Ticker

6/recent/ticker-posts

Zuga Da Habaici a Wakokin Zamani: Nazari a Kan Wasu Wakokin Siyasa Na Muhammadu Buhari a Jumhuriya Ta Hudu – Babi Na Biyar

Cite this as: Ɗangulbi, A. R. (2024). Zuga Da Habaicia waƙoƙin zamani: Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhammadu Buhari a Jumhuriya ta huɗu [Kundin digiri na uku wanda ba a wallafa ba]. Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria. 

ZUGA DA HABAICI A WAƘOƘIN ZAMANI: NAZARI A KAN WASU WAƘOƘIN SIYASA NA MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUƊU

NA

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

A THESIS SUBMITTED TO THE SCHOOL OF POST GRADUATE STUDIES, AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA IN PARTIAL FULFILMENT OF THE REQUIREMENTS FOR THE AWARD OF DOCTORATE DEGREE IN AFRICAN LITERATURE (HAUSA) DEPARTMENT OF AFRICAN LANGUAGES AND CULTURES, FACULTY OF ARTS AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA, NIGERIA

SATUMBA, 2024

BABI NA BIYAR

 NAƊEWA

5.1 Kammalawa

Kamar yadda aka gani, sunan wannan aiki, ‘Zuga da Habaici a waƙoƙin zamani: Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhamadu Buhari’. A babi na farko, an kawo gabatarwa,da bayani a kan manufar bincike, wato manufar da ake son a cimma da wannan nazari. Wannan shi ya kai mu ga tambayoyin da aka yi a kan gudanar da wannan aiki. Bayan haka sai aka yi bayani a kan dalilin bincike da muhimmancin bincike da farfajiyar bincike, da kuma hujjar cigaba da wannan bincike. Akwai hanyoyin gudanar da bincike da suka haɗa da Ginshiƙan hanyoyi da Tattara bayanai da sauransu.An kawo bayani a kan hanyoyin da aka bi aka samo waƙoƙin da aka yi nazari da lokacin da aka aiwatar da su. A ƙarshe an kawo bayani a kan Tarihin mawaƙan da aka yi nazarin waƙoƙinsu da kuma Tarihin Muhahammadu Buhar da kuma ra’in bincike, wato, ra’in da aka ɗora wannan aiki a kansa.

A babi na biyu, an nazarci abubuwan da masana da manazarta da masu ruwa-da-tsaki suka kawo waɗanda suke da nasaba da wannan bincike, da kuma ma’anonin waɗansu muhimman batatuwa , domin fayyacewa. An nazarci Littafai da maƙaloli da kundayen kammala karatun digiri na uku da na biyu da na farko daga jamioi da kuma cibiyoyin bincike da ɗakunan karatu daban-daban.Kamar yadda aka samu wasu bayanan suna da alaƙa da binciken kai tsaye,waɗansu kuma alaƙar ta nesa ce. Da farko an fara kawo gabatarwa, da maanar zuga da asalinta, da nau’o’in zuga da zuga a matsayin turke, da kuma zuga a matsayin salon sarrafa harshe da zuga a matsayin dabarar jan hankalin al’umma da kuma tasirin zuga a zukatan al’umma. Duk a wannan babi an nazarci Habaici da ma’anarsa daga fahimtar masana da manazarta , da habaici a matsayin jigo da habaici a matsayin salon sarrafa harshe da kuma habaici a matsayin salon jan hankali ko dabarar isar da saƙo ga alumma. Akwai tasirin habaici a zukatan alumma, da nau’o’in habaici guda tara da suka haɗa da; Habaici-Gargaɗau da Habaici -Shaguɓau da Habaici- Miƙau da Habaici Sakayau da Habaici-Nunau da Habaici Gama-gari da Habaici-Ƙasƙantau da Habaici-Kaikaitau.

Har wa yau, an nazarci ma’anar waƙa a fahimtar masana da manazarta da tasirin waƙa ga isar da saƙo ga alumma, da bambancin waƙa da sauran kafofin isar da saƙo. An nazarci siyasa a fahimtar masana da manazarta da rabe-rabenta: Siyasar gargajiya da siyasar zamani (Dimokuraɗiyya), da siyasar jumhuriya ta huɗu da kuma naɗewa.

