar Nijeriya da zarar Buhari ya sami nasarar lashe zaɓe.Harwa yauMudassir ya ƙara da cewa:

Masu sace daloli EFCC,

Nai wa gidajensun gwanjo.

(Mudassir; Mu amshi kuɗi mu zaɓi Buhari).

Kalmar masu da mawaƙin ya yi amfani da ta a nan tana nufin ɓarayi waɗanda suke satar dukiyar Nijeriya ta hanyar amfani da ƙarfin iko da suke da shi na gwamnati.Mawaƙin ya yi wa shugabannin jamiyyar P.D.P. masu mulki habaici domin ya mzanta su a idon yan Nijeriya ta hanyar nuna wa talakawa cewa su masu mulkin su ne suke sace kuɗin al’umma suna arzita kawunansu.

2.8.9.Habaici -Kaikaitau

Habaici kaikaitau wani nau’in habaici ne da ake yi, wanda ke nuna ɓaci ko sukar wani mutum ko mutane a kaikaice. A wannan nau’in habaici ana amfani da kalmar ‘a’ da ‘an’ ‘o’o’, da kuma ‘in’, domin a gina habaici da ba ya nufin kowa sai wanda ya san ya aikata laifi ko ya yi wani kuskure.Wato, habaicin bai ambaton suna ko sifar wanda ake yi wa shi, sai dai kawai a bayyana ɓarna ko kuskuren da aka yi domin wanda ya yi shi, ya ji, ya gyara. Mawaƙan siyasa suna amfani da wannan nauin habaici idan suna son su jawo hankalin masu saurare su yi tunane mai zurfi kafin su gano waɗanda ake yi wa habaicin. A ɓangaren masu saurare akwai yiwuwar su iya gano mutumin ko mutanen da ake yi wa habaicin, idan sun san mattsalar da ta faru tsakanin mai yin habaicin da wanda ake yi wa. Misali, Rarara yana cewa:

Ana ta hayagagar wofi,

Ana haka sai kuma ga baba.

 (Rarara: Maraba da Tsoho A.P.C)

Mawaƙin ya yi wa yan Nijeriya, musamman yan adawa masu yaɗa jita-jita, cewa rashin lafiyar Muhammadu Buhari ta yi tsanani. Wasu su ce ya mutu, wasu su ce ba zai dawo ba mutuwa zai yi a can Ingila. Wannan labari da ake ta yaɗawa ya sa mawaƙin ya yi wa yan adawa masu fatar kada Buhari ya dawo domin su maye gurbinsa na shuabancin Nijeriya. Dawowar Buhari ta tayar wa masu adawa da masu neman su haye kujerarsa hankali.Sai mawaƙin ya jefe su da habaici cewa ana ta hayagagar wofi’’,wato kowa na ta shaci-faɗi game da rashin lafiyar Buhari cewa mutuwa zai yi.Saboda haka sai dawowarsa ta baƙanta wa yan adawa da masu neman kujerarsa rai.

Shi kuma Ibrahim Yala hayin banki yana yi wa ‘yan Nijeriya hannunk-mai- sanda ta hayar sanar da su halin da ƙasa take ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki da ya faru a sanadiyar satar kuɗin ƙasa da masu mulkin Nijeriya na wancan lokaci suke yi ba tare da shamaki ba.Mawaƙin yana cewa:

Ana satar kuɗinmu a yau ba shamaki,

Ka ji halin da mu muke ciki Nijeriya.

  (Ibrahim Yala: A.N.P.P 2007).

 

Mawaƙin ya soki masu mulkin Nijeriya na jamiyyar P.D.P da cewa su ne ɓarayin da suke amfani da kujerunsu suna satar dukiyar ƙasa ba shamaki.Ya ce, Ana satar kuɗinmu a yau ba shamaki’,. Mawaƙin bai faɗi sunansu ba amma ya yi amfni da habaici maras ƙaidi saboda kaucewa faɗar sunansu ka iya jawo wata fitina daga magoyan bayansu.Wato bai ƙayyade masu satar ba,saboda haka habaicin yana iya faɗawa ga duk wani shugaba ko ɗan siyasar da yake amfani da muƙaminsa ya saci dukiyar alumma.Saboda haka habaici maras ƙaidi, habaici ne da ke iya faɗawa a kan duk wani ko wasu mytane da ke da irin ɗabi’ar sata da aka yi wa habaici namiji ne ko mace ko kuma wasu gungun mutane.

