Manazarta: Sani, A-U. & Bazango, A.M. (2025). Ƙabarin Burina. A cikin Sabe, B.A., Aliyu, A., Nasudan, Y.A. & Sa’idu, K. (editoci). BURINA: Labarun da Suka Samu Nasara a Gasar Arc. Ahmed Musa Dangiwa, 2024, 1-12. Kangiwa Multimedia and Communication Ltd. ISBN: 9789789875504
Ƙabarin Burina
Abu-Ubaida
Sani
Email:
abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
WhatsApp:
+2348133529736
Da
A’ishatu
Muhammad Bazango
Email: humairau2003@gmail.com
“Sunan wani abu, ƙwarangwal!” Budurwar ta faɗa wa ƙawarta
cikin murya ƙasa-ƙasa. Suka kalli juna cikin dariya sannan suka tafa. Ban sake
komawa ta kansu ba, don hakan ya riga ya zame mini jiki. To wane dare ne jemage
bai gani ba? Ko ba komai ai gaskiya suka faɗa, wai ga zahiri yara sun ga ɗan
kaciya. Na dace tsaf da duk wani yanken Hausawa; wuya kamar mariƙin lema, ƙafa
kamar sandar sabulu... Don an kira ni ƙwarangwal, ko a jikina wai an tsikari
kakkausa.
Na yi ajiyar zuciya yayin da na ci gaba da tunkarar ɗakin
taron. Ina tafe falau-falau tamkar iskar hadarin da ke kaɗawa za ta ɗauke ni
saboda rama da rashin ƙarfi. Abin takaicin kawai a gare ni shi ne, al’umma ta
kasa koyon kyawawan ɗabi’un ƙarfafa guiwa ga waɗanda ke cikin takunkumin ƙuncin
rayuwa. A maimakon dafa musu domin cimma burukansu, sai kyara da wariya waɗanda
suke ƙara wa gyambo gishiri. An watsar da koyarwar Manzo (SAW) da ke cewa “kyakkyawan
zance ma sadaka ce!” A zuciyata nakan ce, da zan samu dama, duk wanda zan haɗu
da shi, ko dai in zama alƙalamin rubuta nasarorin cimma burukansa, ko kuma in
zama ruwan wanke allon damuwoyinsa.
Wanda ya tuna bara bai ji daɗin bana ba! Tun lokacin da karana
bai kai tsaiko ba, a lokacin yarinta,
burukana shiririta ne kawai ga majiyan labaransu. ‘Ina ma a ce zan iya tashi sama in tafi
cikin wata... Da ma a ce in tara kuɗi dubu malala gashin tinkiya...’ Allah
Sarki, jiya ba yau ba! Wannan tun kusan shekaru 19 ke nan da suka gabata,
lokacin ban fi ‘yar shekara 5 ba. Na kasance kyakkyawa, cika
masakinta, mai dogon gashi da har ake yi mini kirari da anti-yalalash a
maimakon asalin sunana Naila.
Na taso mai ilimi da basirar da na zarce na sa’o’ina.
Bugu da ƙari, na kasance mai tsananin buruka da akan jira in ambata domin a yi
dariya. Abin takaici, sun manta cewa da sannu jirgin sama ma ke tashi. Sun kasa
fahimtar cewa, a waɗancan shekaru iya ƙololuwar basirar da yaro zai iya nunawa
ke nan. Abin da ake so kuwa shi ne a ƙarfafa shi, a saita masa tunane-tunane da
burukansa domin ya ƙara kaifin basira da himma. Kushe da tsangwama kuwa, ba
abin da za su haifar masa sai tauyewar hikima da fargabar yin kuskure. To, a
yanzu kam sai dai a ce an bar kyau tun ran haihuwa.
Gidanmu na masu matsakaicin ƙarfi ne. Ina tuna mahaifina
kan ce: “Duk da hannunmu bai cuɗi bayanmu ba, Allah ya sa mun fi ƙarfin sutura
da abin sakawa bakin salati.” Ni kaɗai ce ‘ya a wurin mahaifiyata marigayiya.
Matar babana kuwa, wato Umma Adama, tana da ‘ya’ya uku; Sagir wanda ya kasance
sa’ana, sai Rabi da Aliyu. Mahaifinmu Malam Musa ya daɗe yana fama da ciwon
hawan jini.