Babi na uku an yi cikakken bayani akan gudummawar da zuga ta bayar wajen zuga siyasar Muhammadu Buhari. An nazarci zuga ta fuskar shugabanci da shugabanni da zuga ta fuskar tallata ɗan takara, da zuga ta fuskar tallata jam’iyya da zuga ta fuskar zaɓe, da zuga ta fuskar hana maguɗin zaɓe. Haka kuma akwai zuga ta fuskar hana ha’inci da zuga ta fuskar hana zalunci da zuga ta fuskar bunƙasa tattalin arziki da zuga ta fuskar adawa da kuma zuga ta fuskar tsaro da kuma naɗewa.

Babi na huɗu ya tattauna a kan gudummuwar da habaici ya bayar wajen faɗakarwa kamar haka; habaici ta fuskar salon isar da saƙo da suka haɗa da gabatarwa, da habaici ta fuskar mulkin siyasa da habaici ta fuskar kushe shugaba da shugabanci da habaici ta fuskar kambama jam’iyya, da habaici ta fuskar nagartar ɗantakara. Akwai habaici ta fuskar adalci, da habaici ta fuskar zalunci da habaici ta fuskar ha’inci da kuma habaici ta fuskar rashin cika alƙawari, da habaici ta fuskar adawa, da habaici ta fuskar rashin kishin ƙasa da ya haɗa da bunƙasa aikin gona, da haɓɓaka ilimi da kiwon lafiya da bunƙasa hanyoyin sufuri da tattalin arzikin ƙasa. An tattauna a kan habaici ta fuskar tsaro da habaici ta fuskar yaudara da addin, sannan da naɗewa.

Babi na biyar ya yi bayanin kammalawa ne da sakamakon bincike da shawarwari da manazarta da kuma ratayen wasu waƙoƙin da aka yi nazarinsu.

5.2. Sakamakon Bincike

An gano cewa zuga da habaici sun yi matuƙar tasirin gaske a cikin siyasar Muhammadu Buhari, musamman wajen fito da hoton kyawawan ɗabi’unsa da halayensa nagari a fili; waɗanda su ne, suka jawo hankalin al’ummar Nijeriya har suka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya.Waƙoƙin siyasa, waƙoƙi ne da ke ƙunshe da hikimomi da dabarun jawo hankalin alumma su fahimci saƙon da ake son isarwa gare su. An gano cewa zuga da habaici sun ba da gudummawa wajen faɗakarwa da jawo hankalin al’umma suka aminta da zaɓen Muhammadu Buhari, a matsayin mutumin kirki wanda aka kamanta shi da mutum mai gaskiya da riƙon amana.An yi haka ne domin a cimma manufar da ake son a cimma ta samun shugaba mai adalci, wanda zai yi mulki da gaskiya da riƙon amana ya bai wa talakawa haƙƙoƙinsu cikin adalci.

Daga cikin nasarorin da wannan bincike ya samu akwai gano tasirin da zuga da habaici suka yi wajen ƙara fito da kwarjinin Muhammadu Buhari ta fusakar bayyana wa talakawa kyawawan halaye da ɗabi’unsa na gaskiya da tausayin al’umma.Wannan ya ƙara cusa soyayyar Buhari a zukatan mutane har suka kasa ganin laifinsa ko kurakuransa a lokacin mulkinsa, duk da kasancewar al’umma ba su ji daɗin abubuwan da suka faru na rufe kan iyakokin Nijeriya da wasu kasashe maƙwabtanta ba.Wannan mataki da Buhari ya ɗauka ya yi sanadiyar ƙara jefa talakawa cikin mawuyacin hali da ya fi na gwamnatin da ta gabata kafin gwamnatinsa.

Har wa yau, binciken ya gano nau’ukan zuga uku, nau’o’in habaici guda tara, waɗanda suka taimaka wajen kambama Muhammadu Buhari ya samu damar aka zaɓe shi ya yi shugabancin ƙasa. Waɗannan nau’ukan zuga uku da habaici guda tara da binciken ya yi amfani da su wajen ɗora nazarin wakoƙin siyasa da aka yi wa Buhari sun taimaka wajen ɗaukaka darajar Muhammadu Buhari da kuma daƙushe karsashin jamiyyun adawa da su kansu yan adawa.

