Ticker

6/recent/ticker-posts

Zuga Da Habaici a Wakokin Zamani: Nazari a Kan Wasu Wakokin Siyasa Na Muhammadu Buhari a Jumhuriya Ta Hudu – Babi Na Daya

Cite this as: Ɗangulbi, A. R. (2024). Zuga Da Habaicia Wakokin Zamani: Nazari a kan wasu waƙoƙin siyasa na Muhammadu Buhari a Jumhuriya ta huɗu [Kundin digiri na uku wanda ba a wallafa ba]. Ahmadu Bello University, Zaria, Nigeria.

ZUGA DA HABAICI A WAƘOƘIN ZAMANI: NAZARI A KAN WASU WAƘOƘIN SIYASA NA MUHAMMADU BUHARI A JUMHURIYA TA HUƊU

NA

ALIYU RABI’U ƊANGULBI

A THESIS SUBMITTED TO THE SCHOOL OF POST GRADUATE STUDIES, AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA IN PARTIAL FULFILMENT OF THE REQUIREMENTS FOR THE AWARD OF DOCTORATE DEGREE IN AFRICAN LITERATURE (HAUSA) DEPARTMENT OF AFRICAN LANGUAGES AND CULTURES, FACULTY OF ARTS AHMADU BELLO UNIVERSITY, ZARIA, NIGERIA

SATUMBA, 2024

BABI NA ƊAYA

SHIMFIƊA

1.1 Gabatarwa

Waƙa tana da muhimmancin gaske a fagen isar da saƙo cikin sauri ga al’umma.Ana amfani da ita wajen yaɗa manufofi na addini da siyasa da sauran al’amurran da suka shafi harkokin yau da kullum.Marubuta da Makaɗan Hausa, suna taka muhimmiyar rawa wajen amfani da zuga da habaici cikin waƙoƙinsu domin su ilmantar da jama’a, da kuma faɗakar da su cikin nishaɗi a kan wani muhimmin abu da ya ɓullo wa al’umma.Waƙoƙin siyasa waƙoƙi ne da mawaƙanzamani suke amfani da su wajen tallata manufofin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara ga jama’ar ƙasa.Wato, mawaƙa suna amfani da zuga da habaicia cikin waƙoƙinsu domin su faɗakar da al’umma ko wayar masu da kai ga wani baƙon abu da ba su fahimci yadda yake ba.

Habaici abu ne mai muhimmanci a cikin waƙoƙin Hausa na baka da rubutattu, musamman na siyasa da ake amfani da shi domin a jawo hankalin jama’a su fahimci saƙon da ake son su sani.Wato, habaici wata magana ce da a ke yi a kaikaice ta hanyar ambaton sifa ko halaye ko ɗabi’un wanda ake nufi da shi domin a ƙasƙanta shi ko tozarta shi a idon mutane,(Ɗangambo, 1984, Pp.47). Wato, habaici ɓaci ne a fakaice ta hanyar hannunka- mai- sanda ko gugar-zana dangane da wasu ɗabi’u ko halaye marasa kyau da wani ke aikatawa; domin mai wannan hali ya ji, ya gyara kurakuransa.

Ita kuwa zuga da mawaƙa ke amfani da kalmomin yaboko kirari ta hanyar faɗar wasu kyawawan halaye da ɗabi’u nagari ga wanda suke yi wa waƙa domin su ingiza shi ko harzuƙa shi ya aikata wani abu da ba zai iya yin sa ba idan yana cikin hankalinsa (Bunza, 2009, P. 147).Ana dangantawanda ake yi wa waƙar da iyaye da kakanni ko wasu magabata da suka taɓa aikata irin waɗannan halaye na jaruntaka ko na kyautatawa a lokacin rayuwarsu. Ana gudanar da wannan nazari domin bincikowa, tare da gano irin muhimmiyar rawar da zuga da habaici suke takawa wajen ilmantarwa da faɗakarwa da gargaɗi da kuma nishaɗantarwa a zukatan al’umma domin jawo hankalin jama’a ko masu sauraren waƙoƙinsu, su aminta da zaɓen mutum nagari a mulkin siyasa. Haka kuma da binciko tasirin da zuga da habaici suka yi a zukatan al’umma ko masu sauraren waƙoƙin siyasa dangane da soyayyar da suke yi wa Muhammadu Buhari. Har wa yau wannan bincike ya yi ƙoƙarin gano irin nauin da zuga da habaici suke da su domin amfanin jamaa da masu binciken ƙwaƙwaf a kan adabin Hausa, musamman waƙoƙin siyasa don su ƙara faɗaɗa wannan fanni na adabin Hausa.

1.2. Manufar Bincike

Manufar gudanar da wannan bincike ita ce, a nazarci yadda zuga da habaici da mawaƙan siyasa suke amfani da su cikin waƙoƙinsu na siyasa wajen jawo hankalin mutane. Saboda haka, ƙudurorin gudanar da wannan bincike sun haɗa da:

        i.         Fito da gudummawar da zuga da habaici suka bayarwa wajen faɗakar da mutane tare da jawo hankalinsu su amince wa zaɓen mutum nagari, wanda zai gudanar da mulki cikin adalci don cigaban al’umma da ƙasa baki ɗaya.

      ii.         Yadda zuga da habaici a cikin waƙoƙin siyasar zamani suka taimaka wajen tallata manufofi da aƙidojin Muhammadu Buhari ga jama’a har ya sami gagarumar karɓuwa aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.

   iii.         Fito da nau’o’in zuga da habaici da yadda suka yi tasiri ga ƙara cusa soyayyar Muhammadu Buhari a cikin zukatan ‘yan Nijeriya ta hanyar ambaton kyawawan ɗabi’u da halayensaa cikin waƙoƙinsu da suka yi masa da kuma nazarin saƙo da dabarun jawo hankalin al’umma da mawaƙan siyasa suka yi amfani da su suka gamsar da masu saurare suka fahimci saƙon da ake son su sani.

   iv.         Fito da kwatanci da ke tsakanin Zuga da habaici a cikin waƙoƙin da aka yi wa Muhammadu Buhari tare da nazarin saƙo da salon jawo hankali da ke ƙunshe a cikinsu.

      v.         Fito da tasirin da zuga da habaici suka yi a zukatan al’umma musamman wajen amfana da roman mulkin siyasa ko akasin haka a sanadiyyar zaɓen Muhammadu Buhari da suka yi a matsayin shugaban ƙasa.

1.3. Dalilin Bincike

Masana da manazarta da dama sun yi rubuce-rubuce a kan abin da ya shafi waƙoƙin siyasar zamani. Adamu, (2014: ) da Adamu (2012: ),Wasu sun yi nazarin jigon zuga da zambo, wasu kuma a kan zuga da yabo, wasu a kan zambo da kirari, wasu a kan zambo da yabo a cikin waƙoƙin siyasa. Wasu kuma jigon habaici, musamman abin da ya shafi waƙoƙin siyasar Muhammadu Buhari. Wasu sun yi nazarin jigon zuga, wasu kuma sun yi a kan zuga da zambo, wasu kuma a kan zambo da yabo a cikin waƙoƙin siyasa. Sai dai, kaɗan daga cikin manazarta suka taɓo jigon zuga da habaici a waƙoƙin siyasar Muhammadu Buhari da mawaƙan zamani suka rera masa. sun yi magana a kan salon tallata ‘yan takara a waƙoƙin siyasa a jamhuriya ta huɗu da salo da sarrafa harshe a cikin waƙoƙin jam’iyyun ANPP da PDP. Dukkansu sun yi tsokaci ne a kan salo kai tsaye a cikin bincikensu. Birniwa (2015: ) ya yi nazari a kan matsayin karin magana a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa. Shi ma Sani (2012), ya yi nazari a kan salon sarrafa harshe a waƙoƙin jamiyyar CPC, da Suleman (2013), ya yi nazari a kan salon sarrafa harshe a waƙoƙin Sadi Sidi Sharifai. Idris (2016:) ya yi nazari a kan jigon Bijirewa a rubutattun waƙoƙin siyasa a Ƙasar Hausa 1903-2015. Abdulƙadir (2008 ), ya kwatanta rubutattun waƙoƙin siyasa na Hausa daga 1804 -1966, Ɗiso (1997) ya yi aikinsa a kan Zambo da Yabo a matsayin dabarun jawo hankali a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa na Hausa. Bambancin aikinsa da wannan bincike shi ne,ya yi a kan zambo da yabo, shi kuwa wannan aiki an gudanar da shi a kan zuga da habaici a matsayin dabarun jawo hankalin al’umma su fahimci muhimmancin zaɓen mutumin kirki a mulkin siyasa, wanda zai yi mulki cikin gaskiya da riƙon amana da kuma adalci ga waɗanda ake mulka.