Wata rana a shekarar 2010 mahaifinmu ya shigo gida
fuskarsa a murtuƙe. Ina jiyo muryarsa a ɗaki yana yi wa Umma Adama ƙorafin abin
da ya faru: “Ni da su Malam Mahdi ne mana. Allah wadaran naka ya lalace! Wai
shi Bahaushe ba zai taɓa wayewa ba don samun cigaba? Duk abin da ya gani na
kimiyya mai ban al’ajabi kawai tsafi ne ko shirin fim? Ba mu ko yarda da
fasahar zamani ba, ballantana a samu ‘ya’yanmu sun rungume ta don gogayya da
al’ummu da suka ci gaba?”
Umma Adama ta ba shi baki. Bayan ya sauƙo ne na tsinci
wasu daga cikin bayanan da ya mata. Ashe jayayya ce ta haɗa shi da abokansa
yayin da suke cin abincin dare. Ya kawo musu labarin cewa, nan da wani lokaci
saƙago za su maye gurbin mutane a wurin ayyuka. Za su iya noma da tuƙa ababan
hawa da koyarwa a makarantu da sauransu. Abokan suka bushe da dariya sannan ɗaya
daga cikinsu ya cire hularsa ya ajiye a bayan mahaifin namu yana faɗin: “Na yi
masa waiji. Malam Musa ya shiga santi.”
Washegarin ranar na je ɓangaren sakandare a makarantarmu
na iske Uncle Kwamfuta, wani mai bautar ƙasa da ya zo daga Kaduna. Na
tambaye shi: “Malam wai mene ne saƙago? Wai nan gaba zai iya aiki irin na
mutane?” A nan ya feɗe mini biri har wutsiya cewa, shi saƙago da Ingilishi robot
ake ce masa. Ilimin da ake magana a kansa kuma na ƙirƙirarriyar basira, wai
Artificial Intelligence amma an fi cewa AI. “Uncle akwai
littafin AI ɗin a laburare? Ina son in karanta kuma in kai wa babana.”
Na tambaya cikin zumuɗi.
Ya yi ‘yar dariya sannan ya tambaya: “Kika ce sunanki Naila
ko? Ai wannan fannin ilimi a ƙasar nan sai a matakin jami’a ne ake taɓo shi. A manyan
ƙasashen, an fara koyar da shi tun a shekarar 1956 bayan wani taro da aka yi a
wata makaranta da ake kira Dartmouth College. A nan masana irinsu John
McCarthy da Marvin Minsky suka tattauna yadda AI zai iya ayyuka irin na
mutane...” Na tafi cikin tunani da alwashin zuci cewa sai na ga abin da ya ture
wa buzu naɗi game da ilimin wannan AI ɗin.
A makaranta ajinmu ɗaya da Sagir wanda Allah bai huwace wa
hazaƙar ɗaukar karatu ba, tamkar dai ana shiƙar wake a bayan kifaffiyar ƙwarya.
Ni kullum na ɗaya nake yi. Shi kuwa, sau guda ne ma ya taɓa yin na 20. Ga bisa
dukkan alamu, tsangwamar da mahaifinmu Malam Musa yake yi masa, ita ta fara
wanzar da ƙiyayya tsakanina da shi da kuma mahaifiyarsa Umma Adama. “Ban da
lalacewa wai har mace ta fi ka ƙwazo a aji...?” Kalaman mahaifinmu ke nan da ya
fi ƙona musu rai.
Sagir
yakan ɓata rai na tsawon wani lokaci, daga nan kuma sai ya tattari kayan
jone-jonensa ya shiga harkar da ya saba. Duk da ba ya ƙoƙari a makaranta, Allah
ya zuba masa basirar gyara kayayyakin wuta. A unguwarmu har sunansa ya koma Sarkin
Jone-Jone. Duk ɗakunan gidanmu ya sanya abin da yake kira wayarin. Da
siraran wayoyi ya yi amfani tare da ƙananan ƙoyayen wuta da ya cire daga jiki
tsofaffin tociloli. Faya-fayen solar tocilolin kuwa ya ɗora su a saman rufin ɗaki.
Da dare gidan haske tal ko da babu wutar lantanki.