Haka kuma bisa ga la’akari da fahimtar ma’anonin da masana daban-daban suka kawo na habaici, ya sa wannan bincike ya yi ƙoƙarin ƙirƙiro nauukan habaici guda tara waɗanda aka yi amfani da su wajen nazarin wakokin siyasa da aka rera ma Buhari kamar haka: Habaic- gargaɗau, da habaici-shaguɓau da habaici-nunau da habaici-miƙau da habaici-sakayau da habaici-ƙasƙantau da habaici- gama-gari da habaici-keɓantau da kuma habaici-kaikaitau.

Wannan bincike ya gano cewa zuga da kirari suna da dangantaka makusanciya wajen zaburar da wanda ake yi wa waƙa ya aikata ayyukan alheri ga talakawa da kuma karya manufar ‘yan adawa ko abokan hamayya.Wato zuga da kirari dukkansu suna ɗauke da kalmomin yabo dangane da kyawawan ayyuka da wasu magabata suka taɓa aikatawa a lokacin rayuwarsu sai a danganta su ga wanda ake yi wa waƙa domin ya yi koyi da irin waɗannan halaye na kyautatawa ko jaruntaka.

Dalilin faɗakarwa da gargaɗi da ilmantarwa da nishaɗantarwa da zuga da habaici suka yi, ya sa ‘yan Nijeriya suka jajirce wajen zaɓen Muhammadu Buhari ya zama shugaban ƙasa, sai dai daga bisani mutane suka riƙa korafe-ƙorafe dangane da yadda Buhari ya nuna gazawarsa ga shawo kan matsalolin da ‘yan Nijeriya suka shiga a sanadiyar mulkin jam’iyyar PDP. A zaton jama’a idan Buhari ya hau mulki, zai kawo ƙarshen matsalolin da ‘yan Nijeriya suke ciki. Amma har ya sauka bai iya kawo ƙarshen su ba. Saboda son da talakawa da wasu ‘yan Nijeriya suke yi masa ya sa ba su ga illarsa ba, sai dai irin soyayyar da suke nuna masa ta zahiri ta ragu a zukatansu.Wannan ya harzuka zukatan ‘yan Nijeriya har suna ganin cewa ba Buharin da suka sani ba ne, musamman a lokacin da suke sauraren waƙoƙin siyasar da mawaƙan siyasa suka rera masa suna kambama shi dangane da kyawawan ɗabi’unsa da halayensa na gaskiya da riƙon amana.

Wannan bincike ya gano cewa, mawaƙan siyasar zamani suna amfani da zuga da habaici a cikin wakoƙinsu domin su yi gargaɗi ga shugabanni da ‘yan siyasa su gyara miyagun halaye da ɗabi’u marasa kyau domin su kasance cikin shugabannin da za a iya alfahari da su a fagen mulkin adalci da rikon amana. A dalilin haka ya sa jama’a suka jajirce wajen jefa ƙuriunsu suka zaɓi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa domin ya kawo cigaba ta fuskar bunƙasa zaman lafiya da tsaro da tattalin arziki a Nijeriya. An kuma ga yadda zuga da habaici suka yi tasirin gaske a zukatan al’umma wajen ƙara ɗaukaka daraja da kwarjinin da Buhari yake da shi na halitta a zukatan al’mmar Nijeriya, har ma da na ƙasashe masu maƙwabtaka da Nijeriya. Wato mawaƙa sun kumbura shi suka wanke shi ya zama fari sal a idon ‘Yan Nijeriya, wanda hakan ya sa mutane suka yi tururuwa wajen jefa masa ƙuriunsu a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a 2015.

Saboda tasirin da zuga da habaici suka yi a zukatan ‘yan Nijeriya ya sa mutane suka sha wuya a lokacin da suka bi dogayen layuka domin su tabbatar sun zaɓi Buhari. Mawaƙa sun kambama shi har ya kai wasu na ganin Muhammadu Buhari a matsayin waliyi, wanda shi kaɗai zai iya riƙa Nijeriya ta gyaru, talakawa su samu walwala da wadatar arzikin ƙasa da zaman lafiya.