Garba (1998) ya yi aikinsa a kan maganar azanci a cikin waƙoƙin makaɗan baka na Hausa: Nazarin zambo da habaici da ire-irensu. A aikin nasa ya nazarci saƙonnin da ke ƙunshe ne a ckin zambo da habaici .Wannan bincike yana da kama da nasa domin binciken ya duba salon zuga da habaici wajen jan hankalin al’umma su fahimci saƙon da mawaƙan zamani suke isaewa gare su.’Kaɗan daga cikin ayyukan manazarta da masana da wannan bincike ya samu damar dubawa suka yi magana a kan saƙonnin da salon zuga da habaici suke isarwa ga al’umma kai tsaye.

Mawaƙan zamani su ne waɗanda suke shirya waƙoƙinsu a rubuce ko kuma a baka, su riƙa rerawa tare da amafani da kayan kiɗa kamar su, jita da fiyano da sauran kayan kiɗa masu ba da sauti na zamani. Mawaƙan zamani suna amfani da kayan kiɗa a cikin waƙoƙinsu domin sun fahimci cewa, mutane, musamman matasa sun fi mai da hankalinsu ga sauraren waƙe-waƙe da ke ɗauke da kiɗe-kiɗe a cikinsu domin samun nishaɗi. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa aka ɗauki waƙoƙin zamani na siyasar Muhammadu Buhari domin a fito da tasirin da zuga da habaici suka yi wajen jawo hankalin al’umma su fahimci saƙon da ake isarwa gare su.Haka kuma an zaɓi Muhammadu Buhari daga cikin mutanen da ake alfahari da su, masu gaskiya da riƙon amana; domin a yi nazarin waƙoƙin da aka rera masa dangane da gwagwarmayarsa a cikin harkokin siyasa da nufin kawo sauyi a tafiyar mulkin siyasa a Nijeriya.

An zaɓi mawaƙan zamani irinsu Rarara, da Ibrahim Yala da Murtala Mamsa Jos, da Mudassir Ƙasimu Kano da Yusuf Fasaha da Aminu Abubakar Alan waƙa da sauransu.Waɗannan mawaƙa su ne suka fi sauran mawaƙan zamani ɗaukar Muhammadu Buhari a matsayin Karen-gwadin- dafi a cikin ‘yan siyasa. Saboda haka binciken ya yi ƙoƙarin fito da tasirin zuga da habaici da mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari suka yi amfani da su cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin masu saurare da ‘yan siyasa su fahimci kyawawan ɗabi’u da halayensa nagari a fagen mulki.

An ware kaɗan daga cikin ɗinbin waƙoƙin da mawaƙan zamaninsuka rera wa Muhammadu Buhari domin binciken ya sami damar tantance irin basirar da Allah ya yi wa waɗannan mawaƙan.Haka kuma ya nazarci salon zuga da habaici da mawaƙan suka yi amfani dasu cikin waƙoƙinsu.

Bugu da ƙari, an zaɓi a yi nazarin salon zuga da habaici da mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari suka yi amfani dasu domin fito da gudummuwar da sukabayar wajen faɗakarwa da jawo hankakin mutane da masu sauraren waƙoƙin siyasar zamani su fahimci kyawawan ɗabi’u da halaye nagari na wanda suke yi wa waƙa cikin raha da nishaɗi.Wani dalilin daya sa wannan bincike ya zaɓi siyasar zamani, shi ne, a cikin tsarin siyasar zamani ne ake ba kowane mutum damar zaɓen kowace jam’iyya da yake ra’ayi ba tare da an tilasta masa ba. Wannan shi ke ba wa kowaneɗan ƙasa dama ya zaɓi mutumin da yake zato, shi zai taimaka masa, ya samu nasarar cimma biyan buƙatunsa da samar masa da ayyukan yi don bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da samar da zaman lafiya da tsaro.Dalilin kafuwar jam’iyyu daban-daban ya sa ake samun adawa, wanda hakan yake kawo samuwar waƙoƙin siyasa da dama har wasu mawaƙan suna amfani da zuga da habaici domin su soki wata jam’iyya da ba tasu ba ko wani ɗan takara na jam’iyyarsu ko ta adawa. Wato jam’iyyar adawa wadda ke da manufofi da suka saɓa wa buƙatun yan Nijeriya.Wannan tsari na siyasar zamani ya ba mawaƙa dama su garzaya jam’iyyar da suke so, ta yadda jama’a za su amince da ita. Ko, su soki waɗanda ba su ra’ayi ta yadda jama’a za su ƙyamace ta. Manufar siyasar zamani ta kafa jam’iyya,ita ce, taɗora mutane ga neman abin duniya da biyayya ga manufofi ko buƙatun waɗanda suka kawo ta a ƙasarmu. Dalilin wannan bincike ya yi ƙoƙarin cike giɓin da masana da manazarta suka bari a fagen nazarin zuga da habaici a waƙoƙin siyasar Muhammadu Buhari a jumhuriya ta huɗu.

1.4.Tambayoyin Bincike

A tsarin bincike, ana tsara tambayoyi ne domin su yi wa mai zanari jagora ga samun nasarar kammala bincikensa da ya sa a gaba. Wato, hakan zai taimaka wa mai bincike ya cimma manufar bincike da fito da sakamakonsa tare da ba da shawarwari masu amfani. Daga cikin tambayoyin binciken akwai:

     i.            Wace gudummuwa zuga da habaici suke bayarwa wajen jawo hankalin mutane su amince wa zaɓen mutum?

   ii.            Ta yaya zuga da habaici suka ba da gudummuwa wajen tallata manufofi da aƙidojin Muhammadu Buhari ga al’ummar Nijeriya?

iii.            Ta yaya nau’o’in zuga da habaici da mawaƙan siyasar zamani suka yi amfani da su suka ƙara cusa soyayyar Muhammadu Buhari a cikin zukatan ‘yan Nijeriya?

iv.            Wane tasiri zuga da habaici da mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari suka yi amfani da su ya yi a cikin zukatan al’umma dangane da zaɓen 2015?

   v.            Wace dangantaka zuga take da kirari da mawaƙan siyasar zamani suka yi amfani da su wajen jawo hankalin al’umma su aminta da zaɓen Muhammadu Buhari?

A taƙaice wannan bincike ya ƙoƙarta amsa waɗannan tambayoyi a kan zuga da habaici da mawaƙan siyasar zamani suka yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu da suka yi wa Muhammadu Buhari a jamhuriya ta huɗu a cikin bayanan da za su biyo baya.

1.5. Farfajiyar Bincike

Wannan bincike ya taƙaita ne a kan nazarin zuga da habaici cikin waƙoƙin siyasar zamani; waɗanda aka yi wa Muhammadu Buharitun lokacin da ya fara gwagwarmayar siyasa a 2003-2022.An ɗauki waƙoƙin zamani ne, domin akwai waƙoƙi daga cikinsu da suke kan tsari na rubutattun waƙoƙi, amma sai aka biyo su da kiɗa domin a jawo hankalin masu sauraro. Mafi yawan mawaƙan da aka zaɓo sun shahara a fagen amfani da zuga da habaici a cikin waƙoƙinsu da suka yi wa Muhammadu Buhari domin su ƙara kambama gwarzonsu a fagen siyasa. Haka kuma suna naƙasa abokan adawar Muhammadu Buhari bisa ga sauran mawaƙan da suka rera masa waƙa.Gusau (2014:2), ya bayyana cewa, Hausawa suna rubuta waƙar baka, su rera a sitidiyo tare da amfani da kayan kiɗa da amshi irin yadda Larabawan sudan suke yi wa waƙokinsu na Ugniya. Wannan salon amfani da kayan kiɗa da amshi, shi ne, ya sa ake kiran waƙokin da na zamani, kuma mawaƙan siyasa da aka zaɓo suke amfani da wannan salon a cikin waƙoƙin da suka rera ma Muhammadu Buhari a wannan jumhuriya ta huɗu.

An taskace waƙoƙi 40, saboda buƙatar wannan aikin bisa ga fahimtar cewa, duk waƙar da ta fuskanci shugabanci ko tsarin mulki ta zama waƙar siyasa. Muhimman abubuwan da binciken ya ƙunsa sun tsaya ne a kan:

Nazarin zuga da habaici a waƙoƙin siyasar zamani da mawaƙan suka yi wa Muhammadu Buhari; waɗanda binciken ya yi amfani da su domin cimma nasarar kammala wannan aiki. An keɓance waƙoƙi goma sha hudu domin gudanar da wannan bincike kamar haka: Mawaƙan da waƙoƙinsu sun haɗa da Ibrahim Yala Hayin Banki, waƙoƙi biyu; “Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya, ta APP/ANPP 2003-2007, da CPC/APC 2011-2015. Dauda Kahutu Rarara ya wallafa waƙoƙin “Sai baba Buhari” A.P.C. 2015. Da “Baba Tsoho Ya Sauka”2021-2022. Akwai kuma Murtala Mamsa Jos, da waƙarsa mai suna, “Da na je taron Jari, na gano abin mamaki al’umma” APC 2014-2015, da Sabuwa ta zo’ APC. Akwai, Karen bana maganin zomo da “Runhu an yi Furen Banza” ta Kamilu ɗan almajirin mawaƙa, APC: 2015, da Aminu Alan waƙa,” waƙar guguwar sauyi ta zo APC”2015, da “In ba ka san gari ba saurari daka”APC 2015. Akwai kuma Yusif Fasaha Kano,”Mu bi APC al’ummar Ƙasa” 2015, da ?. da Mudassiru Ƙasimu Kano “Mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari, 2015 ?.” An zaɓi waɗannan waƙoƙi da mawaƙansu ne saboda mawaƙa ne da suke da ilimin addini da na zamaniwanda ya sa suka shahara wajen tsara waƙoƙinsu cikin tsari irin na salon waƙokin Larabci; domin su jawo hankalin masu sauraro cikin raha da nishaɗantarwa da sauransu. Wannan shi ne ya bambanta waɗannan mawaƙa da sauran mawaƙan da ba su da cikakken ilimin addini ko na zamai.