Na
ƙara darajanta wayarin ɗin Sagir lokacin da wani baƙo abokin mahaifinmu
ya zo daga Sakkwato. A ranar ya sanya mahaifinmu gaba: “Haba Malam Musa, ina
hikimakka tat tahi! Yanzu wanga yaro na kaka kira sakare? Shin kai kana iya waɗanga
jone-jone da yay yi? Bambancinsu guda na da Naila. Ita basiratta karatu taz zaɓa,
shi kuma basiratai ƙere-ƙere yaz zaɓa. Ai da ma ba a taru anka zama guda ba.
Abincin wani gubaw wani!” Ya yi ƙwafa sannan ya ci gaba: “Gargaɗi nikai ma
wallah. Idan kat tauye mai gurinai, kuna biyu babu, kamun gahiyar Ɓaidu. Halan
ba ka tallafa mai har Allah ya gwada muku ya zama wata tciya a wagga hwanni? To
walla bone ya duƙa ka ɗare bayanai!” Lallai shi mahaifinmu ya ƙwallafa burin
karatun fasahar zamani a kan Sagir a matsayinsa na babban ɗansa.
Na daɗe
ban ga ranar da mahaifinmu ya mayar da dukkannin hankalinsa a kaina ba kamar
lokacin da na sanar da shi cewa fannin da nake so in ƙware shi ne AI da
kuɗin intanet. Wannan ya faru a shekarar 2012. A lokacin ina aji 6 a firamare.
“Kuɗin
intanet, kina nufin cryptocurrency?” Ya tambaya cikin tsagwaron mamaki
da zumuɗi. Na bayyana masa duk ire-iren tattaunawar da muka yi ta yi da Uncle
Kwamfuta. Na ce ai ya faɗa mini cewa, duk waɗannan sababbin fagen ilimi ne waɗanda
Hausawa ba su mayar da hankali kansu ba. Har ma ya nuna damuwarsa cewa, nan
gaba al’ummun da aka bar su a baya a waɗannan fannoni biyu za su kuka da kansu
domin arzikin duniya zai koma hannayen waɗanda suka taka datacciyar rawar kiɗan
zamani. Na zayyano masa nau’ukan kuɗaɗen intanet da na rubuta a bangon
littafina, wato Bitcoin da aka yi a 2009, sai kuma Litecoin,
Namecoin, da Peercoin. Na faɗa wa mahaifinmu cewa, ni ma ina son in
yi kuɗin intanet ɗina tun da Uncle Kwamfuta ya ce ya zuwa yanzu, waɗanda
ake da su ba su kai ashirin ba. Kafin shekarar 2020 kuwa, za su iya haura guda dubu.
Mahaifina
sai da ya rungume ni don farin ciki, yana faɗin: “Kanya ta nuna biri ya karye.
Mu lokacinmu babu waɗannan abubuwa. Ga shi yanzu ba makaranta zan koma ba ballantana
a yi goyayyar zamani da ni. Allah ya kawo mini mai share mini hawaye.”
Can
kuma sai na ga jikinsa ya yi sanyi. Cikin zulumi da alamun karaya ya ce: “Fatana
Allah ya mini tsawon ran da zan ga cikar burina. Ke mace ce. Ƙalubalen da mata
ke fuskanta a gwagwarmayar cimma buri daban yake.”
Allah
Sarki! Burinsa bai cika ba. Bayan makwanni uku da wannan maganar ya koma ga
Ubangiji. Na yi kuka mai tsanani da ya sanya mini zazzafan ciwon kai. Na rasa
gatana. Gani nake yi tamkar ya rasu ne tare da dukkannin burukana. Kalaman da
yake gwaɗa ni da su, suna je-ka-ka-dawo a ƙwaƙwalwata: “Naila Anti-Yalalash mai
kuɗin intanet”
Na
samu kyaututtuka masu yawa a ranar walimarmu ta kammala firamare. Murnata ta
koma ciki da kalaman Umma Adama: “Karatun mace ai a yi ne kawai. Yanzu kam sai
dai fatan miji nagari.” Na yi shiru cikin takaici. To me zan ce, wai gari duk
dangin kishiya?
“Marainiya
amanar Allah, ba zan taɓa bari ta shiga wani garari da zai sangartar da ita
ba.” Da kalaman nan na Umma Adama, Baffa Umaru ƙanin babanmu ya yarda in ci
gaba da zama a wurinta. Ya ci gaba da ɗaukar takalihun gidan tare da taimakon
sauran ‘yan’uwa.