Wani misali na habaici maras ƙaidi shi ne inda Aminu Abubakarr Alan waƙa yake yi wa yan mulkin jari-hujja irin na kama-karya habaici domin ya faɗakar da mutane muhimmancin zaɓen mutum nagari ya jagoranci al’umma.Yana cewa;

An zaɓu ruɓa-ruɓa namu,

Da sunan wai wakiltarka,

A ba su kuɗi su miƙa mu,

Hannu ƙwarya hannu baka,

Tunanensu iyalansu,

Su tara abin da ba tamka.

 

A mulkin nan na al’umma,

Na zaɓen ra’ayin kanka,

Mulki daga al’umma ake

Cikin zaɓe na son ranka,

Ana yi don mutane ne,

Misalin ba ka ‘yancinka.

 (Aminu Alan Waƙa: Waƙar A.P.C.)

Aminu Alan waƙa ya yi amfani da habaici kaikaitau a ɗa na farko da kuma ɗa na uku a baiti na sama da kuma ɗa na farko da na biyar a baiti na biyu domin ya bayyana wa jama’a cewa mulkin siyasa yana buƙatar a bai wa kowane ɗan ƙasa damar ya zaɓi wanda yake so a ransa. Domin yin haka zai ba shi ‘yancin ya faɗi albarkacin bakinsa idan ya ga shugabanni sun yi abin da ba daidai ba domin su gyara.Shi ma Dauda Kahutu Rarara yana cewa:

An yi gaskiya an gyara ƙasa

Su algaza sai ciwon baki.

(Rarara: Maraba da tsoho oyoyo).

Saboda haka, a wannan fage, na nazarin habaici a cikin waƙoƙin siyasar Muhammadu Buhari wannan bincike ya nazarci nau’ukan habaici guda tara da mawaƙan siyasa na Buhari suka yi amfani da su cikin waƙoƙinsu.

2. 10. Habaici a matsayin Turke.

Habaici wani turke gne a cikin waƙoƙi da mawaƙan Hausa, musamman na siyasa ke amfani da shi su isar da sakonsu ga al’umma.Mawaƙa kan yi amfani da habaici a matsayin jigo domin su faɗakar da al’umma da kuma jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da ake isarwa gare su kai tsaye. Haka kuma ana amfani da shi domin a gargaɗi mutane ko ‘yan siyasa da ake magana a kansu su gyara wasu kurakurai da suke aikatawa, da kuma nuni ga wani abu da ake son su sani game da abin da ya shafi wanda ake yi wa habaicin; wanda ya saɓa wa al’adu ko ɗabi’un al’ummar da yake zaune tare da su. Wato, ana amfani da habaici ne a cikin waƙa domin a ƙaskanta abokan hamayya ko yan adawa da nufin a karya masu zucciya daga yunƙurin neman wani matsayi ko muƙami tare da wanda ake yi wa waƙa.

Habaici, inji masuiya magana, shi ne armashin waƙa, duk waƙar da babu habaici a cikinta takan zama tamkar miya babu gishiri domin saƙon da ake nufin isarwa ga mutane ba zai isa gare su ba, kamar yadda ake buƙata (Yahya 1997). Wato,ta hanyar amfani da habaici ake isar da sako cikin nishaɗi da raha ga masu saurare su fahimta da saƙo cikin hanzari ba tare da sun ƙosa ba ko nuna damuwa ba. Akwai jigon nishaɗi a cikin habaici, sai dai ba akan fahimci haka ba sai tafiya ta yi nisa, lokacin da masu sauraro suka sami kansu cikinsa. Wato shi nishaɗi ba kai tsaye ake fitowa da shi a hahaici ba, sai dai daga irin kalmomin da mawaƙi ya yi amfani da su ya gina habaicin za a sami ban dariya ko alajabi ko makamancin haka. (Ɗangulbi 1996). Misali, Alan waƙa yana cewa:

Ku aje kube sauyi ya zo,

Ku aje kube sauyi ya zo,

\Ku aje kibau sauyi ya zo.

Baƙar malfa,baƙar jarfa,

Mai shanye jinin jikin talaka,

Allah kaɗa guguwar sauyi,

Buhari janar karab da gari.

(Alan waƙa: Guguwar sauyi ta zo).