1.6 Muhimmancin Bincike

Duk wani aiki da ake aiwatarwa, ko za a aiwatar a harkokin rayuwar ɗan’Adam, ba zai rasa wani muhimanci ba ga waɗanda aka yi dominsu. Kowane bincike da ake aiwatarwa, akan yi shi ne domin a zaƙulo wasu muhimman abubuwa da ka iya kasancewa ba a san su ba tun farko, kuma idan an sani wata ƙila ba a fahimce su ba sosai da sosai. Saboda haka muhimmancin wannan bincike shi ne ya taimaka wa ɗalibai da masu nazarin harshen Hausa wajen iya naƙaltar harshe, da kuma yadda mawaƙan siyasar zamani ke sassaƙa kalmomin zuga da habaici cikin baitocin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da suke isarwa gare su. Haka kuma, wannan bincike zai taimaka wa manazarta tarihi, da adabi wajen adana muhimman abubuwa da suka shafi zuga da habaici cikin waƙoƙin siyasar zamani da yadda suka yi tasiri wajen faɗakarwa da ilmantarwa da gargaɗi, da nishaɗantarwa da kuma jawo hankalin mutane cikin sauƙi su fahimci saƙon da ake son su sani.

Haka kuma, binciken zai taimakawa mawaƙa wajenƙara mayar da himma su iya sarrafa harshe a cikin waƙoƙi domin suburge masu saurare, tare da samar da nishaɗi da raha a zukatan masu saurare.Bugu da ƙari,zai taimaka wa masu nazarin siyasa su fahimci yadda ake amfani da wasu kalmomin hikima cikin waƙoƙiwajen tallata jam’iyyu da ‘yan takaraa idon jama’a har su gamsu da abubuwan da aka faɗa a kan wanda ake yi wa waƙa.Sannan,gidajenradiyo da talabijanda sauran kafafen yada labarai za su amfana da hikimar zaɓen kalmomi a lokacin da suke hulɗa da jama’a, da kuma kiyayewa da kame bakinsu wajen isar da saƙonninsu ga ‘yan siyasa da sauran al’umma.

1.7. Hujjar cigaba da Bincike

An samu gagarumar gudummawa a kan adabin Hausa, musamman a fagen waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa. Duk da kasancewa masana da manazarta sun taka rawar gani wajen aiwatar da bincike-bincike a kan waƙa, ba a zurfafa bincike ba a kan nazarin salon zuga da habaici a matsayin dabarun jawo hankalin al’umma ba a cikin waƙoƙin siyasar zamani. Muhammad (1977) da Ɗangambo (1980) da Birniwa (1987) da Yahaya (1987) da Said (2002) da Abdulƙadir (2008) da Usman (2008) da Auta (2008) da Halifa (2012) da Yakasai (2014) da Funtuwa (2015) da Lawal (2016) da Alkali (1989) da Diso (1997) da Tsoho (2014) Idris (2016) da Bunguɗu (2016) da Bunguɗu (2017) da Dunfawa (2002).Dukkansu sun yi bayani a kan abin da ya shafi waƙoƙi kama daga na addini da na zamantakewar alumma, har zuwa na siyasa. Waɗannan ayyuka da masana da manazarta suka aiwatar daban-daban sun yi magana ne a kan jigogi da salo da zubi da tsari na waƙoƙin Hausa don bunƙasa adabi. Amma daga cikin ayyukan da suka gabata ba a samu waɗanda suka yi bayani kan salon zuga da habaici da mawaƙan siyasar zamani suka yi wa Muhammadu Buhari ba kai tsaye. Wannan dalili ne ya sa wannan aiki ya yi ƙoƙarin nazarin zuga da habaici a matsayin jigo, da salon sarrafa harshe da tasirinsu a zukatan al’umma, da kasancewarsu tubalan gina waƙa da ayyukan fasaha da dabarun isar da saƙo na waƙoƙin siyasa da mawaƙan zamani suka yi wa Muhammadu Buhari a jamhuriya ta huɗu.

1.8. Hanyoyin Gudanar da Bincike

A duk lokacin da aka ƙudiri yin wani bincike na ilimi, dole ne a yi tunanin hanyoyin da za a bi domin a samo muhimman bayanai da za su taimaka wajen ganin aikin ya samu nasara.Saboda haka, wannan bincike ya bi hanyoyi da dama wajen tattara bayanai masu mahimmanci domin aiwatar da shi domin a tantance rawar da zuga da habaici suke takawa a fagen isar da saƙo ga masu sauraro. An yi amfani da waɗannan hanyoyi kamar haka:

1.8.1.Hanyoyin Tattara Bayanai

i. Ziyarar ɗakunan karatu na jami’o’i da cibiyoyin bincike daban-daban domin samun bugaggun litttattafai da kundayen bincike da muƙalu da sauran takardu da za su taimaka wajen gudanar da wannan bincike.

ii.Tattaunawa tare da masu ruwa-da-tsaki da suka ƙunshi masu shaawar waƙoƙin siyasa da yansiyasa kansu, da saraun mawaƙa a kan tasirin zuga da habaici da mawaƙan siyasa na zamani suke amfani da su wajen jawo hankalin al’umma su fahimci alfanun zaɓen mutum nagari a mulkin siyasa domin gina siyasa mai ɗorewa da za a sami zaman lafiya da cigaban tattalin arzikin ƙasa.

1.8.2 Ginshiƙan Hanyoyi

Binciken ya duƙufa ne a kan fito da rawar da zuga da habaici suke takawa wajen faɗakarwa da ilmantarwa da kuma nishaɗantawa; domin jawo hankalin ‘yan siyasa da sauran al’umma su fahimci muhimmancin kyawawan ɗabi’u da halaye nagari kafin su zaɓi wanda zai jagorance su a mulkin siyasa. Kamar yadda mawaƙan siyasa na Muhammad Buhari suka yi ƙoƙarin jawo hankalin mutane su fahimci kyawawan ɗabi’unsa da halayensa nagari domin su kambama shi, sannan suka ƙasƙantar da yan adawarsa waɗanda mawaƙan suke suka da rashin kyawawan ɗabi’u domin su cusa ƙiyayyar waɗannan ‘yan siyasa a zukatan jama’a.

1.8.3.Sauran Hanyoyi

Binciken zai fito da hanyoyin da mawaƙan siyasar Muhammadu Buhari suka yi amfani da su a cikin waƙoƙinsu; ta amfani da nau’o’in zuga da habaici domin su taimaka wajen isar da saƙonni ga jamaa cikin hanzari.

Binciken ya dogara ne a kan ra’in da ya dace domin ƙoƙarin fito da saƙon da ake so a fahimta a fagen nazari. An ɗora wannan aiki kan ra’in yabo da kushewa (Epideitic Theory), ra’i ne da yake yaba kyawawan ɗabi’un ɗan Adam domin ya kambama shi a idon jama’a, sannan ya kushe munanan halaye ko ɗabi’u na abokan hamayyar wanda ake yabawa. Ra’i ne da ya samo asali daga makarantar da Aristotle, mutumin ƙasar Girka ya samar a wajajen (350 BCE), wanda Leech (1968) da Nicole Loraux da Poulakos (20th century) da Nancy Fraser (1990) da Muktar (2005) da Lawal (1997), da Abdurrahaman Ado suka yi rubuce-rubuce domin nuna goyon bayansu ga wannan mazahabar.

1.8.4. Hanyar Ƙwanƙwance Bayanai

An ƙwanƙwance bayanai ne a wannan bincike ta hanyar zaƙulo nauoin zuga da habaici a fili tare da kafa hujja da misalai daga waƙoƙin siyasa da aka yi wa Muhammadu Buhari daban-daban domin daidaita bayaninsu.