Na kasance
cikin tsananin ƙunci da damuwa. Na ji na tsani duniya da duk halittun da ke
cikinta. Ɗan abin da ke saka ni farin ciki kawai shi ne idan wani baƙo na jiki
ya zo wanda zan iya karɓar babbar wayarsa in hau intanet. Kullum kalaman Umma
Adama su ne: “Duniyar nan dambu ce, ba a mata cin haɗama. Kada ki bari zulumi
da burukan banza su halaka ki.”
Ba a
jima ba na kamu da ciwon ƙirji mai tsanani. Na sha jiƙe-jiƙen sassaƙe-sassaƙe
da saiwowi. Daga masu cewa shafar iska ne, sai masu cewa jifa aka mini. Hakan
ne ma ya sa tun da Umma Adama ta kai ni asibiti sau ɗaya aka rubuta mini
magunguna, ba ta sake mayar da ni ba.
Kwatsam
wata rana da hantsi sai ga shugaban makarantarmu da waɗansu baƙi su uku daga
babban birnin jaha sun zo gidanmu. Ashe ɗalibai biyu ake so, haziƙan marayu domin
a tafi da su makarantar sakandare ta kwana a babban birnin. Babu yadda Umma
Adama ba ta yi ba don kada a tafi da ni. Ta yi ta jaddada cewa: “Marainiya tana
kwance rai a hannun Allah, ina maganar makarantar boko?” Zakarar da Allah ya
nufa da cara..., Azahar ba ta yi ba, sai da aka sa na yi wanka, aka zarce da ni
asibitin birni. Baffa Umaru ne ya sanya hannu kan takardar da suka zo da ita
bayan sun ba wa Umma Adama baki.
“Depression!” likitan ya furta. Ya ƙara
da cewa, za ta iya yiwuwa ina da bipolar, amma ba za a yanke wannan
hukunci ba sai an ga abin da ya biyo baya. Ina tuna yana cewa, depression shi
ne matsanancin damuwa da ka iya zama cuta. Ya ce masu bipolar sun fi
fama da irin wannan matsala musamman yayin da suka kasa cimma burinsu.
Ya
fuskance ni sosai: “Idan mutum yana da bipolar, matakin farin ciki ko
damuwa da yake shiga yakan yi yawa sosai, nesa da na waɗanda ba su da wannan
matsalar. Yawancin masu fama da bipolar, za ki tarar mutane ne zaƙaƙurai
masu kaifin basira da ɗumbin buruka a rayuwa. Sau tari sun yi wa tsaransu
zarra. Shi ya sa sau da dama ake yanke hukuncin cewa sa hannun maƙiya ne.”
Daga ƙarshe
dai ya ba ni waɗansu ‘yan magunguna da zan sha. Ya ce a yanzu ba ya son ɗora ni
a kan maganin bipolar waɗanda ya ambata da suna Amitriptlline da Olanzapine.
Ya sanar da ni matakai da zan iya ɗauka domin taƙaita damuwa a kaina. Sun haɗa
da guje wa duk wani abin da zai ɓata mini rai; da ƙoƙarin cire damuwa a kaina
ta hanyar bin matakan tattaunawa da wasu; da haƙura da duk wani burin da na san
ba zan iya cimmawa ba; da kauce wa zaman kaɗaici...
***
Zamana
a makarantar sakandare ta marayu ya ɗan sauya mini rayuwa. Ba na ko sha’awar in
tuna garinmu. Cikin watanni kaɗan na yi ƙiba, na yi kyau. Na ci gaba da
karance-karance a ƙoƙarina na tara ilimi kan AI da kirifto. Na auri
laburaren kwamfutar makarantar. Da muka saba da mai kula da kwamfutocin wato ICT
Master, har kujera ta musaman ya ajiye mini. ‘Yan ajinmu sukan zolaye ni da:
“Ta gidan ICT Master.”
Wani
lokaci nakan hau intanet domin binciko damarmakin da ake da su na samun
tallafin tafiya ƙarin karatun gaba da
sakandare. Ko na samu damar, da amincewar wa zan tafi? A jikina ina jin cewa
damuwa za ta iya halaka ni idan karatuna ya tsaya.