Wannan ɗan waƙa yana ɗauke da habaici miƙau ne ku da kuma habaici wanda ke ɗauke da jigon gargaɗi , yayin da saƙon yake ƙunshe da nishaɗi saboda mawaƙin ya yi amfani da kalmomin da ke nuna habaici ga masu son ta da fitina saboda neman biyan buƙatar yan siyasa.Ya yi amfani da kalmomin Baƙar malfa, baƙar jarfa, da mai shanye jinin jikin talaka domin ya soki jamiyyar PDP mai mulkin ƙasa ko ya naƙasa ayyukan da shugabannin jamiyyar suke gudanarwa domin ya jawo hankalin yayan jamiyyar APC su fahimci kasawar jamiyyar PDP. Haka kuma ya ambaci sunayen miyagun makaman da yan siyasa ke amfani da su domin su yi aikin taaddancin bangar siyasa.Misali, yin amfani da wuƙa da kibau da gariyo da sauran miyagun makamai a lokacin yaƙin neman zaɓe wata hanya ce da ‘yan siyasa ke amfani da matasa zauna-gari-banza, suna takura wa al’umma domin kawai su faranta wa ‘yan jam’iyyarsu rai da kuma taimaka masu su cim ma biyan buƙatarsu da sauransu.

2.11. Habaici a matsayin Salon sarrafa harshe.

Habaici a cikin waƙa wani salo ne da mawaƙa ke amfani da shi domin su nuna ƙwarewarsu ga harshen Hausa.Ta hanyar yin amfani da habaici cikin waƙoƙin Hausa, musamman na siyasa mawaƙa kan nuna ƙwarewarsu wajen iya zaɓe da tsara kalmomi tare da sarrafa su kamar yadda dokar harshen Hausa ta tanada.Kalmomin za su jawo hankalin masu sauraro su amfana da saƙon da ake isarwa gare su. Mawaƙa kan so su riƙa amfani da kalmomin karin magana da salon magana da adon magana a cikin waƙoƙinsu domin su nuna ƙwarewarsu ga harshe tare da bin ƙaidoji da dokokin harshe da tsarin da waƙa ta tanadar. Sai dai mafi yawan lokuta mawaƙan Hausa sukan saɓa wa ƙaidar nahawun harshe, idan wata lalurar waƙa ta taso, misali yanke gaɓar kalma ko cire wani abu a yankin suna ko yankin aikatau a cikin jumla, ko kuma cire wasali daga baya a saka shi tsakiya ko ma a jefar da shi. Yin haka wani salo ne da mawaƙan zamani ke amfani da shi na sarrafa harshe domin su sami damar isar da saƙonsu ga jamaa daidai, ba tare da ya gurɓata saƙo ba. Haka kuma, ya jawo hankalin masu saurare, su fahimci abin da ake son su sani. Misali sukan yi amfani da kalmomin lamiri kamar; wani, ko wata, ko wasu, su wane, wane, wanda, waɗanda, ‘yar, ɗan, mutum, mai, masu da sauransu. Idan mawaƙi ya yi amfani da irin waɗannnan kalmomin lamiri, wato kalmomin da ba su bayyana sunan wanda ake yi wa habaici ba, shi ke sa masu sauraro su fahimci cewa mawaƙin ya san harshen da yake magana da shi. Wannan salo shi ke jefa mutane cikin tunanin sai sun gano wanda ake yi wa habaici; domin ba a ambaci sunansa ba. Rashin ambatar sunan shi ne ya sa maganar ta zama habaici domin a ɓaci ko a musguna ma wanda ake yi wa shi. Misali, Rarara yana cewa:

Wanda duk ke haushinka’

Bai ruwan ‘yan sunnah ba.

 (Rarara: Baba Tsoho ya sauka)

 

Mawaƙin ya nuna ƙwarewarsa ga harshe inda ya yi amfani da kalmar ‘wanda’ domin ya yi shaguɓe ga wanda yake yi wa habaicin. Wannan shi ake kira habaici shaguɓau kamar yadda bayani zai zo daga baya a cikin babi na huɗu. Bugu da ƙari ya yi amfani da salon kamancen kasawa ga mutumen da yake yi wa habaici. Ya kamanta mai hassada da ɗan bidi’a, wato hassada ke sa a ji haushin wanda Allah ya yi wa wata baiwa. Saboda haka, mai jin haushin Muhammadu Buhari, to, bai yi kama da ‘yan sunnah ba. Wato, ɗan al’ada ne ko ɗan gargajiya. Domin duk mutumin da ya san cewa, Allah shi ke ba da mulki ga wanda ya so, kuma ya hana ma wanda ya so, to, ba zai yi hassadar mai mulki ba. Mawaƙin ya yi amfani da kalmar Haushi’’ a maimakon hassada domin ya nuna cewa harshen Hausa yana da yalwar kalmomi, kuma ya yi amfani da kalmar domin ya musguna ma wanda yake yi wa habaici. Wannan dabarar isar da saƙo wata ƙwarewa ce ya nuna ga harshen Hausa.