Binciken ya gano cewa, zuga da habaici sun ƙara fito da darajar mawaƙan siyasar Buhari a fili, har mutane suka san su, kuma suna girmama su saboda irin hazaka da hikimomin da suka nuna wajen amfani da zuga da habaici cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin mutane su zaɓi mutum nagari ya jagorance su a shugabancin ƙasa. Da irin wannan dubaru na jawo hankalin masu sauraro ya sa mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari suka taka muhimmiyar rawa wajen ƙara cusa ƙaunarsu da sauraren waƙoƙinsu a duk lokacin da suke son nishaɗi. Wato,ta hanyar amfani da zuga da habaici da mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari suka yi, ya sa suka ƙara samun ɗaukaka da shiga cikin zukatan ‘yan Nijeriya.

Binciken ya gano mawaƙan syasa suna amfani da zuga da habaici domin su ƙara ɗaukaka darajar wanda suke yi wa waƙa ya ji babu kamarsa a fagen siyasa.Sanna kuma a wani ɓangaren su ƙasƙanta abokan hamayyar wanda suke yi waƙa domin su tallata ɗankararsu ga jama’a har ya samu karbuwa.

Wata babbar illar da zaɓen Muhammadu Buhari ta yi wa al’ummar Nijeriya, kamar yadda binciken ya gano ita ce; na farko a sanadiyar soyayyar da al’ummar Nijeriya suka nuna wa Buhari, ya sa jama’a suka yi tururuwa a lokacin zaɓe suka jefa masa ƙuri’unsu ya zamo shugaban ƙasa. Hawan mulkinsa ke da wuya sai ya fara rufe kan iyakokin Nijeriya da maƙwabtanta domin hana shigowa da abinci da sauran kayan masarufi da mutane suke amfani da su a yau da kullum. Wannan rufe kan iyakoki ya yi wa alummar ƙasar nan zafi,domin tashin goron zaɓo da farashen kayan abinci da sauran kayayyaki da ake shigowa da su,suka yi. A sanadiyar haka rayuwa ta yi tsada, talakawa suka shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi fiye da lokacin mulkin jamiyyar P.D.P. Abu na biyu shi ne, ƙara farashen man Fetur da Buhari ya yi ya sa zirga-zirga da sufurin kayan da ake sarrafawa a cikin gida suka tsauwala; rayuwa ta shiga wani hali, wanda ke cin abinci sau uku a yini ya koma sau biyu ko sau ɗaya a yini. Bugu da ƙari, tattalin arzikin al’umma ya taɓarɓare jarin ‘yan kasuwa ya yi ƙasa.Duk waɗannan abubuwa da aka ambata sun faru a sakamakon zuga da habaici da mawaƙan Muhammadu Buhari suka yi masa, ya sa shi Buharin ya aiwatar da haka, a tunanensamataki ne na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ya ɗauka.Wannan mataki da ya ɗauka ya sa aka samu‘ci gaban mai ginar rijiya’, wato, kullum sai ƙara yin ƙasa yake yi, amma ya ce ya cigaba.

Wata babbar illa da wannan binciken ya ƙara ganowa ita ce, ta ɓangaren ilimi da tsaro waɗanda suka zama ƙadangaren-bakin- tulu a Nijeriya. Rashin kula da karatun jami’o’i ya sa ilimi ya fara taɓarɓarewa, ba a kyautata wa malaman jami’o’i da sauran malaman Firamare da na makarantun gaba da Firamare. Matsalolin ilmin ‘ya’yan talakawa da abincinsu yana neman ya buwayi talakawa har wasu suna kasa biya ma ‘ya’yansu kuɗin makaranta saboda tsadar rayuwa da aka shiga a dalin rufe kan iyakokin ƙasa da ƙara farashin man Fetur da sauransu. Amma abin ban haushi saboda so da ƙaunar da jamaa sukeyi wa Buhari har ya sauka daga gadon mulki masoyansa ba su ganin laifinsa, sai dai na maƙarrabansa. Haka su ma iyayen yara ba su ganin laifin Muhammadu Buhari saboda tsananin son da suke yi masa.Hakan ya kawo wa ilimin ‘ya’yan talakawan Nijeriya naƙasu; domin an wayi gari uwaye ba su iya biya wa ‘ya’yansu kuɗin karatu a jam’o’i da sauran makarantu masu zaman kansu a Nijeriya.