Malamai
suna mamakin yadda nake ƙoƙari a dukkannin darussa duk da cewa koyaushe ina
jikin kwamfuta kamar shazumami da zuma. Ni kuwa na san sirrin shi ne cimma buri
na saka a gaba, bakin rai bakin fama. Muna aji biyar na ciyo na ɗaya yayin da
na wakilci makarantar a wata gasa mai suna Young Innovators, wai matasa
masu fasahar ƙirƙira. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa aka ba ni
matsayin shugabar ɗalibai wato head girl yayin da muka shiga aji shida.
Ana
gobe za a yi walimar kammala karatunmu, shugabar makarantar wacce muke kira
Mummy ta sanar da ni a keɓance cewa: “Gobe muna da baƙo mai suna Dakta Ahmad. Zaƙaƙuri
ne lamba ta ɗaya. A harkar kwamfuta da intanet ya ƙware, amma fannin kutse da
ba da tsaro...” “Kina nufin Hacking...” Na tari numfashinta. “Na san kin
sani madam kwamfuta.” Ta faɗa cikin raha sannan ta ci gaba: “Shekara 11
ke nan da ya kammala nan, amma tuni ya zama mutum. Yanzu haka ya yi alƙawarin ɗaukar
nauyin ɗalibai 10 don tafiya jami’a. Dole kina daga ciki.”
Ni da
shugaban ɗalibai maza wato Head Boy ne kaɗai muke da kujeru a sama, kusa
da malamai da manyan baƙi. Na ji takaicin cewa a daidai lokacin fara jawabin
Ahmad, wani uzuri ya fitar da ni. Na dawo daidai inda yake cewa: “... Wasu
burukansu sun mutu sakamakon talauci, wasu kuwa cuta ko haɗari, wasu al’umma ce
ta kashe musu guiwa, wasu kuwa yanayin zaluncin shugabanni a matakai
daban-daban ne ke yin tasiri a kansu... Ina so ku san cewa, ƙalubale bai kamata
ya zama sanadiyyar mutuwar buri ba.
Abin da ya kamata shi ne sake shiri da tunkarar rayuwa. Idan laila ta ƙiya a
koma basha. A cire kasala, a sanya himma, a jajirce, sannan a bi da addu’a da
kyautatawa...”
Duk
da kunnuwana sun ci gaba da jin sautin maganganunsa, ƙwaƙwalwata tuni ta daina
fassara su zuwa kalamai masu ma’ana sakamakon ziyarar bazata da ta kai duniyar
tunani. Tafin da wurin ya kaure da shi, shi ne ya dawo da ni cikin hayyacina
yayin da Dakta Ahmad ke ƙoƙarin komawa kujerarsa.
Kamar
dai yadda Mummy ta faɗa, ni ne na farko a cikin jerin sunayen waɗanda Ahmad ya ɗauki
nauyinsu zuwa jami’a. Mu 6 ne mata, sai 4 maza. Kwas ɗin da na cika kuma aka ba
ni shi ne Computer Engineering, wato ilimin sarrafa kwamfuta. Wohoho, ai kura ta yi
sabon takalmi, jeji ya shiga uku. Na duƙufa da karatu ba kama hannun yaro.
A
makarantar nan, ko masu iyaye ba su kai ni gata ba. Ko bayan isassun kuɗaɗe da
Dakta Ahmad yake turo mana a kowane
wata, ni kulawa ta musamman yake ba ni. Yakan ce mini yana jin daɗin tattaunawa
da ni ne saboda yana tsintar ilimummuka tattare da ni. Ya ce na yi daban da
sauran mata ta fuskar hazaƙa da ƙoƙarin cimma buri. “Mata sai a hankali! Da
yawa daga cikinsu ba su da buri a rayuwa in ban da auren attajiri. Da ka yi faɗa
a ce maka wai su ƙashin haƙarƙari ne, a tanƙware suke.” Wata rana ya faɗi haka
cikin raha.
A
shekarata ta ƙarshe a jami’a ne abubuwa suka juye mini. Wata rana wasu samari
biyu suka neme ni da fasiƙanci. Kalamansu sun ɗaga mini hankali cewa ai suna
sane da ni kawaliyar Ahmad ce. Kuma da ma shi ɗan hannu ne. Har ma suka nuna
mini hotona da na Dakta Ahmad zaune a cikin mota.