Haka kuma mawaƙa suna amfani da habaici a matsayin wata dabara ta isar da saƙo ga masu sauraren waƙoƙinsu ta hanyar jawo hankalinsu wajen sa ido ga wanda ake jifa da habaicin don su fahimci gaskiyar abin da aka faɗa a kansa. Wannan dabarar amfani da habaici a matsayin hanyar isar da saƙo ga masu sauraren waƙa, ta taimaka wa ‘yan siyasa wajen zurfafa tunaninsu kafin su zaɓi mutum a muƙamin siyasa. MasanaSun ƙara da cewa, ba kasafai ake gane wanda ake yi wa habaici ba, domin ba a ambaton suna,sai dai a ambaci wasu ɗabi’u ko sifofi na wanda ake yi wa habaicin.(Ɗangambo 1984).

Mafi yawan habaice-habaice ana yin su idan wata matsala ta faru a tsakanin wanda ake yi wa, da mai yin habaicin. Wani lokaci kuma sai idan mutane sun san abin daya faru tsakanin mutanen biyu, saisu ce, ai wane ake yi wa habaicin (Yahya 1997).Wato, ana yin habaici ga abokan adawar sarki, ko shugaba, ko wani ɗan siyasa da yake gwagwarmayar neman matsayi guda da wanda ake yi wa waƙa. Saboda haka, habaici bai faruwa a tsakanin mai yin sa da wanda ake yi wa, sai idan akwai wata buƙata ko hamayya da ta haɗa su.Wannan ne ya sa aka fi samun habaici a tsakanin mata kishiyoyin juna a zamantakewar Hausawa (Koko :2014). Irin wannan hamayya ta neman muƙami ko matsayi tsakanin mutum biyu take zama musabbabin faruwar amfani da habaici domin a ƙasƙanta abokin hamayya.

Dalilin haka ya sa mawaƙa ke jefa mutane cikin kogin tunani wajen gano mutumin da ake yi wa habaici. Wannan wata dabara ce da mawaƙan Hausa, musamman na siyasa ke amfani da ita su isar da saƙon waƙarsu ga alumma. Misali, Dauda Rarara yana cewa:

Masu murnar mutuwarka,

Yanzu haushi ya ƙaru.

 (Dauda Rarara: Waƙar A.P.C.).

Kalmomin masu,da yanzu kalmomi ne da ke nuna wa mai sauraren waƙa cewa mawaƙin yana da wayon amfani da kalmomi masu jan hankali a wajen isar da saƙonsa ga alumma. A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da habaici a matsayin dabarar isar da saƙo ga alumma ta hanyar sakaya sunayen waɗanda yake yi wa habaici. Hakan na iya zama wata dabara ce da mawaƙin ya yi amfani da ita domin ya jawo hankalin masu saurare su yanke wa kansu hukuncin gano waɗanda yake yi wa habaicin.A maimakon ya faɗi sunayen waɗanda yake yi wa habaici, sai ya ce, ‘masu’ domin ya baddalar da masu saurare. Wannan dabarar isar da saƙo ce,domin idan an faɗi sunaye; mutane za su gane da waɗanda ake yi wa habaici. Koyaushe shi habaici ana yin sa zuwa ga wanda aka yi tarayyar neman wani abu tare da shi, ko ɗan adawa. Saboda haka, ga ƙaidar habaici ba a ambaton suna, sai dai sifa ko ɗabi’a ta wanda ake yi wa shi. Sai a bar mutane da tunani, su yi ta shaci-faɗi a kan wanda ake yi wa habaicin. Saboda haka habaici a cikin waƙa, wata dabara ce ta isar da saƙo ga alumma. Shi ma da yake amfani da habaici a matsayin dabarar isar da saƙo, Ibrahim Yala Hayin Banki cewa ya yi:

Eh! Mun gaji mu da ku a mulkin Nijeriya,

Zaluncinku ya ƙure mu a Nijeriya,

Cin zarafin da cin amanarku gaba ɗaya,

Ya sa ba mu tsoron ku yau Nijeriya.

(Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).

Mawaƙin ya yi amfani da kalmomin mu da ku zaluncinku da sauransu domin ya soki masu mulkin Nijeriya da suka handame kuɗin ƙasa suna shagalinsu ba tare da sun damu da halin da sauran alummar ƙasa suke ciki ba.