Zuga da habaici a mawaƙan Buhari suka yi amfani da su cikin wakoƙinsu domin tallata shi, sun taka rawa wajen haifar da rashin aikin yi ga matasa wanda ya haifar da ayyukan ta’adddanci da rashin tsaro a wasu sassan Nijeriya, musamman yankunan Arewa maso gabas da kuma yankin Arewa maso yamma.Saboda tasirin da zuga da habaici da mawaƙan siyasar Buhari suka yi amfani da su ya sa talakawa suka yi nadama a ƙarshen mulkinsa domin sun fahimci cewa tsananin kaunar da suka nuna wa Buhari ita ce sanadiyar faɗawarsu cikin mawuyacin halin tsadar rayuwar da ba a san iyakarta ba. Sai dai, Allah kaɗai ya bar wa kansa sani.

Daga ƙarshe binciken ya gano cewa waƙoƙin siyasa, waƙoƙi ne da ke ƙunshe da hikimomi da dabarun jawo hankalin alumma su fahimci saƙon da ake isarwa gare su. Mawaƙan siyasa suna amfani da hikimarsu wajen jawo hankalin al’umma su fahimci muhimman saƙonni da suke ƙoƙarin isarwa ga masu saurarensu,domin su jawo hankalin masu jefa ƙuria su zaɓi mutum mai kyawawan ɗabi’u da halaye nagari. Anfahimci cewa,zuga da habaici suna ba da gudummawa wajen jawo hankalin al’umma su aminta da zaɓen mutum nagari domin a cimma manufar da ake son a cimma na samun shugabanni masu gaskiya da adalci.

Dalilin haka ya sa ‘yan siyasa suke amfani da mawaƙa wajen faɗakarwa da gargaɗi da kuma ilmantar da al’umma ta amfani da zuga domin su zaburar da su wajen neman matsayi na siyasa. Haka kuma suna amfani da habaici domin su samu nasarar jawo hankalin ‘yan Nijeriya su ƙyamaci duk wani mutum da yake neman a zaɓe shi ya jagoranci al’umma, amma halayensa da ɗabi’unsa ba su ba da damar a zaɓe shi ba. Wannan dabara ta amfani da habaici wata hanya ce ta tacewa da rairaye ɓaigurbi daga cikin ‘yan siyasa domin fitar da mutane da suka cancanta su riƙa alumma a siyasance. Saboda haka ‘yan siyasa su gyara kurakuransu da halayensu kafin su yi tunanin shigowa fagen siyasa. Idan aka samu haka a fagen siyasa za a samu siyasa mai tsafta da shugabanci nagari. Wannan binciken ya gano cewa mawaƙan siyasar Muhammadu Bihari sun taka rawar gani wajen faɗakar da al’umma game da amfanin zaɓen mutum mai gaskiya da riƙon amana, kamar Muhammadu Buhari a 2015.

5.3.Shawarwari

Wannan bincike yana ba da shawara ga ‘yan siyasa su dage su rungumi mawaƙan Hausa su ba su muhimmanci,domin yin haka zai taimaka masu su koyi darasi mai muhimmanci dangane da al’amuransu na siyasa,ta hanyar gyara kurakuransu da ɗabi’unsu. Su zama mutane nagari kafin su tsaya takarar kowane irin muƙami na siyasa a wannan ƙasa tamu. Bugu da ƙari su kansu mawaƙan siyasa su ci gaba da amfani da zuga da habaici domin kambama mutane nagari su tsaya takarar kujerun mulkin ƙasa a matakai daban-daban. Haka kuma su dage wajen jawo hankalin mutane su fahimci amfanin zaɓen mutum nagari domin a samar da kyakkyawan mulkin adalci da gaskiya da riƙon amana tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka cikin sauƙi.Sannan su cigaba da amfani da habaici a cikin wakokin su domin su naƙasa mutanen da ke adawa da shugabanni masu ɗabi’u nagari domin su jawo hanklain al’umma su kaurace wa zaɓen ruɓaɓɓun ‘ya siyasa daga cikin al’umma. Zuga da habaici da mawaƙan suka yi amfani da su don faɗakar da al’umma da ‘yan siyasa yana taimakawa wajen garzaya ko kambama mutane su aminta da jam’iyyada ɗan takarar da ake tallatawa gare su idan ya kasance mai kyawawan halaye ne da ake alfari da su ga kowane irin shugaba da aka zaɓa.