Cikin
kuka na bar wurin. Zuciyata ta dugunzuma. Na shiga wani tashin hankali da ruɗanin
da ban taɓa shiga irinsa ba. “Irin ƙalubalen da mahaifina ke nufi ke nan? Shin
gaskiya ne haka Ahmad yake? Idan ba gaskiya ba ne ma, ke nan kowa wannan kallon
yake mini?” Ban yi nisa ba wayata ta yi ƙara. Na ɗauko ta daga jaka. Ahmad ne
ke kira na. Na katse wayarsa a karo na farko a rayuwata. Ba a yi mintuna uku ba
sai ga shi ya biyo da saƙon SMS. Ban bi ta kan saƙon ba, sai ma na kashe
wayar na cire batirinta.
Ban
ko biya ta hostel kan kayana ba. Na kama hanyar tashar mota. Dare bai yi
ba sai da na bar garin. Bayan ya da zango da na yi na kwana a tashar Kabuga,
ban sake ya da zango ba sai a Amanawa, wani gari da yake kan iyakar ƙasa.
Mahaifina ya taɓa sanar da ni cewa, wan mahaifiyata limamin wani masallacin
Juma’a ne a garin.
Ban
sha wahalar samun gidansa da yake matambayi ba ya ɓata. Duk da ya tsufa matuƙa,
da gani babu tambaya jinin mahaifiyata ne, don sun yi kama matuƙa da hotunanta
da nake da su. Ya zubar da ƙwalla sosai da jin labaraina.
Na
tuna da maganar likita game da mancewa da burukan da mutum ba zai iya cimmawa
ba don samun sukunin zuci. A ƙasan gadon ɗakin da liman ya sa aka ba ni, na
toni wani rami. Na sanya jakata da walet da wayata a wata leda gari-ya-yi-zafi,
sannan na sanya cikin ramin. Na mayar da ƙasa na rufe da sunan shi ne ƙabarin burina. Na raya cewa, zan rayu
in mutu kawai ba tare da na ga cikar burina ba, tamkar dai mahaifinmu. Maganar
likita ba ta yi mini aiki ba domin kuwa hakan bai rage mini komai daga wutar
ƙuncin da kullum ke ƙara ruruwa a birnin zuciyata ba. Na kama rama kamar kazar
mayu. Liman ya yi ta ba ni ruwan addu’o’i ina sha.
Wata
rana a wayar Aliyu, ɗaya daga cikin ‘ya’yan liman, na jiyo ana shelanta gasar
tsara manhaja. Na ce masa ni ma zan shiga. Da farko abin dariya ya ba shi.
Bayanan da na yi masa kuma sai suka ba shi mamaki. Shi ya yi mini jagoranci
zuwa babban cafe ɗin garin, wurin da ake karɓar hayar kwamfuta mai
intanet domin a yi aiki. Ya taimaka mini sosai da yake ba ni maganin sisi. Yadda
na magance wa masu cafe ɗin waɗansu matsalolin intanet ya sa suka sake
mini kwamfuta ɗaya wadda na yi ta amfani da ita. Ni kuma na yi ta ƙara wa
ma’aikatansu ilimi.
Na
sanya wa manhajar da na samar suna Hisabin Buri. Tana da ɓangarrori
daban-daban, ciki har da shawarwari cikin odiyo da rubutu game da matakan cimma
buruka. Akwai kuma maganganun ƙarfafa guiwa game da cimma buri da shawarwarin
yadda za a kauce wa shiga ƙuncin damuwa yayin da aka gaza cimma buri. Akwai
kuma wuraren rubuta burukan da ake son cimmawa. Mataki-mataki ne tun daga kan burukan
rana-rana da mako-mako har zuwa waɗanda ake son cimmawa cikin tsawon lokaci. Waɗanda
aka cimma za a taɓa kansu inda za su koma ɓangaren da na kira Aljannar Buri.
Waɗanda aka kasa cimmawa kuwa, za a saka su a ɓangaren da na kira Ƙabarin
Buri. Yayin samar da taƙaitaccen bidiyo na bayanin yadda za a yi amfani da
manhajar, na yi amfani da labarin kaina, duk da na sakaya waɗansu abubuwan.