2. 12. Tasirin Habaici a Zukatan Al’umma

Kowace al’umma tana alfahari ta samu abin da zai faranta mata rai ko na wani ɗan ƙanƙanen lokaci ne. Wannan dalili ne ya sa alummar Hausawa suke alfahari da mawaƙan Hausa, musamman na siyasa saboda saka su cikin nishaɗi a duk lokacin da suka saurari waƙoƙinsu. Habaici yakan zo a cikin sigar karin magana ko adon magana mai ɗauke da nishaɗi a cikinsa. Saboda haka ne, ya sa al’umma suke sha’awar su saurari waƙoƙin Hausa daga mawaƙa daban-daban domin su faranta masu zukata, ko gusar masu da wata damuwa da ke cikin ransu.. Mutane suna kallon habaici a matsayin wani gimshiƙin da ke ƙara kare martabar harshen Hausa da mawaƙan Hausa. Haka kuma da ƙara ɗaukaka martabar mawaƙan Hausa a zukatan masu sauraro. Mawaƙan saurata da na siyasa su ne suka faye yin amfani da habaici a cikin waƙoƙinsu; domin su tozarta ko ƙasƙanta abokan hamayyar sarakuna ko shugabanni ko yan adawar yan siyasa. Wannan ya sa mutane da dama suka fi mayar da hankalinsu ga sauraren waƙoƙin da ke ɗauke da habaici a cikinsu fiye da waɗanda ba su da habaici. Ta hanyar sauraren habaici da mutane ke yi ya sa suke dawowa cikin hankalinsu su kalli maganganun da mawaƙa ke yi a kan yan adawa su binciki gaskiyar abin da suke faɗa a kan shugabanni. Hakan na taimakawa talakawa su bayyana wa shugabanni wuraren da mulkinsu ya samu tangarɗa ko naƙasu domin su ji su gyara kurakuransu. Har wa yau habaici ya yi tasirin gaske a zukatan alumma, musamman wajen wayar masu da kai ta hanyar ba su dama su faɗa wa shugabanni gaskiya ba tare da wani shakku ba. Wato habaici ya yi tasiri wajen cire wa talakawa tsoron faɗa wa shugabanni gaskiya ko nuna masu kurakuransu kai tsaye.

2.12. Waƙa

Masana da manazarta daban-daban sun yi bayanai masu gamsarwa game da ma’anar kalmar “Waƙa” bisa ga fahimtarsu. Yahya (1997) da Gusau (1983) da Ɗangambo (2007) da Gusau (2011) da Birniwa (1987), sun bayyana waƙa da cewa, wani zance ne da ake shiryawa, cikin zaɓaɓɓun kalmomi da ake ƙulla batutuwa a samar da gangar jikinta cikin azanci da dabara da naƙaltar harshe, tare da rerawa da zaƙin murya waɗanda suka bambanta waƙa da maganar yau da kullum.

Bunza (2009) ya ta’allaƙa waƙa da hanya ce da al’umma ke sanin asalinsu da kuma al’adunsu. Hisket (1975) da Ɗangambo (2007),da Furniss (1996)da Sa’id (1981) da Gusau (2001) da Yahaya (2001) dukkansu sun danganta waƙa da salo da ake gina shi kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti,ɗango, rerawa, kari (Bahari), amsa amo da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓen su da amfani da su cikin sigogin da ba lallai ne haka suke a Rubutacciyar waƙa ba.

Shi kuwa Mukhtar (2006) ya ce “Rubutacciyar Waƙa wata hanya ceta gabatar da wani saƙo a cikin ƙayadaddun kalmomi da aka zaɓa, waɗanda ake rerawa a kan kari da ƙafiya a cikin baitoci. Yahaya (1985) ya bayyana waƙa da cewa ƙololuwar hikima ce da tunanin ɗan’Adam, ta yin amfani da ƙwayoyin muryoyi sanannu, cikin kalmomi zaɓaɓɓu waɗanda ake jerantawa cikin tsari fitacce ƙayyadadde, rattaɓaɓɓe ta yadda za ta fa’idantar da abin nufi a taƙaice, akasin zance ko hira, ko labari ko magana wadda take kara zube. Koko (2009) ta ce waƙa wani azanci ne mai ƙunshe da salon saƙa kalmomin hikima domin jawo hankalin mai sauraro ya fahimci saƙon da ake son ya sani, kamar yadda Bunguɗu da wani (2006) suke ganin cewa waƙa azanci ne na hikima da ake shiryawa a baka ko a rubuce, a rera ta cikin sautin murya mai armashi domin a isar da wani muhimmin saƙo. Saboda haka ana iya cewa waƙa wani saƙo ne da aka gina shi a kan tsararriyar ƙa’ida ta baiti, ɗango, rerawa, kari, amsa-amo (ko siga) da sauran ƙa’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓen su da amfani da su cikin sigogi da suka banbanta ta da maganar yau da kullum.