1.8.5 Hanyoyin da aka bi aka samo waƙoƙi

An sami wasu waƙoƙi daga kaset-kaset da kuma memori, waɗanda aka saurara domin tsakuro muhimman abubuwa da aka yi nazarin su.Bugu da ƙari, binciken ya yi ƙoƙarin shiga kafar sadarwa ta intaneti da kafar sada zumunta ta WhatsApp, domin samun bayanai masu alaƙa da wannan aiki. An ziyarci studiyo na Musa Nasale a Kantin Kwari, Kano; inda aka naɗi waƙoƙi kusan 45 da aka yi wa Muhammadu Buhari dangane da gwagwarmayarsa ta siyasa a Nijeriya. Daga cikin waƙoƙin da aka samu kuma aka yi nazarin su akwai:’’Guguwar sauyi ta zo’’, ta Aminu Abubakar Alan waƙa, da ‘’Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya,’ta Ibrahim Yala Hayin Banki da ‘’Runhu an yi furen banza, akuya ba ta je dawa dan shi ba’’, ta Kamilu ɗan almajirin mawaƙa Yobe, da kuma ‘’Da na je taron APC’’ ta Murtala Mamsa Jos ,da ‘’Sai baba Buhari da Baba Tsoho’’ na Dauda Kahutu Rarara, da sauransu. An sami waƙoƙin Mudassir Yusuf Kano da na Yusuf Fasaha da Murtala Mamsa Jos, da dai sauransu.

1.8.6. Lokacin da aka aiwatar da waƙoƙin

Bincike ya nuna cewa an sami waƙoƙin siyasa da aka yi wa Muhammadu Buhari na siyasa tun farkon shigarsa cikin gwagwarmayr harkokin siyasa a shekarar 2003. Mawaƙan Hausa da dama sun yi rubuce-rubucen waƙoƙi domin su tallata manufofin Muhammadu Buhari da aƙidojinsa na gaskiya da riƙon amana a idon jamaa. Haka ya sa aka sami mawaƙa daban-daban da suka tsara waƙoƙi domin kwarzanta Buhari tare da jawo hankalin jama’a su karɓe shi ya shugabanci Nijeriya a matsayin shugaban ƙasa na farar hula.

Kafin Buhari ya fara gwagwarmayar siyasa, mawaƙan Hausa da dama sun yi masa waƙa tun lokacin da ya yi mulkin soja. Wannan lokaci ya kasance shugaban ƙasa da ya yi ƙoƙarin daidaita al’amurran mulkin ƙasa. Alhaji Mamman Shata na daga cikin mawaƙan da suka rera masa waƙa domin nuna farin cikinsa ga ƙwace mulki da ya yi daga Gwamnatin Siyasa ta Shehu Shagari. Ga sunan waƙar kamar haka:

   Ku tafi ku huta farar hulla,

Tun da soja sun ƙwace mulkinsu.

(Mamman Shata: Waƙar Ƙwace Mulki da Buhari ya yi a 1984).

Bayan shekaru da soja suka yi mulkin Nijeriya na kusan shekara 16, sai aka sake buga gangar siyasa wadda tun farko aka zawarci Buhari ya shiga a dama da shi. A shekarar 2003 Buhari ya tsunduma kacokam cikin gwagwarmayar siyasa, inda mawaƙa suka duƙufa wajen wake shi domin su tallata manufofinsa da aƙidunsa ga yan Nijeriya. Tun daga wannan lokaci ne a shekarar 2003, mawaƙan Hausa da dama suka ci gaba da rera masa waƙa. Mawaƙi na farko da ake zaton ya fara rera masa waƙa shi ne, Ibrahim Yala Hayin Banki, Kaduna wanda ya waƙe shi kamar haka:

Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya,

Sannu Buhari kai muke so Nijeriya.

(Ibrahim Yala: Waƙar ANPP 2003).

Daga baya sauran mawaƙa irinsu Dauda Kahutu Rarara da Aminu Abubakar Ladan ALAN Waƙa da sauransu suka biyo sahun kwarzanta Muhammadu Buhari a idon duniya har jama’a suka aminta da shi suka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa na farar hula a shekarar 2015.

1.9. Taƙaitaccen Tarihin Mawaƙan da Aka Zaɓo

Ya dace a fahimci taƙaitaccen tarihin mawaƙan da ake nazarin waƙoƙinsu domin mai karatu ko sauraren waƙoƙin siyasa ya iya gano irin hikima da fasahar da Allah (S.W.A.) ya yi wa waɗannan mawaƙa wajen sarrafa harshe domin su jawo hankalin mutane su gamsu da saƙonnin da suke isarwa gare su cikin sauƙi da nishaɗi. Misali:

1.9.1 Ibrahim Yala Hayin Banki Kaduna

An haifi Ibrahim Sale Yala Hayin Banki a 1973, a garin Kawo da ke ƙaramar hukumar mulki ta Kaduna ta Arewa, jihar Kaduna. Wato, ya zuwa yanzu yana da shekara 51 a duniya. Sunan mahaifinsa malam Sale, Mahaifinsa malam Sale ya rasu a shekarar 2002, amma mahaifiyarsa na nan a raye.

1.9.2 Ƙurciyarsa da Ilminsa

Ibrahim Yala Hayin Banki ya soma karatun allo tun yana ɗan shekara shidda a wurin mahaifinsa malam Sale. Har wa yau, malamin ya yi karatun addini daidai gwargwado inda har ya zama malamin Islamiya da na Zaure, a unguwar da yake zaune a Kaduna.

1.9.3 Karatun Boko

 Ya fara karatun Firamare a Kawo a shekarar 1980, har ya kai aji uku (3), sai aka mai da shi Baptis Firamare Hayin Banki, inda ya soma karatunsa daga Firamare aji biyu (2). Wato aka mayar da shi baya daga aji uku ya dawo aji biyu har ya gama aji shida a 1989. Ya shiga makarantar Horon malamai (Kaduna Teacher’s College) ta Kaduna a shekarar, 1990 -1996. Ibrahim Yala ya cigaba da karatunsa na Difloma a fannin gudanar da sha’anin mulki a makarantar Fasaha da Ƙere-ƙere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a 2013, inda ya yi difloma a fannin mulki.

1.9.4 Fara Waƙarsa da Shahararsa

Ya fara waƙa tun shekarar 1993/1994. Ya rubuta waƙoƙi akan yabo da begen Manzon Allah (S.A.W.) da dama, wato, waƙoƙin madahu. Ya kuma fara waƙar siyasa a shekarar 1999, inda ya yi wa ɗan takarar Sanata na wancan lokaci Dr. Bashir Balarabe na jam’iyyar APP waƙa. Haka kuma a shekarar 2003 ya rera wa Janar Muhammadu Buhari waƙa lokacin da ya fito takarar kujerar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin inuwar jamiyyar APP/ANPP, waƙar da ta jawo hankalin yan Nijeriya da dama suka aminta da goya wa Muhammadu Buhari baya don ya kafa gwamnati. Waƙarsa ta farko da ya rera wa Buhari ita ce,

’Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya,

Sannu Buhari kai mu ke so Nijeriya’.

Mawaƙin ya wallafa waƙoƙin siyasa a ƙalla sun fi 200 ya zuwa wannan lokaci da Buhari ya sauka kan mulki.

1.9.5 Gwagwarmayarsa

 Mawaƙi, kuma Jarumi a masanaantar Fina-finan Hausa ta kannywood ta kano. Yana taka rawa a fin ɗin ‘Gidan Badamasi, inda yake ɗaya daga cikin ‘ya’yan Badamasi da ake kira Sha’arani’. Sannan kuma malamin islamiya ne a unguwar da yake zaune a kaduna. Mutum ne mai sa’awar kallon ƙawallo, kuma yana goyan bayan ƙungiyar ƙwallo ta Real Madaril.

1.9.6 Iyalansa

Ibrahim Yala yana da mata uku da ‘ya’ya goma sha uku (13) da jika ɗaya. Kuma yanzu haka yana zaune a Kaduna, sai a duk lokacin da ake shirya Fin ɗin gidana Badamasi yakan bar duk abin a yake yi har sai an gama shirya gidan Badamasi ɗin. (An sami rubutattacen bayanin tarihinsa wanda ya aiko a rubuce ta hanyar Whatsapp a ranar 16, ga Fabuware, 2023)

1.10 Dauda Adamu Kahutu Rararar

An haifi Dauda Adamu Kahutu Rarara a garin Kahutu Ƙaramar Hukumar Ɗanja ta jihar Katsina a 13/09/1986. Sunan mahaifinsa Adamu, wanda ke zaune a garin Kahutu ta ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina.

1.10.1 Iliminsa na Addini

Ɗan shekara 38, Rarara ya fara karatun boko a garinsu Ɗanja, inda daga bisani aka cire shi boko aka kai shi Kano wajen karatun allo (ƙolanta) inda ya ci gaba da karatun allo da almajiranci, wato, karatun Tsangaya.Ya yi rayuwar ƙurciyarsa a garin Kano. Bayan ya sauka Alƙurani mai girma, sai ya karanci littattafan Fiqhu kamar su ƙawaidi, da Ahdari da Ishimawi da sauransu. Rarara bai yi karatun boko ba saboda a lokacin da yake tsangaya ba ya samun damar zuwa makarantar boko. Amma daga baya ya shiga makarantar koyar da karatun manya, inda ya yaƙi jahilci har ya koyi karatu da rubutu da kuma magana da Turanci.