Haka kuma, ya dace manazarta da ke tafe, su ƙara zurfafa tunani wajen haɓɓaka bincike su samo wasu hanyoyin da za su taimaka wajen bunƙasa dabarun jawo hankalin jamaa ta hanyar amfani da zuga da habaici da mawaƙan siyasasuke yi cikin waƙoƙinsu. Wannan bincike yana ba da shawara ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a kan harkokin siyasa da su tashi tsaye su ga sun kafa kyakkyawan tubalin gina siyasa mai ɗorewa ta hanyar amfani da zuga da habaici da mawaƙan siyasa suke yi a matsayin makamin gyaran ɗabi’un ‘yan siyasa kafin su nemi wata kujere ta siyasa. Yin haka zai taimaka a sami shugabanni nagari waɗanda za su kawo wa ƙasa cigaba a siyasance. Ana kira ga al’umma su ba wa mawaƙan siyasa muhimmanci kasancewar su malamai ne masu ilmantar da al’umma su fahimci alfanun da ke ƙunshe a cikin harkokin siyasada mulkin siyasa wanda ke bai wa yan ƙasa dama su shiga a dama da su a gudanar da salon mulki mai bai wa kowa yancin faɗar albarkacin bakinsa. Sannan a ƙara faɗaɗa bincike a kan amfani da zuga da habaici a cikin waƙoƙin siyasa a matsayin wasu makamai na yaƙi da ruɓaɓɓun ‘yan siyasa masu manufar a fasa-kowa –ya rasa a cikin siyasar Nijeriya.Wato, masu mummunar manufa ta rushe tsarin siyasar Nijeriya da mutane masu gaskiya da riƙon amana irin su Tafawa Ɓalewa da sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakwato suka aza tubalin gininta.A ɓangaren masana tariri, ya dace su ƙara ƙoƙarin ɗaukar wannan bincike ya zama abin adanawa domin amfanin na baya, da kuma adana adabin Hausa. Saboda haka sai an adana wannan bincike za a iya gano cewa, mawaƙan siyasar zamani suna da muhimmanci ta fuskar amfani da zuga da habaici a cikin wakoƙinsu wajen faɗakar da al’umma da jawo hankalin ‘ya siyasa su mai da hankali wajen kyautata ɗabi’unsu da halayensu muddin suna son jama’a su aminta da su. wato, ‘yan siyasa su fahimci saƙon da zuga da habaicin suke isarwa gare su domin su gyara kurakuransu. Shugabanci nagari ya dogara ga samun mtane nagari masu gaskiya da riƙon amana.

Daga ƙarshe ina ba wa matasa da yan siyasa da masu nazari kan harkokin siyasa da su ɗauki zuga da habaici da mawaƙan siyasa ke amfani da su da muhimmanci, ba waidon kambama wani mutum ko samar da nishaɗi ko tozarta wani ko wasu ‘yan siyasa ko shugabanni kawai ba, a’a zuga da habaici wasu makamai ne na yaƙi da munanan ɗabi’u da masu aikata su domin su ji su gyara. Samun cimma nasarar yaƙi da miyagun ɗabi’u da halaye marasa kyau ya ta’allaƙa ne a kan jajircewar da alumma, musamman mawaƙan siyasa za su yi ta hanyar amfani da zuga da habaici domin a kawar da ruɓaɓɓun ‘yan siyasa a cikin al’umma. 
Ahmadu Bello University Zariya

Post a Comment

0 Comments