A taƙaice, idan aka yi la’akari da ra’ayoyin masana da manazarta daban-daban da hannuna ya kai gare su, ina mai ra’ayin cewa waƙa wata ƙololuwar hikima ce da ake amfani da ita wajen isar da saƙonni zuwa ga jama’a ta hanyar amfani da zaɓavɓɓun kalmomi da ake tsarawa a rera cikin sautin murya mai rauji da salon jawo hankalin mai sauraro ko karatu.

2.13. Tasirin Waƙa ga Isar da Saƙo ga Alumma.

Waƙa tana da muhimmancin gaske ga alummar Hausawa da ma sauran alummomi na duniya suna amfani da waƙa a matsayin hanyar isar da saƙo.Domin babu wata al’umma da ba ta amfani da waƙa a matsayin hanyar isar da saƙo tsakaninta da sauran alummomi. Babban muhimmancin waƙa ga alumma shi ne faɗakarwa tare da wa’azantarwa ga al’umma.Abu-Ubaida Sani da wasu (2016:10) et Yahya (1987) Ba za a taɓa mantawa da gagarumar gudummawar da rubutattun waƙoƙi suka bayar ba a lokacin jihadin jaddada addinin Musulunci a ƙarkashin jagorancin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

Waƙoki masu ɗauke da jigon wa’azi da gargaɗi da tauhidi, sun yi shura a ƙasar Hausa wajen koyar da alummar Hausawa sanin Mahalicci da yadda ya kamata a bauta masa, da kuma neman ilimin addinin shi kansa. Koyaushe aka yi maganar isar da saƙo ga alumma, Bahaushe yakan dubi hanya mafi sauƙi da saurin isar da saƙo ga alumma. A dalilin haka ya sa ya ƙirƙiro hanyar waƙa domin ya isar da saƙonsa cikin sauƙi. Abdulkadir, (1979), ya ce, ‘Ta hanyar waƙa za a iya gane halayen mutane da al’adunsu da ɗabi’unsu na da da na yanzu. Har ma wani lokaci takan bayyana yanayin wuri da tarihinsa, da abincin mutanen wurin da arzikinsu, da sana’o’insu, da koguna, da ma’adinai. Saboda haka waƙa ta zama madubin da ake lekawa a ga abubuwan da suka faru, ko ma waɗanda suke faruwa a cikin al’umma.

Bugu da ƙari,waƙa tana taimakawa wajen bunƙasa harshe da raya shi, saboda sauƙin shiga kai da faranta zuciyar mai sauraron ta. Har wa yau, waƙa tana kare harshe daga gurɓacewa. Hanyar waƙa ne zalaƙa da fasaha da hikimar Hausa suke bayyana.Kuma ta nan ne ake koyon ingantacciya tatattar Hausa;domin yawancin mawaƙa gwanaye ne wajen sarrafa harshen Hausa, musamman sai sun zaɓi kalmomin da za su yi amfani da su.Ta hanyar lura da waɗannan abubuwa ne za a iya tabbatar da cewa, tabbas amfanin waƙa ya fi gaban a ce don rerawa kawai aka tsara ta.’’(Abdulkadir 1979:10).

 Ɓangaren isar da sako kuma, kowane nau’in mutane a cikin al’umma kama daga maza da mata, samari da ‘yan mata, yara da manya masu mulki da talakawa, da ‘yan siyasa kan buƙaci waƙoƙi iri daban-daban domin su ɗebe masu kewa, ko su samar masu da nishaɗi idan suka saurare su. A lokacin siyasa akan sami walwalar jama’a, musamman idan ana yawon kamfe na neman zaɓen ‘yan takara. Saboda haka, waƙa ta taka rawar gani ga isar da saƙo ga alumma.,

Har wa yau a lokacin da addinin musulunci ya shigo ƙasar Hausa. Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da almajiransa sun yi rubuce-rubucen waƙoƙi da dama domin isar da saƙon Allah(S. W. A.), ga jama’a.Idan aka dubi yadda waƙar ‘’Tabban haƙiƙan,’’ ta Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ta yi tasiri wajen faɗakar da al’umma game da tsarin mulkin Musulunci da yadda shugabanni ya kamata su riƙi talakawansu da adalci; da kuma yadda su talakawan ya kamata su yi biyayya ga shugabanni.Sai a ga cewa, waƙa ta taka rawar gani wajen ilmantarwa da faɗakarwa da kum gargaɗi. Misali Shehu Ɗanfodiyo, a cikin rubutacciyar waƙar Tabban Haƙiƙan yana cewa;

In daɗa ka zamo imamun mutane ,

To tsare alhakinsu balle ubanne,

Ka jikyauta daɗa fa don kar ka kone,

Wanda yaz zam imamu don cin mutane,

Shi wuta kan ci gobe tabban hakikan.