1.10.2 Fara Waƙarsa da shahararsa

Rarara ya fara sana’ar waƙa tun lokacin da ya shiga masana’antar Kannywood, inda yake rera waƙoƙin fina-finai. Ya cigaba da rayuwarsa a Kano har ya kai matsayin da yake yanzu. a masana’antar fina-finai ta kannywood a Kano. Dauda Adamu Kahutu mawaƙin yan siyasa ne a Nijeriya, mawaƙi a fannin rera waƙokin yan siyasa kuma marubucin waƙoƙi. Ya fi kowa taka muhimmiyar rawa wajen rera wa Muhammadu Buhari waƙa, wadda ta sa mutane suka ɗauka cewa, babu kamarsa a fagen ƙara fito da kwarjin Buhari a idon alummar Nijeriya. Ya yi waƙoƙin yan siyasa na jamiyyar APC (All Progressive Congress) da dama baya ga na Muhammadu Buhari a shekarar 2015. Ya yi wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da gwamna Ganduje da sauran jigajigan yayan jamiyyar APC waƙa.Ya zama shugaban ƙungiyar mawaƙan Hausa mai suna 13x13. Ya rera waƙoƙin siyasa da dama kimanin waƙa 66, daga cikinsu har da waƙoƙin da ya yi wa Muhammadu Buhari na masu gudu su gudu, da ga Buhari ya dawo da sai baba Buhari da baba tsoho ya sauka da sauransu.

1.10.3 Gwagwarmayarsa

Bayan da Rarara ya kai wani mataki na rayuwa, sai ya shiga gwagwarmayar neman abinci ba tare da ya dogara ga kowa ba. Sana’ar da ya fara yi ita ce, ta okada da bunburutu da zaman shago da sauran sana’o’i, kafin ya fara sana’ar waƙa ta siyasa.A cikin waƙoƙin da ya rera na siyasa akwai, masu gudu su gudu, da Buhari ya dawo da Buhari ɗoɗar’ da jihata jihata ce, da saraki sai Allah da kuma baƙuwar Rarara da sauransu. Kawo ya zuwa yanzu Rarara yana daga cikin mashahuran mawaƙa a masana’antar Kannywood, kuma shi ne shugaban wata ƙungiya ta matasan mawaƙa da ‘yan fim mai suna, ‘ 13x13.

Shi mutum ne mai sha’awar ƙwallon ƙafa da kasuwanci. Haka kuma yana da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ‘’Rarara Academy, wadda shi ne ke ɗauke da nauyinta. Yanzu haka ana hasashen Rarara ya mallaki sama da gidaje dubu a Kano da Kaduna da kuma a babban birnin Tarayya Abuja.

1.10.4 Iyalansa

Dauda Adamu Kahutu Rarara yana da matan aure da ‘ya’ya (An sami cikakken bayani daga wata hira da aka yi da shi a Gabon Room TV. YOU TUBE SOCIAL MEDIA

1.11 Amin Ladan Abubakar ALAN WAƘA

An haifi Aminu Ladan ALAN waƙa ranar Talata 2 ga watan 10 shekara ta 1973.Wannan na nuni da cewa,ya zuwa wannan lokaci shekarar 2024 ALA yana da shekaru 51 a duniya. An haife shi ne a garin Kano, a ƙaramar hukumar Birni da Kewaye, unguwar da ake kira Yakasai. Sai dai kuma an yaye shi ne a wata unguwa da ake kira Ƙofar Wambai, a hannun kakanninsa. Daga baya kuwa, sai iyayensa suka tashi suka koma ƙaramar hukumar Nasarawa, suka zauna a unguwar Tudun Murtala da ke cikin Kano

1.11.1 Mahaifansa

Sunanan mahaifin ALA shi ne, malam Sani Abubakar ɗan ƙaramar hukumar Jega ta jihar Kebbi. Karatun addini ya kawo mahaifin Ala Kano, inda ya zauna na tsawon shekaru, har ma ya zama ɗan gida. Mahaifin Ala ya yi auren farko a garin Kano

Mutane da dama sukan yi tambaya game da asalin laƙabin ALA. Amsar a nan ita ce, laƙabin ALA ya samo asali daga cikakken sunansa da ake kiransa, wato, Aminu Ladan Abubakar. ALA taƙaitawa ce ta sunan, Aminu Ladan Abubakar. Wannan na nuni da cewa, ambaton wannan laƙabi ALA, daidai yake da kiran cikakken sunansa Aminu Ladan Abubakar. Asalin mahaifinsa ɗan ƙaramar hukumar Jega ne ta jihar Kebbi. Sai dai karatun addini ya kai shi Kano, inda ya zauna tsawon shekaru, har ma ya zama ɗan gida, kuma ya yi aurensa a garin Kano. Sunan mahaifinsa na ainihi kuwa shi ne Malam Sani Abubakar. Malam Sani ya gina masallaci a unguwar Tudun Murtala da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a garin Kano. Sannan ya kasance shi ne ladanin wannan masallaci. Wannan ne ya sanya ake yi masa laƙabi da Ladan. Daga karshe wannan laƙabi ya ɓatar masa da sunansa na yanka, wato, Sani. A maimakon malam Sani, sai aka riƙa kiransa da Ladan. Mahaifin na ALA ya rasu a shekarar 1992.

Mahaifiyar ALA kuwa ‘yar asalin Kano ce. An haife ta a unguwar Rijiyar Lemu, cikakken sunanta shi ne, Hajiya Bilkisu Umma ‘Yar Sharu Adamu mai Doki na Rijiyar Lemu.Ta ɓangaren kakanninsa na wajen Uba kuwa, ya samo asali daga tsatson sarkin Gobir Gwanki. Sarkin Gobir Gwanki shi ya haifi sarkin Gobir Bawa da kuma sarkin Gobir Danbuwa.Tsatson ALA ya ci gaba ƙarƙashin sarki Dambuwa, wanda ya haifi sarkin Gobir Tambulki da kuma mijinyawa. Daga wannan gaɓa ne ta tarihi mulki ya kufce wa gidansu ALA, inda gidan sarkin Gobir Tambulki suka ci gaba da riƙa ragamar mulkin Gobir. Bisa ga wannan dalili ne ya sa aka baiwa ALA sarautar sarkin Gobir na Kano.

1.11.2 Karatunsa na Addini

Alan waƙa ya soma karatunsa na addini a ƙarƙashin malam Muhammadu Sani wanda aka fi sani da laƙabi malam Ɗan-Sakkwato. A wurin wannan malami ne ALA ya haddace izifi biyar. Bayan haka Aminu Ladan Abubakar ya yi karatun islamiya a wata makarantar smai suna, Zaharaddin Islamiya.Ya yi wannan karatu ne a karƙashin kulawar malami mai suna malam Usman Tudun Wada. Ya fara wannan Islamiya ne tun daga rabin aji, har ya kai aji shida. Daga ƙarshe kuma ya zama malami a wannan Islamiya.

1.11.3 Karatunsa na Boko

Hausawa suna cewa, ‘aikin magaji ba ya hana na magajiya’ Alan waƙa bai tsaya ga karatun addini kaɗai ba, domin ya haɗa da karatun boko. Ya fara karatun boko ne a wata makarantar Firamare mai suna, ‘Tudun Murtala Primary School’ a shekarar 1980 zuwa 1986. ALA bai yi wani dogon karatu ba saboda maraici, amma daga baya ya samu dama ya ci gaba da karatunsa na boko, inda har ya yi karatu a makarantar fasaha da sana’o;i da ƙere-ƙere a Kano.

1.11.4 Fara Wakarsa da Shahararsa

ALA ya fara waƙa ne tun lokacin da yake da shekara goma sha ɗaya (11) a duniya. A wancan lokaci malamansa na islamiya ke tsara masa waƙoki na madahu wato na yabon Manzon Allah (S. A. W.), shi kuwa ya rera. Ya rera irin waɗannan waƙoki da dama musamman a wurin mauludi ko saukar karatu ko dai wasu tarurruka makamantan haka. Waƙoƙinsa na wancan lokaci suna ɗauke ne da jigon addini, kamar faɗakarwa da ilmantarwa da yabon Annabi (SAW). A lokuta da dama akan sanya ‘yan mata su yi masa amshi. Hakan ne ya sanya karkashin waƙa ga Ala, wanda hakan ya kai shi ga fara ƙoƙarin samar da waƙoƙi nasa na kansa, mafi yawa waɗanda suka shafi yabon Annabi (SAW).

