Ticker

6/recent/ticker-posts

FULENGHAUSAR: Ƙasidar Fulatanci Da Turanci Da Larabci Da Hausa

Daga:
Abdullahi Abubakar Lamido (Amir)

Mu ambaci Rabbana Sarki da fari 
Because Allahu shi ke kare sharri
From Him ne gaba ɗaya kullu khairin 
Ashe wajib muke godewa Rabba 

Ta'ala God Tabaraka Jaumiraawo 
The one who did halittar bandiraawo 
Ya wo shurɗiyyu mai kamo ɓarawo 
Alal arshistawa bai haifi ɗa ba 

Ilahi shi ya ƙago kulla niɗɗo
Ya ƙagi babarbare ya yiwo shi kaɗo 
Waninmu yana follower wani ko Lamɗo 
A power tai ba za ka ga laulayi ba

Salatina to khairul mursalina
Muhammad Role model ɗin muttaqina
The best person among duka alamina 
Ba ai bawa kamar Al-Mustapha ba 

Rasululahi Khairul Alamina 
Nabiyyullah Imamul Mursalina 
Habibullah Amirul muttaqina 
Ba ai tamkarsa mai kyawun hali ba 

Masoyin Rabbi mai kyawun halitta 
The Messenger da ke da halin bajinta 
Kamaaai babu mai tsantsar nagarta 
Ba ai tamkarsa gun bin gaskiya ba

Ba zan manta da manyan jarumai ba 
Na Khairul qarni ma'ana dai sahaba 
The best people da ke bauta wa Rabba 
Waɗanda ba za a kai su a tarbiya ba 

Sahabbai ka ji soldiers ɗin Rasulu 
Da Ahlul baiti 'yan gatan Jamilu 
The most eloquent wajen iya tsara ƙaulu 
Da ɗai mai sonku bai ɓata ko kaɗan ba 

Taho ga yar ƙasida za ni tsara 
Cikin four languages ne za ni jera 
Fulatanci da Arabic su na fara 
Da Hausa da English ban bar su sam ba  

The reason for rubuto wanga baiti 
Nasiha ce ga yan birni da City 
Ina so kuma na yi ta bi kulli beauty 
Nufi na ba yabo ko tsokana ba 

Ina so ne na ɗan mana yar preaching 
Da ɗan saƙon da zai mana inspiration 
Na ƙarfafi 'yan uwa na yi motivation 

Bi hablillahi wa'tasimu jami'a
Mu bar tafriq mu ɗau tsarin Shari'a 
Mu tattauna cikin ladabi da ɗa'a 
Da ɗai enemies ba sa iya ka da mu ba 

Nufina ne haɗin kan bandiraaɓe 
Mu dunƙule kai dukanmu maza da rouɓe 
Fulani ɗin cikinmu da su da haaɓe 
Haɗin kai dole ne ba nafila ba 

Haɗin-kai is a most a gare mu Julɓe 
Da kanurai da Hausawa da Fulɓe 
Na Lagos har Ebonyi da Jos da Yobe 
Mu ƙaunaci 'yan uwanmu mu kore gaba 

A yau duk al'uma ta ɗau demotion  
Da confusion da lack of calculation 
A ko ta ina mutane sai corruption
Kamar ba al'umar Al-Mustafa ba 

Gaba ɗaya mun yi rauni babu izza
Mutum burinsa rushewar brother 
Ya how TikTok ya zagi uwa da father 
Kamar bai san akwai wata tarbiya ba 

A yau jama'armu ta koma demotion  
Da confusion da lack of calculation 
A ko ta ina mutane sai corruption

The people of ƙasar nan duk ku gane 
Ƙasar nan fa Balad mai arziƙi ne 
Amma if yan ƙasa azzalumai ne 
Ƙasar ba za ta zam miƙaƙiya ba

Akwai oil da gold a cikin ƙasarmu 
Da iron ore da timber ba kamarmu 
Ƙasar noma ko mai faɗi gare mu 
Ta ko ta ina ba ai tamkarmu sam ba 

Wuya ta kama dukkan population
Farashi sau hawa sai inflation 
Talauci yai yawa ba alleviation 
Kamar ba mu da ke da kuɗin shiga ba 

Tuni an rusa health da transportation
Gaba ɗaya an taɓarɓara education 
A yau ba tallafi sai inflation 
Talakkawa ba ai musu taimako ba 

Ku ɗau yanayi na teachers ɗin kasarmu 
Da dukka ma'aikata na ma'aikatunmu 
Talauci ya ragargaza malamanmu 
Kamar su ba mutane 'yan ƙasa ba 

Rawatib ɗinsu la yusmin gare su 
Wala yugni bare su riƙe gidansu 
Ala tilas kawai haka anka bar su 
Wala mafita ba sa iya ƙorafi ba 

Batun minimum wages tilas a ƙara 
Batun su na welfare shi ma a gyara 
Idan an taimake su fa ba asara
Ba za mu yi ɗaukaka ba malamai ba 

Mu'allim wajibinmu mu taimake shi 
Bi tauqirin wa tabjilin gare shi 
Mu ba shi support mu ƙarfafi zuciyarshi 
Ba ai darajar ba bisa illimi ba

Post a Comment

0 Comments