Na
samu sabon buri a rayuwa, wato fatan cin gasar nan. Kullum tunanina yadda zan
inganta manhajar domin ta zama mai amfanarwa. “Lallai buri wani ɓangare ne na
rayuwa!” Na raya a raina. Allah mai iko, ina daga cikin mutanen da suka yi
nasara. Aka gayyace mu Katsina domin biki na musamman.
Allah
ba ya barin wani domin wani! Ana gobe Aliyu zai raka ni Katsina wurin gasa,
Allah ya ɗauki ransa bayan gajeren ciwon ciki da ya yi cikin dare. Na yi kuka
da baƙin ciki matuƙa.
Kasancewar
na san ba za a bar ni ba idan na furta cewa zan yi tafiya, sai na saci jiki
cikin dare na fita. ‘Yan kuɗaɗen da na samu a cafe da waɗanda Aliyu ya
ba ni, ashe ba za su ishe ni ba saboda kuɗin mota ya ƙara tsada. Na roƙa aka
mini ragi. Da isata Katsina sai na tambayi hanyar ɗakin taron. Ashe yana da
nisa daga tasha. Da yake tik nake, sai na kama hanya da ƙafa.
Da
tambaya har ga shi na kawo kusa da ɗakin taron inda ‘yammata biyu suka tarbe ni
da mummunar magana. Matsawar da zan yi gaba na ji an ce: “Ƙashin haƙarƙari.”
Zuciyata ta buga. Sunan da Dakta Ahmad ke kira na da shi ke nan idan na yi wani
abin da yake ganin bai dace ba. Ya sha faɗa mini cewa, duk da ina da basira,
ina da matuƙar rauni wurin mu’amala da mutane da yanke hukunci bisa dokin
zuciya.
Ya
tilasta mini zama cikin mota kafin ya fara magana: “Saƙon da na tura miki waccan
ranar shi ne cewar ina sane da abin da ya faru da ke. Ki tuna datsen na’ura
harkata ce. Na ba wa wasu ma kariya ballantana ke? Na daɗe ina bibiyar wayarki.
Ba zan shiga ƙarƙashin wala ta jassasu ba, don kariya nake ba ki. Kashe
wayar da kika yi ya sa na daina ganin wurin da kike.”
“Wallahi
da ba don mutane da ke gefenmu ba sai na wanka miki mari ko in yi miki shegen
duka. Kin ɓata mini rai.” Dakta Ahmad ya faɗa ba tare da ya juyo ya kalle ni
ba. Da alama yana ƙoƙari ne ya ɓoye mini hawayensa. Bai sani ba ina kallon ɗigarsu
ta cikin madubin motar. Duk kunya ta lulluɓe ni. Lallai na yi wauta da ragon
azanci. Ban yi wa Ummi Adama da Baffa Umaru da duk waɗanda suka san ni adalci
ba.
Nawa
hawayen suka ci gaba da rige-rigen fita. Wataƙila don ya kwantar mini da
hankali, sai ya sako barkwanci da kuma irin labarin da nake so: “Na san kin daɗe
ba ki duba updates ba. To bari ki ji, da Baba yana raye, da za mu faɗa
masa cewa ai ko shi yanzu bai makara ba. A Singapore yanzu haka sun buƙaci
ma’aikatansu da suka kai shekaru arba’in da haihuwa da su koma su sake karatun
digiri domin koyon ilimin AI. Ƙari kan wannan, da za mu faɗa masa cewa
adadin kirifto da ake da su har sun haura hasashen Uncle Kwamfuta. A
shekarar 2020 sun fi dubi biyar. Yanzu kuwa sun fi dubu ashirin da uku. Duk da
ba za mu iya faɗa wa Baba ba, za mu faɗa wa waɗansu.”
Ya ja
numfashi tare da jaddadawa: “Albishirinki! Na samu kwantiragi na aikin shekaru
biyar a Japan. Ina tunanin a can ya kamata ki ci gaba da karatu. Wannan shawara
ta rage gare ki da kuma su.” Ya yi nuni da hannunsa na dama zuwa ga inuwar
bishiyar da ke gefenmu wadda kwata-kwata hankalina bai kai kanta ba kafin
yanzu.
Zuciyata
ta buga da ƙarfi! Ko ni kaina ban san asalin abin da nake jimami ba a yanzu; abin
da idanuna suka gani, imani da tausayawa da amanar Dakta Ahmad, ajizancina, ko Ƙabarin Burina?
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.