Ala ya fahimci cewa waƙa ita ce hanya mafi saurin isar da saƙo ga jamaa. Saboda haka ne ya sa ya kasance mai shaawar waƙa, inda hakan ya sa ya fara samar da waƙoƙi masu tafiya da zamani a shekara ta 2000. Bayan wannan sai Ala ya soma fitowa a kafafen yaɗa labarai a shekara ta 2003, inda aka fara jin amon waƙarsa ta Uwa Ma Ba Da Mamaa gidan radiyon Freedom da ke Kano. Sai dai kuma waƙarsa ta farko a studio ita ce, Amarya Da Ango, wadda ya buga a shekarar 2002

Waƙar farko da ya fara a duniya ita ce, ‘’Raina Fansa Ga Annabi Muhammadu Babba Ɗan Babba’’. Ya yi rubuce-rubucen waƙoƙi da dama na addini da na siyasa da na jamaa. Ya fara samar da waƙoƙin siyasa wanda ya sanya ya samu damar fara fitowa da kasusuwan waƙoƙinsa a kasuwanne.Yakan yi amfani da yan amshi mata, a mafi yawan waƙoƙinsa. ALA yakan rubuta waƙoƙinsa sannan ya rera su a studio ta hanyar amfani da kayan kiɗa na zamani.

1.11.5 Iyalansa

Alan waƙa ya zuwa lokacin da aka sami wannan bayani, yana da mata hudu da yaya goma sha biyar maza huɗu, sauran goma sha ɗaya mata ne. Yana da sha’awar ƙwallon ƙafa da tafiye-tafiye da kasuwanci. (Bayani daga Littafin da,( Yakasai da wasu, 2021) suka rubuta; Diwanin Aminu Ladan Abubakar ALA

1.12. Murtala Abdullahi Mamsa Jos

An haifi Hon. Murtala Abdullahi (MAMSAR) a Samarun Zariya jihar Kaduna a shekarar 1986. Sunan mahaifinsa Abdullahi tshon ma’aikaci a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria.

1.12.1 Karatunsa

Ya yi karatunsa na addini da na Firamare da Sakandare a nan Samarun Zariya. Shi mahauci ne sana’arsa. Bayan ya kammala karatunsa na Sakandare sai ya koma Jos da zama, inda ya ci gaba da rayuwarsa a can. Murtala bai ci gaba a neman ilimi ba, sai ya ci gaba da sana’arsa ta fawa.

1.12.2 Gwagwarmayarsa

Murtala ya shiga gwagwarmayar rayuwa inda ya cigaba da sana’arsa ta fawa da harkokin siyasa gadan-gadan. A cikin gwagwarmayarsa ta siyasa aka zaɓe shi a matsayin kansila mai wakiltar yankinsu a ƙaramar hukumar Jos ta arewa.

1.12.3 Fara waƙarsa da Shahararsa

 Murtala ya fara waƙar siyasa a shekarar 2003, lokacin da Janar Muhammadu Buhari ya fara siyasa har zuwa yau, wato a halin yanzu ya shekara ashirin da tara da komawa Jos, inda har ya yi takarar kujerar Kansila kuma ya samu nasarar cinye zaɓe.

Murtala Abdullahi Mamsar, ya yi wa Janar Muhammadu Buhari waƙoƙin siyasa da dama tun lokacin da ya fara gwagwarmayar siyasa a 2003. Ya yi masa waƙa a jamiyyar APP/ANPP, CPC har zuwa jamiyyar da ya samu nasara aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa na jamiyyar APC a 2015. Misalin waƙoƙinsa akwai:- CPC ta fito wata sabuwa ta iso, da Nijeriya muna tare da baba mai gaskiy, Janar Muhammadu Buhari ka ceci Nijeriya. Akwai, Dawo Janar zo ka sake tsayawa, Idan ka bar mu wallahi za su kashe mu, Dan ba su da tawsai. Akwai kuma; Sabuwa ta zo, APCnmu mun amince yan Nijeriya da sauransu.

1.12.4 Iyalinsa

 Murtala Abdullahi Mamsar yana da mata da ‘ya’ya biyar, ɗaya daga cikinsu Allah ya yi masa rasuwa. Daga cikin ‘ya’yansa akwai, Husna, da Zainab, da Buhari da Hafsat. A halin yanzu yana zaune a garin Jos yana ci gaba da harkokin rayuwarsa da kasuwancinsa. An sami wannan bayani a wata hira da aka yi da shi ta kafar Whatsapp a ranar 23/02/2024.

1.13. Mudassir Ƙasimu

An haifi Mudassir Ƙasimu Jibril a unguwar Kurnar Asabe, Kano a shekarar 1978. Ya tashi tare da mahaifinsa malam Ƙasimu, inda a wurinsa ne ya fara karatun addini a nan unguwar Kurnar Asabe. Daga baya sai ya koma rijiyar Lemu ya cigaba da karatunsa na addini a hannun malam Sharuf Abdulmjid da ke zaune a rijiyar Lemu. Ya karatu tare da abokansa a wurin malam Ɗanborno da malam Mukhtar da kuma malam Adinga, wanda a yanzu haka shi ne naibin limamin masallacin Abuja. Daga nan kuma sai suka koma karatu a wurin malam Usman a Kurna sannan da malam Yahuza duk a Kurnar Asabe kano. Mudassir ya yi karatun alƙuani da Tajawidi a hannun malam Ɗanlami Arze a kurnar Asabe.

1.13.1 Iliminsa na Boko

Mudassir ya shiga makarantar Firamare a 1985, inda ya kammala a 1990. Ya yi Gurgurawa Spececial Primary School a unguwar kurna, sannan ya shiga ƙaramar sakandare da ke a ƙofar ruwa inda ya shekara uku a nan. Ya karanci harkokin addini saboda kasancewar makarantar ta addini ce da harshen Larabci. Daga nan sai ya shiga makarantar S.A.S. ya shekara ɗaya,sannan ya canja salon karatunsa daga sashen addini da Larabci ya koma sashen karatun boko. Daga wannan makaranta sai Mudassir ya koma makarantar Gwamaja , inda ya kammala karatunsa na sakandare a 1997. Har wa yau Mudassir ya ciga da karatu a kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tayya da ke Kano, inda ya sami takardar shaidar karatu a fannin mulki da kula da ma’aikata. A shekarar 2008zuwa 2009 ya yi karatun aikin jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano. Bayan haka kuma ya shiga makarantar koyon harkokin shari’a Kano, a shekarar 2019 zuwa 2022.

1.13.2 Fara Waƙarsa da Shahararsa

Ya fara waƙa tun yana makarantar Firamare, inda yara da suke buga masa tebiri yana rera waƙa a duk lokacin da babu alami a cikin ajinsu. Da haka ya fara har ya cigaba da waƙoƙin gaɗa da ladabi da tsafta da karatu. Daga nan kuma sai ya fara rera waƙoƙin madahu da suka haɗa da bege da yabon Manzon Allah (S.A.W.). Ya shiga ƙungiyoyin mawaƙa daban-daban kamar babbar ƙungiyar Madinatul Ahbab da ke Kurnar Asabe. Ya kasance yana ɗaya daga cikin mawaƙan da sua shahara a waƙoƙin yabo da na mandiri a wancan lokaci. Ya zama malamin Islamiya a Nurul Adafali Islamiya da ke Kurnar Asabe Kano.

A fannin waƙoƙin fin-finai kuwa, ya fara waƙa a kamfanin Sarauniya Fim a 1998, inda da shi da yaransa suka fara waƙa mai suna, ‘Sannu-sannu halifa, jinjina muke maka, inda rai da lafiya mulkin ga kai za ka riƙa, da Ga mu cikin harka, manoma na shuka daminar ga da albarka. Duk waɗannan waƙoƙi sun yi su ne a Saraunya Fim a wancan lokaci. Daga nan sai suka fara waƙa a fina-finai inda suka rera waƙa a fim ɗin Allura da Zare mai suna, ‘Na fa duk aiki kuke’. Haka kuma ya rera waƙar a Fim ɗin Zarge, da fim ɗin Sarauniya, inda ya yi waƙar; ‘Na amince, kai za ka zan majibincin lamurina’. Sannan ya yi waƙar Kamilalla Zubaina kyakkyawa ce, ya za a yi wai in samo’. Ya cigaba da waƙoƙi kala-kala tun daga na fina-finai har zuwa na siyasa a wannan lokaci. A halin da ake ciki ya wallafa waƙoƙin madahu da na fina-finai da siyasa sun tasamma 600-800. Mudassir ya yi waƙoƙi a fannonin rayuwa daban-daban tun daga na nishaɗi da faɗakarwa da ilmantarwa da gargaɗi da makamantansu. Haka kuma ya ƙware a cikin harkokin waƙoƙin tallace-tallace a fina finai da sauran kafafen yaɗa labarai. Shi ne wanda ya fara fito da tsarin tallace-tallacen hajoji da salon waƙoƙin fina-finan Kannywood. Haka kuma shi ne ya fara amfani da kalangu da gurmi da kukuma a cikin salon waƙoƙin kannywood. Sannan shi ne, ya fara waƙoƙin da ake kira waƙoƙin haɗaka, (Remix). Ya yi waƙa a Kannywood wadda ake kira:

 ‘inda hankali da tunani ɗan riƙo ba zai kashe aure ba,

  inda lafiya a jikin kowa da arziki a gari almajiri ba zai rasa loma ba’.