  (Shehu Ɗanfodiyo: Tabban hakiƙan)

 

Haka kuma akwai waƙoƙida Shehu da almajiransa suka rubuta masu ɗauke da jigon addini, irin waƙar Lalura ta Nana Asma’u da sauransu. Duk waɗannan waƙoƙi suna karantar da alumma sanin Allah da kuma abin da ya shafi makoma a Lahira.Idan aka duba, sai mu ga cewa waƙa ta yi mutuƙar tasiri wajen faɗakarwa da ilmantarwa da isar da saƙo ga alumma, (Hiskett 1975). Misali a cikin waƙar,’Tabban haƙiƙan’’,Shehu ya yi kakkausan suka da gargaɗi ga masu cin dukiyar riba da ha’inci, a kasuwanci, da aikata sauran zunubai cewa, idan ba su tuba ba suka mutu;tabbas wuta ce makomarsu a gobe kiyoma. Yana cewa;

 Masu cin kura kasuwa duk akwai su,

Wansu keri su kai su samo bukinsu,

Wansu na nan ina faɗa ma kamassu,

Masu cin dukiya ta baital wasunsu,

Su wuta kan ci gobe tabban haƙiƙan.

  (Shehu Ɗanfodiyo: Tabban haƙiƙan).

Da Turawan mulkin mallaka suka zo ƙasar Hausa, suka buɗa makarantun boko, sai Hausawa suka koyi karatu da rubutu.Wannan ilimi na zamani da suka koya ya kawo sauyin salon isar da saƙo ta hanyoyi daban-daban. Wato, sai Hausawa suka fara rubuce-rubuce na kagaggun labarai da sauransu, don su isar da saƙo. Amma hakan bai yi wani tasiri ba kamar yadda waƙa ta yi.Misali mawaƙa sun taka rawa wajen faɗakar da al’umma a lokacin da siyasa ta kunno kai a ƙasar Hausa.

A jamhuriya ta farko, mawaƙa irin su, Lawal Maiturare da Mudi Sipikin da Sa’adu Zungur da Gambo Hawaja da Aminu Kano sun rera waƙoƙin siyasa domin su wayar wa alumma kawunansu.Misali Gambo Hawaja ya yi wa jamiyyar adawa ta NEPU waƙa don ya tallata manufofinta ga al’umma. Yana cewa:

Albarkacin Manzonka zan yabi jam’iyya,

Mai son ta turbuɗe zaluman Nijeriya.

Ita jam’iyyar nan NEPU ta ɗau anniya,

Sai ta ga bayan zaluman ga masha giya.

  (Gambo Hawaja: Waƙar NEPU, 1954).

 

Shi ma Aƙilu Aliyu ya yi wa NEPU waƙa , don ya faɗakar da al’umma saƙon jam’iyyar NEPU na kawar da mulkin zalunci a Nijeriya.a cikin waƙar yana cewa:

Haba jama’a ku ƙi zaɓenta,

Saboda mu taru mu kashe ta,

Ta faɗi da bayan bayanta,

Mu yarda da NEPU mu zabe ta,

Mu huta masifar NPC.

 

Fa ku talakawa duk taku,

Muna magana ne dominku,

Muna kuma yaƙi dominku,

Saboda mu tabbata girmanku,

Mu tsere azabar NPC.

(Akilu Aliyu: Baƙi uku sharrin NPC).

Waƙa ta yi matuƙar tasiri ga alumma musamman a lokacin yaƙin neman zaɓe,mawaƙa suna amfani da wannan dama su baje kolin hajar tunanensu wajen amfani da basirarsu su rera sabbin wakoki ga tsofin jamiyyun siyasa da kuma sabbi domin su wayar wa jamaa kai (Ɗantumɓishi:2007:201). A wannan lokacin siyasa ne ake amfani da motoci masu ɗauke da lasifikoki suna zagaye cikin birane da ƙauyuka dauke da Waƙoƙin jamiyyun siyasa daban-daban.