 

 Wannan waƙa fitacciya ce a masanaantar Kannywood. A wannan gaɓa kuma sai Mudassir ya cigaba da waƙoƙin tallace-tallace, inda ya yi wa kamfanin jiragen sama na I.R.S. da Max Air, da Kabo Air waka. Har wa yau, ya yi wa kamfanin Maggi da kamfanin Ammasco da Boxcer da Kamfo da sauransu waƙoƙin tallata hajojinsu. Sannan ya yi aiki a gidan radiyon Freedom da ke Kano daga 2003 zuwa 2009 inda ya gabatar da shiraruwan Dandalin fin-finai, amma daga baya ya canja shiri ya koma gabatar da Dandalin siyasa.

Mawaƙin ya yi aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOS), yana rera masu waƙa da wayar da kai dangane da abin da ya shafi kiwon lafiya da haihuwa da sauransu. Mudassir ya samu kyaututtukan yabo daga kamfanoni da ƙungiyoyi daban-daban da kuma manyan makarantu daban-daban. Yana daga cikin mawakan da suka shahara wajen ƙara fito da kwarjin Muhammadu Buhari a zukatan yan Nijeriya. Bugu da ƙari yana cikin manyan jagororin da suke tafiyar da ƙungiyoyin mawaƙan Hausa, inda yake jagorantar ƙungiyar Fasaha ta mawaƙan zamani. Yana sanaoi da suka haɗa da kafofin sadarwa na zamani (Social Media) da aikin jarida.

1.13.3 Iyalansa

 Yana da matan aure biyu da ‘ya’ya shidda. Yana sha’awar harkokin siyasa da tafiye-tafiye da wasanni.

1.14 Kamilu Hussaini Adamu (Ɗan almajirin Mawaƙa)

An haifi Kamilu Hussaini Adamu a gari Ɓeta ta ƙaramar hukumar mulki ta Sumaila da ke jihar Kano a shekarar 1976. Ya yi karatun Firamare a garin Ɓeta a shekarar 1982 zuwa 1988, amma bai cigaba da karatun boko ba. Domin mahaifinsa yana sana’ar sayar da maganin gargajiya, saboda haka sai ya riƙa tafiya da shi garin Guru a jihar Yobe yana taya shi sai da magani.

1.14.1 Karatunsa na Addini

 A garin Guru ne mahaifinsa ya saka shi makarantar allo, inda ya fara karatunsa na addini.Ya yi karatu a makarantar malam Sani dogon Ƙwame inda ya sauki Alƙurani mai tsarki, ya kuma ci gaba da karatunsa na littattafan Fiƙihu a can Yobe. Ya yi karatun littattafai da dama, tun daga ƙawaidi da Ahdhari da Ishmawi da Iziya da sauransu.

1.14.2 Karatunsa na Boko

Duk da kasancewar Kamilu bai yi karatun boko mai zurfi ba, amma ya iya karatu da rubutun Hausa, da kuma magana da harshen Turanci da rubuta shi. Bayan ya karanci littattafan addini da yawa sai ya ga cewa ya dace ya koyi sana’a wadda zai iya dogaro da kansa.

1.14.3 Gwagwarmayarsa

 Kamilu ya shiga cikin gwagwarmayar rayuwa domin nema wa kansa sana’ar da zai kore wa bakinsa ƙuda.Sana’ar da ya koya har ya ƙware a kanta ita ce, sanaar ɗinkin Tela. Yana cikin wannan sana’a ce ,sai sha’awar waƙa ta zo masa a rai a dalilin sauraren rubutattun waƙoƙi da ake yi waɗanda ke ɗauke da kari mai armashi da ƙafiya. Wannan kari mai armashi da ƙafiya da yake ji a waƙoƙin Hausa ya sa masa tunanin shi ma ya fara rubuta waƙa ta ƙashin kansa domin ya fito da basirar da Allah ya yi masa a fili..

1.14.4 Fara Waƙarsa da Shahararsa

Ya fara rubuta waƙarsa ta farko wadda ya yi wa wani malami na Ahlul sunnah mai suna malam Sani Inuwa.Wannan waƙa ta samu ɗaukaka da karɓuwa a zukatan mutane, kuma ita ta fara fito da sunansa a fili. Bayan wannan waƙa ya kuma wallafa waƙoki da dama cikinsu har da waƙar da ya yi wa ministan yan Sanda na yanzu, wato, tsohon Gwamnan Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam, da wakar da ya yi wa Sumaila Bala Boni da Dila na Kamba, wani masoyinsa. Ya yi waƙoƙin siyasa da dama, inda ya waƙe jamiyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari. Waƙar da ya yi wa jamaiyyar APC ita ce, Runhu an yi furen banza akuya ba ta je dawa don shi ba, da kuma waƙar,Gafara koko tun da mun samu fura da sauransu.

1.14.5 Iyalamsa

 Kamilu yana da matan aure biyu da ‘ya’ya goma sha uku (13) maza bakwai(7) mata biyar (5).

1.15. Wane ne Muhammadu Buhari ?

An haifi Muhammadu Buhari a garin Daura ta jihar Katsina a ranar 17, ga Disamba,1942.Muhammadu Buhari ya yi karance -karancensa na boko a Katsina, sannan ya halarci kwasa-kwasan aikin soja a Kaduna Nijeriya da kuma ƙasar Burtaniya da Indiya da kuma Amuruka. Yana daga cikin sojojin da suka yi wa Yakubu Gowon juyin mulki a shekarar 1975, inda aka tura shi jihar Arewa maso Gabas (Borno) a matsayin Gwamna a wannan shekara.An naɗa shi Ministan Albarkatun Man Fetur a Gwamnatin Janar Olusegun Obasanjo. Wadda ya gada daga Janar Murtala Muhammad bayan kashe shi da aka yi a wani juyin mulkin da bai yi nasara ba a 13th ga watan Fabarairu na shekarar, 1976. Buhari ya zama sakataren majalisar ƙoli ta mulkin soja a shekarar 1977. A watan Satunba 1979 ya sake komawa a aikinsa na soja, inda ya shugabanci wani sashe (Division) na sojojin Nijeriya a Kaduna. A wannan shekara ceta 1979, aka zaɓi Alhaji Shehu Aliyu Shagari a matsayin Shugaban ƙasar farar hula a jumhuriya ta biyu. An zargi gwamnatin Shehu Shagari da cin hanci da rashawa, wanda ya haddasa sojoji suka yi masa juyin mulki; sannan aka naɗa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban ƙasa na mulkin soja ranar 31, ga Disamba, 1983.

1.15.1 Shugaban Mulkin Soja

Gwamnatin soja ta MuhammaduBuhari ta sami tsangwamar matsin lamba dangane da taɓarɓarewar tattalin arziki daya sa Buhari ya ɗauki matakin tsuke bakin aljihu. Ya ɗauki ƙwaƙƙwaran matakin hukunta ɗaruruwan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da manyan jami’an gwamnati da ke da hannu a almundahana da dukiyar al’umma. Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ƙaddamar da kwamitin yaƙi da rashin ɗa’a, shirin da ya ƙuduri dawo da martabar al’umma da darajar Nijeriya a idon duniya; ta hanyar amfani da dabarun gudanarwa a hukumance. Duk da ƙudurin daƙushe manufofinsa da wasu ‘yan Nijeriya suka yi, Buhari ya ɗauki tsattsauran matakan hana ‘yan jaridu da ‘yancin ‘yan siyasa da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu yin katsalandan ga daƙushe shirin yaƙi da rashin tarbiya daya ƙirƙiro.

Yawancin ‘yan Nijeriya sun yi maraba da wannan shiri na kawar da cin hanci da rashawa a tsakanin al’umma don farfaɗo da martabar al’umma bisa ga tsauraran matakai da gwamnatinsa ta ɗauka a kan taɓarɓarewar tattalin arziki da ci gaban ƙasa, wanda hakan ya haifar da gamsuwa da mulkin Buhari ga ‘yan Nijeriya. Buhari ya ci gaba da mulki har zuwa 1985, kwatsam sai ranar 27 ga Agusta Janar Ibrahim Babangida ya kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari ya ci gaba da mulki. An tsare Muhammadu Buhari a kurkukun Benin, inda daga bisani aka sake shi a ƙarshen shekarar 1988.