2.14. Bambancin waƙa da Sauran Kafofin Isar da Saƙo

Idan aka koma wajen bambancin waƙa da sauran kafofi ko hanyoyin isar da saƙo na yau da kullum, sai a ga cewa, waƙa ita ce hanya mafi sauki da kuma sauri wajen isar da saƙo ga alumma (Yahya: 1997). Haka ya kasance, idan aka yi la’akari da farkon shigowar addinin musulunci a ƙasar Hausa, malamai sun yi amfani da waƙa wajen koyar da mutane ilimin Tauhidi da wa’azi da Gargaɗi da sauran hukunce-hukuncen addini.A wancan lokaci malamai ba sukan mai da hankali ga ƙirƙira labari ba, domin suna jin kunya su faɗi abin da ba na gaskiya ba (Yahaya :1988).Don haka, sai suka fi mai da hankali ga amfani da waƙa wajen koyarwar addini bisaga ba da labarin da ba na gaskiya ba. Wannan ba ƙaramar rawa waƙa ta taka ba, saboda mutane ko yara sun fi sha’awar sauraren waƙa bisa ga duk wata hanya ko wani abin da za a faɗa masu cikin wata magana da ba waƙa ba. Mutane ko yara sun fi saurin fahimtar abun da aka koyar da su cikin sauri, idan har cikin waƙa aka koyar da shi. Sannan kuma waƙa ta fi sauƙin a hardace ta domin sautin murya mai rauji yakan jawo hankalin zukatan masu sauraro.Idan aka faɗi magana cikin maganar yau da kullum, ba akan mai da hankali ga abin da saƙon yake ɗauke da shi ba,kamar yadda akeisar da shi cikin waƙa. (Yahya 1997).

Da Turawan mulkin mallaka suka zo ƙasar Hausa, suka ci ta da yaƙi, sai suka kawo ilimin zamani wanda ya zo da sabon salon rubuta ƙagaggun labarai da waƙoƙi, musamman masu ɗauke da jigogi daban-daban na rayuwar yau da kullum. A sanadiyar haka ne, aka samu mawaƙa suna rera waƙoƙi a baka ko a rubuce domin su faɗakar da al’umma gameda wani sabon abu da ya ɓullo wa jama’a. Haka kuma aka samar da wasu hanyoyin sadarwa na zamani da ake amfani da su ana isar da saƙo. Daga cikin sauye –sauyen jigo da aka samu akwai abubuwa da suka haɗa da rayuwar yau da kullum da kuma siyasa, wadda a kanta ne wannan binciken keƙoƙaringano tasirin da waƙa ta yi wajen faɗakar da al’umma da kuma wayar masu da kai game da muhimmancin mulkin siyasa.

2.15. Naɗewa

A wannan babi an duba ayyukan da masana da manazarta suka yi game da adabin Hausa, musamman ɓangaren waƙa.Domin masu nazari ko bincike su ƙara fahimtar muhimman abubuwan da suke shige masu duhu a fagen bincike. An nazarci littattafai da muƙaloli da kundayen digiri na uku da na biyu da na farko daga jami’o’in da muke da su.An kuma ziyarci wasu cibiyoyin bincike da ɗakunan karatu daban-daban; domin kafa hujja ga cigaban wannan aiki. Kamar yadda aka tsakuro waɗannan bayanai dukkansu suna da alaƙa makusanciya ko ta nesa da wannan bincike. Da farko an yi bayanin salon zuga da habaici da saƙonnin da ke ƙunshe a cikinsu,da jawo hankalin mutane da dabarun isar da soƙo da suke ɗauke da shi. Haka kuma an yi bayanin fahimtar masana daban-daban a kan zuga da habaici da yadda suka yi tasiri a waƙoƙin siyasa dangane da samun nasarar kafa mulkin jumhuriya ta huɗu da ake ciki.An bayyana ma’anar waƙa da asalin samuwar waƙa, da kuma samuwar waƙoƙin siyasar gargajiya da ta zamani.Haka kuma an yi bitar Tarihin Muhammadu Buhari da taƙaitaccen tarihin mawakan da aka yi nazarin waƙoƙinsu. Wannan bincike ya mayar da hankali ne ga nazarinzuga da habaicicikin waƙoƙin siyasar zamani waɗanda mawaƙan siyasa na Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu suka rera masa. An kuma yi bitar ma’anar waƙa da tasirin waƙa ga isar da saƙo ga alumma da bambancin waƙa da sauran kafofin sadarwa da sauransu.

Ahmadu Bello University Zariya

Post a Comment

0 Comments