1.15.2. Shigarsa Gwagwarmayar Siyasa

Muhammadu Buhari ya shiga harkokin siyasa tun a shekarar 2003, inda ya tsaya takarar kujerar shugabancin ƙasa aƙarƙashin inuwar jam’iyyar APP, amma bai sami nasarar cin zaɓe ba.Ya sha kaye daga Olusegun Obasanjo na jam’iyyar PDP wanda ya sake haye kujerar mulki a karo na biyu. A shekarar 2007, Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takara, a nan ma bai yi nasara ba, inda ɗan takarar jam’iyyar PDP, Umar Musa ‘Yar aduwa ya ka da shi a zaɓen da masu sa ido na ƙasa-da-ƙasa suka ce, an tabka maguɗi. Har wa yau, Buhari, ya sake tsayawa takara a 2011, nan ma ya sha kaye a hannun Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP a zaɓen da aka ce an kamanta adalci. Duk gwagwarmayar da ya yi bai sami nasara ba, wannan bai karya zuciyarsa ba ga ƙudurinsa na tsayawa takarar shugabancin ƙasa.

1.15.3 Laƙabin Gaskiya Dokin Ƙarfe.

Tsare gaskiya da riƙon amana da Muhammadu Buhari ya nuna a lokuta daban-daban da ya riƙa muƙamai, (bai yi sata ba ko ha’inci da dukiyar al’umma ba); ya sa ake yi masa laƙabi da “gaskiya dokin ƙarfe”.Wannan laƙabi ya ƙara wa Muhammadu Buhari kwarjini da daraja ƙari ga wanda yake da shi na halitta a idon ‘yan Nijeriya, har Jam’iyyar gamayya ta APC ta tsayar da shi, ya yi takarar kujerar shugaban ƙasa a 2015. Saboda gaskiyarsa da riƙon amana da ya nuna a muƙamai daban- daban da ya taɓa riƙawa a lokacin da ya yi mulkin soja, da ministan man fetur, da kuma shugaban asusun amintattu na rarar man fetur a 1995, (lokacin mulkin Janar Sani Abacha); ya sa mutane suke ɗokin ya yi shugaban ƙasa don ya ceto Nijeriya daga mawuyacin halin da aka jefa ta cikinsa. Wannan laƙabi na gaskiya dokin ƙarfe ya sanya mawaƙa da dama suka yunƙara wajen tallata Muhammadu Buhari ga alumma domin su amince su zaɓe shi ya shugabanci jama’a don ya kawar da azzaluman shugabannin Nijeriya, ya kafa mulkin adalci. Duk da haka Buhari bai ci zaɓe ba saboda wasu manyan ‘yan siyasa da masu faɗa-a ji ba su ra;ayin ya kafa gwamnati. Domin idan ya kafa gwamnati zai zaƙulo duk wani azzalumi da ya saci dukiyar alummar ƙasa ya hukunta shi.

1.16 Ra’in Bincike

An gina wannan bincike a bisa mazhabar yabo da kushewa (‘Epedeitic Theory’) ta masanin Falsafar nan ɗan ƙasar Girka,wato Aristotle’ wadda ta yi daidai da zuga da habaici wajen yabon kyawawan halaye da ɗabi’u na ɗan Adam domin a kwarzanta shi ya aikata abubuwan alheri, da kuma kushe masu ɗabi’u da halaye marasa kyau don a jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da ake isarwa gare su.Leech (1968) da Muktar (2005) da Lawal (1997) da Gusau () da Abdurrahman Ado (), sun yi rubuce-rubuce da ke nuna goyon baya ga yi amfani mazahaba wajen ɗora kowane irin nazari da za a gudanar. Domin ta hanyar salo ne ake isar da saƙo ya shiga jikin masu sauraro. Mawaƙan siyasa suna amfani da salon zuga da habaici domin su jawo hankalin masu saurare su fahimci saƙon da ake isarwa gare su. Saboda haka mawakan da suka yi wa Muhammadu Buhari waƙa sun yi amfani da wannan salon jawo hankali na zuga da habaici domin su yaba kyawawan halaye da ɗabi’unsa tare da ƙara masa kwarjini bisa ga wanda yake da shi tun asali domin mutane su ƙara son shi a zukatansu. Har wa yau, sun yi amfani da habaici domin su naƙasa ko tozarta yan adawa da maƙiyan Muhammadu Buhari a idon alumma.

Idan aka koma wajen adabi kuwa, sai aka sami cewa, abubuwan da ke ci ma al’umma tuwo-a ƙwarya su ne irin rikice-rikice dangane a yadda mahukunta suke wawure arzikin ƙasa su mayar da nasu. Da yadda talakawa suke ɗanɗana azaba a hannun waɗannan ‘yan tsirarun mutane. A irin wannan adabin, marubuci zai yi amfani da falsafar yabo da kushewa domin ya nuna yadda tlakawa suka jajirce wajen nema wa kansu ‘yanci daga ƙangin bautar da mahukunta suka jefa su ciki. Wannan dalili ne ya sa mawaƙan siyasa na Muhammadu Buhari suka dage wajen amfani da zuga da habaici domin su jawo hankalin alumma su zaɓi wanda ke da manufofi da kyawwan ɗabi’u a lokacin zaɓe. A taƙaice dai Leech (1968), ya goyi bayan wannan ra’i, na yabo da kushe ɗabi’u masu kyau da marasa kyau, inda ya nuna cewa, amfani da salon yabo da kushewa a cikin waƙa kan sanya waƙa ta yi armashi har ta iya jawo hankalin mai saurare ya fahimci saƙon da ake isarwa gare shi cikin sauƙi, kuma ta sanya mawaƙi ya yi fice. Haka kuma a ɓangaren talakawa su fahimci cewa, tabbatuwar samun zaman lafiya da walwala da cigaban tattalin arziki ya ta’allaƙa ne a kan zaɓen shugabanni masu gaskiya da riƙon amana. Muktar (2005), ya bayyana cewa, salo shi ne waƙa; don haka ne ya yi nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa na masu jihadi a kan rain yabo da kushewa domin jawo hankalin masu saurare su tuna da abubuwan da suka faru a baya da kuma waɗanda za su faru a gaba.

Da aka koma wajen adabi kuwa, sai aka sami cewa, abubuwan da ke ci ma al’umma tuwo- a- ƙwaryi shi ne irin rikice-rikice dangane da yadda mahukunta suke wawure arzikin ƙasa su mayar nasu. Da yadda talakawa suke ɗanɗana azaba a hannun waɗannan‘yan tsirarun mutane. A irin wannan adabin, marubuci zai yi amfani da falsafar yabo da kushewa domin ya nuna yadda talakawa suka jajirce wajen nema wa kansu ‘yanci daga ƙangin bautar da mahukunta suka jefa su ciki. Wannan dalili ne ya sa mawaƙan siyasa na Muhammadu Buhari suka dage wajen amfani da zuga da habaici domin su jawo hankalin alumma su zaɓi wanda ke da manufofi da kyawawan ɗabi’u a lokacin zaɓe. A taƙaice dai, Leech (1968), yana ganin dole adabi ya san yadda zai yi, ya sauya al’umma ko da ta hanyar farfaganda ce.

Masu wannan ra’in sun ƙara da cewa, sa-in-sa tsakanin masu hali ko masu mulki (the bourgeois) da kuma talakawa ko marasa hali (feudal overlords). Gwagwarmaya ce tsakanin masu mulki ko masu hali saboda morewa da suke yi sakamakon matsayinsu, da kuma marasa hali ko mulki saboda irin matsin da suke ciki sakamakon yanayin da suka sami kansu a ciki. (Wilmot eds p 204) yana cewa, wanda yake kan mulki a kullum yana ƙoƙarin ya ci gaba da zama a kan mulki. Shi kuma wanda ake mulka da yake ƙasa yana neman mafita a game da halin matsi da ƙuntatawa da yake ciki a wurin masu mulki. Irin wannan gwagwarmaya a hankali takan zama juyin-juya- hali (Wilmot eds Pp 292).

Lee T. Lemon da Marion J. Reis (1965) suka ce, harshen fasaha a cikin adabi ba kamar harshen maganar yau da kullum yake ba, harshe ne da yake ɗauke da ƙa’idoji da manufofi masu tasiri wajen isar da saƙo.Domin haka ne mawaƙan Hausa, musamman na siyasa suke amfani da salon zuga da habaicin a cikin waƙoƙinsu domin su jawo hankalin masu saurare su canza duniya ta koma tamkar sabuwa ga al’umma ta zama kamar lokacin mutane suka fara rayuwa a cikinta ta hanyar zaɓen mutane masu kyawawan halaye da ɗabi’u nagari.

1.17. Naɗewa

Babin ya yi bayani filla – filla, yadda binciken zai kasance a sharar fage..An fito da manufar bincike da dalilin bincike da tambayoyin bincike da muhimmancin bincike da farfajiyar bincike da hujjar ci gaba da bincike da hanyoyin gudanar da bincike da kuma ra’in da aka ɗora binciken a kai.

Ahmadu Bello University Zariya

Post a Comment

0 Comments